Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA HAMSIN

Not edited🫠



~
BABI NA HAMSIN
~






Baffa na zaune a falo hankalin shi a kan telebijin inda ya ke kallon labaran dare. Ummi ta shigo hannunta dauke da tray da kayan shayi ke kai.

Shigowarta ya dauke hankalin Baffa daga kan TV din. Murmushi ya mata yana karban tray din ya ajiye a kan teburin da ke gaban shi.

"Sannu Ummi," ya ce murya cike da zolaya.

Dariya ta yi ta ce, "Yauwa Baffa." Ta hada mai tea din yanda ya ke so ta mike mai sannan ta zauna a kusa da shi.

"Nagode," ya ce yana karba. "Ba za ki sha ba."

Kai ta girgiza. "Sha kayan ka na koshi."

Kallon labaran su ka cigaba da yi. Baffa na yi yana kurban shayin shi. Bayan ya shanye ya ajiye kofin a kan tray.

"Ina son zuwa Bauchi in ga Inna." Da sauri Ummi ta juya ta kalle shi cike da mamaki. Baffa ya cigaba da cewa, "Bai kamata in daina bibiyar su ba Rabi, basu chanchanci haka ba."

Ummi ta saki ajiyar zuciya. A baya dama idan ba shi ya nemata ba za su iya yin shekara ba su gaisa ba. Ita tafi so ya yi nesa da su ba dan ta zama butulu ba sai dan tana so ta kare shi daga tashin hankalin da zai sa ciwon shi dawowa.

"Yaushe za ka tafi?"

"Sai na yi magana da Nasir da Abdullahi. Mun taba yin maganan su ka ce za su raka ni ban san ko yanzu za su ba, sai dai na tambaya. Sannan zan sanar da Mama."

"To Allah Ya taimaka." Ummi ta ce tana addu'an kar hannun agogo ya koma baya. Halin mutanen nan kaff babu wanda bata sani ba.

Baffa ya yi murmushi. Ya san bata so ba amma ba zata taba yi mai musu ba. "Ameen Rabi na. Allah Ya yi mi ki albarka." Ya ce yana shafa fuskarta.

Washegari kaman yanda Baffa ya fada wa Ummi ya samu kannen shi Nasir da Abdullahi. Tayin da suka mai na raka shi na nan. Tare su ka isa falon Mama. A kullum Baffa na mamaki idan ya gan shi gaban mahaifiyar shi. Allah mai iko.

Mama (Jaddati) na zaune a falonta su ka shigo su uku a jere. A kullum idan ta gan su tare sai ta ji inama Alhaji Lamido na nan ya gan su a haka.

Sun dade suna hira kafin Nasir ya sanar da Mama abunda ya kawo su. Ta nuna farin ciki sosai har ta nuna tana so ta je amma Nasir ya lura Baffa bai son hakan ya faru dan haka ya ce mata ta yi hakuri ba sai ta je ba.

"Mama ba ki jin dadi ba za ki iya doguwar tafiya ba."

Ba ta yi musu ba ta ce to shikenan Allah Ya kai su lafiya. Sun yanke shawaran tafiya karshen sati kuma mota za su bi, Sameer ne zai tuka su. Sun dade tare da Mama kafin kowa ya koma gidan shi.

Baffa ya samu Ummi a daki tana gyaran wardrobe. Babban rigar shi ya cire ya tayata. Sun yi aikin na su ne cikin shiru har su ka gama.

Baffa ya dauko robobin ruwa guda biyu daga cikin fridge din da ya ke dakin ya mika mata guda daya.

"Nagode," ta karba tana murmushi.

"Ranan asabar za mu tafi in Allah Ya kaimu."

Ummi ta dan yi jim. "Allah Ya kaimu."

"Ameen." Baffa ya amsa.

Ummi ta mike ta dauko akwati madaidaici ta hadawa Baffa kayan tafiya.

Ranan assabar da asuba su ka dauki hanyan Bauchi. Tafiya ta yi kyau an yi ta cike da raha. Tafiyan ta dauke su awa shida da dori. A gajiye su ka isa garin Bauchi da misalin karfe daya da rabi na rana, dukan su sun dade ba su yi tafiya mai nisa haka ba.

"Sannu Sameer," Baffa ya ce ya na duban shi. Sameer ya yi murmushi. A wani otel su ka sauka. Daki hudu su ka kama kowa da na shi Sameer ya yi musu (checking in). Sun rabu a kan kowa zai kimtsa a masaukin shi sai su hadu a restaurant su shi abinci dayake sun yi sallah a hanya.

Ummi ya kira ya sanar da ita sun iso kafin ya yi komai. "Alhamdulillah, yanzu za ku je gidan Inna?"

"A'a sai zuwa anjima in Allah Ya yarda."

"Ta san da zuwan ku dai ko?"

Kai Baffa ya girgiza kaman tana gaban shi. Tun ranan da ya yi mata maganan tafiyar ya ke kiran lambar Inna bai samu ba, bata shiga kwatakwata. Gashi ya rasa lambobin yaran da ke zama da ita.

"Ban sameta a waya ba."

Shiru Ummi bata ce komai ba kafin daga baya ta ce, "To, Allah Ya tsare."

Ameen ya amsa daga nan ya kashe wayar. Ruwa ya watsa ya chanza kaya ya nufi restaurant din. A nan ya same su ya basu hakurin bata musu lokaci da ya yi. Abdullahi ya ce suma ba su dade da isowa ba.

Baffa bai iya cin abinci ba sosai saboda fargabar irin tarba da Inna za ta yi musu. Da shi kadai ne hankalin shi ba zai tashi haka ba. Addu'an shi daya kada ta wulakanta mai 'yan uwa.

Da suka tashi nufan gidan bayan sallan la'asar Baffa ne ya shiga gidan gaba dan ya nunawa Sameer hanya. Babu dadewa su ka iso Sameer ya yi parking a kofar gidan.

A tare su ka fito daga motar mutanen unguwa na ta kallon su, suna tunani su waye su ka zo haka. Wanda daga gani ba kananan mutane ba ne.

Suna tsaye wata matashiya ta fito. Turus ta yi ganin su a kofar gidan. Gaishe su ta yi ta yi gaba Baffa ya dakatar da ita. Tambayar ya yi ko bata gane shi sai a sannan ta lura waye.

"Allah sarki Baffa ban gane ka ba, ina wuni." Fara'ar fuskarta ta fadada.

"Lafiya lau. Allah Ya sa Inna ta na nan?"

"Tana nan Baffa, bismillah ya ka tsaya a waje."

"A'a shiga ki sanar da ita tukun."

Hakan ya bata mamaki amma ta yi yanda ya ce din. Bayan minti biyu sai gata ta dawo tana ce musu su shigo.

Duka su rankaya su ka shiga Baffa a gaba. Fatan shi dai komai ya tafi daidai ba tare da rai ya baci ba.

Hajiya Inna na zaune a falonta kan kujera tana bare gyada. Ajiye farantin ta yi tana gyara zama ganin mutanen da bata sani ba. Laure ta ce mata Muhammdu ne ko dai bata ji da kyau ba. Babu wanda ya yi kama da Muhammadu a cikin su, kuma dai a iya saninta Muhammadu ba zai zo da manyan mutane haka ba. Ko su waye? Ko dai abokan Bello ne su ka zo gaishe ta. Allah Ya sa sune dan ta san ba za su tafi haka nan ba tare da sun yi mata ihsani ba.

Washe baki ta yi tayi aka gaisa. Ta kira aka kawo musu ruwa. "Duba cikin firijin da ke dakina ki dauko musu fura don Allah. Sabuwa ce yanzu na damata. Yi sauri."

Dubanta ta maida kan su. "Sassanun ku. Ya iyali? Duk suna nan lafiya ko?"

"Lafiya lau Inna."

"Madallah! Madallah! Kun san abunku da tsohuwa, ban shaida ku ba."

Nasir, Abdullahi su ka juya a tare suna kallon Baffa. Itama Inna ta maida hankalinta kan shi. Sai a sannan ta kara lura da fuskar shi. Kaman ta san wannan fuska.

"Muhammadu ne Inna."

Inna ta saki salati tana zaro ido. Muhammadu fa? Shine ya shigo tare da mutanen nan yana cika mata ido. Abun mamaki Baffa ya yi mata kwarjinin da ta kasa furta abunda ta yi niya sai ta buge da cewa, "Muhammadu kai ne haka? Ina ka shiga?"

Wani yawu Baffa ya hadiya ya yi gyaran murya. "Ni ne Inna. Mun same ku lafiya?"

"Lafiya kalau ya wurin su Rabi da 'ya'yan naka? Yaya sabon wuri kuma, Bello ke fada mun gidan naka da sauran aiki. Da fatan dai ba haka kuka yi damuna ba wuri ko rufi babu?"

Ba Nasir kadai ba harta Sameer sai da ya ji zancen a baibai. Baffa ya yi murmushi. Hali zanen dutse duk yanda ta so dannewa saida ta yi dan halin.

"Eh ai mun ma tashi daga garin gaba daya. Mun koma Abuja da zama."

"Habuja fa? Kai da iyalin gaba daya? Ina ka samu kudin? Su waye wa'anan ma dai tukun."

Gyaran murya Baffa ya yi sai dai kafin ya ce komai Abdullahi da tun dazu ran shi ya gama baci ya riga shi. "Mu 'yan uwan shi ne Inna."

"Yan uwa? 'Yan uwa fa? Muhammadu ina ya ga wasu 'yan uwan banda su Bello da suka dade suna taimaka mai."

Abdullahi ya hade rai. Bai bar komai ba ya yi mata bayani filla filla yanda zata gane dan ya ga take-taken ta sai a hankali. Yaya bai taba sanar da su haka halinta ya ke ba, dan zaman nan da su ka yi da bai fi na minti goma ya gama karantar wace irin mata ce. Da farko da bata gane su waye ba faram-faram da ita amma yanzu ta chanza gaba daya kaman ba ita ba.

Inna ta yi ta sallallami tana kallon bawon Allah nan da ke koro mata wasu bayanai na daban. Gashi ya cika mata ido babu bakin fadin magana. Sai a sannan ne ma ta sake lura da irin tsantsar kama da su ke yi gaba dayan su harda dan matashin da ke gefe kuwa.

"....mahaifiyar mu taso zuwa saidai bata da isasshen lafiya. Ta ce a gaishe ki kuma tana godiya da irin abunda kika yi mata na kula da Yaya Muhammad tsawan wannan shekarun. Lallai ba zata taba iya biyan ki saidai ta yi miki addu'a Allah Ya saka miki da mafificin alkhairi."

Nasir ne da wannan bayanin. Tuni ya katse Abdullahi kafin ya fadi abunda bai dace ba.

Inna ta daskare a wurin kwakwalwarta ta kasa daukan bayanan da a ke yi mata. Muhammadu ya hadu da 'yan uwan shi harda mahaifiya tsawon watanni. Ita ba makauniya bace taga babban chanji a tattare da shi daga fatar jikin shi zuwa sutar da yake sanye da ita. Tabdijam!

Nasir ya kira Mama ya hadata da Inna. "Ga mahaifiyar mu nan zata yi miki magana."

Inna dai ba zata iya cewa ga takamaimai abunda ta fada ba ta gama ta mika mai wayar. Daga nan kuma aka shiga kallon juna duk an rasa abunda za a ce.

Kaman an tsunguleta ta yi zumbur. "Yanzu Muhammadu a ce 'yar nan taka mai ida....Maimuna ta yi aure ban sani ba. Ka kyauta kenan? Tun ba'a je ko ina ba ka yarda mu, to dai ko ina zaka je mune asalinka dan nan kayi rayuwar ka kaff, ba za ka taba iya chanza mu ba ehe."

"Na yi kuskure Inna, ki yi hakuri."

"Ah toh. Nan Ardo ya kawo mun kai cikin mawuyacin hali. Na dauke ke tamkar dan da na haifa, ban taba nuna banbanci tsakanin ka da su Bello. Bai kamata ka saka mun haka ba."

Baffa ya runtse ido yana sauraron sababin Inna da ta saba yi. Allah sarki rayuwa, a da babu abunda ya so kaman Inna ta kalle shi yanda ta ke kallon sauran, ta janyo shi jiki kaman yanda ta ke wa 'yan uwanshi. Chan kasan ran shi bai yi mamaki ba lokacin da gaskiyar asalin shi ta fito dan tabbas da walakin goro a miya. Kowa ya san tana nuna banbanci sai dai a lokaci ya yi tunanin ko dan rashi wadata ne da Allah bai bashi ba ya sa take mai hakan, ashe ashe.

Ganin zancen nata ba karewa zai yi ba, Baffa ya ce zasu tafi.

"Tun yanzu? Ba ku ci abinci ba."

"A'a, a koshe muke. Gobe in Allah Ya yarda zamu tafi."

"Da wuri haka. To yaushe za ka kaini Habujan in ga sabon wuri?" Ta tsare shi da idanu tana jiran amsar shi.

"Har gida za a zo a dauke Inna." Nasir ya amsa da murmushi a fuskar shi.

Itama Inna ta yi murmushi, amsar ta yi mata dadi. Daga gani wannan yafi dan uwan shi saukin kai. Inna ta shiga daki ta dawo da kulle-kulle da aka san tsofaffi da su ta ce su kai ma Mama.

Daga nan su ka yi sallama. Baffa bai ce komai ba har su ka isa masaukin su. Sai anjima ya yi musu ya tafi daki.

Abdullahi ya yi yunkurin bin bayan shi Nasir ya dakatar da shi ta hanyan dafa shi a kafada. "Kyale shi, yana so ya kasance shi kadai."

"Amma Yaya...."

Katse shi Nasir ya yi. "Idan ba shi ya dauko maganan ba dan Allah kar ka dauko mai zancen abunda ya faru."

"To. Allah kadai Ya san ya tsakanin su yake in har ta nuna halinta haka a farko haduwar mu da ita."

"Babu ruwan ka, ko ya halinta ya ke ba zai chanza taimakon da suka yi wa Yaya ba, ni da kai da Mama da sauran ' yan uwa gaba daya are indebted to her na kula da shi da tayi."

"Haka ne," Abdullahi ya ce yana gyada kai. "Amma kana gani ka yi daidai da ka ce mata haka? Matar nan ba ta yi kama da wanda zata mance alkawari ba."

"Ka san dole Mama zata nemi ta zo Bauchi, gwara a kai mata Inna din. On our territory."

Kai Abdullahi ya jinjina alamun ya gamsu da bayanin dan uwan shi.

Baffa na zaune a bakin gado, sam abunda Inna ta yi bai bashi mamaki ba kuma cikin ikon Allah bai dame shi ba har ya yi mai ciwo. Dan ya yi zaton fiye da haka daga wurinta. Ummi ya kira ya fada mata yanda su ka yi.

Itama ta yi mamakin dan ta gama sakawa a rai Inna zata ci musu fuska. Ba karamin murna ta yi ba jin Baffa bai saka abun a ran shi, sai dai abu daya ne bai kwanta mata a rai ba.

"Kana ganin zuwan ta ba zai kawo matsala ba?" Ta tambaya tana tuna lokutan da ta ke zuwa daga Bauchi a da. Tana zuwa ita da yaranta sun yi wa kwanciyan hankali sallama kenan musamman Maimoon.

"Babu wata matsala Ummi. An wuce zamanin da zuwan Inna zai rika tada mana hankali, an wuce."


***

Su Baffa na barin gidan Inna ta sa a ka dauko mata wayarta a ka kunnan sannan ta ce a kira mata Bello.

Bello da ke zaune a falon shi na sama shi kadai ya ji wayar shi na vibrating a aljihu. Karamin tsaki ya yi ganin sunan Inna. Yanzu haka kudi zata ce a tura mata bayan ta yi mursisi ta ki cewa Abdulkarim komai. Rabon da su yi magana da dan uwan na shi an dade sosai wanda da a rana sai wuya yafi sau uku.

Da kaman ba zai dauka wayan sai kuma ya chanza shawara. Bai ce komai ba ya kara wayar a kunne.

"Bello kana ji na, yanzu Muhammadu ya zo da wasu manyan mutane biyu."

Zumbur Bello ya mike. "Mai kika ce Inna?"

"Abunda ka ji na ce. Muhammadu ya zo da wasu wai 'yan uwan shi ne. Da farko ban yarda ba sai da na kalle su da kyau na ga tsantsar kama da su ke yi. Ina zaune kawai sai ga s—"

"—Inna!" Bello ya katse ta. "Ya sunan 'yan uwan na shi."

"Nasiru da Abdullahi sai wani dan saurayi da ban san sunan shi ba."

"Sune! Wallahi sune!" Bello ya furta da karfi har saida Inna ta firgita.

"Sune suwa? Gamo ka yi Bello?"

"Suna ina? Suna nan ne ko sun tafi? A ina suka sauka?"

"Kai lafiya kake mun tambayoyi kaman sabon dan jarida?"

"Inna. Ki amsa mana, sun fada miki lokacin da zasu bar garin?"

"Gobe za su tafi. Ban san a ina suka sauka ba nima ganin su kawai na yi daga sama."

Tsaki Bello ya ja cike da takaici. Amma shi wani irin mara sa'a ne a ce mutanen da ya dade yana bibiya sun je har gidan su amma bai sani ba.

"Bello alamu sun nuna akwai maiko a tattare da mutenen nan. Kai ka ga Muhammdu kaman ba shi ba. Shi yasa na ce mai ina son in je Habuja in je in yago nawa rabon daya a cikin su ya ce har gida za a zo a dauke ni."

Cak Bello ya tsaya jin abunda Inna ta ce. Anya ya ji daidai kuwa? "Inna me kika ce?"

"Har gida ya ce za a zo a dauke ni inji Nasiru dan yafi dan uwan shi saukin kai daga gani. Kai kaga yanda ya ke ma......."

Wani irin shu'umin murmushi Bello ya yi. Tsuntsu daga sama gasassashe. "Inna saurare ni ki ji....."













~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro