BABI NA SHIDA
~~BABI NA SHIDA~~
"Bello lafiya na ganka haka?" Baffa ya tambaya. Gyara zaman babba rigar shi Daddy yayi, kafin yace. "Lafiya? Ina fa lafiya Muhammad? Nace ina lafiya?"
"Subuhanallahi, to zauna." Kai Daddy ya girgiza. "Zama bai ganni ba, wannan magana tafi ƙarfin a zauna. Ka barni a tsaye kawai."
Ajiyar zuciya Baffa ya sauke. Da ido yama su Maimoon nuni su shiga ciki, har Ummi. "Bismillah, mai ya faru?"
"Ka bani kunya Muhammad, wallahi ka ban kunya. Dan Adam butulu. Meye ban maka ba a rayuwa? Kana zaune a gidan da nake zama, to ka faɗa mun meye ban maka ba? Amma har kai zaka bata mun suna, har kai zaka ci zarafina a bainan nasi ka tozartani? Lallai dan adam butulu."
Kalaman ba ƙaramin sukan Baffa sukayi ba. Ya gaji da gorin da ake masa, ya gaji da wulakancin da akeyi masa a gaban yaran shi. Amma in sha Allahu, in Allah yaso ya yarda, ya kusan shawo kan matsalan nan, da izinin Allah.
"Ban fahimci abunda kake nufi ba Bello, mai na maka na tozarci?"
Hannu Daddy ya watsa sama, yana huci kaman ya rufe Baffa da duka. "Da kai da waccan bakar ƴar taka mana. Kwaila da ita har ta isa ta rusa mun abinda na dade ina shiryawa."
Ya kara sa Baffa a duhu, saboda haka ya nemi karin bayani.
"Aikatau taje tana yi gida gida, ko zaka ce baka sani ba?" Daddy bai jira amsan Baffa ba yaci gaba da cewa. "Ita ce wanki, ita ce wanke wanke, ita ce shara, harta surfe. Gidan ɗan majalissan da ya dawo unguwan nan kwanan nan taje tana aiki. Da barin bakinta, Allah kadai yasan mai ta fadawa matan shi, matan kuma tayi bincike ta gano dangartakar ta da ni. Taje ta samu mijin ta, yanzu yace bazai mara mun baya ba in samu kujerar da na dade ina muradi."
Baffa jiri yaji yana neman kwashe shi. Maimunatu? Maimun shi?
"Wannan miskilan yarinyan kullun cikin hijabi harda wani niqabi amma ta iya kulle kulle, makirci da munafinci. Kasan abinda na rasa saboda ita? Kasan tarin dukiyan da nayi asara? Toh wallahi ka ja mata kunne, ka dau mataki Muhammad. Dan na rantse ta shigo hannu na baza taji da dadi ba. Taji darajar ƴan uwantakan dake tsakanin mu amma wallahi da kulle ta zanyi. Aikin banza aikin wofi." Fuu! Ya ja babban rigar shi ya bar gidan.
Baffa jikin ci har rawa yake saboda tsananin bacin rai. "Maimunatu!" Yanda ya kirata dole ko waye ya firgita. "Fito nan," da ta dauki lokaci bata fito ya ƙara cewa. "Ki fito nace kafin inzo wurin nan."
Maimoon duk tabi ta rude, ta fita da sauri, gaba ɗaya a firgice take. Ya akayi Daddy ya sani? Allah ne shaidan ta bata taɓa maganan kowa da matan ba, iya kar abunda ke shiga tsakanin su gaisuwa, sai kuma in zata aike ta ko tasa ta aiki. Da ta fito taga yanayin mahaifin nata sai ta ƙara firgita. Bata taɓa ganin shi yayi fushi irin haka ba.
Tsum tsum, ta taka ta tsaya agaban shi dukkan illahirin jikinta kyarma yake. Batayi aune ba taji ya dauke da mari har sai da ganin ta ya dauke, fuskar ta ta ɗau zafi. Ya daga hannu zai ƙara mata, Ummi tayi saurin rike masa hannu. "Dan Allah ka yi hakuri."
"Kin ji abinda ya fada Rabi, kin dai ji. Dama duk makarantar da dake cewa ta tafi karya take! Mai ta nema ta rasa, da har za ta fita nema ba da izinin kowa ba. Kin bani kunya—"
"Baffa dan Allah," Kuka take kaman ranta zai fita. Yau ta shiga uku. Sai da Habiba ta ce mata ta faɗa ma iyayenta amma tai ta jinkirtawa, ai ga irinta nan. Iyayenta da tayi dan su suna fushi da ita.
"Mai zakice mun? Bana buƙatar wani bayani. Kin fi son kiga ana wulakanta ni ko? Kin fi son haka?"
Da sauri ta girgiza kai, hawaye nabin kumatun ta. Babu abunda ta tsana kaman ganin ana wulakanta iyayen ta, abun na mata ciwo matuƙa. Dalilin da yasa ma ta fara aikin kenan. Ta raka Habiba taji ana naiman mai aiki tace zata yi. Duk dan ta taimaka ma iyayenta. Babu yanda Habiba bata yi ba ɗan kar tayi amma taƙi ji.
"Tun yaushe?" Baffa ya tambaya, muryar shi a dake.
Cikin in'i'na tace. "Wata shida."
Salati Ummi tayi. Baffa ko ji yake ƙafafun shi bara su iya rike shi ba. Wuri ya samu ya zauna. "Tashi ki bani wuri, ban son ganin ki."
Rarrafawa tayi har inda yake ta riƙo mai hannu. "Baffa dan Allah ka saurare ni." Da sauri ya fizge hannun shi. "Dan Allah Baffa."
Tsawa ya daka mata wanda ta ƙara firgita ta. "Nace ki tashi ki bar wurin nan kafin in raunata ki. Kin fi kowa sanin yanayin da muke ciki, amma ace ke ce kika je kika dauko mana abun magana."
Takasa tashi, kuka kawai take yi. Ina zata sa ranta taji sanyi, Baffa ko kallon ta yaƙi yi. "Rabi kice mata ta bace a wurin nan."
Ummi ta rasa abunda zatayi. Kwatakwata batayi zaton haka zai faru ba, bata san Maimunatu ta yanke shawaran yin haka ba. Tasan ƴar ta kuma tasan abunda zata iya da bazata iya ba. Maimunatu bata da surutu, miskilar kanta ce sai in ta saba sosai da mutum. Kuma aikatau da taje tanayi tasan tausayin mahaifin ta ne yasa ta aikata hakan.
"Tashi ki shiga, Maimunatu."
Da ta isa ɗakin su, kan katifa ta kwanta ruf da ciki, ba abunda takeyi sai kuka. Zuciyarta na mata zafi kaman zata fashe. Allah ya gani ba tayi haka bane dan ta batawa Baffa rai ko ta janyo mai magana. Taimakon shi take son yi dan yana matuƙar bata tausayi. Nan ta kwanta tana ta kuka har zazzabi mai zafi ya rufe ta.
~~~
Daddy da ya bar nan cikin gida ya nufa, zare babban rigar shi ya fara yi. Bai sanar da mai ɗakin shi abunda ake cike ba dan ba abunda zata iya yi sai dai ma ta ƙara bata mai rai.
Kai kawo ya dinga yi a dakin, ya zagaye ɗakin yafi a ƙirga. Waya ya dauko, ya kira babban wan su, Alhaji Abdulkarim. Yana dagawa ko gaisawa bai bari sunyi ba. "Komai ya baci Abdulkarim, baƙar yarinyan nan ta ruguza komai."
Daga dayan gefen Alhaji Abdulkarim yayi murmurshi. "Ka kwantar da hankalin ka Bello, dan shi kaɗai ya zare hannun shi ba matsala bane. Kujera kasa a ranka ka gama samu. Ita kuma yarinyan ka rabu da ita, mahaifin ta kadai ya ishe ta dan na tabbatar ba da sanin shi tayi haka ba."
"Ya zaka ce bada sanin shi tayi ba? Bai ga tana fita kullun ba har tsawon wata shida?"
"Bello, ka manta wai waye Muhammad? Rayuwar wani da abun wani basu taɓa damun shi ba, saboda haka bayanda za'ayi ya tura ta, kaima ka sani."
Daddy dai bai ce komai ba. Ji yake kaman ya koma ya kama baƙar yarinyan ya mata ɗan banzan duka. "To wai yaushe zasu bar mun gida ne, ni fa na gaji. Tsawan shekara bakwai fa kenan, ina dalili? Nace ma zan bashi ɗaya daga cikin gidan da na ke badawa haya, ka ƙiya, dole sai a gidana."
"Kai dai ka ƙara hakuri, ni nasan abinda nake yi."
Sun jima suna magana kafin suyi sallama.
~~~
Baffa abun duniya sun taru sun mai yawa. Ya rasa inda zai sa ran shi yaji sanyi. Kalaman da Bellon ya faɗa mai sai yawo suke mai a kai, da wanda ya faɗa yanzu, da wanda ya faɗa a baya.
Ummi ta shigo ɗakin, hannun ta ɗauke da tray ɗin abinci. Ajiya zuciya ta saki ganin halin da yake ciki. "Dan Allah ka cire damuwa a ranka," Murayar ta a raunane tayi magana. "Kasan dai baka dade da dawowa daga asibiti ba, dan Allah komai ya wuce."
"Rabi'atu, meye Maimunatu ta nema ta rasa? Nasan ba duk abunda take muradi ba ta ke samu ba, amma ina iyakar bakin kokari na inga na ci da ku, na tufatar da ku. To me sa..." sai kuma ya dakata bai cigaba da magana ba.
"Kafi kowa sanin halin diƴar ka. Kasan abunda zata iya aikatawa da wanda bazata iya ba. Ina da tabbacin tausiya ne ya kamata, watannin baya da akayi ta fama."
Baffa bai sake cewa komai ba. Abincin ya ci, shima ba sosai ba dan babu abunda ke mai dadi.
Washe gari assabar, Baffa da wuri ya fita. Mimi da Sadiya ma sun tafi makaranta, ana masu extra lesson.
Shiru Maimoon bata fito ba, abun ya ba Ummi mamaki. Amma sai ta ƙyale, wata kila bata samu daman yin bacci ba jiya da daddare. Amma har wurin sha biyu Maimoon bata fito ba. Nan hankalin ta ya tashi. Ta shiga ta same ta a kwance, jiki ba kwari, zazzabi mai zafi ya rufe ta. Salati Ummi tayi, "Maimunatu wani irin rashin hankali ne wannan, baki da lafiya baza ki faɗa ba kin rufe kanki da bargo."
Da ƙyar Maimoon ta dago da kanta, dan ji take kaman zai faɗi saboda azabar ciwo, ga idanun ta duk sun kumbura bata ma iya bude su. "Ummi ina kwana."
"Rike gaisuwan ki bana so."
Shikenan Ummi ma fushi take da ita. Yau ta shiga uku. "Ummi dan Allah ki saurare ni."
"Muje ki yi wanka, mai yasa zaki mun haka Maimunatu. Baki da lafiya baza ki faɗa ba, kin san haka na.." sai kuma tayi shiru.
"Ummi fushin ku masifa ce a gareni. Ummi dan Allah."
"Kin san da haka kike yin abunda ranki ya raya miki? Mai yasa bakizo kin same ni ba? Ko ban ce in kina da matsala kizo ki faɗa mun ba, amma yarinya sai zurfin ciki."
Ina zata je ta samu Ummi ta ƙara mata damuwa, da wanne mahaifiyar tata zata ji dashi. Da rarrafe ta janyo wata jaka, sannan ta fiddo ƙaramar purse.
"Gashi Ummi," ta mika mata purse din. "Ko kwandala ban taɓa ba, sai wanda nayi siyayya da shi jiya. Ki ba Baffa, Ummi dan shi nayi. Jarabawar su Mimi sai kara matsowa takeyi. Ummi itama ta samu tayi WAEC ɗinnan." Duk maganan da take yi a wahale take, muryar ta shaƙe bata fita sosai.
"Tashi muje." Ummi ta kamata ta kai ta bayi tayi wanka da ruwa mai zafi. Aiko har taji daɗin jikinta, sannan taci abinci Ummi ta bata magani.
Zama tayi tawa Ummi bayanin komai. Eh, tayi aiki a gidan minista amma bata taba hira da matar shi ba ko ƴan aiki. Sai dai in matar ce tasa akamata bincike a kanta. Sannan ta faɗa mata duk gidan da tayi aikin, da kitson da take zuwa yi.
Alhamdulillah, Ummi ta gamsu da bayanin ta. Ta mata faɗa sosai, sannan ta mata nasiha mai ratsa jiki. Saura Baffa, ta san kuma sai tayi da gaske kafin Baffa ya saurare ta. Bashi da saurin fushi, amma fa in ya hau kafin ya sakko sai Allah.
~~~
Yau sati daya kenan da zuwan Daddy. Tun lokacin kwanciyan hankali ya ma Maimoon sallama. Duk ta rame, tayi ƙasusuwa saboda rashin kuzari. Tun ranan Baffa gaisuwan ta kaɗai yake amsawa. Ko tayi abinci baya ci, dole Ummi ta fara masa girki da kanta. Ranan farko da yace ba zai ci ba, Ummi ta dauka wasa yakeyi, amma sam! Ba wasa yakeyi ba, wunin ranan bai ci abincin gidan ba.
Kuma ya hana Maimoon fita, ko nan da bakin get taje yace bai yafe ba, tunda fitarta ba alkhairi bace. Wannan bai dame ta ba, dan dama ita ba mai son fita bace, ba dan aikin da taje tanayi ba sai tayi sati ko bangaren su bata bari ba.
Da Ummi ta kai mai kudin, watsi yayi dasu. Ranshi ya ƙara ɓaci, laifin Maimoon har yaso ya shafi Ummi.
Maimoon na zaune taji hayaniya a waje, kaman muryan Sadiya take ji. Ummi bata nan, taje barka a makwafta. Hayaniyan taƙi ƙarewa, kaman ma faɗa ake yi. Da sauri tasa hijab ta fita dan gannin mai ke faruwa. Manyan idanun ta ta zaro. Me take gani haka? Kannenta biyu rike da ƙugu, da ga gani faɗa suke shirin yi. Sai Radiya da Fauziya suna lallashin Khalifa dake kuka.
"Mai yasa zaki duke shi? Muguwa, kawai ki kama yaro ki duka saboda tsaban mugunta." Radiya tayi magana tana nuna Sadiya da yatsa manuniya.
Sadiya ta juya idanun ta amma bata ce komai ba. Fauziya ta miƙe daga tsugunniyan da tayi, tayo kan Sadiya zata buge ta. Da sauri Mimi ta ture Sadiya gefe, ta kuma bankaɗe Fauziya har ta kusan faɗuwa.
"Kar ki kuskura wallahi," Mimi ta faɗa rai a bace. "dan kika taɓa ta, zamu kwashi ƴan kallo a nan. Shi ƙannin naku kunsan mai yayi? Kawai baku san mai ya faru ba kun yanke hukunci. To ba laifin ta bane."
Fauziya ta rige ƙugu tana kaɗa kafa. "Ke Amina, ni sa'ar ki ce."
Radiya da ke gefe tace. "Fauzi muje dan Allah, ki daina bata lokacin ki akan sakarkarun nan."
Sadiya tayi wuf! Tace. "Ai sai sakarai ke sanin sakarai." Nan ma Radiya tayi kan Sadiya.
Ganin suna ƙoƙarin fara dambe, Maimoon ta kira sunan su. "Mimi, Sadiya, ku wuce ciki." Tana gama faɗan haka ta juya, ko kallon su Fauziya bata yi ba dan bata da lokacin su.
"Ku baku da hankali? Meye na tsaya wa chachan baki da su? Sa'anin ku ne?" Sadiya ta murguda baki, aiko Maimoon ta kai ma bakin duka. "Haba Adda! Ki tsaya kiji abunda ya faru mana."
"Ban son ji. And this should be last time zaku tsaya kuna faɗa dasu. In da Mommy ta fito fa? Kar ku sake. Kuje ga abincin ku chan a kitchen."
Sadiya ta fara tafiya, sai kunkuni takeyi. Taya za'ayi ace tana kallo ɗan ƙaramin yaron chan yana zagin ta. Kuma ace bazata duke shi ba? Sam! Baza ta saɓu ba.
Baffa bai dawo ba sai bayan sallar isha'i, ya dawo ya sami Ummi da ƴan matan ta a tsakar gida suna hira. Ya amsa gaisuwar kowa da fara'a amma da Maimoon ta gaida shi sai ya haɗa fuska ya amsa a takaice.
Ran Maimoon ya sosu. Sai taji bazata iya zaman wurin ba. Mimi taje kitchen ta dauko wa Baffa abinci shi, da ta dawo Maimoon har ta shiga ciki. Ajiyar zuciya ta sauke, tasan ƴar uwar ta na cikin wani hali. Sadiya ta ja gefe suka yi magana. Ƙwarai Sadiya ta gamsu da shawarar ƴar uwar ta, dan ita ma ganin Adda Moon a wannan hali na daga mata hankali.
Sai da suka jira Baffa ya gama cin abinci kafin suka yi magana. Sadiya ta fara cewa. "Baffa?"
"Na'am yar auta." Baffa ya amsa yana mata murmushi.
"Baffa alfarma muke nema." Wannan karon Mimi ce tayi magana. Baffa gyara zaman shi yayi ya basu dukkan hankalin shi.
"Alfarman mai kuke nema?"
"Baffa dan Allah kayi wa Adda Moon haƙuri, ka yafe mata." Mimi ta faɗa kaman zatayi kuka.
"Dan Allah Baffa," Sadiya ma tace. "Kullun na tashi da dare sai naji ta tana kuka, Baffa dan Allah kayi haƙuri, ka yafe mata."
Lumfashi Baffa ya ja. Shi karan kan shi baya jin daɗin abunda yake ma Maimunatu, amma abinda tayi ba daidai bane, kuma dole a nuna mata laifin ta saboda gaba. "Je ku kira mun Addar taku."
Da gudu Sadiya ta nufa daƙi, a zaune ta iske Maimoon, ta haɗa kai ta gwiya tana zubar ƙwalla.
A hankali Sadiya ta taka gare ta. "Adda?" Ta dafa mata kafaɗa. Da sauri Maimoon ta goge fuskar ta, saidai idanun sunyi ja jawur, sun ƙara fitowa. "Adda kizo Baffa na kira."
Gaban ta sai da ya faɗi. Daga kai kawai ta iya wa Sadiya, ta dauko hijab tabi ta a baya. Da suka isa tsakar gida, Baffa ya shiga daki. Ummi ta ce mata ta shiga ciki. Kamar wacce bata son taka ƙasa haka take tafiya, kaman ta juya ta ruga a guje take ji. Fargaban abunda Baffa zai ce mata take yi.
A zaune ta same shi a gefen gado. Tayi sallama, ya amsa ba tare da ya kalleta ba. "Baffa gani." Wuri ta samu a bakin kofa ta tsugunna.
"Shigo ciki." A hankali ta taka, chan nesa dashi ta zauna. Dan gani take zai kara marinta. Bata taɓa batawa mahaifin ta rai haka ba, tana tsoro kar wannan ya zama dalililn rushewar fahimtar dake tsakanin su.
"Maimunatu abunda kika yi baki kyauta ba, sam! Ban ji dadin abunda kika yi ba."
Kan ta a ƙasa ta fara magana. "Baffa dan Allah kayi hakuri, ban yi haka dan in bata ma rai ba. Nayi kuskure Baffa, amma ina roƙon ka da ka yafe mun. In sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba."
Ajiyar zuciya Baffa ya sauke, ance ba'a shaidar ɗan yau amma shi ya yarda da hankali da tarbiyar Maimunatu. Fushi ne ya rufe mai ido har ya aikata abunda ya aikata. "Na yafe miki Maimu, Allah ya yafe mana gaba daya."
Maimoon bata san sanda hawaye suka fara zuba daga idanun ta ba. Wani sanyi mara misaltuwa taji yana ratsa illahirin jikinta. Hannu mahaifin ta ta kama, tana masa godiya. "Nagode Baffa, nagode."
A hankali Baffa ya sa hannun shi ya shafa saman kanta dake rufe da hijab. "Ya isa haka Maimunatu, kukan ya isa haka."
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro