BABI NA TALATIN DA BIYU
Kun ji ni shiru ko? Ayi hakuri, ABU ta shako mun wuya ko lumfashin arziki bana iya yi😩
~
BABI NA TALATIN DA BIYU
~
Ashe haka kwanciyan hankali ya ke da dadi? Baffa bai taba samun natsuwa da kwanciyan hankali irin haka ba. Fatar shi ta murmure, har wata 'yar kiba ya yi.
Kaman yanda Jaddati ta bukata, satin su uku a Kaduna su ka tattaro su ka dawo Abuja. Nasir da Abdullahi ba su bari sun dauko komai daga chan ba. Daga su sai kayan jikin su suka taho. Sun samu komai a gidan daga kayan amfani har zuwa kayan sawa.
Sadiya an chanza mata makaranta an sata makarantar da sauran yaran Baba Abdullahi ke zuwa.
Baffa na ganin likita duk da Abdullahi ya dage sai dai a fitar da shi kasar waje dan a duba lafiyar shi sosai.
Shi da Abdullahi da Nasir kuwa sai son barka. Baffa ya saki jikin shi sosai cikin 'yan uwan shi.
Baffa ya samu mai dakin shi akan yana son sanar da Inna da su Bello halin da ya tsinci kan shi a ciki.
Ummi ta nuna mai lokaci da za su sani bai yi ba. "Ka dan jinkirta, ka bari ka gama sabawa da 'yan uwanka tukun. Lokacin da ya kamata su sani na nan zuwa, amma ba yanzu ba."
Baffa ya gamsu da shawararta, dan ya san a duniya babu mai kaunar shi kaman Rabi'atu. Ta yi mai abubuwan da wani dan Adam bai taba mai ba, kuma ba ya jin wani zai iya yi mai rabin abunda ta mai a rayuwa. Shi yasa kullum ya ke cikin sa mata albarka da rokon Allah Ya bashi dama kyautata mata fiye da yanda ta ke kyautata mai.
A duk sanda Baffa ke tare da Mama(Jaddati) ya kan ji kaman babu wanda ya kai shi gata duniya. Dama haka uwa ke da dadi? Duk da sun rasa shekaru da dama da baza su taba dawowa ba, zasu yi amfani da wannan damar da Allah Ya basu wurin gina alaka mai karfin gaske tsakanin 'da da mahaifiyarshi.
Sabuwar rayuwar su na tafiya lafiya lau, cike da kwanciyan hankali da son juna. Baffa ba zai taba daina wa Ubangiji godiya ba akan irin rahamar da ya mai.
Sai maganar aiki. Kannen shi sun dage akan ya zauna ya huta, ba sai ya yi aikin komai ba. Shi dai yana sauraron su ne kawai. Bai taba zama hakanan ba, kuma ba zai fara yanzu ba.
Baffa na zaune a falo ya na kallon labarai Nasir ya yi sallama. Da murmushi shimfide a fuskar shi Baffa ya mike ya tarbe shi.
"Ina wuni Yaya?" Nasir ya gaishe shi.
"Lafiya lau Alhamdulillah. Ya aiki?"
Nan suka gaisa, Sadiya ta kawo mai ruwa sannan ta juya. Baba Nasir ya gyara zama. "Dama Yaya taimako na zo nema..." nan ya fada mai wata matsala da aka samu a ma'aikata ko zai ta ya shi warwarewa.
Nan ta ke Baffa ya kawo shawarar da kwakwata ba ta zo ma Baba Nasir rai ba. Abun ya ba shi mamaki matuka. Wata kila ko dan shi ya yi aiki cikin kananan ma'aikata sosai shi ya sa ya san yanda za'a shawo kan matsalar.
Godiya sosai ya mai. Washegari ya yi amfani da shawarar Baffan cikin ikon Allah aka warware matsalan a take. Baba Nasir ya samu Baba Abdullahi ya na fada mai abunda ya faru.
Baba Abdullahi ya ji dadin abun matuka. Tun daga lokacin basu sake yanke hukunci ba sai sun samu Baffa. Daga karshe su ka ce suna son ya zaman musu (special adviser) saboda yana da (human relation) sosai, ya fi su fahimta abubuwa dan gane da kananan ma'aikata.
Amma sam Baffa ya ki ya, ya ce shi ina ya ke da ilimin da zai yi aiki da su haka. Magana dai sai da ta je gaban Jaddati. Dole Baffa ya hakura dan ba zai iya gardama da umarninta ba. Hakan ya yi wa su Baba Nasir dadi, dan dama neman aikin mara wuya da zasu ba shi suke. Ya wahala sosai, lokaci ya yi da zai huta shima.
Zama wuri daya ya sa jikin Ummi ya mulmule, fatar ta yi kyau, haskenta ya sake fitowa. Kaman yanda Baffa ya ke tare da 'yan uwanshi haka Ummi ta ke da Ammi da Maman Anwara. Cikin lokaci kadan sun saba sosai. Ummi ta kan zauna ta yi kuka, ita da 'yan uwanta su ka gujeta sai gashi Allah Ya kawo mata wa'inda su ka fisu.
Rayuwa su ke yi cikin lumana da kwanciyan hankali.
****
Sayfullah Abdur-Rahman Hambali na zaune kan kujera ya na jujjuyawa, ya yi zuefi cikin tunani bai san sanda aka shigo ofishin ba sai dai jin karan saukar takardu kan teburi ya yi. Kyafta ido ya yi, hankalin shi ya dawo jikin shi.
"Yi hakuri Oga Sayf, ina ta sallama ba ka ji ba." Masinjan da ya kawo takardun ya ce.
Hannu Sayf kawai ya daga mai. "Kar ka damu, takardun na meye...."
Sayf bai ji rabi da kwatan bayanin da aka mai ba, kawai ya amsa da to ne. Ture takardun gefe ya yi, ya ji kawai zaman office din bai mai ba. Dukda lokacin tashin shi bai yi ba, haka ya nemi izini ya tafi.
Ya na isa gida ya samu Mami na shirin fita.
"Yauwa Sayf, Allah Ya kawo mun kai. Zo ka kai ni unguwa dan Allah, dama bana son yin tuki."
Murmushi ya yi, ya ce ta bari ya sa wani abu a cikin shi sai su tafi. Dukda bai da (appetite) din abincin haka ya tura. Mami bata fada mai inda zata je ba, kawai ta ya yi mai kwatance ne.
Mami na ta mai hira amma hankalin shi baya wurin. Sai da ta dan taba shi sannan hankalin shi ya dawo kanta.
"Na'am Mami?"
"Lafiya kuwa Sayf? Tunanin mai ka ke yi haka? Akwai wani matsala ne?" Mami ta jefo mai tambayoyi.
Murmushi ya kakalo. "Babu komai Mami, gajiya ce kawai."
Mami kawai ta ji shi ne ba dan ta yarda ba. Ta dade ta na lura da shi kwanakin nan, kullum ya na cikin tunani mai zurfi. Ta yi zaton ko sun samu matsala ne da daya daga cikin iyayenshi amma ta bincika ta ga ba haka ba ne. Toh mai ke damun danta haka?
Lumfashin ta sauke. Allah Ya sa wannan ziyaran da za su yi ba zai kara mai matsalan da ke damun shi ba.
"Shiga kwanan nan," ta ce mai. Ta ga lokacin da ya fahimci gidan da za su. Bai ce mata komai ba ya cigaba da tuki, sai ta dena mai kwatance ma.
Gaba daya ya ji jikin shi kaman an daure shi da igiyoyi. Mami ta mai ba zata. Ya na jin idanun Mami a kan shi amma bai waiga ya kalleta ba.
Zuwan shi gidan daya tun farkon dawowar su garin. Shi har ga Allah har mantawa ya ke yi ta dawo kasar ma.
Bayan ya yi parking, ya fito ya zagaya ya bude ma Mami kofa. Ta bude baki za ta yi magana ya kauda kai. Haka ta hakura ta yi gaba ya na biye da ita.
Babu kowa a farfajiyar gidan, wurin ya yi shiru. Daya daga cikin gidajen da ya kasance na Ammi su ka shiga. Mami ce mai jagora Sayf na biye da ita a baya.
Tun kafin su shiga cika ya ke jiyo hayaniya sama-sama. Yanayin da ya ga mutanen gidan ya sa ya ji wani zafi ya soke shi a zuciyarshi.
Ammi zaune da mijinta akan kujera kowannen su da yarinya a kan cinya sai yaran su da ke zaune kasa sun zagaye su.
A perfect and complete family.
Ammi ce ta fara mikewa ta mika ma daya daga cikin yaran yarinyar da ke hannunta. "Marhaba Mami, sannun da zuwa...." Chak ta tsaya ganin Sayf a baya. "Sayfullah," murmushin fuskarta ya fadada.
Daurewa kawai Sayf ya yi ya karasa cikim falon. Hannu Sameer ya mika mai su ka gaisa sannan ya gaisa da mijinta. Bayan an gaisa Alhaji Nasir ya fita.
Tunda su ka gaisa ya samu wuri ya zauna bai sake cewa komai ba. Ko ruwa da snacks din da Waahidah ta aje a gaban shi bai taba ba. Gaba daya a takure ya ke.
"Ammi Jaan ke fada mun company na ta bunkasa," Sameer ya ce ya na son jan dan uwanshi da hira. "Allah Ya taimaka."
Murmushin da ya fi kama da yake ya yi. "Ameen Ameen. Nagode."
"Ya Sayf kai ka dai ne ba ka zo matriculation dina ba." Waahidah ta ce ta na dan turo bakinta.
Sayf ya ji ba dadi. Musamman ta turo mai text amma ya share. Ya san in ya je he will be out of place ne a cikin su, shi yasa.
"I'm sorry, aiki ya mun yawa lokacin. Ki tuna mun in turo maki da congratulatory gift in sha Allah."
"Toh! Nagode."
Yanda ta yi maganan ya sa Sayf murmushi. Murmushinsa na farko tunda ya shigo. Ya na daga kai suka hada ido da Ammi tana kallon su tana murmushi. Da sauri ya kauda kai.
Duk signal din da ya ke ma Mami akan su tashi su tafi ta yi burus kaman bata gani ba ma. Daga karshe ma tashi ta yi suka hau sama da Ammi.
Daga karshe dai anan su ka yi sallar maghriba. Tare da Sameer su ka je masallaci, bayan an idar su ka tsaya gaisawa da iyayen shi maza.
Su uku ne zaune a kan kujera suna maganan su. A iya sanin shi Baban su Sameer kani daya gare shi, shi kuma dayan mai kama da su ko waye? Kai ya girgiza da sauri dan wannan ba hurumin shi ba ne.
Bayan an gaisa, Baban Sameer ke cewa. "Yaya wannan 'da na ne Sayfullah."
Sa ke gaishe shi ya yi, mutumin na da faram-faram ya sake mikowa Sayf hannu su ka yi musabaha. Daga sama Sayf ya ji Baban Sameer na fada musu ai ya bude kamfanin sarrafa shinkafa. Daga nan zancen ya koma kan noma, inda mutumin da aka gabatar a matsayin Yaya ya ke ta mai 'yan tambayoyi. Tambayoyin ne ma ya sa Sayf dan sakin jikin shi.
Ba su suka bar gidan ba sai bayan sallar isha'i. Ammi ta kafe dole su ka tsaye a ka ci abincin dare da su. Gaba daya ji ya ke kaman a kan kaya ya ke. Kwakwata zaman wurin bai mai ba saboda ya na fama mai ciwon da ya dade da zaton ya warke.
Ya na sa shi wasu tunanin da ba su kamata ba kwatakwata, da iyayenshi ba su rabu ba da mai zai faru?
Har sun kai mota Ammi ta ce, "Ya salam! Na manta, Mami baku gaisa da su Ummin ba."
"Oh Allah. Muje to a gaisa a gurguje kafin a sake dawowa," kai ta daga ta kalla Sayf. "Mu je ko?" Tasan ba zai yi gardama ba shi ya sa ta yi gaba abunta.
Sun shiga sashen an gaisa a gurguje. Nan Sayf ke jin labarin abunda ya faru da su. Ya yi mamaki matuka. Tabbas in da rai da rabo, bayan shekara sama da hamsin Allah Ya kara hada su. Tabbas babu abunda ya fi karfin Allah SWT.
***
Wayar shi ya kura wa ido. In ya kira zata dauka? Fitowar shi kenan daga wanka bayan sun dawo. Maganan da Mami ta fada mai ya ratsa shi sosai.
"Sayfullah. Kai abunda ka ke yi kana ganin ya dace? A ce mahaifiyarka da 'yan uwanka suna shakkar yi maka magana saboda su na tsoron ka ki kula su. Kaman yanda na sha fada ma, you need to let go. Ka daure ka yi hakuri, ka bude zuciyarka. Ta hakan ne kawai zaka samu sauki a ran ka. Kar ka manta zumunci na daya daga cikin abubuwan da su ka fi komai muhimmanci a rayuwar musulmi. Shin ya da ce ka yanke zumunci saboda fushi da ka ke yi? Ka na ganin Allah ba zai kama ka da laifi ba? Amminka ta yi kuskure, amma ko Allah muna mai laifi Ya yafe mana. Find it in your heart to forgive her and let her in. Ta na kokari, she's taking the steps amma kana karya mata gwiwa. Open your heart Sayfullah before it's too late."
Kan sunanta ya danna, har ta gama ringing ba'a dauka ba. Dama ya san baza ta dauka ba. Hannu ya sa ya na (massaging) kan shi da ke mai ciwo.
Bai san da wanne zai ji ba, da kin kula shi da Maimoon ke yi ko kuma da mahaifiyar shi da ke son maida mai hannun agogo baya?
Bai san mai ya samu Maimoon din shi ba. Lokaci daya ta daina daukan wayar shi, in ya tura text bata maido mai da amsa.
Tun ranan da ya kirata ya mata jajen jikin Baffa su ka dan fara shiri. In an kwana biyu ya na kira su yi hira duk da ba mai tsawo ba.
Amma lokaci daya abu ya chanza kaman an yi ruwa an dauke. Ya yi tunanin, ya yi tunanin har ya gaji ko zai iya gano laifin da ya mata. Shi a iya sanin shi ko gabatar da niyar shi akanta bai yi ba. Da ya bari sai an dan saba, toh ga abunda ya faru tun ba'aje ko ina ba.
Habeeb ya so sa matar shi tambayanta me ake shi Sayf ya hana shi. Ba ya bukatar taimakon kowa a wannan issue din. Shi da kan shi zai shawo kan matsalar ba ya son outside forces su yi influencing decision dinta.
Maimoon za ta amince da shi da kan ta, zai tabbatar hakan ya faru.
Bai fara dan ya karaya da wuri ba. Abubuwa masu muhimmanci da daraja a rayuwa ba ta hanyan sauki a ke samun su ba. Dan haka a shirye ya ke.
•
•
•
•
•
•
Ko me yasa Moon ke ma Sayf yanga? Oho, ni ma ban sani ba🤣🤣
Honest feedback dan Allah. Dan ni kai na ban san abunda na rubuta ba dan kaman writers block na neman kama ni. What do you think? Is it making sense ko kuwa😩
Ban san yaushe zan yi wani update ba gaskiya dan an koma makaranta. In na samu time za ku ganni, in kun ji shiru kuma to a taimaka a yi hakuri🙈
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro