BABI NA TALATIN
~
BABI NA TALATIN
~
Sun ga gata.
Iyalan Malam Muhammadu da suka saba rakubewa gefe in sun shiga 'yan uwa yau su ne ake wa tarba haka cikin karamaci da mutunci.
Tun a fililn jirgi su ka fara ganin abun al'ajabi. Motoci sun fi biyar da suka zo daukan su, ga 'yan rakiya cikin 'yan uwan da suka kasa jiran Baffa ya iso.
Maimoon da sauran 'yan matan su ka shiga motar da wani matashi ke ja. Shi ne babban dan Baban Nasir kaman yanda Anwara ta fada mata. Sunan shi Sameer. Shima faram-faram aka gaisa dashi.
Tafiya mai tsawo su ka yi daga filin jirgin, tafiyar ta yi ta minti arba'in. Idanuwanta na kan fala-falan titin da ke garin. Da haka duka kasar ta ke ai da an huta.
Sun isa wani katafaren gida da ke unguwar Asokoro. Tun daga waje Maimoon ta san ba karamin gida bane. Masu gadi da ke sanye da uniform ne su ka bude get din motocin su ka shiga ciki a jere.
Bakinta har kasa, Allah Ya so da niqabinta babu wanda zai ga kauyacin da ta ke yi. A hankali motar ta tsaya su ka firfito.
Harabar gidan dauke ya ke da mutanen da bazata iya kiyasta adadin su ba dan suna da yawa. Idanuwanta ta ji sun fara yaji. Wannan duk dan su ake yi?
Kallonta ta maida kan gidan, ko kuma ta ce gidaje. Dan babban compound ne mai dauke da gidaje wurin shida, gudu uku masu hawa biyu sauran kuma hawa daya.
Kasan gidan gashinan shi ba interlocks din da ta saba gani ba, shi ba titi ba. Ga furanni da bishiyoyi da suka cika wurin su ka kayata shi.
Baba Nasir ne ya kira su. A kusa da shi ta tsaya. Chan ta hango Baffa cikin mutane anata gaisawa Ummi na gefen shi. Suma da su ke tsaye wasu mata su ka gabatar da kansu. Maimoon ta dage niqabinta ana ta gaisawa.
Daya daga cikin gidajen da ba bene ba suka dunguma suka shiga. Suna shiga wani ni'imtaccen kamshi ya yi musu sallama. Wata tsohuwa ce tsaye da hawaye na bin fuskarta. Ko ba'a fada ba tasan wacece ita.
Baffa bai lura da ita ba saboda kan shi na kasa. Da ya ji wurin ya yi tsit ya dago kan shi su ka sauka kanta. A take shima hawaye su ka subce mai.
Bude hannayanta ta yi, a hankali Baffa ya taka inda ta ke ba tara da dogon tunani ba ya rungumeta. Wani irin kuka ta saki mai karfi ta na nanata 'Alhamdulillah.'
Kowa a wurin saida ya ta ya su kuka. Ko ya su ke ji? Bata san wa ye ya tura su ba, kawai ta ganta tsaye kusa da su.
Tsohuwar da ta dade ta na jin labarinta wurin su Anwara ta dago ta kalle su. Murmushi ta ke yi mai hade ta kuka. Ummi ta fara rungumewa sannan ta rungume su Maimoon. Anwara ba ta yi karya ba da ta ce kalar fatarsu daya ba, yanzu da ta ganta ta san inda ta dauko manyan idanu.
"Jaddati ita ce takwarar shi," Nanah ta fada daga chan nesa.
Kara rungumeta Jaddati ta yi, ta na fadin wani abu da Maimoon bata ji ba. Hannun Baffa ta kamo kaman karamin yaro ta ja shi ciki. Sai duk aka bisu.
Falon a kayace ya ke kaman sauran gidan, dauke ya ke da kujeru (royal chairs) da labule masu kyau da daukan ido.
Ganin Baffa cikin 'yan uwanshi ya na ta murmushi ya sa Maimoon ta ji wani sanyi ya ratsa illahirin jikinta. In akwai wanda ya chanchanci wannan abun to bai wuce mahaifinta ba. Lokaci ya yi da shima zai san me ye zumunci da kulawa daga wurin 'yan uwanshi.
Dama Anwara ta fada mata danginsu suna da yawa. Dukkan su ne a wurin kwan su da kwarkwatan su. Sunaye dai har ta daina rikewa. Walimah ce aka hada mai zaman kanta. An ci, an sha an yi raha. Sannan Baba Nasir, wanda Maimoon ta fahimta shi ne babba kuma jigon gida, ya mike tsaye.
Ya yi jawabi da ya sa zuciyoyi su ka karaya. A cikin su babu wanda ya taba tsammanin Baffa zai dawo gare su bayan shekara aru aru.
Lallai sun san muhammacin dan uwa da har basu taba mantawa dashi ba na tsawon wannan shekaru.
Baffa na gefen Jaddati a zaune. Duk bayan minti za ta waiga ta kalle shi, wani sa'in ta yi murmushi ko kuma ta fashe da kuka. In ta fara hawaye masu raunin zuciya su tayata.
Kiran salla ya sa taron ya watse. Anwara ce ta kai su wurin da zasu yi sallah inda ya kasance gidan su ne. Sun hadu da Maman su da matar Baba Nasir Ammi sai kannen su Baba Nasir din mata da su ke uwa daya uba daya su biyu, Anty Maryam da Anty Rukayya. An sake gaisawa kafin su haye sama dakin su Anwara.
Su zaune aka turo kofa wata matashiya ta shigo da yara biyu a hannunta. Nanah ta mike da sauri ta karba yaran. "Ya Kydah sannu da zuwa."
Sadiya ta mika hannu ta karba daya daga cikin yaran daga hannun Nanah. Kama ta nuna diyar Baba Nasir ce. Ta samu wuri ta zauna aka gaisa, ta ke tambaya su ne 'yan uwanta. Nan aka yi raha kafin ta mike itama ta yi arwala dan yin sallah.
Bayan Kyda ta idar da sallan ta na shafa mai kaman an tsunkuleta ta juya ta kalla Anwara. "Ina turare na? In ba ki taho dashi ba ki shirya barin mun na ki kawai."
Anwara ta fashe da dariya. "Kwantar da hankalin ki Maman 'yan biyu, mai turaren gaba daya ma na taho miki da ita," ta ce tana nuna Maimoon.
Zaro ido Kyda ta yi tana fadin, "Wow!"
"Tunda na zo hutun semester ta ji kamshin ta isheni. To ga kamfanin nan sai ki siya dama ni ba kudin da zan siyan miki na ke dashi ba."
"Ki ji tsoran Allah Anwara," Kyda ta ce tana dariya. Jusa da Maimoon ta koma daga nan hirar turare ta barke a tsakanin su.
Duk miskilancin Maimoon sai ga ta ta sake a cikin su kaman ba ita ba.
Da dare sun sake taruwa a falon Jaddati an ci abinci, dukda an ragu sosai yawanci duk sun tafi gida. Da Maimoon ta kalla sai taga saura 'ya'yan Jaddati.
"Alhamdulillah Ya Allah," Jaddati ta fada tana kallon su. "Allah na gode Ma ka da ka nuna mun wannan ranan, gani nan zaune da dukkan 'ya'yana da jikoki na," sai kuma ta fara kuka. "Allah Ya jikan mahaifinku. Allah bai yi ba zai ga wannan ranan ba. Allah Ya gafarta mai da sauran 'yan uwanku da suka riga mu gidan gaskiya."
Dukkan su su ka amsa da 'Ameen'.
Washegari ma gidan a cike, wanda ba su samu daman zuwa ba sun zo suma. Abunda dai ba'a cewa komai sai san barka.
Baffa ya yi kuka ya yi kuka har ya gaji. Har yanzu gani ya ke kaman mafarki ya ke yi nan ba da dadewa zai farka komai ya koma yanda ya ke da.
Gashi ga mahaifiyar shi, lamarin gaba dayan shi abun al'ajabi ne. Ya bata tun bai mallaki hankalin shi ba gashi yau ya dawo.
Duk tsawon lokacin nan da ya rasa soyayyar Inna kwana daya tare da mahaifiyar ya goge duk wani tabo da ke tare da shi. Ko a yau Allah Ya dau ranshi ya san zai tafi cikin farin ciki da kwanciyar hankali saboda akwai wanda zasu kulan mai da iyali.
Babban tashin hankalin shi a kullum shi ne in Allah Ya dauki ran shi wani hali Rabi'atu da 'yan matan su za su shiga. Duk sanda ya tuna wannan hankalin shi ba karamin tashi ya ke yi ba.
Yasan Nasir da Abdullahi za su kula da su. Dukda bai san su ba, ba su yi kama da mutanen da za si wulakanta dan Adam ba. Yanda su ka cigaba da neman shi bayan ba su da tabbacin samun shi ya tabbatar mai da ko bayan ran shi za su kula da iyalin shi.
Hannu a kan kafadan shi ne ya sa Baffa ya dawo daga zurfin tunanin da ya fada. Kwanan su biyar a garin, kafar ta daga yanzu kam babu kowa.
"Yaya tunanin me ka ke yi haka?" Alhaji Nasir ya tambaya. "Da fatan babu wata matsala ko? Ko in kira likita ne?"
Kai Baffa ya girgiza ya na murmushi. "Ba sai ka kira kowa ba Alhaji, lafiyata kalau."
A ta ke fuskar Baba Nasir ta chanza. "Har yanzu ba ka yarda ni kanin ka bane kenan."
Kallon rashin fahimta Baffa ya mai. "Na yarda mana."
"Amma shi ne kake kirana Alhaji ina matsayin kanin ka," zama ya yi kusa dashi. "Na san babu sabo a tsakanin mu, kuma mun rasa shekarun da ba za su dawo ba amma ina son mu yi amfani da second chance din nan da muka samu mu kulla alaka mai daurewa. Saboda haka dan Allah ka saki jikin ka kaj?"
"In sha Allah....Nasir."
Murmushi su ka ma junan su sannan su ka shiga ciki inda mahaifiyar su ke kiran su. Sun samu Abdullahi, Maryam da Ruqayya. Jiya su ka yi taro gaba daya gidan, yanzu kuma ya su ya su za su yi.
Bayan an gaisa su ka fara abunda ya kawo su. Wato su na son jin labarin rayuwar Baffa. Ya fada musu duk abunda ya faru daga yarintan shi har zuwa yanzu, sai dai ba komai ya fito ya fada musu a fili ba. A ganin shi wasu abubuwan bai kamata su sani ba.
Jaddati ta lumfasa sannan ta fara fada musu yanda Baffa ya bace. "Babanku zai yi tafiya zuwa Bauchi daga sama ya ce in shirya ka tare za ku tafi. Da naso in kiya ganin aiki zaije wa zai yi dawainiya da kai, lokacin duka shekarunka biyar, amma ya nuna babu komai. A hanyar ku ta dawowa 'yan fashi suk tare hanya," tsayawa ta yi dan ta saita kanta kafin ta cigaba. "Sai dai 'yan fashin kaman akwai wanda su ke nema dan sai sun tare hanya sun duba mota sannan su ce su yi gaba, duk wata mota da su ka tsaida sun bari ta wuce saida su ka zo kan ku."
Zuciyar Baffa ta tsaya chak! Jin abunda ta ke cewa.
Jaddati ta cigaba da cewa. "Suna ganin mahaifinku su ka fito dashi tare da dreban su ka nufi daji. Babu mai iya taimakon ku saboda da makamai a hannun," kwalla ta zuba daga idonta ta girgiza kai. "Bazan iya fada muku mai ya samu mahaifinku a wannan lokacin ba saboda har yau na tuna raina bai daina kuna ba. Watan mahaifinku daya a wurin su, ban san yanda zan fada muku irin tashin hankalin da muka shigaba. Da kyar aka samu jami'an tsaro su ka gano inda su ke, sai dai da aka je daya daga cikin su ya dauki Muhammad ya tafi dashi a matsayin horar da mahaifinku, dauke Muhammad ne ya sa su ka shawo kan shi ya amsa musu tambayoyin su."
Wurin shiru. Kowa da abunda ya ke sakawa a ranshi. Jaddati bata taba fada musu ainihin yanda ya Muhammad ya bata ba, su dai su san akwai dan uwansu da ya bata amma ba su san taya ba.
"Tashin hankali ba kadan ba muka tsinci kan mu a ciki. Dukda mahaifinku ya dawo da kwanciyan hankali bamu san a wani hali dan mu ya ke ciki ba. Ko da aka gano inda mutumin ya ke kafin a isa wurin shi ya yi hadari a mota ya mutu. Daidai da rana daya bamu taba mantawa da kai ba Muhammad, da kai mu ke kwana, mu ke tashi. Allah har Ya dauki ran mahaifinku bai daina neman ka ba, bayan rasuwar shi 'yan uwanka su ka cigaba daga inda ya tsaya. Lamido baya da rabon sa ke ganinka, ina addu'a Allah Ya hada fuskokin ku a aljannah."
Duka aka amsa da Ameen.
Ko ya aka yi ya fada hannun Ardo? Babu wanda zai iya amsa mai wannan tambayan. Saboda haka ya fitar da ita gaba daya daga ranshi, babu amfani ya yi ta hasashen da baya da amfani. Tunda dai yanzu komai ya daidaita, shikenan.
****
Satin su Maimoon daya a Abuja su ka koma makaranta ita da Anwara da Nanah. Mota aka bada ta kaisu har kofar hostel. Kafin su taho an hadota da sha tara ta arziki, Jaddati ta bata, Baba Nasir, Baba Abdullahi, Anty Maryam da Anty Rukayya harda Maman su Anwara da Ammi, matar Baba Nasir. Abun dai kaman wasu masu gasa.
Sun samu karatu da yawa kam, haka kowa ya dage ya maida hankalin shi dan an yi gaba an bar su.
Da chan da su ke matsayin 'yan daki daya suna shiri sosai bare yanzu da suka gano su 'yan uwa ne sai abunda ya karu Masha Allah.
Suna isa Maimoon ta tura ma Kyda turarenta dan ko ranan da suka taho saida ta kara jaddada mata dan tuni ta biya kudi.
Su Baffa sun kara sati biyu. Da su ka zo tafiya Jaddati ta kafe babu inda za su je. Da kyar aka samu ta yarda sai dai ta ce ta yarda su koma su kimtsa dan tana so su dawo kusa da ita.
Daman su Baba Nasir abunda su ke so kenan har an fara gyara musu daya daga cikin gidajen.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!
****
Shigowarta daki kenan wayarta ta yi kara. Bincike jikar ta yi kafin ta nemota. Ta yi mamakin ganin sunan Sayfullah a fuskar wayar.
Wuri ta samu ta amsa wayar. Bayan ta kashe ta samu kanta da yin murmushi, har kasan ranta ta ji dadin kiran.
•
•
•
•
•
•
Kun ji ni shiru ko?😅 kun san December ba zama. Jama'a ya sanyi? Ina typing hannuwana kaman zasu sankare😂
Kar ku manta ku yi voting, sannan ina son jin ra'ayoyinku da kuma abunda kuke tunani zai faru a gaba.
Nagode💕
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro