Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA TALATIN DA BIYAR





~
BABI NA TALATIN DA BIYAR
~



Maimoon ta warware, sauki ya samu sai dai ramewa da ta yi, hakan ya sa idawunta suka kara fitowa. Kwana goma bayan ta dawo daga asibiti su ka fara jarabawa. Har da fargaban jarabawar ya sa ta rame sosai.

Karutu su ke yi babu kama hannun yaro, daga ita har su Nanah babu mai lokacin kan shi. Sai da dare su ke haduwa tunda da rana kowa ya tafi karatu.

Da ya ke Anwara aji uku ta ke da riga Maimoon da Nanah da ke aji daya gamawa. Amma zata zauna har sai sun gama su tafi tare. Tsokanan su ta rika yi in suna karatu. Tun a nan Anwara ta fara huce gajiyarta.

Jarabawar ta dauki sati biyu inda za su rubuta (GENS) karshe. Maimoon bata samu natsuwa ba har saida ta fito daga dakin jarabawa. Alhamdulillah! Ta yi ta maimaitawa dan tamkar an zare nauyin da ya rataya a wuyanta ta ke ji.

Ta san ta yi kokari, ta dage sosai saura kuma ta bi su da addu'a. Tana son ta fito da sakamako mai kyau, dan kanta dan kuma ta farantawa iyayenta rai. Saboda wani lokaci a baya wannan duk mafarki ne a wurinta, bata taba zaton zai zama gaskiya ba. Ta gode ma Allah da Ya bata wannan daman, akwai wasu da yawa da za su bada komai na su dan su samu dama irin haka.

Ana gobe za'a zo daukan su Nanah ta dage sai sun fita yawo. "Mu dan warware mana kafin mu koma."

Taron dangi su ka mata shi yasa har ta yarda. Dan da ita da an siyo komai sai a  dawo daki a ci hankali kwance. Wurin da Nanah ke son a je na m wajan makaranta babu nisa saboda haka a kafa su ka taka. Sai dai da su ka isa wurin cike ya ke makil da 'yan makaranta ana ta sharholiya session ya kare.

"Sai da na ce muku ai," Maimoon ta ce tana musu dariya kasan niqabinta.

Wurin babu masaka tsinke. Nanah aka tura ta yi siyayyan sai su koma daki. Kafin ta tafi ta kumburo baki. "Adda Moon kin yi winning. Hala ma tunda muka taho kike addu'a."

Mintin su goma tsaye ta dawo suka rankaya su ka koma cikin makaranta. Jilbab da niqab dinta ta cire ta linke ta aje shi kan gado. Har ta hada akwatinta, su kadai ta bari waje wanda za ta sa gobe. Duk sun gama shiri, dakin ya koma kaman ba shi ba sun kwashe komai na su. Lockers din da su ke cike makil da kaya yanzu wayam su ke.

"Zan yi missing dakin nan," inji Anwara. "(We made lots of memories here.) Sanadin dakin nan ne mu ka gano 'yan uwan mu." Ta na magana ta  na murmushi.

Hakan ya dago hira, Anwara ke sake ba su labarin yanda ta firgita da ta ga Baffa. Da yanda da rika kokarin samo karin bayani daga wurin Maimoon din amma ta ki bada hadin kai.

Dariya Maimoon ta yi. Abun na bata mamaki in ta tuna ba'a cika shekara da su ka san juna ba amma ta na ji kaman ta san su duk tsawon rayuwarta.

Abubuwa da yawa sun faru da ita—da su—wannan shekaran. Rayuwar da su ka sani ta ruguje lokaci daya. Komai ya ruguje musu, al'amura su ka chabe. A daidai lokacin da su ka karaya, Allah Ya sauya musu yanayin gaba daya.

Lalle ne tare da tsananin nan akwai wani sauki.

Baffanta ya samu so, kulawa da kaunan da ya chanchanta daga wurin mahaifiyarshi da 'yan uwanshi. Iyayenta sun samu hutun da suka dade suna bege. Kannenta na lafiya, suna makaranta. Duk wata bukata da zata taso zasu iya magance ta da yardan Allah. Yanzu tana iya kwanciya ta yi barci ba tare da fargaban mai zasu riska in sun waye gari ba.

Ta rasa abu da yawa amma Allah Ya maye mata gurbin su da abu mafi alkhairi.

Maimoon, Anwara da Nanah kwana hira su ka yi.

Karfe takwas wanda zai dauke su ya iso. Tunda asuba Anwara ta sa aka ida kimtsa komai. Nanah na son komawa barci tunda basu kwanta da wuri jiya ba amma sam yayarta ta hana ta.

"Wai Ya Wara saurin me kike yi ne! Sai wani zumudi kike yi."

Da suka fito da kayan su ka ga wanda ya zo daukan su, Nanah ta juya ta kalla Anwara ta na shu'umin murmushi. "Shi yasa kika kasa tsaye kika kasa zaune. Ki ce Babe ne zai zo."

Duka ta kai mata duk da ta kasa danne murmushinta.

Ahmad saurayin Anwara ne ya zo daukan su. Wannan ne karo na farko da Maimoon ta gan shi duk da Anwara ta taba hada su da Ahmad din a waya sun gaisa. Yaron Anty Maryam ne, autar Jaddati. "Addan mu ina wuni."

Murmushi ta yi, maimakon ta amsa sai ta gaida shi itama. Ta na jin wani iri idan mutumin da ya girme ta ya gaisheta. Kuma ba sai an fada ba ta san Ahmad ya girmeta.

Ita da Nanah su ka shiga baya, Hajiya Anwara ta kame a gaba ana ta shan soyayya. An sa musu rana karshen shekara, nan da wata uku. Nanah tai ta tsokanan su har ta gaji dan kanta ta barsu.

Rashin barci da wuri da kuma tashin safe da su ka yi ya sa idanuwanta su ka yi nauyi. Gyara zamanta ta yi, daga nan sai barci.

Bata farka ba saida su ka kusan shiga garin Abuja. Ba su samu hold up ba tunda suka baro Zaria sai da suka zo gab da gida. Wurin awan su daya a wurin sakamakon hadari da a ka yi.

Nanah ta yi tsaki tana tura kai gaba duk da bata iya hango komai daganan. "Anya Ya Ahmad ba zan sauka in karasa a kafa ba."

Anwara ta juyo ta harareta. "Sai ki sauka ai, Allah Ya baki sa'a."

Zumboro baki Nanah ta yi ta koma ta zauna. Maimoon ta yi mata dariya amma itama da da hali da ta sauka ta karasa. Ta yi kewar su Baffa sosai. Bata taba kai tsawon haka bata gan su ba.

A hankali hanya ya bude su ka karasa.

Gidan Jaddati su ka isa gaba dayan su inda su ka same ta zaune a falo tare da Sadiya da Waahidah. Da gudu Sadiya da Waahida su ka taso su ka rungume 'yan uwansu, kowa na murna an dade ba'a hadu ba.

"Sannun ku da zuwa 'yan makaranta. Ya hanya?" Jaddati ta ce da murmushi a fuskarta.

Gaisheta su ka yi, Nanah na tsokananta ya ta ji da bata nan. "Nasan gidan bai yi miki dadi. Kar ki damu, gani na dawo."

"Ni matsa mun," Jaddati ta tureta. "Ke da wancan," ta nuna Sadiya. "ban san wa yafi surutu ba. Ku zo ku cika ma mutane kunne."

"Haka za ki ce Jaddati," Sadiya ta turo baki. "Babu komai. Ke da kan ki za ki zo neman mu."

"Me zan yi da ku ga takwara ta dawo. Ku je chan ku damu iyayenku."

"Addan zata koma makaranta ta bar mu ai."

Sun je sun gaida iyayen su mata, inda su ka fara shiga gidan Baba Nasir su ka gaida Ammi daga nan su ka shiga gidan Mama, Maman su Anwara kenan.

Wurin Ummi ne karshe. Maimoon ta kasa jira ta shiga da sauri. Ummi na tsaye a falo, da saurin ta idasa inda ta ke ta rungumeta. Hannu Ummi ta sa ta rungume 'yar ta.

Maimoon ta ji  kwalla ya taru a idanunta, sauri ta yi ta hadiye su.

"Ummi na yi kewar ki sosai." Ta ce tana kara rungumeta. "Nima haka Maimu." Janye jikanta Ummi ta yi, ta bude hannu alama su Anwara su zo suma. Murmushin fuskar su ya fadada su ka rungume matar yayan baban su.

Bayan an gama gaisawa, Ummi ta ce su karasa (dining table) abincin su na chan.

Idanun Maimoon na kan Ummi duk motsinta suna bi. Kaman ba Umminta. Ta chanza gaba daya, ta yi haske, fatarta ta yi kyau har kiba ta kara. Jan leshi ne a jikinta da ya karawa farar fatarta kyau. Kyawuan Ummin nata ya kara fitowa sosai.

Suna hada ido Ummi ta yi mata murmushi da ya nuna ta san mai Maimoon din ke tunani.

Kan dining table din kuloli ne jere ga trays da jugs. Kowa ya zauna, babu karan komai sai na chokali.

Maimoon ta kasa hakuri, ta tambaya. "Ummi yaushe Baffa zai dawo?"

"Bayan sallar la'asar za su dawo in sha Allah."

Lokacin ya yi mata tsawo, kaman ta tafi inda ya ke ta ke ji. Bayan sun gama cin abinci su Anwara su ka tafi. Maimoon kuma Sadiya ta ja ta su ka hau sama.

Allah mai iko! Yau sune a irin wannan gidan. Dukda ta ga gidan a hoto, ganin shi a zahiri daban ya ke. Gidan ya kayatu matuka, babu hayaniya, komai an sa shi daidai gwargwado.

A kasa akwai (main parlor), kicin, (dining room), sai dakin baki da kuma bandaki. Sama akwai palo biyu, daya na Ummi daya na Baffa. Sai dakuna hudu kowanne da bayi a ciki.

Dakin Baffa hada ya ke da palon shi na sama, sai gefe dakin Ummi. Ta dayan bangaren kuma sauran dakunan ne tare da palon Ummi.

"Adda ga dakin ki nan," Sadiya ta ce tana bude kofar dakin.

"Dakina kuma? Ku banda ku?"

Kai Mimi ta girgiza. "Wancan ne namu, wannan naki. Baffa ya ce a ba mamanshi dakinta ita kadai, wai mu dena damun ki."

Fashe Maimoon ta yi da dariya ganin yanda Sadiya ke tabe baki. "Are you jealous?"

"Ni me yasa ba'a samun Maimunatun ba?"

Dakin nada girma sosai. (Turkish bed) ne a ciki kalan ruwan kasa da ratsin (milk color) hade da (wardrobe) da (dressing mirror) din shi. A gefe guda an sa teburin karatu ya na kallon window, sai kuma dan karamin (shelf) din da aka jera mata turarenta na saidawa.

"Dakin ya miki Adda? Mu muka tsara." inji Sadiya.

"Ya yi kyau, nagode."

Barin ta su ka yi ta hutu. Maimoon ta kara zagaye dakin, ta yi bude-budenta. Duk abunda zata bukata a matsayinta na mace akwai a dakin daga kayan sawa, na kwalliya da sauran su.

Wannan karan bata hana hawayen zubowa ba.

Ruwa ta watsa sannan ta dauki doguwar riga mara nauyi ta zura. Dakin su Mimi ta nufa. Ko waccen su na zaune a kan gadonta ta na latsa waya. Sadiya ta fara dago kai. "Adda har kin fito. Shigo mana."

Kan gadon Mimi ta zauna, kallon su ta ke yi sanyi na ratsa zuciyarta. Nan suka zauna ana ta hirar yaushe rabo. A cikin hirar ne Sadiya ta dago Jasrah. "Ni kunyanta ma na ke ji. Mun kwana biyu bamu yi waya ba. Ni bana son kiranta ma dan bana jin dadin rashin fada mata abunda ya same mu."

"Nima wallahi," Mimi ta ce. "Amma ya zamu yi, Ummi ta ce kar mu fada. Amma ita da Hamma sun chanchanci a fada musu gaskiya, musamman Hamma."

Kai Sadiya ta jinjina. Ita dai Maimoon bata ce komai ba sai ma wani zancen da ta dago.

Karan bude get su ka ji, Sadiya ta ce; "Ga su Baffa nan."

Maimoon na jin haka ta mike bata tsaya sauraron Sadiya da ke ce mata sai ya shiga wurin Jaddati zai shigo ba.

Ummi ta samu zaune a falon. "Baffa bai shigo ba?"

Dariya Ummi ta yi. "Yanzu zai shigo, inaga ya je su kaisa da Jaddati."

Kai ta gyada ta samu wuri kusa da Ummi ta zauna. "Ummi ya sabon wuri?"

"Sau nawa za ki tambaye ni Maimu? Sabon wuri Alhamdulillah."

"Ummi? Kina cikin farin ciki?"

Hannu ta sa ta tallabo kumatun Maimoon. "Ina cikin farin ciki sosai 'ya ta, farin cikin da ban taba tsintan kai na a ciki ba."

Kanta ta daura kan kafada Ummi. "Nima haka Ummi."

Suna zaune haka Baffa ya turo kofa, sanye ya ke da fararen kaya babban rigar shi sai walkiya ta ke yi.

Kaman yanda ta ke yi sanda tana 'yar karama, da gudu Maimoon ta isa wurin mahaifinta. Wannan karan bata iya hadiye kukanta ba.

"Toh? Ke kuma kuka a ke koya mu ku a Zarian?" Baffa ya ce ya na dariya.

Kukanta kara tsananta ya yi. Baffa ya sa hannu ya bubbuga mata baya a hankali har saida ta yi shiru. Hannunta ya kama su ka isa kan kujerun. Ummi itama kasa danne nata kukan ta yi. Dole Maimoon din ta yi kuka saboda Baffanta kaman an chanza shi.

Maimoon bata matsa daga kusa da Baffa ba saida aka kira sallan Maghriba. Babu kalaman da za su iya bayanin dadin da ta ji da taga mahaifinta cikin koshin lafiya da kwanciyan hankali.

Bayan sallan kowa a gidan ya taru a falon Jaddati. Nan ta gaida iyayenta maza wato Baba Nasir da Baba Abdullahi. Daya daga cikin dalilin da Baba Abdullahi ya sa lokacin da ake ginin gidan palon nata ya kasance babba. Dan a taru haka, kowa da kowa.

Anata hira ana raha. Sadiya da Nanah na ta tsokanan Jaddati ta na biye musu. Anan aka ci abincin dare. Maimoon bakunta bai gama sakinta ba, tana ta nokewa gefe.

Bayan sallan isha'i aka yi ma Jaddati sai da safe inda iyalan Malam Muhammadu su ka koma gidansu aka daura daga inda aka tsaya. Baffa na ta kallon su murmushi makale a fuskarshi.

"Allah Ya yi muku albarka."

Duka su ka amsa da Ameen.

***

Majalisar ta su bata tashi ba sai karfe goma Baffa ya ce kowa ya tafi ya kwanta.

Maimoon ta shiga daki ta ji ya yi mata shiru. Ta saba kwana da su Anwara. Ta gama shirin kwanciya kenan ta hango wayar na haske. Tunda ta dawo bata bi ta kanta ba.

MTN ne su ka yi mata messages din da su ka saba. Bayan ta goge messages din taga ta na da missed call har biyu daga wurin Sayf, daya da rana, dayan kuma bai fi minti uku da kira ba.

Tun ranan da ya su ka yi wayan nan bayan ta dawo daga asibiti alakar su ta chanza. Kaman yanda ya mata alkawari bai kara dago maganan ba. In an kwana biyu ya na kira su gaisa. Ya samu lokaci kafin su fara exams ya zo Zaria ya dubata.

Bata taba zaton haka Sayfullah ya ke ba dukda ta na jin labarin shi sosai daga wurin Adda Salma. Yana da kirki, tausayi da kyauta. Kuma daga labaran da ya ke bata za ta iy cewa shi mutum ne mai hazaka da dagewa akan abu, wanda hakika abin yabawa ne.

Tunda bai dade da kira ba, bari ta kira shi. Wayar ta buga sau biyu ta katse, sai ga kiran shi ya shigo.

Kaman duk lokacin da taga kiran shi ya shigo wayarta, bugun zuciyarta ya tsananta. "Assalamu alaikum," deep voice ya daki kunnenta.

"Wa'alaikumus salam, ina wuni."

"Lafiya lau. Maimoon an tafi gida har an manta damu."

Dariya ta yi. "A'a, ba haka bane."

"Hakane mana, kin ci tuwon Ummi mai dadi kin manta da ni. Ya kika samu 'yan gidan, da fatan kowa ya na lafiya."

"Lafiya lau Alhamdulillah. Ya aiki?"

"Aiki alhamdulillah, gashi nan ya sa ni a gaba."

"Allah sarki, Allah Ya taimaka."

"Ameen Ameen Maimu. Yanzu an gama exams hankali ya kwanta ko?"

Dariya ta sake yi kunya na kamata. Ya kirata ana gobe zata rubuta physics, lokacin duk ta rude, tun ranan ya ke tsokananta. Ya ce mata lokacin da ya yi ABU shi ba serious student ba ne irin ta.

"Sosai. Exams din were very stressful. Na ji dadi da na gama."

"Sannu. Allah Ya sa aga sakamako mai kyau."

Addu'an ya yi mata dadi. "Ameen Ameen."

"Bari in bar ki ki kwanta ko? Dama na kira in ji ya kuka isa. Allah Ya huta gajiya."

"Ameen Ameen. Nagode." Daga nan su ka yi sallama.


****

Kwanan su hudu da dawo gida, Baba Nasir ya ce su shirya su zagaya gidan 'yan uwa su yi gaishe gaishe.

Da wuri kowa ya shirya. Maimoon, Anwara, Mimi, na mota daya tare da kannen Nanah 'yan maza guda biyu Ameer da Hydar inda Anwara ce dreban. Sadiya, Nanah, Waahidah na dayan motan da Sameer zai ja.

Gidan Kyda, diyar Baba Nasir su ka fara zuwa. 'Yan biyunta Huda da Inas sun kara wayo. Ta na ganin su zuga guda haka ta ce itama da ita za'a je. Nan ta kira mijinta ya bata izini su ka tafi tare.

Sun je gidan Anty Maryam, gidan su Ahmad kenan. Anwara tai ta nokewa a dole ita tazo gidan surukai.

Ranan dai basu yini a gida ba. Bayan an gama zumunci Sameer a matsayin shi na yaya babba ya kai su shan ice cream. Daga nan aka maida Kyda gidanta aka dawo gida. Ko da aka dawo gidan Jaddati aka shiga inda aka bude sabon shafi.

Maimoon na shan ice cream dinta tana kallon yanda kowa ke raha. Ana su ka samu su Baffa, da iyaye matan gaba daya.

Ashe haka 'yan uwa ke da dadi. Da ko in sun shiga 'yan uwansu suna rakube a gefe suna dar dan ba su san wani irin wulakanci za'a yi musu ranan ba.

"Takwara zo ki gani," Jaddati ta ce tana mata alama da hannu ta taho. Haka kawai ta tuna da Inna da irin yanda ta ke yi musu in tazo.

Kai Maimoon ta girgiza bata son tunanin Inna ko na wasu daban ya dame ta. Duk wancan a baya ya faru, yanzu chanji ya zo.

"Gani Jaddati.."

"Yauwa kin ga wanchan jakan, janyo mun ita..."











Barci na ke ji, banyi editing ba.

Vote, comment, share and follow🙏🏽💕

~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro