BABI NA TALATIN DA BAKWAI
Silent readers dinna yawa ne da ku, sai fitowa kuke yi saboda na ce zan tafi hutu. Toh kuna komawa nima zan ajiye alkalami.
No comments, no updates, kawai haka za'ayi.
~
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
~
"Babu wanda ya kai gashi na kewar ki Maimoon," Adda Salma ta ce tana zare dankwalinta. Zama ta yi gaban Maimoon ta mika mata comb da kibiya. "Kin san kaina baya da hankali, da kyar na samu wanda hannunta ya karbe ni. Ba ki ga yanda ya yi ta zuba ba."
"Gashinan ya kakkabe sosai."
"Ai nan ma da arziki. Harda dawowa nan din da mu ka yi, kafin mu samu mai kitso an dade. Gashi kuma ba kya nan kyuya ya kama ni, dama saboda ke na ke wanke kai akai-akai dan na san ba za ki yi mun kitso kai da datti ba."
Maimoon ta yi dariya. Ta zo wuni gidan Adda Salma yau. Tunda safe bayan an ajiye 'yan makaranta aka sauketa. Ta yi kewar su sosai, jira ta ke yi Ikram da Amira su dawo ta gan su, ta san sun kara girma.
Kitso ta zauna ta yi ma Adda Salma mai kyau sosai. Dayake ta dade ba ta yi kitso mai yawan haka sai yatsunta suka dunga yi mata zafi. Haka nan dai daure ta kammala mata kitso.
Adda Salma ta dauko madubi ta kasa dena kallon kan. "Wato wanda ya iya ma daban ya ke. Maimoon ba zan kwace hannun ki ba kuwa. Ji yanda kai na ya yi saboda Allah."
"Adda tukuici kawai za ki kawo mai tsoka. Bari baban Ikram ya zo shima ya bada na shi na musamman."
Dariya Adda Salma ta yi ta ce mata kada ta damu ta na da kyauta na musamman. Hirar yaushe gamo su kai ta yi. Bayan Ummi, Adda ce kawai Maimoon ke iya fada ma matsalolinta kai tsaye ba tare da fargaba ba. Ta zame mata tamkar yaya. Wani lokacin Addan na yawan tuna mata da yayanta da ya rasu Hamma Mu'azzam. Tasan da ya na da rai da shakuwar da za su yi ba kadan ba ce.
Kicin su ka shiga dan dafa abinci rana. Dayake Adda Salma gwana ce a kicin din, ta iya abinci sosai kala daban-daban.
"Kina dai daukan komai da na ke yi ko," Adda Salma ta ce ta na motsa tukunyan da ke kan wuta. "dan Baba Sayf akwai son cin dadi."
Shiru Maimoon din ta yi bata amsa ta ba hakan ya sa Adda ta waiga ta kalleta. Dariya ta yi. "Wai kunya ki ke ji? Satan amsa na ke ba ki 'yar kauye. Bature ya ce 'a way to a man's heart is through his stomach. Yayana kuma na son cin dadi saboda haka dole a rika dafa mai."
"Yau kuma yayanki ya zama?"
"Ai dama Baba Sayf yayana ne, kin ga a matsayi na na kanwarsa dole in rika mai campaign, so kina kula dashi ko? Idan kika tsaya yi mana yanga wata zamu nemo mai."
"Ku nemo mai wata kawai zai fi."
Dariya Adda ta kwashe da shi. "Ana so ana kaiwa kasuwa, bar fada kar ki je ki kasa barci. Sayfullah na Maimoon ne ita kadai, in sha Alla." Kashe gas din ta yi ta juya gaba daya ta fuskanci Maimoon. "Da fatan komai lafiya, babu wata matsla."
Kai ta girgiza. "Babu wata matsala, kawai dai..." sai kuma ta yi shiru. Abun ya dade ya na tsungulinta, amma kuma ya dace ta furta?
"Kawai me?"
Kai ta sake girgizawa. "Babu komai." Ido Adda ta kureta da shi har ta takura. "Naga tunda na dawo bai ce zai zo ba." Ta kasa hada ido da Adda saboda matsanancin kunya da ya rufeta. Sai ta furta ta ga shirmenta.
Amma sai dai Adda ba ta yi dariya ba kaman yanda ta yi tsammani sai ma cewa da ta yi; "In na fahimce ki, so ki ke ya je gida ku gaisa," kai ta daga. "Kenan kin shirya ya je ya samu su Baffa."
Sai yanzu ta dago kanta. "Su Baffa kuma?"
"Kwarai kuwa. In har kin ji kina son ya je gida ya gan ki, kenan kin yarda ya je ya samu iyayen ki."
"Bai yi wuri ba? Adda ko sanin shi ban gama yi ba fah."
"Watan mu biyu da haduwa aka sa mun rana da Habib. Maganan sanin shi kuma ba za ki taba gama sanin mutum a haka ba. In ko sai kin gama sanin shi kafin za ki bashi daman ya gabatar da kansa wurin iyayenki toh ko baza ki taba shiryawa ba."
"Har yanzu ina tsoro Adda." Ta ce murya a karye.
"Ki sallamawa Allah komai. Ki zauna ki nutsu ki tambayi kan ki, is he the one?"
Ita kadai ta san amsar tambayan.
****
Bata bar gidan Adda Salma ba sai bayan sallar maghriba. Ta na nan su Ikram su ka dawo, ta ji dadin ganin su su sosai. Sun kara girma da wayo.
Kamar kada ta tafi dan sosai ta ji dadin yini a gidan. Habib ma ya dawo ya sameta a gidan. Har ya ke ce mata yanzu su ka rabu da mutumin nata. Haka dai su kai ta tsokanarta shi da matarsa. Campaign su ke yi mai kaman yadda Addan ke cewa. Dukda Habib ya cire wasa ya fada mata abubuwa da dama game da abokin na shi.
Ita dariya ma su ka bata. Akwai dai abu daya da ta tabbata, tasan Adda ba zata taba yi mata karya ba ko ta nufeta da sharri.
Washegari Anwara ta ce ta shirya ta raka ta wurin mai dinki. An fara shirin bikin Anwara gadan-gadan kusan kullum sai Mama ta fita wani lokacin Ammi da Ummi kan rakata.
Kydah ta kwana gidan da ita su ka tafi sai ta barwa su Nanah 'yan biyu a gida. A Gwarimpa wurin dinkin ya ke. Maimoon na ganin wurin ta san za su yi dankaran tsada, illan kuwa sai gashi an kirawo wasu ma'udan kudi, kuma wai dinkin kwara daya. A kalla kudin zai yi mata dinki hudu zuwa biyar.
Ita ko uwar gayyan ko a jikinta. Wani katon littafi aka bata dan ta duba style din ta ke so. A tsakiya su ka sa ta suna taya ta dubawa.
"Wow! Wannan ya yi." Anwara ta ce ta na nuna wani style da ke tsakiyar shafin.
Kallon kayan Maimoon ta yi da kyau ta na kankance idanu. "Wannan din?"
"Ko Ya Ky....na manta ta fita." An kira Kydah a waya ta fita ta amsa. "Mai ya samu style din, bai yi ba ne?"
Rigar fah bata da hannu kuma rabin kirji duk a waje ya ke. Anya kuwa hoto daya su ke kallo da Anwara? Sai da ta kara tambayanta wani style din, shi din ne kuwa. "Gaskiya ki duba wani."
Anwara ta dage sai ta fada mata me ye bai mata a style din ba. Maimoon ta daga har yanzu bata je ghana ba ta fito mata a mutum ta fada mata bai kamata sam ta sa kalan kayan nan ba.
"Ba girman ki bane ki shiga cikin mutane da rika irin haka. Ga maza ga kowa."
"Da bridal shower zan sa fah. Babu maza, daga ni sai kawaye na. Baba ya ce babu event daga walima sai daurin aure, da kyar ya yarda in yi bridal shower din ma."
"Ko ma matan ne. Za'a dauke ki hoto daga nan hoton ya bi duniya kowa ya gan ki a haka. Shi Ahmad zai ji dadin a ce hoton matar shi na yawo da irin wannan shigan? Ba ki san wayar wa zai shiga ba. Ke ma kin san da an sa abu a social media ya shiga kenan har abada ba'a taba goge shi. Ko kin manta mutane ba za su taba mantawa ba, wani ya nan ajiye da shi jira ya ke yi abu ya taso ya kara fito da shi. Yanzu you're excited, ki yi tunanin gaba. Ko so kike yi wata rana yaran ki su nana mi ki hoton su na tambayan ki a kan shi. Na tabbata ba za ki so hakan ba. Yanzu excitement ne ke dibar ki sai nan gaba za ki rika cizon yatsa. Saboda haka maganin bari kar a fara."
Dan jim Anwara ta yi ta na tunani sannan ta gyada kai. "Hakane. Mu dubo wani."
Maimoon ta ji dadi da ba ta yi watsi da abunda ta ce ba. Tasan ba kowa bane ya ke daukar shawara ba, musamman a irin wannan abun. Wasu suna ganin shi a matsayin takura. Da taso ta yi shiru sai ta ga kuma bai kamata suna tare ba ta ki fada mata gaskiya.
Kydah ta dade ta na waya. Lokacin da ta dawo Anwara har ta zaba wa ni style din. Wannan kam da mutunci komai a rufe, dogon hannu ne kuma bai kama jiki ba.
Wani daki Anwara ta shiga aka auna ta. Daga nan kuma su ka wuce saloon inda Kydah ke son ta wanke kai. Dayake saloon din mata ne kadai Maimoon ta cire hijabinta. Itama sai ta yanke shawarar wanke kan kawai.
Ta sanar ta daya daga cikin ma'aikatan wurin ta ce mata ta taho tunda babu kowa. Ta na zare dankwalinta kowa ya fara kallonta sai ta ji inama bata cire ba.
Wata bairabiya a wurin ta kasa shiru har tasowa ta yi daga inda ta ke zata taba mata gashi ta na tambayanta. "You be fulani ko?"
Sai da ma'aikaciyar ta yi mata magana sannan ta koma ta zauna amma har ta koma wurinta ba ta daina maganan gashin ba.
Ita dai Maimoon ta na ta nanata 'Aʿūdhu bi-kalimātil-llāhi-t-tāmmāti min sharri mā khalaq' a zuciyarta. Saboda irin haka ya sa ta daina zuwa saloon a makaranta. Ba dama ta bude kai mutane sai sun tofa albarkacin bakin su.
Bayan an gama matar da ta wanke mata kai ta ce zata bata shawara yanda za ta kula da kanta sosai in bata damu ba.
Maimoon din ta ce babu damuwa. Ta yi mata bayani yanda zata wanke kai, so nawa a wata, yanda zata shafa mai da sauran abubuwan da ya mata ta sani kuma ta kiyaye. Daga karshe ta yi mata talla sun saida duk abubuwan da ta lissafo kayan su kuma (natural) ne babu hadi da chemicals.
Ba Maimoon kadai ba, Anwara da Kydah ma sun gamsu. Kydah dama makociyarta ta dan fada mata kadan daga abubuwan na su shiya sa ma tazo wurin dan ta gwada. Kowaccen su da jaka a hannu su ka bar wurin. Amarya Anwara na cewa nan zata zo yin gyaran kai idan lokacin bikinta ya yi.
A mota ana dai ta hira. Anwara da ke gaba ta juyo ta na fuskanta su da ya ke da dreba su ka taho. Cikin hirar biki ne Kydah ke fadan yanda ta hadu da mijinta Bilal.
"Through mutual friends mu ka hadu, da haduwan mu da auren mu duka bai wuci wata shida ba."
"Wata shida fah? Da wuri haka?" Maimoon ta zaro ido abun ya na bata mamaki.
Murmushi Kydah ta yi. "Maimoon idan right person din ya zo, you just know, kin gane. Mutane ai yi ta chanchakwato duka yaushe su ka hadu, wa ya mutu wa ya tashi. Bamu taba regretting ba. Shi aure in kin samu wanda ya yi miki kawai a yi shi, babu amfanin bata lokaci, ai duk sai a gama soyayyar a waje."
Haka dai su kai ta hira Maimoon na juya maganan Kydah a kan ta. Bata san wani matsayi ta ba Sayf ba ta san dai duk wani abu da Kydah ta lissafo ta na jin haka game da shi.
Sai dai ta na tsoro ko ita kadai ke kida da rawa dan bai taba cewa komai game da manufarsa akanta ba. Haka dai ta yi ta sakawa da kwanacewa a ranta.
*****
A na sauran kwana shida su koma makaranta kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU ta tafi yajin aiki.
Amarya Anwara abun ya yi mata dadi zata yi biki a tsanake babu fargaban makaranta akan ta.
Maimoon dai bata so ba sam. Idan aka fara yajin aikin nan ba'a san ranan da zai kare ba. Amma za ta yi amfani da lokacin ta yi abubuwa masu muhimmanci.
Wayarta na makale a kuunenta ta na waya da Habiba da Safara'u. Sun kai awa daya ana ta hira. Ta yi kewar su sosai kaman ta yi tsunstuwa ta tafi Kaduna ta ke ji.
Duka sun gama bautar kasan su har sun karbi certificate sai kuma neman aiki.
"Su Habiba an gama boko sai a zo ayi aure." Maimoon ta ce cike da tsokana. "Kullum dama maganar ki sai kin gama makaranta. To dai yau Mungo Park ta sauke."
Dariya Habiba ta yi. "Masters zan daura."
Du ka suka kwashe da dariya Safara'u ta ce; "Allah Ya bada sa'a. Mu dai wanda mu ka yi Allah Ya yi mai albarka ni dai na kare boko gaskiya."
Habiba ta ce; "Ke da kike cewa wasu su je su yi aure ke me ya hanaki?"
"To ai ni ban gama bokon ba ko. Kuma ga yajin aiki ana yi kinga kuwa babu rana."
"Ki ka biye wa ASUU kina ruwa wallahi. Wai ina mutumin na ki. Oh ni Habiba Maimoon ta girma. Daga na tura ki jami'a sai ki dawo mun da saurayi."
Dariya Maimoon ta yi. "Ni na ce miki saurayi na ne?"
"Eh toh, gaskiya bai da ce a kira shi da saurayi ba kalman ta yi mai kadan. Ni da zai taimaka ya fito kawai kinga sai ki yi ABU mai labule."
Kiran sallan Maghariba ya sa su ka kashe wayar. Gani ta yi ashe Sayf ya kira ta na cikin waya har sau biyu. Bari ta yi sai ta yi sallah sannan ta kira shi.
"Salamu alaikum," ta furta a hankali.
"Wa'alaikumus salam Maimoon. Kin gama wayan?"
"Eh. Da su Habiba ne. Har ka dawo?" Satin shi daya a Legas ya je seminar sai yau ya dawo.
"Na dawo. Har na ci tuwon Mamina."
Dariya ta yi. Daga ji akwai shakuwa mai karfi tsakaninsa da mahaifiyarsa. Ya na yawon ambaton ta. "Hankalin ka ya kwanta ko."
"Sosai. Na ji ASUU sun tafi strike. Yaushe su ka ce zasu dawo?"
"Wa'annan su na da ranan komawa ne? Sai ranan da aka ji su kawai."
"This is so unfortunate gaskiya. Sai ki yi amfani da daman nan ki yi focusing akan sauran abubuwan. Kun samu kun fara kuwa?"
Kaman yanda ya ce zai taimaka mata shi ya hadata da (graphic designer) din da ya yi mata haddaden logo da stickers. Ta yi da mutumin zai yi mata guda hamsin sai gashi an kawo fiye da haka. Da ta tambaya ya ce ai Sayfullah ya ce ayi.
"Ina fah. Mun dai siyo komai da komai. Anwaran ce bata zama yanzu ana ta shirye shirye." Ko jiya sai da su ka koma wurin dinkin nan ta kai musu kari.
"Oh haka. Biki ya na ta matsowa."
"Wallahi."
"Allah Ya nuna mana. Saura ke."
"Ameen. Saura ni a me?"
"Auren mana. Ko ba ki shirya ba?"
Tsuke baki ta yi. "Idan mijin ya zo mai zai hana."
"Kin shirya tarban shi in ya zo?"
Lebenta na kasa ta ciza maganan na yi mata nauyi amma duk da haka ta daure ta bashi amsa. "Ya fito ya gani mana."
"Maimunatu." Sayf ya kirata da wata irin murya da ya sa bugun zuciyarta tsananta. Bai taba kiranta da sunan ba.
A sanyaye ta amsa. "Na'am."
"Kin tuna na ce za mu yi muhimmiyar magana amma sai kin warke?" Bai jira amsarta ba ya cigaba da cewa. "Za mu iya yin ta yanzu? Kin warke din?"
Chan kasan makoshi ta amsa da eh.
"Maganar ta fi karfin a yi ta a waya. Kin bani izini in zo gidan in gan ki?"
Maimoon sarkin kunya harda rufe fuska da tafin hannu. "Na bada."
"Nagode Mahnoor. Allah Ya saka da alkhairi. Sai ki sanar da su Baffa zan zo ko and text me the address."
Hirar ta su bata tsawaita ba saboda matsanancinyan kunyan da ya dabaibaye ta. Ba ta iya ba shi amsa ma sai mm ko mm mm. Ya na mata dariya ya ce mata sai da safe. Kafin ya kashe ya tambaye ta mai zata ajiye mai.
"Me ka ke so?"
"Ke kadai ma kin isa. Ganin ki kawai na ke so in yi."
Kaman ta nutse a wurin. Ya na dariyar ta ya kashe wayan.
Kan gado ta fada tana dafe da wayan a kirjinta sai murmushi ta ke yi. A haka kannenta su ka shigo su ka same ta aiko su ka saka ta gaba da tsokana. Tuni sun san da Sayf saboda ranan nan suna cikin waya su ka shigo ya ce ta basu su gaisa.
"Su Adda manya." Sadiya ta ce tana dariya. Duka Maimoon ta kai mata ta matsa da sauri tana kara fashewa da dariya.
Bata da abokan shawara da ya wuce su. Saboda haka ta tambaye su mai ya kamata ta yi mai. Sai kuma babban matsalan, ta ya zata fara fadawa Baffa zai zo?
Na shiga uku! Ta ce a zuciya.
Sai washegari da safe ta je ta samu Ummi. Ta na zaune a dakinta ta na karatu, ajiye Qur'anin ta yi ganin Maimoon. Bayan ta gaisheta ta samu wuri ta zauna sai kame kame ta ke yi.
Ummi da ta gaji ganin 'yar ta ta bata da niyan cewa komai kuma daga gani akwai magana a bakinta ta ce; "Fadi mai ya kawo ki Maimoon."
Kunya ta kamata duk da bata yi mamakin sauri dagota da Ummin ta yi ba. Kai a kasa ta yi wa Ummi bayani tun daga farkon haduwarsu har zuwa yanzu.
"Ma sha Allah. Ki ka ce jikan Ammah ne?" Kai Maimoon ta gyada. "Toh madallah. Zan sanar da Baffan na ku."
Maimoon ta sha tsokana wurin 'yan uwanta ranan da zai zo dan tun safe ta shiga kicin. Ta kira Adda Salma dan ta bata recipe itama sai da ta gama tsokanarta iya san ranta kafin ta bata.
Ita kanta zumudin da ta ke yi ya bata mamaki sosai. Amma ba ta zauna yin dogon nazari a kai ba.
Da yamma ya ce mata za su zo wurin karfe hudu zuwa biyar, su biyu ne amma bata san waye dayan ba. Tafi tunanin Habib ne mijin Adda.
Tun karfe uku ta gama shirya komai. Ta koma sama ta yi wanka ta yi sallan la'asar sannan ta shirya. Daya daga cikin dogayen rigunan da Ammi ta bata ta zaba daya a ciki. Rigar sky blue ce ta haska fatarta sosai sai mayafinta kato ya sauko har kugunta.
"Adda Moon ba dai niqabi za ki sa ba?" Anwara da shigowarta kenan ta tambaye ta. "Fuska dai ba al'aura ba ce ba tohm. Ki bari bawan Allah ya ga fuskar ki. Na yi mamaki ma da bai taba ganin ki ba."
Dariya Maimoon ta yi. Itama tana mamaki sosai. Ko dai ya taba ganin fuskarta a wani wurin ne?
"Ba sawa zan yi ba."
"Better," Anwara ta gyda kai. "Ki bari in yi miki makeup."
"Nan fa daya. Bana so."
"Ke 'yar kauye ce."
"Na ji koma meye."
Wayarta ta dauko ta na latsawa ta zauna zaman jiran isowar Sayfullah. Sai dai har hudu ta yi, biyar ta yi babu Sayf babu labarin shi.
Da farko hankalinta ya ta shi ta fara tunanin ko wani abu ya same shi dan ta yi ta kiran shi bai dauka ba kuma wayar na shiga.
Har karfe tara ga wayar ta shi ta daina shiga. Tuni Maimoon din ta tsure ta fara tunani ko hadari su ka yi a hanya. Dole ta kira Adda Salma ta tambayeta mai ke faruwa dan ta san tabbas da Habib zai zo.
Jin ba su zo ba ya sa Adda rudewa itama. Ta ce bari ta kira Habib din ta ji zata sake kiranta.
Maimoon na ta safa da marwa cikin dakin ta na jiran kiran nata. Chan sai gashi ta kira. "Adda lafiya ko?"
"Eh lafiya lau."
"Mai ya faru Adda? Wani baida lafiya ne? Kowa lafiya?"
"Kowa lafiya lau."
Maimoon na jiran sauran karin bayani Adda ta yi shiru. "Toh me ya hana su zuwa?"
"Nima ban sani ba Maimoon." Ta bata amsa muryarta a sanyaye.
Wani lumfashi ta zuga da karfi. "Suna ina?"
"Suna gida amma Maim..."
Kashe wayar ta yi wasu zafafan hawaye na bin kuncinta. Ya na gida lafiyarsa kalau ya barta nan cikin tashin hankali. Ya san ba zai zo ba ya saka mata rai? Ya amsa wayar shi kuma ya kiya.
Zuciyarta na tafarfasa ta tuge gyalen ta yi wrapping matsayin hijab ta wular da shi.
Me yasa Sayfullah zai yi mata haka?
Ke ma dama wa ya kai ki? Ai gashinan kin janyowa kan ki. Kenan har kin manta abubuwan da su ka faru a baya? Kar ki ga laifin kowa sai na ki.
Tabbas laifinta ne ba na kowa ba. Abubuwan da suka faru a baya a maimakon su zamo mata darasi ta kiyaye amma ta yi wurgi da su saboda ta na ganin shi ba kaman sauran bane.
Mimi ce ta shigo da sauri ta goge fuskarta. "Adda lafiya? Wani abu ya samu Hamma Sayfullah din?"
Da karfin hali ta girgiza kai. "Ki fadawa Baffa an samu emergency a gidan su shi yasa bai samu damar zuwa ba."
Mimi ta tsareta da idanu. "Adda kaman kuka ki ka yi?"
"Wani abu ya shigan mu ido. Yi sauri ki fadawa Baffa dan Allah. Kulolin da ke kasa kuma ku cinye ko ku bayar da shi. Ni zan kwanta kai na na ciwo."
Mimi ba dan ta yarda ba ta tafi. Ta san ko ta matsa Adda Moon ba zata taba fada mata ba.
Mimi na fita Maimoon ta sa ma dakin mukulli. Kuka ne ya kubce mata a nan ta durkushe kasa.
****
Ta na kallon wayan ta na kara har ta gama. Ko sakwan biyu ba'a dauka ba wayar ta sake fara ringing.
Tunda safe ya ke kira har karfe biyu ta yi.
Shima ya ji yanda ta ji jiya idan da dadi.
Text ne ya shigo bayan kiran ya kara tsinkewa.
Maimoon dan Allah ba dan hali na ba ki dauki waya. Ba ni da abunda zan kare kaina da shi amma please hear me out. Ki taimake ni. Ki dubi girman Allah, dan Allah.
Da matsanancin ciwon kai ta tashi. Ko da ta sauka kasa babu wanda ya yi mata maganan jiya. Hakan ya yi mata dan suna magana zata iya fashewa da kuka.
Wannan wani irin cin fuska ne? Shi da kan shi ya ce zai zo sannan kuma ya yi mata haka. Ta yi kokari ta samo mai uzuri amma zuciyarta ta ki yarda. Ko ma meye ya faru ai zai iya daukan waya ya kirata ko ya yi mata text. Za ta fahimta, shi bayani dadi ne da shi. Amma shine ya shanyata kaman kayan wanki. Wannan ai wulakanci ne.
Daga karshe dai daukan wayan ta yi amma ko kala bata ce ba.
"I'm sorry Maimoon. Ban san da wasu kalamai zan baki hakuri da su ba, I am so sorry. Ki gafarce ni."
"Ba ka da lafiya?" Ta tambaya murya a murtuke. Sa ke bata hakuri ya yi. "Ka bani amsa ba ka da lafiya ne?"
"Lafiyata kalau."
"Mami, Nusayba ko wani a gidan bai da lafiya ne?"
"Duka kowa lafiya."
"An kira ka wurin aiki ko an samu wani matsala a ma'aikatar ku?"
"A'a."
"Tambaya ta karshe, wayar ka ta lalace?"
"A'a. Amma Maimo—"
Saurin katse shu ta yi. "Toh babu abunda za ka ce mun. You could have called. Kira daya za ka yi ko ka yi text, shikenan. Amma.." kai ta girgiza.
"Na sani. Ki yi hakuri. Let me explain."
"No. Ko ka yi bazan fahimta ba. I'm too angry and hurt to understand you."
"Maimoon..."
"Sai anjima." Ta kashe wayar.
I'm so sorry Mahnoor.
Hawaye ne sun ka sauko mata bata yi yunkurin share su ba.
•
•
•
•
•
•
•
•
Jama'a a tafa mun😩😂 longest chapter 😮💨 how was it??
Wannan ne update na karshe sai bayan azumi in sha Allah. In kun taba karanta books dina kun san bana update da azumi.
Ranan lahadi zan koma makaranta akwai abubuwa da zan yi focusing a kai. Hence the extra long chapter 🙂
Sai in ce ayi azumi lafiya💕
Ta ku a kullum,
Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro