Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA HAMSIN DA UKU





~
BABI NA HAMSIN DA UKU
~






Karamin abu a wurin ta na nema ya zama babban al'amari. Bata taba zatan fushin da ya yi zai kai haka ba. Wannan satin gaba daya bata je makaranta ba saboda satin gaba daya babu lectures (lecture free week). Da sassafe ya ke fita baya dawowa sai wurin shida, da ya ci abinci zai tafi masallaci nan ma ba zai dawo ba sai an yi isha'i daga nan kuma sai barci.
Suna gida daya amma gaba daya bata ganin shi. Zaman hira da suka saba yi duk babu kullum yana aiki.

Tana zaune ita kadai ta yi jungum jungum. Gobe ne taron ta rasa yanda zata yi, tun dazu ta nemo sunan Ammi a (contacts) dinta amma ta kasa kiranta saboda tana gani ta yi (disappointing) dinta. Dole ta daure ta kirata.

"Ammi ki yi hakuri," Maimoon ta ce bayan sun gaisa hawaye na taruwa a idonta.

"Babu komai Maimoon, dama na yi tsammanin hakan. Kada ki saka abun a ran ki, ya wuce kin ji."

A hankali hawayen su ka sauko fuskarta. Ammin ta bata tausayi sosai, daga jin muryarta ba haka ta so ba.

Ba zata ce ta san yanda Sayfullah ke ji ba saboda bata taba tsintar kan ta a irin halin ba. Amma duk da haka Ammi bata chanchanci haka daga wurin shi ba ko dan kawo shi duniya da ta yi. Allah kullum muna mai laifi yana yafe mana, muma ya kamata mu kamanta hakan tsakanin mu ko dan kwadayin samun rahamar Allah. Bare uwa ai ba abun yardawa ba ce komin ya ta ke kuwa.

Ranta duk a cunkushe ta wuni ranan ko abinci ta kasa ci. Gashi dai tana jin yunwan amma bata son saka komai a bakinta.

Yau dinma bai dawo ba sai karfe shida. Bayan ta mai sannun da zuwa ta shige ofis dinta itama ta bar shi a wurin. Har karfe tara na dare tana ciki bata fito ba.

Bude kofa da a ka yi yasa ta dago kanta. Sayf ne sanye da farar jallabiya tsaye a bakin kofa. "Ba ki gama ba?"

Rubutun ta ta cigaba da yi. "Ban gama ba."

"Dare ya yi ki bari sai gobe mana."

"Bana jin barci."

Kaman zai yi magana ya fasa, "To sai da safe," ya ce yana juyawa.

Hararar kofar ta yi tana gyada kai.

Washegari ta ce mai ya sauke ta gida. Bai tambaye ta mai zata je yi ba itama bata fada mai ba. Dan shi ya ce ba zai je ba ba shi zai hanata zuwa ba.

Ammi ta ji dadin zuwan Maimoon sosai. Sameer ya ja su a sienna su ka biya su ka dauki Kydah a gidan ta sannan su ka nufa wurin da za a gudanar da taron.

Ammi ta janyo Maimoon jikinta sosai dan a kusa da ita ma ta zauna duk wanda ya zo gaisheta sai ta nuna mai Maimoon din tun kafin ma a tambaya wacece ita tunda bakuwar fuska ce. "Diyata ce, matar Sayfullah."

An gudanar da taron cikin walwala da nishadi. Iyaye sun yi nasihu masu ratsa jiki sun kara jaddada muhimmancin zumunci a rayuwar dan Adam, irin tarin ladan da ake samu da kuma kuskuren da ke cikin yanke shi. Rike zumunci abu ne mai wuya musamman a wannan zamani dole sai an daure wurin sada shi.

An ci an sha an yi hotuna domin ajiye tarihi. Yana mata ciwo a ce Sayfullah duk ya rasa wannan, shima ya kamata a ce yana nan cikin 'yan uwa shi.

Wasu mata da suka kasance kakan ni wurin su Sayf sai tsokanar su Waahidah da Kydah su ke yi.

"Wannan kishiyoyin naga sai kiba su ke kara yi, suna cinyewa mai gida dan kudin retire da ya tara ko."

"Ai kuwa dai ga kumatu nan Masha Allah. Allah Ya raya su. Maimunatu in kin je ki ce wa mai gidan ki haka a ke auren ko ziyara babu."

Murmushi kawai ta iya yi. Duk wanda ta hadu da su babu laifi masha Allah duk sun sakan mata fuska. Ana ta tambayanta ina Sayf din ya ke ta ce musu wani aiki ne ya rike shi yasa bai samu zuwa ba. Babba da ita ya sata yin karya.

Tana cikin cin abinci kiran shi ya shigo wayarta. Waje ta fita domin amsa wayar saboda hayaniyan da ke cikin hall din.

"Noor kina ina? Na zo gida Ummi ta ce kin fita."

"Ina tare da su Ammi mun zo wurin event din. Katin na cikin console din motar ka zaka ga address din sai ka zo ka dauke ni."

Runtse ido ta yi tana jira ta ji mai ze ce. Shiru bata ji ya yi magana ta zata ma ya kashe wayar sai da ta duba taga har yanzu yana kan layi. "Hello?"

"Idan na iso zan kira ki fito."

Hamdala ta yi a zuciya, ta ce mai to. Idan ya iso zata san yanda za ta yi ya shigo ko da na minti daya ne.

Bayan kusan awa daya da kiranta Sayfullah ya iso. Wurin cike ya ke da motoci. Chan nesa ya yi parking sannan ya kirata.

Babu dadewa Maimoon din ta fito. Sai da ta girgiza kai ganin inda ya yi parking. A hankali ta bude ta shiga tare da gaishe shi. Kafin ya tayar da motan ta ce, "Ba za ka shiga ba? Tunda ga ka kazo wurin dan Allah mu shiga."

"Noor..."

"I'm asking for much, na sani. Amma ba dan ni ba, ba dan Ammi, dan Allah za ka yi saboda darajar zumunci. Please Habibi. Mu je ka ji?"

Ta bi ta wani marairaice ta tsare shi da idanuwan nan nata ma su rikita shi.

"Please?" Ta sake cewa tana kifta ido.

Ajiyar zuciya Sayf ya yi yana fata kada abunda zai yi ya zama kuskure. "Minti daya kawai zan yi."

Har wani dan tsalle ta yi tana tafa hannu. Kai ya girgiza ya bita a baya. Suna shiga ciki hankalin kowa ya dawo kan su, a take ya fara tunanin mai yasa ma ya biyewa Noor din ya yarda. Saidai yanzu ya rika da ya shigo dole ya daure ya cigaba da takawa.

Tebur din Ammi ke zaune Maimoon din ta kai su. Ammi sai kifta ido ta ke yi dan ta kasa gazgata abunda ta ke gani. Dagaske Sayfullah ne? Juyawa ta yi ta kalli Maimoon da ke gefen shi sai murmushi ta ke yi. Maimoon din ta gyada kai kaman ta san mai Ammin ke tunani.

Minti daya ya koma awa daya dan kuwa an ki bari su tafi. Mutanen da Sayf ba zai iya tuna rabon da ya gan su  ba yau ya gan su. Wasu ya gane su wasu kuma saida a ka tuna mai. Tare da su a ka tashi taron daidai ana kiran sallah.

Bayan an fito daga hall din a ka tsaya waje ana ta hotuna. Kowa na ta so a dauke shi tare da Sayf wasu na cewa gwara su dauka dan ba su san ranan da za su sake ganin shi ba kuma.

Daga nan kuma duk a ka shiga mota a ka kama hanya. Maimoon ta nufi motar Sameer don raka Ammi dole Sayf ya bita. Ita ta budewa Ammi kofa ta shiga.

Bayan Ammi ta shiga ta kalle su sosai tana ji farin ciki na ratsa ta. "Nagode, nagode sosai."

Sai kuma Sayf ya ji jikin shi ya yi sanyi yanda tun dazu ta ke ta mai godiya. Murmushi kawai ya iya yi mata yana jin ran shi babu dadi.

"Saida safe Ammi." Maimoon ta ce.

"Saida safe Maimoon."

Sauran 'yan uwanta ta yi wa saida safe. Sayf shima ya yi tare da gaisawa da Sameer. Suna tsaye har motar su ta bar wurin kafin suma su ka nufa ta su motar.

A hanyar su ta komawa ba su yi wata hira ba Sayf nata sakawa yana kwancewa a zuciyar shi. Ko da suka isa gida Maimoon ta tambaye shi mai za a kawo mai ce mata ya yi ya koshi.

Ganin yana bukatar ya kebe ya sa bata bi shi daki ba.

Bayan sun gama shirin kwanciya Sayf ya zauna ya jingina da allon gado. "Noor," ya kira ta a hankali.

Ajiye kayan da ta ke linkewa ta yi ta juya ta kalle shi. Hannu ya mika mata ta ji zuciyarta ta cure wuri daya musamman da taga yanayin fuskar shi. A hankali ta taka sannan ta sa hannunta duka biyu a na shi, gab da shi ya zaunar da ita.

"Ki yi hakuri," ya ce yana matsa mata hannu. "Ki yi hakuri yanda na yi behaving kwanakin nan. Na rasa mai ke damuna kuma bana son hakan ya shafe ki ko dangantakar mu shi ya sa na yanke hukunci yin nesa da ke. I'm sorry."

"Are you okay?"

"To," ya sauke ajiyar zuciya. "Alhamdulillah za a ce."

Dauke idon shi ya yi daga kanta. "Na dawo makaranta wata rana banga mahaifiyata ba. Na zata ko ta fita ne amma har dare ya yi bata dawo ba. Na yi kukan na yi kukan har na gaji amma babu wanda ya fada mun ina ta tafi. Mahaifina da ya kamata ya janyo ni ya rarrashe ni shima bai yi ba ya barni hannun masu aiki. Nasan dai ta kwana a gidan tunda ita ta sa ni bacci to ina ta tafi. That was the last time I saw her, sai bayan shekara bakwai."

"A tsakanin shekarun nan wani irin tsanarta ya dasu a raina. Saboda a lokacin na yi tunanin da tana nan da wasu abubuwan ba su same ni ba. Alhaji ya kara aure, abubuwa su ka kara tabarbarewa. Noor ina kwana uku ban ci ko kwarar shinkafa daya a gidan ba sai dai idan na je makaranta Habib ya bani abincin shi. Alhaji baya zama kullum yana wasu kasashen bai damu da wani hali na ke ciki ba. Mami ta so tafiya dani amma Alhaji ya hana. Ban sake ganin Ammi ba sai da na shekara sha biyu, shima Mami ce ta kai ni Katsina wurinta ta zo hutu. Zuciyata ta karye da na ganta da wasu yaran, ni ta tsana shi yasa ta tafi ta samo wasu. It made things worst."

Maimoon ta ji itama zuciyarta ta karye. Tuni hawaye su ka cika mata ido. Magana ya ke yi cike da kunci da ciwo.

"Inada shekara sha hudu Ammah ta zo ganin likita a Kaduna ganin mawuyacin halin da na ke ciki ya hanata komawa, dalilin dawowarta Kaduna kenan. Zuwan Ammah ne ya kawo cigaba a rayuwata, gaba daya ma sashenta na koma. Haka har nagama secondary school na samu admission a ABU International relations. A nan ne kuma na so in fara biyewa abokan banza, ganin haka Mami ta dage dole sai na koma wurinta. Wannan karon dole Alhaji ya yarda tunda Ammah ma ta goyi bayan hakan. Mami tried to fix things amma bai yiwu ba. Bana mantawa lokacin da naje wurin ta a Katsina Sameer ya yi zazzabi, ba ki ga yanda hankalinta ya tashi ba, ta kasa motsawa daga gefen shi. Ta san irin ciwon da ni na yi? Wa ya kula da ni?"

Maimoon ta fashe da kuka tana boye fuskarta a kirjin shi.

"Mahnoor," ya furta a hankali yana shafa mata baya. "Ban fada miki ba dan ki yi mun kuka. Sai dai ina son ki yi kokari ki fahimce ni idan na ce miki bana son yin maganan. A duk sanda na tuna ina jin wani irin ciwo a zuciyata, ina komawa wani iri. I don't like the person I turn into. Shi yasa na ke nesa da ita da duk wani abu da zai tuna mun."

Kuka sosai Maimoon ta yi tausayin shi na mamaye gaba daya. Sai ta tuna lokacin da ta ke jin tausayin Baffa idan Inna ta yi mai halin da ta saba. Shima kusan haka ne ya faru da shi.

Janye jikinta ta yi ta dube shi. "Ka yi hakuri," ta furta zuciyarta na karyewa tana hango karamin yaro ya na kuka yana neman mahaifiyar shi. "I'm so sorry Habibi."

Murmushi ya yi mata mai kunshe da ciwo. Share mata hawaye ya yi. "Ya isa haka, kwanta mu yi barci." Tana jikin shi su ka kwanta sai dai shi sam barcin ya ki zuwa.

Tunani kala kala ya ke yi game da rayuwar shi. A kasan ran shi ya sani abunda ya ke yi baya kyautawa sai dai kuma idan ba hakan ba bai san ya zai yi ba. A ganin shi yin nesa da ita shine mafita a gare shi. Saboda a duk sanda ya ke kusa da ita yana komawa wannnan karamin yaron nan da ba a so ba. The unwanted child.

Tun wannan lokacin Sayfullah ya kasa samun sukuni. A da ya kan manta da Ammi na nan ma musamman kafin auren su. Amma banda yanzu, dan ko ya so mantawa ba zai yiwu ba. Hakan ya ke sa shi tunane-tunanen da ba ya so.

Ba ya son ya samu Maimoon da maganan saboda a ganin shi wannan matsalar shi ce shi kadai, dole ya samarwa kan shi mafita ba tare da ya daura mata (unnecessary) nauyi ba. Lokaci ya yi da zai kulle wannan babi na rayuwar shi gaba daya. A haka ya ke so ya karasa rayuwar shi? Amsar a fili ta ke. Saidai a duk lokacin da yayi kokarin yin hakan ciwon da zuciyar shi ke yi na tsananin da ba ya iya daurewa.

Sayfullah ya samu mutum daya da ya zan zata saurare shi kuma zata fahimce shi. Bai boyewa Mami komai ba sai wasu abubuwan da ya san sirrin shi ne bai kamata ta sani ba.

"Mami bana son in cigaba da rayuwa a haka."

Mami ta gyada kai tana kokarin hadiye kukanta. Bata son ta sakar mai da gwiwa. "Alhamdulillah Sayfullah. I'm so proud of you. Hakan da ka yi shine daidai. Ka dage da rokon Allah Ya kawo maka sauki a dukkan al'amuran ka. Akwai wani therapist that was highly recommended, idan ka shirya sai in hada ka da shi. Zaka iya yin sessions din online ko kuma one-one physically."

Dan jum ya yi na dan wani lokaci. "Na shirya." Ya yanke shawaran yin komai online din. Tunda Mami ce ta yi recommending bai da shakku ko kadan.

Wani karamin kati ta mika mai. Ya karba yana jujjuya shi. Dr. Suleiman Sale Shinkafi. Wallet din shi ya ciro ya adana katin a ciki. Ido ya daga ya kalli Mami yana jin kimarta da darajarta na karuwa a zuciyar shi.

"Nagode Mamina."

"Tashi ka tafi Sayfullah." Ta ce tana nuna mai kofa.

"Nagode, Allah Ya saka miki da alkhairi. Ya saka ki a aljannah firdaus..."

"Na ce ka tashi ka tafi ko?" Ta sake cewa muryarta na rawa.

Hannuwanta Sayfullah ya kamo yana murmushi. "Nagode da baki tafi kin barni ba. Ke kadai ce baki gaji dani ba Mami."

Hawayen da Mami ta so hadiyewa tuni suka sauko. "Ina son ka sosai Sayfullah dina."

"Nima ina son ki sosai Mami na."

Bayan ya baro dakin Mami ya ciro wayar shi tare da katin da ta ba shi. Zuciyar shi kaman zata fito yayin da wayar ke ringing. Babu dadewa a ka dauka.

"Salamu alaikum, sunana Sayfullah Abdur-Rahman Hambali and I will like to make an appointment......"

****

Zaune ya ke gaban laptop din shi tun dazu. Link kawai zai dannan ya sada shi da likitan amma ya kasa.

Furzar da iska ya yi sannan ya danna. Nan da nan kiran ya yi connecting. Dr Suleiman Sale dattijo ne mai kimanin shekaru hamsin a duniya. Sam Sayfullah bai yi tsammanin haka zai gan shi. Sun hadu da ya je (confirming appointment) din shi saboda haka ka'idar likitan ta ke, ko da online za ka yi session din sai ka je ofishin shi.

"Assalamu alaikum. Da fatan ka wuni lafiya. Sunana Dr. Suleiman Sale Shinkafi."

"Wa'alaikumus salam. Alhamdulillah. Sunana Sayfullah Abdur-Rahman Hambali."

"Madallah Sayfullah. Kafin mu fara zan kara jaddada maka cewa tattaunawan da za mu yi har zuwa karshe zai zama confidential. This is a safe space for you to explore your thoughts and feelings without judgment. Akwai wani abu da kake son yin magana a kai yau ko kuma kana so ka fara bani dan labari a kan ka?"

"Nagode Dr. Inaga zan fara da baka labarin yanda na taso. Na dade ina yawo da weight din watsar dani da iyayena su ka yi ina karami. Kuma ya dade yana affecting dina amma na ke ture matsalar gefe. Bayan na zauna na yi tunani naga lokaci ya yi da zan shawo kan matsalar har in rabu da ita da yardan Allah."

"Hakane. Ka yi daidai Sayfullah. Zan saurare ka da kunnen basira kuma in baka goyon bayan da zaka bukata. Yanzu zamu fara da fahimtar abunda ya faru. Zaka iya fada mun yaushe su ka watsar da kai kuma ta yaya?"

Sayfullah ya runtse ido kafin yayi gyaran murya. "Ya faru inada shekara uku. Iyayena sun rabu sai mahaifiyata ta tafi ba tare da bayani ba. Kawai na wayi gari bata gidan. Mahaifina kuma ya maida duka hankalin shi kan aikin shi bai damu dani ba. I felt so alone and unwanted."

Dr Suleiman ya jinjina kai. "Wannan abu ne mai wuyar gaske ga ƙaramin yaro. Dole za ka ji an watsar da kai kuma ba a son ka idan aka yi la'akari da yanayin. Ta yaya wannan abin ya shafe ka yayin da kake girma?"

"Eh toh...."

Sun tattauna na tsawon minti hamsin. Daga karshe Dr Suleiman ya kara ce mai ya kwantar da hankalin shi, zai taimaka mai wurin cin ma burin shi. Sun amince zasu rika haduwa duk bayan sati biyu ranan alhamis.

***

"Abunda na ke so ka gane Sayfullah shine, barin ka da iyayenka su ka yi ba laifin ka bane. Laifin ya rataya a wuyan su ne ba naka ba."

Sayfullah ya jinjina kai. Ya fahimci hakan. "Wani lokaci ina jin kamar ya kamata in shawo kan lamarin zuwa yanzu. An yi shekaru da yawa."

"It's completely normal ka ji haka, warkewa daga (trauma) yana daukar lokaci. It's a gradual process."

***

"Me yasa ka fi jin zafin abunda mahaifiyar ka ta yi a kan mahaifin ka? A ganin ka laifin su ba daya bane?"

"Ba daya bane. In a twisted way Alhaji bai yarda ni gaba daya ba duk da bai sauke duka nauyin da ya rataya a wuyan shi ba. Amma Ammi..."

"Cigaba ina sauraron ka."

"Ita uwa ce. Uwa aka sani da tausayin yaranta amma ta iya tafiya ta barni na tsawon lokacin nan."

"Ka ce ta sake aure kuma ta haifi yara?"

"Eh hakane, ta haifi yara uku bayan rabuwarta da mahaifina."

"A lokacin da ka gano hakan yaya ka ji?"

"Raina ya baci sosai. Hakan ya kara tabbatar mun cewa ni din ne bata so, akwai wani abu a tattare da ni da yasa ta ki ni."

"Yan uwanka fa? Ya ka ji game da su?"

"Na ji haushi kuma na yi kishi saboda suna samun kulawa da kaunar da nake so amma ban samu ba."

"Har yanzu haka kake ji game da su?"

"A'a. Not anymore."

***

"Alhamdulillah Sayfullah kana ta making progress Masha Allah. Ayyukan da na baka kuma duka na gamsu da response din ka. Aikin ka na yau shine positive affirmation. A psychotherapy wasu jimloli ne da zaka rika maimaitawa a ko da yaushe da zai ƙarfafa maka tausayin kan ka wato self-compassion. Sai dai mu musulmai addini ya tanadar mana da addu'o'i da zikiri da zamu rika maimaitawa ko da yaushe musamman a lokacin da muka tsinci kan mu a mawuyacin hali. Saboda haka Sayfullah ina son ka kara rike adhkar din ka."

"In sha Allah doctor."

Daga nan su ka yi sallama, Sayfullah ya rufe laptop din shi. Furzar da iska yayi yana kallon ofis din shi wanda a nan ya ke (sessions) din shi.

Alhamdulillah. Yana ganin cigaba sosai tun fara ganin Dr. Suleiman Sale Shinkafi. (Mental health) wanni fanni ne na lafiyar dan Adam da ba a cika kula da shi ba musamman a wannan yanki na duniya. Wanda hakan ba karamin kuskure bane. Lafiyar kwakwalwar na da mahimmanci kamar lafiyar jiki.

Wayar shi ta yi kara. Yanzu haka Noor ce dan lokacin tashinta daga makaranta ya kusa. Yana dubawa kuwa yaga ita din ce ke kira. Saidai da ya amsa ya ji tana kuka. Da sauri ya mike yana tambayar lafiya.

"Habibi...."

"Mahnoor menene? Fada mun? Me ya same ki? Me ya faru?"

"Habibi Ammi ta yi hatsarin mota."










🙊🙊


Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro