BABI NA HAMSIN DA HUDU
~
BABI NA HAMSIN DA HUDU
~
Akwai wani abu da ake kira da 'out of body experience' inda za ka ji kaman wani ya ari jikinka yana amfani da shi kai ka koma gefe kana kallo.
Hakan ne ya faru da Sayfullah. Tunda Maimoon ta fada mai abunda ya faru a waya bai san takamaimai me ya faru bayan nan ba. Ya san dai ya iso asibiti inda ya tarar an yi cirko-cirko ana jiran likita ya zo yayi musu bayanin halin da Ammi ke ciki.
Ammi ta fita unguwa ne a hanyar dawowa wani mai mashin ya gitta musu hakan yasa motar ta subucewa dreban suka fada gefen titi. Motar ta fadi ta gefen da Ammi ke zaune shi yasa nata raunin yayi tsanani. Shi dreban buguwa ce sai kurjewa da yayi kadan a hannu.
Sayfullah na zaune a kan kujerun da ke jere a (reception) din asibitin. Tunda ya zo bai zauna ba saida ya ji jiri na nema ya kada shi. Maimoon na zaune a gefen shi ido ya yi ja jawur tun dazu take kuka amma baida karfin rarrashinta.
"Mamana kukan ya isa haka, addu'a za ki yi," inji Baba Nasir. Tun dazu ya ke ta kokarin kwantar musu da hankali amma shima daga gani hankalin shi a tashe ya ke.
Lokaci sam ya daina yi musu sauri, mintin su talatin a wurin amma ji su ke yi kaman sun shekara. Maimoon da Waahidah na zaune sun yi tagumi, yayin da Sameer da Sayfullah suke ta safa da marwa a wurin.
Sameer ya dauko Waahidah da Maimoon daga makaranta aka kira a ka sanar da shi abunda ya faru. Nan da nan shima ya kira Baba Nasir ya sanar da shi abunda ya faru kafin ya dauki hanyar asibiti. Kusan tare su ka iso da Baba Nasir din da ya zo daga ofis shima.
Sauran 'yan uwa suna gida, tun dazu Jaddati ke kiran Baba Nasir din ya ki dauka. Chan sai ga Baba Abdullahi ya zo shima ya bar Baffa tare da matan.
Likitan na fitowa duka suka mike.
"Likita me ye condition din ta?" Sayfullah ya tambaya yana fargabar amsar da zai bada.
"Ku kwantar da hankalin ku mun shawo kan matsalar she is out of danger. Ta samu fracture a hannunta na dama sai kuma buguwa da ta yi. Saboda buguwa da kanta ya yi ta samu mild concussion. Mun yi sedating dinta yanzu dan ta samu hutu, zata farka bayan awa biyu ko uku."
Duka su ka yi hamdalah sannan su ka yi wa likitan godiya. Baba Nasir ya bishi ofis tare da Sameer.
"Hamma?" Wahidaah ta kira Sayf. Bai ji ta ba sai da ta sake kira. "Ga ruwa."
"Nagode," ya ce yana karban goran ruwan daga hannunta.
Kai ta gyada mai sannan ta nufi wurin Baba Abdullahi dake shirin tafiya.
Maimoon na zaune kusa da Sayfullah har ya gama shan ruwa. Bai rufe ba ya mika mata. Kadan ta sha ta ajiye.
"In kai ki gida?"
"A'a."
"Kin tabbata?"
"Eh."
Bayan awa uku kaman yanda likita ya ce Ammi ta farka. A lokacin wurin karfe biyar na yamma. Kydah da mijinta Bilal sun zo. Sauran 'yan gidan Baba Nasir ya ce su yi hakuri sai gobe. An maidata private ward. Baba Nasir na ciki likita ya shiga ya dubata.
"Za ku iya shiga," ya sanar da su bayan ya fito. "Amma mutum biyu a lokaci daya kuma kar a yi hayaniya dan Allah. Allah Ya bata lafiya."
"Hamma ka shiga kai da Adda." Inji Sameer.
Sayfullah ya kalle shi da mamaki, yana kokarin cewa a'a yaga saura suna kada kai alamun sun yarda. Kai ya dagawa Sameer din su ka shiga tare da Maimoon.
Ammi na kwance hannunta na dama an daure shi da (cast), kanta kuma an nade shi da (bandage). Zuciyar Sayfullah ta sake karyewa. A hankali ya taka zuwa gefen gadon.
Duk da halin da ta ke ciki bai hanata yi mai murmushi ba. Hannunta mara ciwon ta ke kokarin dagawa Sayf ya riko shi a hankali. "Sannu Ammi."
"Sayfullah...." ta furta a hankali. Hannu ta daga da kyar ta shafa fuskar shi. "Sayfullah ka yi hakuri...." Da kyar take iya maganan.
Sayf ya girgiza kai. "Ya isa Ammi. Ki yi shiru, you need all the energy you can get."
Kwalla har sun tarun mata a ido. "Na kware ka, ban kyauta ba. Da na mutu mai zan je in cewa Ubangiji? Abunda na yi ta tunani kenan. Na kasa rike amanar da Allah Ya bani."
"Amma ya isa haka.."
"Ka yafe mun Sayfullah, ni da mahaifin ka mun kware ka. Mun bari matsalolin da ke tsakanin mu sun shafe ka. Ka sani ba laifin ka bane, laifin namu ne. Ka yi hakuri Sayfullah, ka yi hakuri."
Kokarin hadiye hawayen shi ya yi amma sai da wasu su ka zubo. Ganin haka ya sa Ammi ta share mai su da hannunta. Sayfullah ya runtse ido yana ji zuciyar shi a cunkushe.
"Ki huta Ammi, bari in kira sauran," ya ce yana kokarin mikewa.
Hannu shi da ke cikin nata ta rike gam tana girgiza kai. "A'a, kar ka tafi."
Komawa ya yi ya zauna sai a sannan ya lura Maimoon bata dakin. A waya ya kirata ya sanar da ita yanda ake ciki.
Sayfullah na zaune gefen Ammi duk sauran su ka shigo su ka dubata. Babu wanda ya ce komai amma daga gani an san Sayf ya sha kuka saboda saman hancin shi ya yi ja jawur.
Sai karfe tara na dare su ka bar asibitin. Gaba daya baya jin karfin jikin shi da kyar ya ke tuka motar. Suna isa ya kulle kan shi a daki, wannan karon bai hana kan shi kuka ba. Kalaman Ammi na ta mai yawo a kai. Ji ya yi kaman ana warware daurin da aka yi mai a zuciya.
***
Kwanan Ammi uku a asibiti. Kullum Sayf sai ya je kafin ya tafi wurin aiki, idan ya taso da yamma ma ya biya. Ta samu sauki sosai duk kumburin ya ragu sai dai ciwo da jikin ke yi har yanzu.
Ranan da aka sallameta a motar shi ta koma gida.
Sayfullah na kokarin amfani da (techniques) din da Dr. Suleiman ya bashi wuri mu'amala da mahaifiyar shi. Baya bari tunanin da ya saba yi a baya ya yi tasiri a kan shi yanzu, wanda a da da ya fara tunanin zai ji kaman abun ya dawo mai sabo. Amma yanzu kam alhamdulillah, baya jin bai iya lumfashi a kusa da ita kuma bacin ran da ya ke experiencing ya ragu sosai.
Tasowar shi daga aiki kenan ya tsaya a hanya ya siya gyada na kwalban nan da ake durawa. Da safe Ammi ta ce tana marmarinta.
Bangarenta ya nufa, a dakin da ke kasa ta ke zama. Shigan da zai yi yaga tana kokarin janyo kwano, da sauri ya isa gefenta. Kankana ce yanke a ciki, yasa fork ya dauko ya mika mata.
"Nagode," ta ce da murmushi a fuskarta. Harda zuwan Sayfullah ke kara mata kwanciyar hankalin da take samun sauki sosai.
"Ammi ya aka yi ke kadai? Ina Waahidah?" Ya tambaya bayan ya zauna a kan kujerar da ke gefen gadon.
"Waahidah na da lectures yau bata dawo ba. Mai aikin kuma yanzu ta fita taje kawo mun abinci."
Ba dadewa mai aikin ta dawo dauke da tray din abinci. Sayf ya ce mata shikenan ta tafi. Zuba abincin yayi sannan ya fara ba Ammi.
Ammi ta kasa dauke idonta daga kan shi. Addu'ar da ta dade tana yi yau Allah Ya amsa mata. A duk sanda ta tuna yanda ta tafi ta bar shi sai ta ji tsananin nadama ta lullubeta. Wace irin uwa ce ita da ta iya tafiya ta bar karamin yaro? Tuni hawaye suka cika mata ido. Dan yanzu abu kadan ke saka ta kuka.
"Sayfullah."
Jin yanda ta kira sunan yasa shi saurin waigawa dan yana hada kwanukan ta kira shi. "Ammi lafiya?"
"Hakuri na ke son in sake baka Sayfullah. I am so ashamed of myself...a'a dan Allah ka bari in fada ko zan ji saukin radadin da zuciyata ke mun," ta ce da ya fara girgiza kai. "Babu abunda zan ce da zai yi excusing abunda na yi sai dai ina so ka sani daidai da rana daya ban taba daina son ka ba Sayfullah. Kawai na bari fushin da na ke yi da mahaifinka a lokacin ya rufe mun ido. Da zan iya komawa in chanza hukunci da na dauka da nayi saidai ba zan iya ba. Shi yasa na ke baka hakuri, ni da mahaifin ka mun yi laifi muna fatan zaka iya yafe mana."
"Allah Ya yafe mana gaba daya Ammi. Na fara therapy a while back ya fahimtar da ni abubuwa da yawa wanda a da na kasa fahimta. Abunda ya faru a baya ya riga da ya wuce, fushin mu da bacin rai ba zai chanza hakan ba. Abu daya da zamu iya yi shine mu maida hankalin mu a kan yanzu da gaba. Ba a ce idan abu ya same ka ka ture shi gefe ba, a'a you are allowed to be hurt, to feel the pain. Sai dai kada ka bari wannan (emotions) din sun runjaye ka ka kasa cigaba da tafiyar da rayuwar ka yanda ya dace. Mun bari abunda ya faru a baya ya shafi rayuwar mu for too long. Lokaci ya yi da za mu rufe wannan babin kuma mu ci gaba da rayuwarmu."
Ammi ta fashe da kuka mai ban tausayi. Sayfullah bai hanata, shima da zai samu dama da ya yi. Da ya furta kalaman nan sai ya ji kamar wani tsuntsun keji da aka sake shi ya sake fiffikensa ya tashi. It was freeing.
"Nima ina me baki hakurin duk wani abu da na yi miki da ba daidai ba."
Kai Ammi ta girgiza. "Ba ka yi mun komai ba Sayfullah."
Hannunta Ammi ta bude Sayfullah bai yi dogon nazari ba ya rungume ta. Ammi ta runtse ido. Ga hawaye ga murmushi ta rasa wanda zata yi.
Alhamdulillah Ya Allah!
***
"Da aka sanar da kai Ammi ta yi hatsari, wani tunani ya fara zuwa maka?" Muryan Dr. Suleiman ya isa kunnen Sayfullah ta cikin ear piece din da ya ke sanye da shi.
"Panic. Mami ta taba ce mun in godewa Allah mahaifiyata na raye, akwai mutane da yawa da zasu bada duk wani abu da suka mallaka a duniya da za a ce za a dawo musu da mahaifiyar su ko da na minti daya ne. Maganar bata taba tasiri a kai na ba sai a lokacin da nake zaune a asibitin muna jiran fitowar likita."
"And what did you realize?"
"Muna yawan mancewa kwanakin mu na duniya kullum karewa su ke yi. It hit me hard. Tambayan da na yi ta wa kaina shi ne, 'ya zan yi idan na wayi gari Ammi ta bar duniya?' Ban taba wannan tunanin ba saida accident din ya faru. Na gane fushina da kin yarda da ita baya da amfani saboda in yau Allah Ya dauki ranta zan yi nadamar rashin bata damar gyara kuskuren ta. And I don't want to live with that regret."
"Alhamdulillah, Sayfullah. Ka samu babban cigaba, ba kowa bane ke samun wannan level of self-awareness din a cikin karamin lokaci. Ya ka ji da ka yafe mata?"
"Freeing. It felt freeing and empowering."
"Hakane. Yana daukar kokari mai yawa kafin mutum ya iya yafewa wanda ya mai ba daidai ba. Ina taya ka murna."
"Nagode Doctor."
"Mahaifin ka fa? Wani mataki ka dauka a kan shi?"
"Eh toh, karshen satin nan zan je Kaduna in sha Allah. Shima ina so mu zauna mu yi magana mu fahimci juna. Lokaci yayi da zan bar wannan matsalan a baya in maida hankalina wurin ganin na gina rayuwa mai inganci tare da matata."
"Allah Ya taimaka."
"Ameen Ameen Doctor."
***
A karshen satin Sayfullah ya kama hanyar Kaduna. Yayi tafiyar cike da fargabar ya zata kasance. Kafin ya taho saida ya je wurin Ammi. Ba karamin farin ciki tayi ba da ya sanar da ita ga abunda zai je yi, ta yi ta sa mai albarka.
Bangaren Ammah ya fara nufa bayan isowar shi. Ta yi murnar ganin shi dan bai sanar da ita zai zo ba.
"Ina ka bar Maimunatun?"
"Tana gida, tana gaishe ki."
"Ina amsawa, jiya ma mun yi waya da ita ai."
Sayf yayi murmushi. "Alhaji fa?"
"Wani Alhaji?" Ammah ta kalle shi kaman bata fahimci wa yake nufi ba.
"Baba, yana nan?"
"Au to wai Abdur-Rahman. Ka ce mun wani Alhaji kaman a kasuwa. Dazun nan ya tafi wurin wani taro, nan ba da dadewa ba za ka ji shi ya dawo."
Sai yamma Alhaji ya dawo. Shima yayi mamakin ganin Sayfullah. Tare su ka ci abinci dare a falon Alhaji wanda hakan ya sake ba shi mamaki dan Sayf idan ya zo wurin Ammah ya ke cin abinci, da ya shigo ya gaida Alhaji bai sake ganin shi.
Alhaji Abdur-Rahman ya kasa hakuri sai da ya tambaya, "Sayfullah lafiya dai ko?"
Dariya Sayf ya yi. "Lafiya lau Baba."
"Ba dai wani abun ya faru ba kake boye mun ba ko?"
Kai ya girgiza. "Uhm dama...dama ina son mu yi wata magana da kai."
"Bismillah ina sauraron ka."
Sayfullah ya ja lumfashi kafin ya amayar da duka abunda ke cikin shi. Bai boye komai ba kaman yanda Dr. Suleiman ya ke yawan ce mai.
Alhaji Abdur-Rahman ya saurare shi ba tare da ya katse shi ba. Duk jikin shi yayi sanyi.
"Ka yi hakuri idan na bata maka rai."
Alhaji ya lumfasa. "Dago kan ka ka kalle ni Sayfullah. Ba ka yi laifi ba. Ni ya kamata in baka hakuri. Mun bari matsalar mu ta shafe ka wanda sam mu ba haka aka yi mana ba. Ka gafarce mu, kuma in Allah Ya yarda zan gyara kaman yanda ka bukata."
"Nagode Baba. Allah Ya saka da alkhairi."
"Allah Ya yi maka albarka."
***
Gaba daya weekend din yayi a Kaduna. Sun je A.R.H motors tare da Baba. Wannan karon Sayfullah ya tsaya ya saurari duk abunda ke fita daga bakin Baba sannan ya fahimta kuma ya adana bayanan. Ba kaman wancan zuwan na shi ba da yazo ba a san ran shi ba.
Ranan lahadi kuma su ka je gonar shi shi da Habib. Baba yayi mamakin irin cigaba da suka samu cikin kankanin lokaci kuma ya yaba da kokarin su sosai. Nan take ya ce zai kara musu hannun jari don su sake inganta ma'aikatan.
A ranan Sayfullah yaso komawa Abuja sai dai Ammah ta ce sam bata yarda ba. Wannan zuwan Baba ya kwace shi dole ya kwana su yi hira. Sun ko yi hirar dan sai wurin sha daya ya bar bangaren Ammah. Ammah harda kukan farin cikinta da ta ji Sayfullah ya sasanta da iyayen shi.
Sayfullah ya cigaba da (therapy) amma maimakon sau biyu a wata ya koma so daya. Alhamdulillah, yana ta ganin cigaba. Ba shi kadai ba, mutanen da ke kusa da shi sunga chanji a tattare da shi.
***
Tun dazu take kokarin ganin ta gama hada kan komai. Ga shi Sayfullah daga fita nemo fruits yayi zaman shi sai ka ce an aiki bawa garin su.
Shekaran jiya suna shirin kwanciya Sayf ke ce mata ba su taba (hosting) 'yan uwa ba tunda su ka yi aure. Da daren ya turawa kowa sakon gayyata.
Maimoon na ganin chanji tare da mijinta tunda ya fara (therapy). Ta yi matukar murna ganin sauyi a yanda ya ke mu'amala da iyayen shi. Tun kafin ta san ya fara therapy din ta lura yanda ya ke (behaving) a gaban Ammi ya chanza. A da da ka kalle shi zaka san a takure ya ke amma a hankali ta lura ya fara sakin jikin shi. Wanda ba lallai wani yayi la'akari da hakan ba sai ita da ta san shi sosai.
Ta fi kowa murna saboda yanzu mijinta zai samu soyayyar iyayen shi da ya dade yana nema.
Sayfullah ya ce a nemo masu abinci su yi komai ba sai ta wahalar da kanta ba. Hakan aka yi, dazu su ka kawo komai shine ta ke shirya wurin. A falon kasa mazan zasu zauna matan kuma su hau sama.
Tana cikin jera plates kan dining Sayfullah ya dawo. Saida ta harare shi hakan ya sa shi tuntsirewa da dariya.
"Sorry Noor."
"Tun dazu na ke jiran ka. Kai zaka yanka ni na tafi in shirya."
Kai ya gyada yana gimtse dariyar shi. "Ba komai, zan yi."
Doguwar rigar leshi ta saka kalar sararin samaniya. Kalar ta haska ta sosai. Tsayawa tayi tana kallon kanta a madubi, gani tayi kumatun ta sun wani kara girma. Rannan Sayfullah ke tsokanarta wai bata jin wahalar makaranta kwata-kwata.
Bayan ta gama shiryawa ta koma kasa ta samu har ya gama yanka kayan lambun.
"Sannu Habibi," ta ce tana tsayawa a gefen shi.
"Yauwa matar Habibi. Kin yi kyau," ya ce yana kalleta tsaf har hakan yasa ta jin kunya. Dariya yayi ya girgiza kai.
Shima sama ya tafi domin ya shirya.
Adda Salma da Habib suka fara isowa. Maimoon ce ta bude musu kofa da murmushi a fuskarta tana yi musu sannun da zuwa.
Daya bayan daya duk suka iso. Kydah da mijinta tare da 'yan biyu sai Anwara da Ahmad, Amir din su ya girma ya kara wayo. Daga nan sai 'yan mata su Mimi, Sadiya, Nanah da Waahidah sai daga gidan Mami 'yan biyu da Nusayba.
An dade ba a hadu gaba daya haka ba dan haka an sha hira sosai. Safara'u da Habiba ma sun halarta amma fa ta waya. Dan uwa mai dadi kaman kada a rabu. A nan suka yini sai yamma sosai su ka bar gidan.
It was a time well spent.
Tun ranan da su ka yi 'yar karamar walimar nan Maimoon ta kwanta zazzabi. A da sun zaci ko wani abu da tashi ya bata mata ciki saboda amai da ta rika yi.
Ganin abun ya ki ci ya ki cinyewa duk first aid maganin da ta sha basu yi aiki ba Sayfullah ya ce ta shirya su tafi asibiti.
Kasancewar dare ne babu mutane da yawa nan da nan suka shiga ganin likita. Tare suka shiga ofis din likitar yana rike da hannunta dan sam babu karfi tattare da ita.
Likitan ta gabatar da kanta a matsayin Dr. Hafsa. Bayan ta gabatar da kanta ta shiga yiwa Maimoon tambayoyi wanda duk yawanci Sayfullah ke amsawa.
Dr. Hafsa na yi tana rubutu a file. "Yaushe kika ga al'adar ki karshe?"
Dan tunani ta yi kadan ta ce mata wata uku kenan.
"Ya saba yi miki haka?"
"Eh," Sayfullah ya amsa. Yayi mata bayanin condition din Maimoon na Endometriosis.
Kai Dr. ta jinjina. "Zan dauki jininta ayi mata test amma sai gobe sakamakon zai fito."
"Babu damuwa." Inji Sayfullah.
Maimoon na langwabe kan kujera burum ta tashi ganin likitar ta nufota da allura. Da sauri ta waiga ta kalla Sayfullah dan bata ji abunda ta ce ba.
"Zata dauki jinin ki ne." Sayfullah ya ce mata a hankali.
Ita da allura da magani duka ba shiri su ke yi ba. Runtse ido tayi ta rike hannun Sayfullah gam har aka gama.
Sayfullah ya rankwafo yayi mata rada a kunne. "Baby kawai."
Da idanunta dake nuna tsananin gajiyar da ke tare da ita ta harare shi.
Sayfullah ya kauda kai yana murmushi. Taimaka mata yayi su ka tafi mota kafin su isa gida ta yi barci.
Washegari yaje karban sakamakon test din da aka yi. Lab attendant din ta yi mai murmushi ta mika mai envelope.
"Congratulations, matar na dauke da ciki tsawon sati shida."
Jin shi yake kaman yana yawo a sama. Noor din shi na dauke da ciki. Subhanallah! Kaman yayi tsuntsu ya gan shi a gida. Wurin aikin da bai je ba kenan ya dauki hanyar gida bakin ci dauke da hamdalah yana godewa Allah SWT.
Da sauri ya haye sama ya nufi daki inda ya sameta a tsaye. Cikin taku da bai wuci goma ba ya isa gabanta. Chak ya dauketa yana jin hawaye na taruwa a idon shi.
"I love you so much Raihanatul Qalb. Ina son ki sosai."
Maimoon da bata san me ke faruwa ba tayi lamo cikin rukon shi tana shakar kamshin turaren shi. "I love you more Habibi."
A hankali ya sauketa ya hade goshin su wuri daya. Ya kasa bude baki yayi magana saboda kar kuka ya subce mai. Allahu Akbar! Allah Ya amsa mai addu'ar shi.
Hannunta ya kamo ya daura saman cikinta tare da na shi. Yana murmushi ido cike da hawaye ya kalleta. Kafin ma yayi magana ta fahimci abunda ya ke nufi.
Nan da nan nata idon ya cika da hawaye. "Dagaske?"
Kai ya gyada mata. "Sati shida."
"Ya Allah!" Ta furta tana runtse ido.
"Allah Ya yi miki albarka Mahnoor. You have made me the happiest man on earth. Ki fada duk abunda kike so."
Maimoon ta girgiza kai. Ita kuma mai take so yanzu a rayuwa? Ai ta gama samu. "Just love me for the rest of our lives."
"Kin gama samun wannan Noor, kin gama," ya ce yana hade bakin su wuri daya.
•
•
•
•
•
🥹🥹🥹🥹 A chapter left before we say goodbye.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro