BABI NA TAKWAS
~~BABI NA TAKWAS~~
Maimoon ɗin shi? Lallai ma mutimin nan ya raina mata wayo, wai Maimoon ɗin shi? Kallon ka raina mun hankali Sadiya da jefe shi da shi.
"Maimoon ɗin ka fa kace Ya Faaiz? Ko dai ka samu memory loss ne?" Bata tsaya jin abunda zaice ba ta juya ta cigaba da tafiya. Tana tafiya tana mita a zuciya. Bayan abunda yawa Adda Moon har zaizo ya dinga cewa wai Maimoon ɗin shi, wai Maimoon ɗin shi! Kambuu!
Mimi ta samu a kitchen tana kwashe abinci. Sadiya bata ce mata komai ba ta dauko roba ta juye kayan lambun da ta siyo.
"Mai aka maki kika shigo kina kumbure kumbure?"
"Hmm, ki bari kawai Adda Mimi," ɗan karamin tsaki Sadiya taja. "Akwai ƴan rainin wayo a duniyan nan wallahi tallahi."
"Mai ya faru?"
"Kin san wana gani a kofar gida?" Mimi kai ta girgiza. "Ya Faaiz!"
Cokalin hannun Mumi ya faɗi saboda firgita da tayi. "Ya Faaiz fa kika ce Sadiya." Ta tambaya tana zaro idanu, hannun ta ta daura a girji saboda yanda zuciyar ta ke bugawa. Mai ya kawo shi har yake ma Sadiya magana?
"Shi fa, ki bari kawai. Baki ma san abinda ya ce mun ba..." nan Sadiya ta kwashe duk abunda ya faru ta faɗa ma Mimi.
"Amma dai ya samu tabun hankali ko?" Mimi tace rai a bace. "Wani irin abu ne wannan? Bayan abunda yawa Adda Moon, dan bashi da kunya, baya da ta ido shi ne zaizo yana faɗan shashanshi da shirme."
"Ki bari kawai Adda, ni dai fatana kada su haɗu da Adda Moon."
Ajiyar zuciya Mumi ta sauke. "To Allah ya sa."
~~~
Maimoon ta gama gyaran ɗaki, tayi kwaliman kayan ta da su Mimi, ta fidda wanda suka tsufa. A cikin leda tasa su, in anjima zata kaiwa Inna Laraba, wata tsohuwa dake ma su Mommy aiki da. Duk da suma ba wani sutura suke dashi mai yawa ba, amma kyauta nada kyau. Saboda hakan sai Allah ya buda masu.
A ƙasa tazauna ta mike ƙafafunta da suka rike, tun da asuba da ta tashi take aiki, gashi har ankira la'asae. Wayar ta dake gefe ta fara ringing, dauka tayi taga baƙuwar number. A kunne ta kara wayan, sannan a hankali tace. "Salamu alaikum?"
Shiru ɗayan bangaren ba'ace komai ba. "Hello? Assalamu alaikum?" har yanzu babu amsa, yatsine fuska tayi, ta ciro wayan ta duba ta gani ko kiran ya tsinke, amma sai taga ba haka ba. "Assalamu alaikum?" Da dai taga ba'a da niyan cewa komai, sai ta kashe kiran.
"Assalamu alaikum." A ka rangada sallama daga waje. Da sauri Maimoon ta mike ta sa hijab, sannan ta fita dan gannin wake sallama. Ɗan karamin tsaki taja ganin, aminiyarta Habiba.
"Ke ce ma ashe, kike wani rangada sallama kaman gidan baƙon ki ne," Maimoon ta juya ta koma cikin daki. Habiba tayi murmushi tabi bayanta. Bata zauna ba saida ta aje wa Habiba abinci da ruwa. "Ke nace maki ciki na a cike ya ke fa."
"Aiko sai kin ci, in ba haka ba ni dake."
Nan suka zauna suka dan taɓa hira, kafin Habiba ta cire hijab tana gyara zama. "Ke nifa kitso nazo kimun."
"Ki ce ba zuwan Allah da annabi kika yi ba," Maimoon ta faɗa tana juya manyan idanun ta. "To ni a halin yanzu bazan iya kitso ba, dan na gaji."
Habiba ta marairaice fuska, ta juya tana kallon Maimoon. "Haba ƙawas, kar muyi haka dake, wallahi yau na wanke kan. Ke ma kin san na barshi ya kwana, zan ji jiki. Ki taimake ni."
"I thought lokacin da na fara kitson in ta bin kanki ke da Safara'u kuzo in maku kitso, kuka dinga mun rashin M. To nima yanzu banga daman yi ba."
Habiba ta fashe da dariya, tana kallon Maimoon da ta wani haɗe fuska kaman an mata laifi. "Ai mun baki hakuri, kuma fa kince kin hakura. Dan Allah Moon ki taimaka, haba Moon ɗin Baffa da Ummi."
"Ni matso in miki, ba sai kin cika ni da daɗin baki ba. Kuma duk wanda naga dama zan miki."
Habiba tayi dariya tace. "To naji."
Ita ma Masha Allah Habiba nada gashi, sai dai ita nata cika gare shi, bai cika tsawo ba. "Wallahi kan ki kaman gonan auduga, sai shegen cika. Yanzu Allah kadai yasan yaushe zamu gama."
"Ji mun fa, kanki baiyi ukun nawa ba?"
"Banda sharri, kuma kitso kike mun? Ai ni ban wahalar da mutane ince sai anmun kitso."
"Wannan kuma ke kika ga dama, saboda gashin ki na da kyau ko shekara zaiyi a kunce ba abunda zai same shi. Niko nawa bashi kwana biyu ya zama kaman goruba."
Maimoon ta taɓe baki, ta tashi ta dauko comb da kibiya taba Habiba, sannan ta fita waje ta dauko ƙaramar kujera. Ta dawo ɗakin Habiba na sharce kan, ta baza shi yayi kaman afro.
"Badan halinki ba, wani iri kike so?" Maimoon ta tambaya bayan Habiba ta zauna. Habiba tayi murmushi har haƙoranta na bayyana. "Shuku zaki mun."
Maimoon tayi ƴar ƙaramar dariya. Dama tasan bazai wuce shuka ba, kullun shi ne a kan ta. Sai tsakiyar kanta ya cinye tukun zata yi bayani. Bismillah tayi ta far ma ƙawar tata kitso. Ƴan ƙanana take yankan su, saboda ita bata iya manyan kitso ba. Gashi tana da sauri, kuma hannunta ba zafi, kaman tana ma susa. Shi yasa mutane da yawa ke son tazo ta masu kitso.
Bata kitso a gida sai dai taje, saboda Daddy yace bai yarda mata su dinga ciwo mai gida anyhow ba. Dama shima Baffa bai goyi bayan a dinga zuwa gidan ba, saboda yana gudun abunda zai haɗa shi da Bello. Sai dai kuma duk inda Maghriba tayi ya kasance tana gida.
"Moon baki san mai ya faru ba?" Habiba tace bayan wasu yan sa'o'i.
"Ya akayi?"
"Wai Abdul ni zai kai ƙara wurin Aunty Maryam? In gaya maki mata ta kira ni tana zazzaga mun masifa, wai ba kyau wulakanci, wa ya mutu wa ya tashi, wai ita nan ƙanin mijinta. Tun farko saida na ce mai I'm not interested in any kind of relationship da shi, shi ƙanin mijin yayata, ni kuma ƙanwar matan yayan shi, abunda kadai ya hada mu kenan. Amma yayi ta insisting, kuma ace ina wulaƙanta shi. Bayan tun farko I told him the truth, na fada mai gaskiya. Ni yanzu Allah ya gani ban shirya yin aure ba, to akan me? In ya matsu yaje ya nemi wata mana."
In banda dariya ba abunda Maimoon ke yi. Habiba taja tsaki. "Ban son iskanci, ina faɗa maki abu kina mun dariya."
"Sorry," Ta ce tana ƙoƙarin danne dariyarta. "Amma ke ma Beebs ki saurari bawan Allah nan mana. Shekara nawa yana binki, tsakani da Allah."
Habiba ta turo baki gaba kaman ƙaramar yarinya. "Wannan shekaran zan gama degree in Allah ya yarda, in yi service next year, sai maganan neman aiki, nima in tsaya kan ƙafafuna, sannan a fara maganan aure."
Taɓe baki tayi, ta cigaba da abunda ta keyi. "Sannun allazi boko, sai kinga ƙarshen biro ko? Why not kiyi service gidan mijinki?"
Kwace kan ta Habiba tayi, ta juya tana harararta. "Ke mai yasa ba kiyi auren ba? Naga dai shekarun mu daya."
Maimoon tayi dariya, tace, "Allah bai kawo mijin ba."
"To ni Allah ya kawo ne?"
"Baga Abdul ba?"
Habiba ta gyada kai, ta cigaba da hararar Maimoon dake gimtse dariyarta. Sarai ta san kwatakwata Habiba bata son Abdul, neman tsokana ne kawai.
"Ni zauna in cigaba, kina bata mun lokaci."
"But on a serious note Maimoon, even if I'm ready to get married, to fa ba da shi ba. Bana son Abdul, at all. I tried to for the sake of dangantakan dake tsakanin families din mu, but I couldn't. Kwatakwata bana son shi, kuma bana so in wulakanta shi. Amma ya ƙi ya gane, sai shegen naci kaman ƙuda."
"Kiyi ta addu'a Allah ya raba ku lafiya, Allah kuma ya zaba mana mafi alkhairi."
"Ameen Ameen." Habiba ta amsa.
Duk yawan gashin Habiba, a ƙasa da awa biyu Maimoon ta gama. Habiba ta mike tana ma Maimoon godiya. "Nagode Maimun din Baffa, Allah saka da alkhairi. Allah ya kawo miji na gari."
Maimoon murmushi tayi tana girgiza kai. Waje taje ta wanke hannu, har yanzu ba wanda ya dawo a cikin ƴan gidan. Mimi da Sadiya sun tafi islamiya, Baffa ya tafi wajan aiki, Ummi kuma taje ziyara.
Maimoon ta raka Habiba har waje inda tayi parking motarta. Bata bar wurin ba har saida ta dena ganin motar Habiba. Juyawan da zatayi suka haɗa ido da namijin da ke tsaye a wurin. Mummunar faɗuwar gaba ta ziyarce ta a lokacin, duk ta rude amma sai ta dake bata nuna hakan a fili ba.
Ko dai idon ta ne ya fara ganegane? Amma kiran sunanta da yayi ya tabbatar mata ba illusion bane, dagaske Fa'iz ne agabanta. Ya Arhaman Rahimin! Me yake yi anan? Me ya kawo shi? Rabon da ta gan shi an fi shekara, tun sanda yayi aure bai ƙara bari sun haɗu ba ko so ɗaya, mai yasa ya mata magana yau?
"Maimoon." Sautin muryar shi ya daki kunnen Maimoon, sai a sannan take da na sanin fitowa babu niqab. "Assalamu alaikum." Ya sake cewa karo na biyu, dan bata ji na farkon ba.
Murya chan kasa ta amasa sallaman shi. So take ta tafi, amma ƙafarta kaman an sa mata super glue, in ta kalle shi wani zafi, takaici, da ƙunci ke cika mata kirji. Da sauri ta nufi hanya gate.
"Maimoon dan Allah ki saurare ni, please." Fa'iz yayi saurin cewa.
Cak! ta tsaya amma bata juya ba. Fa'iz ya cigaba da cewa. "Turn and look at me, juyo ki kalle ni in baki hakuri. Ban san da wasu kalamai zan baki hakuri ba Maimoon, amma ina rokon ki da ki yafe mun."
"Allah yafe mana gaba daya."
"Maimoon I still love you, har yanzu ina son ki...."
Bata san sanda ta juya ta jefe shi da wani mugun kallo ba, manyan idanun ta sun kada, sun yi ja. Yako san abunda yake faɗi? Yana da hankali kuwa?
Kaman ya san abunda take tunani, yace. "Da hankali na Maimoon, I haven't gone crazy, da hankali na. K—
"Dakata Fa'iz!" Ta daka mai tsawa, tana daga hannu. "Ko ka mance mai ya faru ne?" Bayan abunda ya mata har yana da bakin da zai tsaida ta a hanya ya faɗa mata wannan kalaman da basu da dadin ji ko kadan?
"Maimoon..."
"Kar ka manta da matar ka, har da yarinya..."
"..wannan ba matsala bane Maimoon, ni mijin mata hudu ne."
Mamaki ya cika Maimoon, ta tsaya tana kallon ikon Allah. Mutumin da ya yaudare ta bayan ta gama yarda da shi, tun da yayi abunda yayi bata sake ganin shi ba sai yanzu, amma shine zai tare ta yana faɗa mata maganganun banza da na wofi. In shi bai da hankali, ita tana da shi. Saboda haka bazata tsaya a bakin titi ba tana musanyan yawu dashi ba, tafi ƙarfin haka.
"Maimoon dan Allah ki saurare ni. Maimoon bada son raina nayi ba, ƙarfi na aka fi. Please Maimoon, ki tsaya kiji."
"Ko ka mance wacce kake aure ne Fa'iz?" Maimoon ta tambaya a fusace, ranta ya gama baci. "To bari in tuna ma, cousin dita kake aure, ɗiyar ƙanin Baffa na, wanda a gidan shi muke zama, mu ke cin arziki kaman yanda yake cewa."
Ji take kaman ta kwala ihu, in ta tuna abunda ya faru sai taji kaman ta fiddo zuciyar ta ta yarda, ko taji saukin tafasar da take yi. Bata tsaya jin abunda zai ce ba, dan kwatakwata bata son ganin shi, ko mai kama da shi bata son gani.
Tana tafiya kawai taji tayi karo da mutum, bata tsaya ganin waye ba dan kanta a ƙasa yake. "Yi hakuri." Ta ce sannan ta cigaba da tafiya. Tayi mamaki da bata ji an fara zaginta ba, dan duk zaton ta ɗaya daga cikin ƴan matan gidan ne.
"Moon, wait." Taji muryar Hamma Ashmaan. Sam! Bata son haɗuwa dashi, saboda haka taƙi tsayawa.
Da yaga haka ya bi bayanta, har ta turo ƙofar ya sa hannu shi, saura kaɗan ta datse tare da hannun, ba yanda ta iya, dole ta bar shi ya shigo.
A hankali Ashmaan ya taka zuwa inda take, amma taƙi dago kai ta kalle shi. "Moon me ya same ki?" Ya tambaya cike da damuwa.
Muryar ta chan ƙasa ta ce mai ba komai. Amma bai yarda ba, hannun shi yasa ƙasan haɓarta ya dago kanta. Hawaye ne kwance a cikin idanun, saura kaɗan su fara zubowa.
"Maimoon," Ashmaan ya kira sunan ta cike da tashin hankali. "Mai ya faru? Mai yasa kike kuka? Talk to me Moon."
Da sauri ta ja baya, ta goge hawayen da ke kokarin zubowa. "Babu komai."
"Ya zaki ce mun ba komai bayan gashi kina kuka, Moon ki gaya mun mai ya faru? Mai yasa kike kuka?"
"Na ce maka babu komai Hamma," Maimoon ta faɗa ba tare da ta kalla inda yake ba. "Dan Allah ka tafi."
"Ba inda zani har sai kin gaya mun me ya same ki. In tafi fa kika ce, kema kin san hakan will never happen. So, please Moon ki faɗa mun mai ya faru? Wa kika gani a waje har yasa ki kuka?"
A hankali Maimoon tace. "Fa'iz."
Jim Ashmaan yayi, ya tsaya yana kallonta cike da tausayi. Family ɗin shi sun zalumce ta, suna ma cikin yi. "I'm sorry Moon, I'm sorry family na na hurting ɗin ki, I'm sorry da har yanzu ban dau mataki ba, kiyi hakuri Maimoon, ki yafe mun. Kuma ki cire Fa'iz a ran ki, Allah bai ƙaddara zaki aure shi ba, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ki, wani hanin ga Allah baiwa ne, in sha Allah zaki samu wanda ya fishi. Nasan kina hakuri Moon, ba kaɗan ba, ki kara hakuri, mahakurci mawadaci. In sha Allah wata rana sai labari."
A hankali ta daga mai kai, ta ji ɗaɗin shawarar shi, duk da tana yin abunda ya ce. Kalaman shi sun sanyaya mata rai. Kuma Fa'iz tuni ta cire shi a rai. "Nagode Hamma."
Murmushin ƙarfin hali ya mata. "Promise me in na tafi baza ki cigaba da kuka ba."
Kai ta girgiza. "In sha Allah."
"Innallaha Ma'as Sabirin." Yana faɗan haka ya fita, a zuciya ya ce. Don't worry Moon, in sha Allah na kusan fidda ki daga wannan yanayi, you'll know nothing but happiness.
Bana jin dadin rashin comment dinku gaskiya😕 Ko in tafi hutu ne?
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro