BABI NA HAMSIN DA BIYU
~
BABI NA HAMSIN DA BIYU
~
Zaune take a kasa kwalaban turare a gabanta tana (sorting) dinsu. Littafin da take amfani da shi wurin (tracking orders) ta dauko ta duba dan ta tabbatar ba ta yi kuskure ba. Tunda ta gama gyaran gidan tayi girki take zaune a nan bayanta har ya kage. Mikewa tsaye ta yi ta zagaye dakin ko bayan zai saki.
Dakin matsakaici ne dauke da (cabinets) marasa murfi da (wardrobe) babba guda daya da Sayfullah ya sa aka yi mata lokacin da a ka yi 'yan gyare gyare a gidan. Jere su ke da kwalabe kala daban daban. An sawa wurin fitilu masu haske haka ya kara fiddo kyalli da shekin da katakon ke yi. A lungu kuma an saka tebur da ke dauke da (probs) din daukan hoto sai (ringlight) da ke jingine jikin bango.
Wardrobe ta bude ta dauko jakar kwali da ke dauke da sunan sana'arta. Girman jakukkunan hawa-hawa ne. Kasa ta koma inda ta yi kashi-kashi na turarrukan ta saka ko wanne a jaka. Bayan ta gama wannan ta dauko takarda da biro ta rubuta sunan wanda za su amsa sakon, lambar waya da kuma adireshi. Duka kayan a nan Abuja za a yi delivering din su.
Hankalinta ya yi nisa cikin aikinta bata ji karan tsayuwar mota ba bare karan bude kofa da a ka yi.
Sayfullah ya jingina jikin kofar yana kallon yanda ta tattara duka hankalinta take aikinta. Yau sam ofis din bai yi mai dadi ba, Allah Allah ya rika yi ya dawo gidan kaman ya janyo lokaci. Ya dade tsaye a wurin yana kallon hasken zuciyar shi kafin ta dago kai.
Murmushin da ta yi mai yasa shi jin duk duniya babu wanda ya kai shi sa'a. Janye jikin shi ya yi daga jikin kofar ya taka cikin dakin. Tuni ta mike tsaye yana isa gabanta ya tattaro ta gaba daya ya rungume yana sakin ajiyar zuciya.
"Sannu da zuwa ban ji shigowar ka ba."
"Kina ta aiki. Ki tuna mun maganan (desk) din, wannan bayan ki sai ya yi ciwo ai."
Tare su ka gama hada kan kayan. Masha Allah! Orders din da yawa sosai wannan na cikin gari ne ma ba ta fara na sauran garuruwan ba. Alhamdulillah Allah Ya albarkaci kasuwancinta tana ta samun cigaba. Yanzu haka ma akwai turare da zata hada na kawaye da wata amarya ta yi (order) zata saka a (souvenir).
Suna cikin aikin Sayfullah ya ke fada mata (director) din su ta yi (order) din kajiji guda biyar. Da yake Maimoon din ta saka mata sample size a kayan biki da ya kai mata.
Saida su ka gama tas tukun su ka bar wurin. Sayfullah ya kira mai delivery din da ya samo mata. Ba dadewa sai gashi ya iso ya fita ya bashi kayan tare da yi mai bayanin da ya kamata.
Ya dawo ya sameta ta mike kafafuwanta kan kujera. Ya zauna gefenta yana janyo kafafuwanta kan cinyarshi sannan ya hau matsa mata su. "Sannu Noor."
Ta amsa da yauwa tana lumshe ido. Kan ka ce me barci ya yi gaba da ita. Sayf ya yi murmushi ya dauke chak ya kaita daki. Bayan ya kwantar da ita ya rufa mata bargo mara nauyi ya rage mata sanyin ACn sannan ya sumbaci goshinta.
Sayfullah da Maimoon sun cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyan hankali, sun kara fahimtar junan su. An gama komai a kan admission din su Maimoon lokaci kawai su ke jira su fara zuwa makaranta. Biological science dinta zata cigaba. Sayfullah na zuwa aikin shi ita kuma tana gida tana nata aikin na turare da sai kara habaka ya ke yi. Karshen sati kuma su kan je su ziyarci iyaye da abokan arziki.
Har yau basu je gidan Kydah ba kuma abun ya fara ba Maimoon haushi. Kullum ta yi mai magana sai ya san yanda zai yi ya watsar da zancen. Bata taba zata haka alakar su ta tabarbare ba, sam baya son hulda da su kaman ba ciki daya su ka fito ba. Ita ta taso bata da abokai da suka wuce kannenta shi yasa hakan ke daure mata kai. Duk da ta sani ba za a hada yanda ta taso da na shi ba. Ko maganan Ammi ta yi bai cika kulata ba. Abun ya fara damunta sosai, ta san dama kudurin da ta dauka zai yi wuya amma ba ta yi tsammanin zai kai haka ba.
Yau ya kasance juma'a an tashi da ruwan sama kaman da bakin kwarya. Sayf dama ba zai je aiki yau ba dan haka su ka kara dunkunkunewa a bargo.
Maimoon ta fara farkawa, a hankali ta bude ido ta ganta cikin rukon mijinta. Dan lumshe ido ta yi tana sakin ajiyar zuciya. Ganin barcin na kokarin kara danneta ya sa ta janye jikinta a hankali. Agogo ta duba, karfe sha daya, har yanzu kuma ruwan bai tsaya ba. An dauke wuta sai inverter da ke aiki. Bayi ta shiga ta yi wanka sannan ta shirya cikin riga da sket na atamfa. Har ta gama shirinta Sayf bai motsa ba.
Kicin ta nufa dan tanadar musu abunda za su ci. Tun jiya ta jika shinkafar tuwo da zata yi masa. Bayan ta markada da blender ta ji sha'awar cin sinasir dan haka ta raba kullun gida biyu, daya ta yi mai kwabin waina dayan kuma na sinasir. A gefe kuma miyarta ta hau kan wuta.
Tana cikin aiki ta ji motsi a sama haka yasa ta gane Sayf ya tashi. Daidai ta fito dining Sayf ya sauko cikin shadda da babbar riga. Duk juma'a ya kan sa babbar riga wanda ba karamin kyau ya ke yi ba. Kafin ya matso kusa da ita kamshin turaren shi ya cika mata hanci.
"Ina kwana Babe." Maimoon ta gaishe shi tana matsawa kusa da shi.
"Lafiya lau Noor," ya amsa yana janyota jikin shi. "Yau mun zama mashiririta."
"Aikuwa dai," ta yi dariya. Dama abincin da zai ci kafin ya tafi masallaci ta fito ajiyewa.
Kicin ta koma ta fara tuyan waina. Tana cikin aiki Sayf ya shigo ya rungomata ta baya yana ce mata ya tafi. Bayan sun yi sallama ta cigaba da aikin ta. Ba ta dauki lokaci ba ta gama komai ta sa a kula, zasu gidan Mami dan haka ta dauko wasu kulolin ta zuba wanda zata kai musu.
Bayan Sayf ya dawo sun ci abinci su ka tafi gidan Mami. Duk lokacin da su ka je gidan Mami tana ganin wani bangare na Sayf da bata cika gani ba. Shakuwar da ya yi da Mami mai karfi ce sosai. Mami ce ta kasance mahaifiya a wurin Sayf a rashin Ammi. Sayf bai cika son maganan yanda ya taso ba amma yana yawan bada labarin Mami, yanda ta ke zuwa gidan yayanta hutu duk da aurenta dan kawai ta kula da shi. Kima da darajar Mami sun karu a idanun Maimoon.
Basu dade gidan Mami ba hakan ya yi mata dadi dan dama yau ta sa a ranta sai sun je gidan Kydah sai dai duk abunda zai faru ya faru.
A daya daga cikin one sitters din da ke falon ta same shi zaune, itama sai ta zauna a dayar da ke gefen shi. Bai ce mata komai ba ya ci gaba da kallon shi itama ta yi gum tana kallon Tvn.
"Ba yanzu zamu tafi ba, kar dare ya yi."
"Ina zamu?"
Ta ja numfashi tana tausasan zuciyarta. Sarai ya san mai ta ke nufi. Amma babu komai kai da kake nema ba ka ji haushi ba ai. Kuma irin haka sai da siyasa.
"Gidan Kydah mana, ka manta ko ka fara tsufa ne." 'Yar dariya kawai ya yi. Maimoon ta karya murya, "Tashi mu tafi mana Habibi, ka ji?"
Sai da ya ja mata aji kafin ya ce to bari ya dauko abu a daki sai su tafi. Kaman ta yi tsalle amma dai ta kama kanta. Yana barin wurin ta kira Kydah ta sanar da ita ga su nan zuwa.
"Kai Adda Moon, shi ne sai yanzu za ki fada mun."
Kydah kenan, ta ce a zuciya. Da tasan wuyar da ta sha da bata ce haka ba. "Ba gashi na fada miki ba, ki tanadar mana da kayan dadi."
"Dole, yanzu zan shiga kicin."
Da suka isa Kydah ta rasa inda zata saka su dan murna, sun samu mijinta Bilal a gida. Kydah ta cika gaban su da snacks daban-daban. Suna zaune a falon 'yan biyu su ka shigo a guje. Maimoon ta yi murmushi tana kallon su Tubarakallah Masha Allah yaran sai kara girma su ke yi.
Ganin bakin fuska a falon ya sa su ka yi wurin Maman su gaba daya. Kydah ta riko su tana nuna musa Maimoon da Sayf da ke zaune a kujera daya. "Je ku gaida su."
Da 'yan kananan kafafuwan su suka nufo wurin su, sai dai dukan su wurin Sayf su ka tafi. Sayf ya yi murmushi yana jin yaran sun burge shi. Dukan su biyu yau dauka ya daura kan cinya. Kydah na ta kallon su cike da farin ciki.
Basu wani dade ba su ka tafi. Har su ka zo tafiya 'yan biyu na hannun Sayf suna wasa abunsu Huda nata kokarin cire glass din shi. Sayf ya yi wa 'yan biyu kyauta mai tsoka iyayen su nata godiya. Bilal na yi wa Sayf sallama Kydah ta ja Maimoon gefe.
"Nagode Adda Moon."
Dariya ta yi. "Kin dai dage da Addan nan Maman 'yan biyu."
"Kin chanchanci a kira ki Addan ai. Allah Ya saka da alkhairi, Allah Ya bar zumunci."
Murmushi Maimoon ta yi tana ce mata babu komai ta bar yi mata godiya.
Bayan tafiyar su Kydah ta kira Ammi ta sanar da ita abunda ya faru itama ta yi farin ciki sosai.
Ranan lahadi Adda Salma ta kira Maimoon tana tambayarta ko su Ikram za su samu kitso mai kitson su bata zo ba. Maimoon ta ce mata babu matsala ta turo su. Tuntuni ta ke bin kan Addar ta rika turo su kawai ba sai an wani kira mai kitso ba amma ta ki ji.
Suna zaune a falo a ka kwankwasa kofa. Sayf ya mike dan bude kofar. Bayan dan wani lokaci ya dawo dauke da Amira, rike da hannun Ikram. Maman su ta hada so da kayan kitso, Maimoon ta mike su ka fita veranda da ke bayan kicin. Nan da nan ta gama musu kitso ta saka musu beads. Da gudu su ka yi ciki suna rige-rigen nunawa Baba Sayf.
Tana wanke hannu a kicin tana jiyo su daga falo yana, "Wow! Masha Allah! Anty Moon din ku ta iya kitso gaskiya." Kai ta girgiza tana dariya sannan ta nufa zubawa su Ikram abinci.
A nan su ka yini sai bayan Maghriba suka mika su gida. Isha'i a nan ta riske su, Sayf da Habib su ka tafi masallaci. Maimoon da Adda kuma bayan sun idar su ka daura hirar su.
A hanyan su ta komawa Sayf ya ce su je su mike kafa. Babu kowa titin estate din sai tsiraran mutane. Hannusu tsarke Maimoon na wurga shi kaman dai yanda yara ke yi. Suna tafe suna hirar su cike da nishadi.
"Raihanatul Qalb yaushe za ki bani babies? Ina son irin na Kydah, yan mata masu kama da ke."
Tambayar ta zo mata a bazata nan ta ji kunya ta lullube ta. Allah Ya so ma idanunshi shi ba a kanta su ke ba da abun ya fi haka. Daurewa ta yi ta tattaro duk wani karfin hali da take da shi ta ce, "Kaman nawa ka ke so?"
Dariya Sayf ya yi. "Kaman goma haka zuwa sha biyu. Zan fi son dozen gaskiya. Zan samu?"
Maimoon ta kwashe da dariya. Shima ya yi dariya. "Dagaske Noor. I want a big family. I was an only child, it was lonely, bani da abokin wasa a lokacin sai idan 'yan biyu sun zo."
Hannun shi ta dan matsa kadan. Sayf ya ja numfashi. "Baki bani amsa ba."
"Kai dai ka yi addu'a Allah Ya kawo masu albarka."
"Ameen Ya Allah."
****
Kwanaki da dama sun shude, rayuwa ta cigaba da gudana. Maimoon ta fara zuwa makaranta tare da 'yan uwanta. Da kyar ta saba dan ranan farko ta sha wuya jiki ya saba da hutu. Course daya su ke yi da Sadiya hakan ya yi mata dadi dan dama chan tunanin yanda zata fara sabawa da wasu mutanen ta ke yi.
Lectures dinta yawanci na safe ne tare da Sayf su ke fita ya ajiye ta. Wani lokaci shi zai dauko ta daga makaranta ko kuma ta tafi tare da kannenta sai ya dauketa a gida, musamman idan ya na da aiki sosai a ofis.
Abubuwa sun nemi su chabe mata. Karatu, kula da gida ga harkan turare a gefe. Sai da Sayf ya zaunar da ita su ka yi tsari yanda za a ba komai hakkin shi. Tare su ke aikace-aikacen gidan, idan ta dawo a gajiye musamman farkon komawarta shi ya ke shiga kicin ya dafa musu abinci.
A watan October Anwara ta haifi jaririnta kyakyawa namiji da ya ci sunan Baba Nasir amma za a kira shi da Amir. Farin ciki wurin Anwara da mijinta Ahmad ba a magana. Tare da Sayf su ka je su ka dubata a asibiti kafin a sallame ta. Ganin babyn ya sa Sayf kara jin sha'awar yara. Bayan kwana bakwai kuma a ka yi taron suna da ya kayatu matuka.
Tana zaune a cafeteria tana jiran Sayf ya zo daukanta kiran Habiba ya shigo wayarta ta Whatsapp. Ba karamin kewar kawayen ta ta yi ba. Sun dade suna hira tare da Safara'u da aka kira su ka hada group call. Sun dade suna hira kafin su ka yi sallama. Ba dadewa sai ga kiran Sayf.
Tana shiga motar ta tunbuke niqab din. Gaba daya wani kasala ta ke ji. Sayf ya yi mata dariya yana tambaya ko lafiya.
"Numfashi na naji na kokarin daukewa."
A hanya sun tsaya a hold up taga masu saida lemu a leda suna yawo. Maltina ta hango mai sanyi har wani zufa-zufa ya ke yi. Miyau ta hadiya tana bin ledar da kallo.
Da sauri ta juya ta kalli Sayf. "Babe ka siyan mun Malt."
Da mamaki ya kalleta, ya san dai irin wannan abubuwan ba su dame ta ba. "Malt za ki sha?"
"Eh," ta daga kai. "Yi sauri kada a bamu hannu."
Sayf ya sauke glass ya siyan mata ledar gaba daya mai dauke da gwangwani shida. Da sauri ta yaga ledar ta ciro, tunda ta kafa kai bata sauke ba sai da ta shanye.
"Ahhhh!" Ta furta tana dafe kirji. Kokarin ciro wani ta ke yi Sayf ya kwace ledar. "Bai isheni ba fa."
"Sai kin ci abinci. Yaushe kika fara kwadayi?"
Zumbura mai baki ta yi. "Ka bari in sha dan Allah."
Wurin kafafun shi ya ajiye ledar ya ce, "Sai mun je gida."
Sai dai da su ka isa ko kallon shi bata sake yi ba sai shi ne ma ya fasa daya ya sha.
Ranan wata laraba Maimoon ta tafi gida tare da 'yan uwanta Sayf zai dauke idan ya tashi aiki. Bata samu Ummi da Baffa a gida ba sun fita tare da Maman Anwara da Baba Nasir. Tana kwance a tsohon dakinta Waahidah ta shigo ita bata je makaranta yau ba bata da lectures. Bayan sun gaisa ta ce mata Ammi na kiranta.
Maimoon ta nemi mayafinta ta nufi sashen uwar mijinta. A dakinta ta same ta. Ammi ta yi mata murmushi tana yi mata maraba. Maimoon ta gaishe ta Ammi ta amsa tana tambayanta yaya su ke.
Shiru ne ya ratsa wurin kafin Ammi ta yi ajiyar zuciya. Wani karamin kati ta dauko ta mikawa Maimoon. "Wani dan uwa na ya hada lunch na family members din mu da ke nan Abuja, na san kowa zai halarci wurin tare da iyalin shi. Na san ba lallai Sayfullah ya yarda ya je ba, duk da haka ina son in jarraba. So please Maimoon. Na san na daura miki nauyi amma dan Allah ki tai—"
"—In sha zai zo," Maimoon ta yi saurin katse ta. "Ammi ki kwantar da hankalin ki."
"Ba shi kadai ba, harda ke."
"Zamu je Ammi. In sha Allah."
Hannuwan Maimoon Ammi ta kamo. "Nagode, nagode." Kwalla Maimoon ta ji ta tarun mata a ido.
Karamin kati ne amma kaman ta dauko buhun sumunti haka ta ke jin nauyin shi a jakarta. Nan da sati uku ne taron, dan haka tana da kwana ashirin da daya wurin shawo kan mijinta mai shegen taurin kai.
***
Ledoji guda uku ya dauko daga boot ya rufe motar, bai shiga da ita ba saboda zai kara fita anjima. Wasu yan kayakin da su ke bukata ne ya siyo. Ya sameta tana assignment a daki. Shima da aikin da ya kamata ya yi. System ya dauko ya zauna ya fara na shi aikin.
Tun dazu ya ke lura da ita ta kasa zama wuri daya kaman ana tsungulinta. Tana so ta yi mai magana sai ta fasa. Tun ba yau ba ya lura da hakan amma ya san ko ma meye zata same shi idan ta shirya saboda sun gina dangantakar su inda zasu iya tattauna komai da juna.
Ta gaban shi ta zo wucewa ya janyota ta zauna gefen shi. "Fada abunda kike so."
"Ni?" Ta zaro ido. "Babu abunda na ke so."
Hura mata iska ya yi a ido hakan ya sa ta kifta. Bai ce komai ba sai kura mata ido da ya yi. "To! Akwai amma dan Allah ina so ka saurare ni kafin ka yanke hukunci."
Gaban Sayf ya fadi da jin furucinta. Wani kati ta miko mai, a hankali ya karba yana fargaban abunda zai gani a rubuce. Ajiyar zuciya ya saki ganin ba wani abun tashin hankali bane. Sai dai da ya nutsu ya karanta ya gane dalilin da ya sa ta ce haka. Katin ya mika mata ba tare da ya kalleta. "Ba zan je ba."
"Babe..."
"Noor, ki bar magana. Ba zani ba."
"At least ka tsaya ka saurare ni dan Allah. 'Yan uwa duk za a taru yawanci baka san su ba suma ba su san ka ba, Ammi ta na son ta nuna ka cikin dangi..."
Dariya Sayf ya yi yana girgiza kai. "Ba su san ni ba? Laifin waye wannan? A lokacin da ya kama ta nuna ni cikin dangin, tana ina? Sai yanzu?"
"Laifinta ne kuma ta amince da hakan. Ta na so ta gyara kuskurenta amma baka bata dama."
"Idan kin fasa kwalba kina iya maida ta exactly yanda ta ke?" Ba tambayar da ya ke bukatar amsa ba ce dan haka ya cigaba da ce wa, "Ba za ki iya ba. Akwai abubuwa da dama da idan su ka lalace gyara su ba zai yiwu ba."
"Ammi ta yi laifi babba, bata kyauta ba. Duk ta san haka shi ya sa..."
"....dan Allah Noor ya isa. Bana son maganan."
"....shi yasa ta ke kokarin gyarawa. Kana cikin tsanin fushi shi ya sa baka lura amma Ammi na so.."
"....Ya isa na ce Maimoon."
Maimoon bata saurare shi ba. "Tana son ka, she loves yo—"
"Ya isa na ce!" Ya daka mata tsawa har saida ta firgita. "Ya isa! Bana son ji." Mukullin motar shi da ke kan tebur ya warta ya yi waje. Sam bai saurari kiran da Maimoon ke mai ba ya fice.
•
•
•
•
Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro