BABI NA HUDU
~~BABI NA HUDU~~
Yau Maimoon ta tashi bata jin daɗin jikan ta, zazzabi na nema ya rufe ta. Tsaki ta dunga yi dan ta san period dinta ne yake kan hanya. A daddafe tayi aikin gidan. Ummi tayi tayi ta bari amma taƙi. Daga ita sai Ummi a gidan, Baffa yayi tafiya tun shekaran jiya amma In Allah ya yarda yau zai dawo. Sadiya da Mimi kuma na makaranta. Haka dai ta samu ta gama komai, kafin la'asar zazzabi ya rufe ta.
A ɗaki ta kwanta, taƙi taje ta faɗa ma Ummi. Sai da su Mimi suka dawo wurin ƙarfe hudu su ka ganta a kwance tana juye juye.
"Adda lafiya?" Sadiya ta tambaya, hankalinta a tashe. Maimoon ko magana bata iyayi saboda azaba.
"Mimi, kira Ummi da sauri." Da gudu Mimi ta fita, ba'a ɗaɗe ba sai gata ta dawo da Ummi. Sadiya har ta fara hawaye, ganin Addan su a halin nan kullum tada mata hankali ya ke yi.
Ummi ma duk ta ruɗe. "Kin cika taurin kai, tun ɗazu baki da lafiya amma baza ki faɗa ba. Kin san yanda abun nan yake miki amma baza ki tanada magani ba. Mai yasa kike haka Maimunatu?"
Ita dai azaba ta hana ta magana, haka take fama ko wani wata. Duk lokacin watan ta haka za tai ta fama da ciwon mara, ciwon baya, ciwon kai, zazzabi da sauran su, wani lokacin harda su suma.
"Sadiya je ki haɗa mata ruwan wanka, Mimi duba cikin jaka ki dauka kudi ki siyo mata magani."
Ko waccen su da sauri ta tafi yin abunda maihifiyar su tasa su, ita kuma Ummi ta gyara wa Maimoon kwanciya, ta daura kan ta a cinyar ta tana shafawa a hankali.
"Ummi na haɗa," Da taimakon Sadiya, Ummi ta kai ta banɗaki. "Ki tabbata kin gasa jikin ki sosai."
Ita dai bata san yanda akayi tayi wanka ba har ta fito lafiyar ta ƙalau bata fadi ƙasa ba, dan harta cinyoyinta ciwo suke, har wani karkarwa suke yi. Ummi ce ta taimaka mata ta shirya, sannan ta kawo mata abinici. Ɗan kaɗan taci abincin dan kwatakwata bata sha'awar ci, dan ma Ummi ta tsare ta.
Duk a takure take, kunya ta lullbe ta. Da dai sun barta ta ji da kanta, wannan ba sabon abu bane amma ko yaushe sai sun tada hankalin su, yaci ace sun saba yanzu ai.
"Tashi ki sha magani." Maimoon kaman tayi kuka, ta tsani haɗiyan magani, gwara a mata allura. Haka dai ta daure ta sha, a hankali bacci ya dauke ta.
Ummi kusan gadin ta tayi, duk sanda Maimoon ke ciwon nan hankalin ta tashi yake. Sunje asibiti, likitan tace ba komai bane, kashi araba'in cikin ɗari ana samun mata da menstral cramps din su ke tsanani.
Da ta tashi ta ɗan samu sauki, tasan ita da dawowa dai-dai sai nan da ƴan kwanaki. Gashi tasan Ummi bazata barta tafita ba. Dole ta kira Habiba ta faɗa mata abunda ake ciki.
"Wayyo, Allah ƙara sauki. Zan kira in faɗa dalilin rashin zuwan ki."
"Yawwa Habiba, nagode."
"Bakomai, Allah ƙara sauki, sai nazo dubiya."
"Ke dallah ba ciwo nake yi ba, kaji fa, wai dubiya. Sai kace wata mara lafiya."
"Lafiyar ki ƙalau yanzu?" Maimoon shiru tayi, bata ba ta amsa ba. Ƴar hira suka ɗan taɓa sannan suka ma juna sallama.
Tana zaune taji muryan Ummi ta na sallama, hannun ta dauke da tray. Murmushi Maimoon tayi tana kallon mahaifiyar ta har ta zauna. "Sannu Maimu, ya jikin?"
Ita abun ma kunya yake bata, ba dama ace lokaci yayi sai kowa ya sani, har Baffa da.... Wani zugi taji zuciyar ta ta fara, da sauri ta kawar da tunani.
"Ummi ni fa garau nake." Ummi murmushi tayi, sannan ta miƙa mata abincin. Macaroni ne da miya. Wannan karan taci abincin sosai, saboda yunwa take ji.
"Ummi Baffa bai dawo ba?" Sai yanzu ta tuna yaci ace ya dawo.
"Wani aiki ya rike su kuma wai, sai nan da kwana biyu." Ummi ta amsa tana girgiza kai. Ita batasan mai zataji game da lamarin ba, daɗi zata ji Baffan su ya fara samun aiki, ko damuwa zatayi da nisa dasu da yayi.
"Ummi in sha Allah zai dawo lafiya." Maimoon tace kaman tasan abunda ke damun mahaifiyar ta. "Allah yasa."
Suna nan zaune Mimi da Sadiya suka shigo dauke da plate din abinci. "Adda Moon ya jiki?" Suka tambayi ƴar uwar su cike da kulawa.
Murmushi tayi musu. "Da sauki ƴan biyun Ummi." Tace cike da tsokana.
Haka Ummi ke ce masu wata sa'in saboda alaƙa mai karfi dake tsakanin su. Nan aka bude shafin hira. Hira suke hankalin su kwance, cike da so da ƙaunar juna. Ummi na bada labarin yarintan kowa.
"Mimi ƙyuyar tsiya gare ta. Ba wanda ya isa ya dauke ta, har Baffan ku wata sa'in."
Dukkan su suka yi dariya banda Mimi da ta zumburo baki gaba. Haka Ummi tai ta basu labari har aka kira sallan Maghriba.
Sai a lokacin Maimoon ta fita. Da taje bayi har ta fara bata jikin ta, ruwa ta ɗaura, sannan tayi wanka ta kimtsa kanta. Da kyar bacci ya dauke ta saboda ciwon da cikin ta da kanta ke mata.
Haka tai ta fama har kwana shida, kafin ta samu sauki. Kwanan Baffa uku da dawowa ya kwanta bai da lafiya. Hankalinsu duk a tashe yake. Sunyi dashi akan a tafi asibiti amma yaƙi. Sai haƙura sukayi, suka cigaba da mai addu'ar samun lafiya.
~~~
"Maimunatu!" Daga sama taji Ummi ta kwala mata kira, ko lafiya take kiran ta haka? "Na'am Ummi, ga ni nan zuwa." Da sauri ta rage wutan risho din, sannan ta wanke hannu kafin ta nufi ɗakin su.
"Assalamu alaikum, Ummi—" Bata gama faɗan abunda tayi niya ba wani gigitaccen ƙara ya fitondaga bakinta. Da gudu ta nufi inda Ummi take a tsugunne da Baffa a ƙasa ko motsi ba yayi, babu ma alamar lumfashi a tattare da shi.
"BAFFA! Ummi me ya faru? Baffa ka tashi!"
Bata tsaya sauraren ta ba ta fita da gudu, ba dankwali bare hijab. Ba ta nufi ko ina ba sai sashen Hamma Ashmaan, ta san shi kadai ne zai iya taimaka musu, in ta shiga cikin gida wurin Mommy bata lokacin ta kawai zatayi. Gashi bata da isasshen lokaci dan komi zai iya samun Baffa in har bata yi sauri.
Duka ƙarfin ta tasa tana dukan ƙofar palon shi, saura kaɗan ta faɗi da ya bude kofaf. "Wai waye ke buga mu—Maimoon lafiya?" Hamma Ashmaan ya tambaya a rikice ganin halin da take ciki. Maimoon ba hijab, ba dankwali, aiko akwai matsala babba.
"Hamma...Baffa...ka taimake mu..B-b-baffa kar ya mutu, Hamma Ashmaan dan Allah." Ƙara rikicewa Ashmaan yayi.
Da gudu suka koma bangaren su Maimoon. Har yanzu Baffa ko motsi ba yayi, ba alaman rai a jikin shi.
Hamma Ashmaan ne ya ɗauke shi ya kai shi mota. Maimoon da Ummi suka sa hijabai suka bishi. Mai gadi tuni ya bude get, ganin halin da Ashmaan ya fito da Baffa.
Mommy na kallo amma ba tayi yunƙurin taimakawa, sai ma taɓe baki da ta yi. Sai mita ta keyi akan Ashmaan zai dawo ya same ta.
Gudu kawai Hamma Ashmaan yake yi. Da yardar Allah suka iso Garkuwa specialist hospital lafiya. Emergency room aka tafi da Baffa. Maimoon ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai safa da marwa take a reception ɗin.
"Moon zo ki zauna." Hamma Ashmaan yayi magana a sanyaye. Maimoon kallon shi kawai tayi, ido cike da kwalla. Ummi ma na zaune a gefe tana hawaye.
Hamma Ashmaan tashi yayi ya koma kusa da Ummi. "Ummi addu'a zamu mai, ba kuka ba. In sha Allah ba abinda zai same shi." Daga kai kawai Ummi ta iya, sannan tasa hannu ta goge hawayen, amma basu daina zuba ba. Yanzu in Baffan su ya mutu ya zatayi? Wa take da shi? Ita da bata kowa sai Allah, sai shi da yaran da Allah ya azurta su da su.
Maimoon kasa zama tayi. Waje ta fita, ta nufi masallacin asibitin ta dauro arwalla sannan ta hau darduma ta fara sallan nafila. Kuka take yi Allah ka ba Baffa lafiya, Allah kar ka dauke mana shi, Ya Hayyu Ya Qayyum!
Saida taji ta samu natsuwa sannan tayi sallama, amma bata bar masallacin ba, addu'o'i ta zauna ta dinga yi. Tana cikin yi ƴar wayar ta Nokia mai torchlight tayi ƙara. Ganin kiran Ummi ne sai bata dauka ba amma ta nufi cikin asibitin. Gaban ta sai faduwa yake yi. Kar taje ta tarda Baffa ya rasu, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Haka dai ta nufi asibitin cike da fargaba da tsoro.
Da Hamma Ashmaan ta fara haɗuwa. Yanayin shi baiyi kaman na wanda aka wa mutuwa ba, sai hankalin ta ya ɗan kwanta. Amma ba zai gama kwanciya ba sai taga Baffa da idanunta.
"Yawwa Moon ke na fito nema. Muje ga ɗakin da aka kai shi chan." Suna isa likita na barin ɗakin, Hamma ya tsaya suna tattaunawa ita kuma Maimoon ta nufi wurin gadon Baffa.
Yana kwance yana bacci. Sai taga kaman an kara mai shekaru, a ƴan awanninnan har ya ƙara tsufa. "Allah ya baka lafiya Baffa," ta faɗa a sanyaye kafin ta juya gun mahaifiyar ta. "Ummi mai likitan yace ya same shi?"
Sai da Ummi ta dau dan lokaci kafin ta bata ansa. "Zuciyar shi ce ta kusan bugawa." Salati ta yi. "Amma dai ba wata matsala ko Ummi?" Ta tambaya muryan ta na rawa. Girgiza kai Ummi tayi. "Alhamdulillah, mun iso akan lokaci. Ba abunda ya same shi."
Daga nan ba wanda ya sake cewa komai. Kowa da abunda ke mai yawo a kai. Bayan wurin mintina arba'in Hamma Ashmaan ya dawo. Da sallama ya shigo, a hankali suka amsa. A kujerar plastic ya zauna, ya duba me jiki. Ummi kadai ta iya amsawa.
"Ummi an baku gado," ya faɗa yana miƙewa tsaye. Kai kawai ta iya dagawa. "Ni da Moon za muje gida mu dauko abunda zaku buƙata."
"To Ashmaan, bamu da abunda zamuce sai Allah ya sanya..."
"Haba Ummi," Ashmaan yayi saurin katse ta. "Babu godiya a tsakanin mu. Ummi nima fa danki ne, in kina mun godiya sai inga kaman baki dauke ni kaman su Maimoon ba."
Kasa magana tayi, wani abu ya tokare mata maƙogaro, da kyar ta samu tace, "To shikenan ɗa na, Allah ya maka albarka." Ameen Ashmaan ya amsa. Ummi ta mai murmushi sannan ta maida idanun ta kan Maimoon. "Maimoon tashi kuje."
Kaman wanda kwai ya fashewa a ciki, haka take tafiya har suka kai bakin mota. Shi ya bude mata gidan gaba ta zauna. Tunda ta shiga motan waje take kallo, hawaye na zuba daga idanunta. Yanzu da Hamma baya nan ya za suyi?
"Moon?" Ya kira da tattausar murya, hawayen ta na damun shi. "Please ki bar kukan haka. Dan Allah ya isa, Baffa is fine and in sha Allah babu abunda zai same shi. Addu'a zaki dinga mai, Allah ya ƙara mai lafiya. Shi kaɗai yake buƙata."
Kai ta daga, sannan ta goge fuskar ta. Idanunta duk sunyi ja, gashin idon sun jiƙe da hawaye. Ashmaan ya shagala da kallon ta ta gefen idon shi har ya kusan faɗawa rami.
"Hamma Ashmaan, ban san da wasu kalamai zan fara gode ma ba..."
Da sauri ya dakatar da ita ta hanyan daga mata hannu. "You're treating me like an outsider, kina dauka na kaman bare, ni fa ɗan uwankin ne Moon, yayan ki, jinin ki. Babu godiya a tsakanin mu, kinji? Daga yau bana so ki sake gode mun in na miki abu."
"Allah ya saka da alkhairi, Allah ya baka mata ta gari." Addu'o'in ta sun mai ɗaɗi, bai san sanda murmushi ya bayyana a fuskar shi ba.
"Ameen Moon."
Da suka isa, Maimoon ta nufi side dinsu, shi kuma ya nufi cikin gida. Kitchen ya fara zuwa, ya ce wa mai aikin ta daura mai girkin da zai kai wa su Baffa.
"Sannu Ashmaan!" Muryar Mommy ta daka mai tsawa. "Me kake mun a kitchen? Daga ina kake?"
"Mommy Baffa ne ya samu attack na kai su asibiti. Ku shirya muje ku duba shi."
"Dallah yi mun shiru!" Ta daga mai hannu. "Kai ban san wani irin kunne gare ka ba. Kullum in ta nanata abu ɗaya. Nace ka fita harkar Rabi'atu da iyalin ta amma baka ji."
"Haba Mommy! Wai meye haka? Ta ya zaki ce in fita harkarsu. Ƴan uwan mu ne fa. Da Daddy da Baffa uwar su daya uban su daya..."
"Ka mun shiru nace. Ka kiyaye ni fa Ashmaan. Yaro sai kace wanda aka ma asiri, ko ma an shanye mun kai ne?"
Ran Ashmaan yayi matuƙar baci, bai sake cewa mahaifiyar shi komai ba ya fita. Yana ji tace wa mai aikin ta kashe abunda aka daura. Ya rasa yaushe lamuran gidansu zasu gyaru. Wai ace kana hantarar ɗan uwanka, in baka taimaki ƴan uwanka ba to wa zaka taimaka? Baya ganin laifin kowa sai na Inna, ita ke goyon bayan Daddy da Mommy su ke wulakanta Baffa da Ummi. Da yanada yanda zaiyi da tuni sun bar gidan nan, sai dai kash! Iyayen shi sun hana, kuma baze iya saɓa ma umarnin su ba. Tun balle Mommy da ke ikirarin tsine mai wata sa'in.
A bangaren Maimoon kuwa, tana shiga gida Mimi da Sadiya suka rufe ta da tambayoyi. Sai da ta danne zuciyar ta kafin ta iya faɗa masu, duka suka sa kuka. Haka ta rungume ƴan kannenta suka yi kukan su tare. Tana jin tausayin kanta da ƴan uwanta da mahaifiyar su in yau aka ce babu Baffa, ko wani hali zasu shiga? Su da basu da kowa a duniyan nan. Ummi ba ta da kowa a duniyan nan, ita kadai iyayenta suka haifa, tunda suka bar duniya kuma babu wanda ya damu da ita. Da sukan je Yola in wani sha'anin ya taso amma tunda wani ɗan uwansu ya buda baki yace sun yafe zumuncin basu ƙara zuwa ba, duk da hakan Ummi kan kira su a gaisa. Ƴan uwan Baffa kuwa da su da babu duk ɗaya. Kai dama ace babu ɗin.
Da kyar ta samu suka bar kukan sannan suka hau shirya masu abinci. Dama Maimoon ta gama miya dazu, yanzu shinkafa kawai ta daura. Ita kuma Mimi ta haɗa ƴan kayan da zasu buƙata su flask din ruwan zafi, kofi, plate da sauran su. Ita kuma Sadiya ta haɗo kayan sawan su.
Ba dadewa Hamma Ashmaan ya shigo. "Har kun shirya." Mimi ce ta ansa mai da eh. "Toh muje."
A tare suka isa bakin motan dake waje, dan ɗazu bai shigo da ita. Sadiya ta tura gaba ita kuma ta shige baya. Ba haka Ashmaan ya so ba amma bai ce komai ba. Kafin suje asibitin supermarket ya nufa, nan ya siyo kayan tea, bredi, da duk abunda ya san zasu buƙata. Sannan yace su Sadiya su zaɓa abunda suke so amma suka ƙi. Ba yanda baiyi da su ba amma suka ƙiya, haka ya haƙura.
Opposite asibitin akwai mai saida fruits, nan ma ya tsaya ya siya kafin su shiga ciki. Da su Sadiya suka ga Baffa a kwance, dan har yanzu bai tashi ba, sabon shafin kuka aka bude. Nanma da kyar Ummi ta lallashe su. Tausayin su ya kama Ashmaan, ya dau alkawarin taimakon su har sai inda ƙarfin shi ya ƙare.
A dage a dinga voting da commenting dan Allah.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro