Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA TALATIN DA HUDU






~
BABI NA TALATIN DA HUDU
~






A hankali ta mike zaune ta jingina da kan gadon. Ta na ganin nos ta shigo ta bata rai. Nos din bata san lokacin da dariya ya kubce mata ba.

"Haba Maimunatu, wannan hada rai haka." Dariya sauran 'yan dakin su ka yi.

Anwara, Nanah da Rukayya kenan. Dan Sayf kudin (private ward) ya biya.

Fuska Maimoon ta kara tsukewa. Tsakanin zuwanta asibitin da yanzu an yanzu an yi mata allurai sun fi biyar. Allurai biyar a cikin awa arba'in da hudu ai ba wasa ba ne. Ga nos din da ke mata zafin hannu gareta.

Ashe rashin sani ne ya ke sa ta cewa gwara a yi mata allura da a bata magani. Dan yanzu da gudu za ta hadiyi ko kwayoyi nawa ne da wannan alluran da ake mata.

Haka dai rai a bace nos ta yi aikinta ta gama. Kwanciya ta koma ta yi dan zaman na takura mata.

"A zubo abinci?" Anwara ta tambaye ta.

Kai ta girgiza mata. Sam bakinta babu dandano, komai ta ci kaman ta na cin dussa. "Zan dai sha tea."

Cikin kayan da su Nanah su ka kowa da safe ta bude ta dauko kofi da cokali, sannan ta hada mata tea din. Ita ta kwana da ita. Idan ba'a sallameta yau ba kuma Rukayya zata kwana.

Tea din shima ta na sha ne kawai amma ba wai dan ta na jin dadin shi ba. Tana cikin sha wayarta ta yi kara daga cikin jakar Nanah. Ita ta sha ma wayar ta fadi ne.

Ummi ce ke kira. Maimoon na amsawa Ummi ta fara jero mata tambayoyi.

"Ummi.... Ina wuni?"

Duk wanda ya ji muryarta ya san bata da lafiya.

"Ba ki amsa ni ba? Me ya same ki? Asibitin na da kyau? Ana kula da ke? Ko dai za ki taho gida ne, ko kuma ni in taho."

"Haba Ummi," ta jiyo muryan Baffa. "Ba su Anwara sun fada miki komai ba, ki kwantar da hankalinki. Maimu ya jikin?"

"Da sauki Baffa. Ina wuni?"

"Lafiya lau. Allah Ya kara sauki. Kina dai shan maganin da aka baki ko? Nasan halinki."

Dariya Maimoon ta yi. "Ina sha Baffa."

"Toh Allah Ya kara sauki. Duk abunda kuke bukata ku kira ku sanar dani. Jiya mun yi magana da Anwara na tura mata kudin magungunan da na daki."

"Mun gode Baffa. Allah Ya saka da alkhairi, Ya kara budi."

"Ameen Maimu, Ameen. Ki kula da kan ki kin ji? Ki sha magani akan ka'ida, kuma ki dage da addu'a. Ga Umminku nan ta na son tada hankalinta."

"Maimu," Ummi ta kira.

"Ki kwantar da hankailinki Ummi. Na ji sauki ai. Zuwa anjima ma wata kila a sallame ni."

"Toh Alhamdulillah. Idan kun koma hostel din dan Allah a kiyaye. Hala baki kwana cikin net ne har sauro ya jiye ki."

Tunda ta cire net din ta wanke, bata maida shi ba. Shiru ta yi, ai ko Ummi ta dago ta.

"Allah Ya shirye ki toh. In kin koma kar ki saka. Cramps din fah? Shi sun rubuta miki wani magani ne?"

"A'a, likitan ta tambaye ni wani iri na ke sha, da na fada mata sai ba ta rubuta wani ba ta ce a siya wancan din."

"Toh. Allah Ya kara sauki. Ku kula da kan ku. Ina su Anwara? Ba su mu gaisa."

Mika musu wayan ta yi sannan ta cigaba da kurban tea din ta.

"Toh kin ji Adda Moon," Anwara ta ce bayan sun ta kashe wayan. "Ummi ta ce in ba ki sha magani ba in yi miki dure."

Murmushi ta yi. "Yauwa, ya ba ki cewa Baffa an biya kudin daki ba?"

Idanu Anwara ta zaro. "In ya tambaya wa ya biya in ce mai wa?"

"Wa kuwa? Ba kun dauko ATM dina ba?"

"Wa ya fada miki haka?"

"Haka Nanah ta ce da na tambaye ta da safe." Kallon Nanahn ta yi taga ta na cira idanu. "Ko ba haka kika ce ba Nanah?"

Nanah ta daga kai. Sai kuma da sauri ta ce. "Ya Wara ke ki fada mata."

"A fada mun me? Me ke faruwa?"

Dan karamin huci Anwara ta yi. "Kin san Sayfullah ya zo jiya ko?"

"Na sani. Amma me ya hada zuwan Say.....ba dai shi ya biya kudin ba?"

"(He insisted!)" Anwara ta ce tana yin baya daga jikin gadon dan Maimoon ta taso kaman zata kai mata duka. "Wallahi Adda Moon, dagewa ya yi. Ni ban ma ga bill din ba, doctor din shi ta ba, kawai ya dawo da ledan drugs dinne. Ban ma san harda kudin daki ya biya ba sai da na je biya jiya."

"Kar ki manta cash din da ya ajiye kafin ya tafi." Rukayya ta ce daga gefe ta na murmushi.

"Harda kudi kuma?" Ido Maimoon ta runtse. "Tsakani da Allah abunda kuka yi ya dace? Daga zuwan mutum ya fara kashe kudi kuma ku tsaya kuna kallo. Kun san shi ne?"

"Mun san—kin san shi ai, kaman mun san shi kenan." Anwara ta bata amsa.

"Ni na ce muku na san shi?"

"Adda Moon kin yi saving number din shi fah. Kuma irin mutanen nan ne da kwarjinin su ba zai bari ka yi musu gardama." Inji Nanah.

"I'm sure da zai iya shi zai yi jiyanki ma," Rukayya ta ce, dariya ta yi saboda fuskar Maimoon kaman za ta yi kuka. "Maimoon kar ki ce mun shi ne ki ke kin daukar wayar shi?"

Maimoon ta bude baki zata ce mata a'a sai ta tuna shima Sayfullah din ai ta daina daukar wayar shi. Hasbunallah! Sai ya ce bata da kunya ai. Bata dauka in ya kira amma ta iya karban abun hannunshi. Wallahi su Anwara ba su kyauta mata ba. Yanzu mai zai yi tunani?

"....ranan ina kallo ya na kira amma ta ki dauka." Rukayya ke ba su labari. "Wallahi Moon irin wa'annan ba'a ja musu aji. Wai kin gan shi kuwa? Ko dai ba ku taba haduwa ba? Ni in ba kya so, ki ban number din shi."

Dariya suka fashe da shi. Anwara ta ce, "ki yi a hankali Rukayya. Kin ga irin kallon da ta yi miki."

"Kwantar da hankalinki sister, wasa na ke yi. Sayfullah na ki ne ke kadai."

"(They will make a cute couple!)" Nanah ta ce harda dan tsalle ta tafi.

Kai Maimoon ta rike, kwanciya ta yi ta juya musu baya. Tun tana ji suna tsokanarta har barci ya dauketa.

Da misalin karfe biyar aka sallami Maimoon daga asibiti bayan ta gama shanye ledojin karin ruwan da likita ya rubuta mata. An kuma hada ta da tulin magunguna. Sun yi sallama da 'yan asibitin inda Nos dinnan ke tsokanar Maimoon ta na ce mata kada ta sake dawo musu asibiti idan ba haka allura zata dunga mata kullun.

Kasancewa ranan litinin ne har yanzu makaranta cike ta ke da dalibai da ke hidindimun su. A kofar hostel din su Napep din da su ka yi shata ya tsaya.

A hankali Maimoon ta take takawa, daya daga cikin security din da ke kofar hostel ta yi mata sannu da yake ta ga lokacin da aka fita da ita.

Sai huci ta ke yi kaman wacce ta yi gudun fanfalaki, har yanzu karfin jikinta bai dawo ba.

Lafiyar gado ta bi ta kwanta, 'yan uwanta kuma su ka kimtsa kayan da suka dawo da su. Rukkaya bata nan, ta tafi aji.

"Sannu Adda Moon," Nanah ta ce. "Ba ki bukatan wani abu?"

Kai Maimoon ta girgiza ta na yi mata murmushi. Ta san ko Mimi da Sadiya iyakar kulluwan da za su bata kenan. "Nagode Nanah."

"Ba sai kin yi mun godiya ba. Idan Sadiya ce za ki ce mata kin gode?" Kai Maimoon ta girgiza. "Toh kuma."

'Yan cikin hostel da su ka san ta duk sun shigo sun dubata. Hakan ya yi mata dadi. Ta yi waya da Sadiya da Mimi, inda Mimi ta hada musu conference call. Sun kai awa daya sun hira duk dai ba sosai ta ke magana wannan aiki na Hajiya Sadiya ne. Maimoon ta yi kewar kannen nata sosai.

Adda Salma ma ta kirata. Ko bata tambaya ba ta san wa ya fada mata. Wani ikon Allah ba su taba maganar Sayfullah da Adda Salman ba. Maimoon ta zata za ta yi mata maganan shi amma shiru. Ita kuma ta na jin kunyar dago zancen.

Kaman kuwa Adda Salma ta shiga zuciyarta ta ce, "Yanzu mutumin ki ya bar nan?"

Kaman wata mara gaskiya ta ji bugun zuciyarta ya karu. "Wa ye kuma mutumi na?"

"Hmm, Moon kenan," Adda ta yi dariya. "Kallon ki kawai na ke yi ai. Ina sha kin bar zurfin cika amma ina...yanzu a ce akwai wani abu tsakanin ki da Baba Sayf amma ki kasa fada mun?"

"Ayyah Adda ni ban san me zan ce miki ba."

"Kaniyanki. Sayf dai ya ce baya son in shiga maganan amma gaskiya naga bazan iya shiru ba. Mai ke faruwa Maimoon? Fada mun komai."

"Like I said Adda ni ban san me zan fada miki ba...." Duk da haka ta fada mata komai da ya faru daga farkon haduwar su zuwa yanzu. "Duk da bai fito fili ya fada mai ya kawo shi ba—"

Da sauri Adda ta katse ta. "—bai fito fili ba ko ba ki bashi dama ba? Wanne a ciki?"

Dariya Maimoon ta yi. "Toh. Za'a iya cewa ban bashi dama ba."

"Babu wani za'a iya cewa, haka ne. Me yasa ba ki ba shi daman ba?"

Ajiyar zuciya Maimoon ta yi. "Kin fi kowa sani Adda."

"Ban sani ba Maimoon, sai kin fada mun."

Ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta furta a hankali. "Ina tsoro Adda. Saboda ina tsoro."

"Maimoon..."

"Abunda ya faru da Fa'iz da kuma Hamma ya sa mun tsoro da fargaba. Ina tsoron ba wani namiji dama saboda ban san mai zai biyo baya ba. If anything should happen, bazan iya dauka ba Adda. Bazan iya ba. So shiyasa ma, maganin bari kar a fara."

"Maimoon ya kamata ki gane Sayfullah daban da sauran. Shi ba kaman su ya ke ba."

"Duk haka su ke cewa. Shi wancan abu ya taho kaman dagaske daga sama na ji an daura mai aure da 'yar uwata. Shi kuma dayan ko sama da kasa za su hade iyayenshi ba za su ta ba yarda ba. Shi kuma wannan ban san da mai ya zo ba."

"Bai zo miki da komai ba sai alkhairi. Maimoon. Ko waye hakan ya fara da shi dole zai ji tsoro, amma ki sani ba duka aka taru aka zama daya ba. Dole ki yarda cewa akwai sauran mutanen kirki a doran kasa, ban ce sauran na banza ne ba, amma ba kowa bane zai yi (hurting) din ki ba. I can vouch for Sayf. Tunda na san shi ban tana gani ya kula wata ba sai a kan ki, wannan kadai ya sa na yarda dagaske ya ke. Na san kina tsoro amma kika bari tsoron nan ya yi (controlling) rayuwar ki, akwai matsala."

"Kin san me ye Adda? Da kin ba shi shawara kawai ya hakura ya nemi wata. Dan harga Allah ban san mai ya gani a tare da ni ba."

"Kar ki ce haka Maimoon."

"Dagaske na ke Adda. Kawai bata lokacin zai yi. Ban shirya ba, I am not ready. Ba ni da abunda zan ba shi. An ce you can't pour from an empty cup. Ban san ya zan yi miki bayani ba but I feel so empty Adda. So empty."

"Oh Allah! Maimoon. Ban zata maganan nan zai dauki wannan direction din ba, da ban dago ta ba. Ki Yi hakuri na bata miki rai. Oh ni Salma, gashi duka dazu kika dawo daga asibiti."

Duk da hawayen da su tarun mata a ido sai da ta yi dariya jin yanda Adda Salman ta rude.

Hannu ta sa ta share hawayenta. Bata taba fada ma kowa ba, amma yanzu da ta fada ma Adda ta ji kaman an cire mata wani nauyi da ya danne mata zuciya. Yanzu ta na ji zata iya lumfashi da kyau.

"Yanzu abunda ke kunshe a ranki kenan tuntuni ba ki yi magana ba har sai ya illata ki. Ya kamata ki ko yi expressing kan ki, in kina (bottling up emotions) din ki haka wata rana zuciyar ki zata buga.

Ina son ki sani duk abunda ya faru da ke ya faru ne saboda haka Allah Ya so. Allah bai rubuta Fa'iz da Ashmaan cikin kaddaran rayuwar ki ba shi yasa hakan ya faru. Amma ba dan wai kina da wani aibu ko kuma matsala ba. Wannan shaidan ne kawai ya ke rudan ki. Ki kara dagewa da addu'a, na san kina yi amma ki kara akan wanda kike yi. Kada ki bari shaidan ya ci galaba akan ki. You are lovable Maimoon. Ki san wannan. Sayfullah shi ya san abun da ya gani tattare da ke ya ce yana so. Ki yarda kema kin chanchanci a so ki kaman ko wace 'ya mace."

Kalaman Adda sun sosa mata zuciya. A hankali hawayen ta dade tana dannewa su ka rika kwarara daga idanuwanta.

"In magana irin haka na baki wahala, akwai wani abu da ake ce ma (journaling), inda za ki rika rubuta abubuwan da su ke miki nauyim furtawa. Ki gwada ki gani."

"In sha Allah Adda. Nagode sosai."

"Babu komai Moon. Ba sai kin gode mun ba, abunda ko wace yaya za ta yi ma kanwanta kenan. Ki kwanta ki huta Allah Ya kara sauki."

"Ameen Ya Rabbi."

"One last thing Maimoon. Sayfullah is a good man. Sai anjima." Da wanna Adda ta kashe wayan.

Littafi ta dauko daga cikin jaka dan ta gwada yin abunda Addan ta ce. A hankali hannunta ya fara motsi akan takardan, kan ta ce mai ta cika shafi wajan hudu. Bayan ta gama ta saki ajiyar zuciya(sigh of relief), kaman an sake rage mata nauyi haka ta ji.

Karkashin pillow ta tura littafin. Sallaman Nanah ya ta maida hankalinta kan kofa. Ba ta lura sanda su ka bar dakin ba ma.

An yi sallama amma shiru ba'a shigo ba. Mikewa ta yi ta nufi kofan, tana bude wa taga tullin kaya jere.

"Adda ba dai mun tada ki ba."

"A'a, idona biyu. Wannan kayan daga ina?"

Murmushi Nanah ta yi. "Bari mu gama shigo da su za ki ji bayani."

A kasa ta samu wuri ta zauna tana kallon ikon Allah. Kaya ne kaman ana shirin bude shagon provision. Ruwa katon sun fu biyar, ga ledoji da kuma kwalaye.

Bin Anwara da Nanah kawai ta ke yi da ido suna shigo da kayan. Bayan sun shigo da ledojin karshe suma su ka samu wuri suka zauna a kasa.

"Adda sai kin biya dakon da na yi gaskiya," Nanah ta ce tana mike kafa.

Kallonta kawai Maimoon ta yi, irin mai kike nufi.

"Toh Ya Wara yi mata bayani."

"A'a nima ba sai na ce komai ba, gashi," ta mika mata envelope. "Wannan zai miki bayanin komai."

Assalamu alaikum,

Maimoon ya jiki? Allah Ya kara sauki Ya sa kaffara ne.

Sallaman ne kawai ban goge ba. Da za ki ga office dina, cike ya ke da takardun da na yi squeezing.

Da farko dai ina son in ba ki hakuri. Na zauna na yi tunani, na yi realizing abunda na yi akwai takura da damu. For that I'm sorry, and for making you uncomfortable too.

In kin yarda zan kira ki anjima mu yi magana. If it's okay with you, sai ki yi mun dropping message.

Ga kayan dubiya nan. Na so in dawo yau in duba ki amma ban samu dama ba.

Ki kula da kan ki sosai dan Allah. Allah Ya kara sauki

-Sayfullah Abdur-Rahman Hambali.

Karatun farko dai bata fahimci komai ba. Saida ta natsu ta kara karantawa. Kumantun ta ji suna wani dumi-dumi.

Anwara ce ta dawo kusa da ita. "Yaya dai?"

Mika mata takardan ta yi. Da sauri Nanah ta dawo kusa da Anwara dan itama ta karanta.

"Aww! So cute!" Nanah ta ce.

Anwara ta lura da yanayinta, kafadar Maimoon ta dafa. "Are you okay?"

"Ina son in mai godiya. Amma ban shirya maganan da ya ke so mu yi ba. Me ya kamata in yi?"

"Ki mai dropping message din kaman yanda ya bukata, sai ki san yanda za ki fada mai. Inaga hakan zai fi dan bai kamata ki yi ignoring din shi ba."

Kai Maimoon ta daga alamun ta gamsu da shawarar yar uwarta. Sai da ta bari an yi sallan magrib sannan ta tura mai sakon da ke kunshe da sallama kawai.

Ba'a dade ba sai ga kiran Sayfullah ya shigo. Kallon wayan ta ke yi kaman wani abu daga ciki ai fito ya cinye ta. Ganin ta kusan tsinkewa ya sa ta yi sauri ta daga.

Kaman yanda su ka yi dazu da tana waya da Adda, Nanah da Anwara su ka fita dan Maimoon din ta ji dadin yin wayan.

"Salamu alaikum Maimoon."

Dukda iskan fankan da ke dakin zufa Maimoon ke yi. "Wa'alaikumus salam. Ina wuni?"

"Lafiya lau Maimoon, ya jiki?"

"Da sauki Alhamdulillah. Uhm, dama...nagode Allah Ya saka da alkhairi, Ya kara budi."

"Ameen, Ameen."

Daganan shiru ya ratsa tsakanin su. Maimoon kiris ta ke jira ta arce.

"Maimoon," Sayfullah ya kira a hankali.

Hakan ya sa bugun zuciyanta ya tsananta.

"Na'am."

"Na takura ki ko?" Shiru ta yi tana cizo lebanta na kasa. "Mu bar maganan sai kin warke ko?"

Da sauri ta ce eh. Sautin dariyan shi ya bugi kunnenta. Runtse ido ta yi, itama sai ta yi dariyan.

"Toh shikenan. Allah Ya kara sauki. Ki kula da kan ki kin ji?"

"Ameen. In sha Allah. Nagode."

"Uhh toh Malama Maimoon, an yarda in dunga kira za'a dauka ko shima a bari sai kin warke?"

Kunya ta ji ya lullubeta harda rufe fuska.

"Uhm? Kin yarda ko kuwa?"

Kalaman Adda Salma ta tuna. Ki yarda kema kin chanchanci a so ki kaman ko wace 'ya mace. Maimoon ta tsinci kanta da furta "eh" a sanyaye.

"Toh godiya na ke. Allah Ya saka da alkhairi. Sai da safe."

"Allah Ya tashe mu lafiya."

"Ameen," ya amsa.

Jim shiru bai kashe wayan ba, ya sa ta kashe. Sai bayan ta gama wayan ta lura tunda ta fara hakoranta a waje suke.













Ahh ahh! Abun fa babu sauki Jama'a!🙊💕

Ayi mun afuwa ban yi editing ba🙏🏽 zuwa gode in sha Allah. Ina ta sauri in yi muku update ne.

Please please comment🥹 silent reader na beg i dey beg, dan Allah let me know what you think. In baku sani ba, comments ne ke bani giner so please 🙏🏽💕💕

~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro