Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA GOMA SHA TARA








~~BABI NA GOMA SHA TARA~~







Tsit wurin ya ke kaman babu kowa a wurin. Shiru ne mai dauke da kalamai masu yawa. Kowa da irin abunda zuciyarsa ke saka mai. Saidai duk akan dalili daya ne.

A yau iyalan Malam Muhammadu sun tsinci kansu a wani mawuyacin hali mai wahalar fassarawa. Duniya tai musu zafi sun rasa inda za su sa kansu su ji sanyi. Rana zafi, inuwa ƙuna.

Maimoon ba zata iya cewa ga abunda ya faru awanni uku da suka wuce ba. Mommy ta fadi kalmomin da su ka tarwatsa su baki daya. Ta san dai sun shiga cikin wurin da ya kasance matsugunnin su na tsawon sheraku bakwai, sun kwashe duk wani abu da suka mallaka.

Suna tsaye bakin titi sai ga Suraj, babban abokin Ashmaan, tare da motar kwasan kaya. Bai ce da su komai ba bayan gaishe da Baffa da Ummi da ya yi. Da shi da dreban da suka zo tare su ka sa kayan a mota da taimakon su.

Motar Suraj su ka shiga, Baffa na mai kwatance har su ka tsaya gaban wani gida a Badarawa. Gida ne da in bada rufi, kofofi da tagogi babu komai ciki, ko ceiling babu.

Gidan na dauke da bangare biyu, daya a gaba daya a baya. Na gaban dauke ya ke da dakuna biyu madaidaita kowanne da bayi ciki sai falo. Sai na bayan kuma na da dakuna uku, falo sai kicin. Ba babban wuri bane sosai sai dai komai a wadace ya ke babu takura.

Wuri ne da ake kan aikin gini, datti ni sosai ba su san ta ina za su fara gyara shi ba. Tamkar kurame haka su koma. Cikin shirun su ka kimtsa wurin da za su iya gyarawa.

"Adda," Sadiya ta ce murya a dashe. "Ya kamata a duba kan ki, har yanzu bai bar jini ba."

Hannu Maimoon ta sa ta shafa goshinta ta ji da lema. A halin yanzu she feels numb, babu abunda ta ke ji. Tsumma ta samu ta jika shi da ruwa, ta sa ta goge ciwon. Sanna ta sa gishiri dan jinin ya tsaya, ko zafin yin hakan ba ta ji ba.

Suraj bai ta fi ba sai bayan salar isha'i tare da alkawarin dawowa washegari. Kafin ya tafi ya tsiyo abinci ya aje sai dai babu wanda ya kalli kulolin. Flat din farko mai dakuna biyu suka gyara. Iyayen su ka dauki daya, yaran su ka dauki daya.

Ba'ayi wiring wutar lantarki ba, a cikin duhu suke zaune. Ga sauro da ke addabar su dukda an fesa magani kuma coil na ci har yanzu. Babu wanda ya yi bacci cikin su. Cikin dare Maimoon na iya jiyo sautin kukan Sadiya sai dai bata da karfin rarrashinta. Itama da zata samu ta yi kukan da ta yi. Sai dai wani abu tamkar dutse ya danneta.

Da ta tashi da safe bata taba tsammanin al'ammura za su chanza mu su haka ba. Rayuwarsu ta birkice gaba daya.

Fuskar Hamma Ashmaan ke mata yawo a ido duk sanda ta rufe su. Lokacin da ya mata rumfa da jikinshi dan kareta daga dukan Mommy da idanun shi lokacin da su ke kwasan kaya.

Yanzu duk abunda ya faru yau ya faru ne kawai dan Mommy bata so danta ya auri Maimoon. Ba tare da tunanin komai ba ta rushewa Baffa ginin rayuwarshi.

Tabbas ta san kasancewarta da Ashmaan abu ne da bai zai taba faruwa ba, amma sai dai chan kasan zuciyarta akwai wani dan karamin hope da abubuwa za su juya.

Sun juya kam dan bata taba zatan abun zai kai haka ba.

Lallai biri ya yi kama da mutum. Ta dade tana tantama sai dai bata taba tsammanin hasashenta zai zama gaskiya ba. Wayyo Baffa. Ko ya ya ke ji yanzu? Duk tsawon shekarun nan bai taba sanin shi waye ba. Ta ina zai fara? Su waye yan uwansu?

Su shikenan haka rayuwa zata kasance musu? Babu dangin uwa, yanzu ma na uban babu.

Yanda ta ga rana haka ta ga dare. Kanta ciwo ya ke yi kaman zai tsage. Da sassafe sai ga Suraj kaman yanda ya yi alkawari. Ya taho musu da karin kumallo. Ganin shi na tuna mata da Hamma, sai kirjinta ya fara ciwo kaman zai tarwatse.

"Baffa," Suraj ya kira ya na gyara zama akan tabarmar da ya kawo. Da ya tabbatar hankalin Baffa na kan shi, ya ce, "Baffa gidan nan ba zai zaunu ba. Babu wuta, babu ruwa, ko ceiling babu."

A kwana daya Baffa ya kara tsufa. "Suraj idan ba nan ba ina zamu?"

"Akwai gidajen haya da mahaifina ke da su nan kusa, flat daya babu kowa a ciki..."

Kafin ya karasa maganan Baffa ya fara girgiza kai. "A'a Suraj, ba sai an yi haka ba. Ka bar mu anan din ma ya yi. Guntun gatarin ka ya fi sari ka bani. Akwai rijiya a baya, wuta kuma zamu yi maneji a haka."

"Amma Baffa—"

"—ka da muja maganan Suraj. Nagode sosai da irin karamcin ka. Kar ka damu nan din ma ya isa. Duk abubuwan da ka ke cewa babu da sannu za'a saka su in sha Allah."

Yana gama magana ya koma ciki, Ummi ta bi bayan shi.

Maimoon na tsaye a daki ta na jin su. Mimi ce ta shigo tana hawaye da waya a kunnenta. Ba ta ce komai ba ta mika ma Maimoon wayar ta fice.


Sunan Ashmaan ne akan wayan, ta na gani ta kashe. Ba bata lokaci wani kiran ya shigo. Har ta gama kara ta tsinke Maimoon ba ta yi yunkurin dauka ba. Bai fasa kira ba har sau biyar.

Hannunta na karkarwa ta amsa kiran ta kara wayan a kunne. "Moon," muryar shi da daki kunneta. "Moon ki yi hakuri. I will fix everything, zan dadaita komai, na miki alkawari. Ka Suraj nan, zai kula da ku kafin in zo. Moon...."

Katse kiran ta yi dan ba zata iya cigaba da sauraron shi ba. Shirin fita ta yi ba tare da ta san inda zata je ba. Bata sanar da kowa ba ta fita. Tafiya ta ke yi kawai. Duk inda kafarta ta ja ta nan ta ke yi.

Mutane nata hidimar su. Amma bata lura da su ba. Wata bishiya ta hango, ba tare da wani tunani ba ta nufi wurin. Babu kowa a wurin sai mota a aje. Akan dutsen da ke jikin bishiyar ta zauna.

Kaman an zare mata wani abu kawai ta fashe da kuka. Kuka ta ke yi kaman ranta zai fita. Lumfashinta har daukewa ya ke. Ciwo marar misaltuwa ya mamayeta har cikin kasusuwanta.

Kuka ta ke yi cike da kunci. Bata hana kanta ba, ta hakane kawai za ta iya rage nauyin da ke kirjinta.

"Ya Allah!" Ta kira baki na karkarwa. "Ya Allah Ka bamu ikon cin jarabawar nan. Ya Allah! Kai kadai Ne gatan mu. Ya Rahman!"

Bata san tsawon lokacin da ta dauka a wurin ba tana kuka. Tun tana yi jikinta na karkarwa har ya koma hawaye ne kadai ke zuba. Niqabin ta ya jike sharkaf da hawaye. Bata cire ba, bayan hannunta ta sa ta goge idanunta.

Ba zata karaya ba. Dole ta daure, ta jure ko dan iyayenta da kannenta.




***

"Bauchi zan je Rabi," Baffa ya ce ma Ummi. "Na san bai kamata in yi nisa da ku ba amma..."

"Ba sai ka ce komai ba Baban Mu'azzam. Allah Ya kiyaye hanya, Ya tsare ka. Da izinin Allah babu abunda zai same mu har ka je ka dawo."

Karfe hudu na yamma Baffa ya sauka a garin Bauchi. Tunda ya hau mota a tasha ya ke maimaita 'Hasbunallahu wa ni'imal wakeel'

Bayan rasuwar Ardo Abdulkarim ya dawo da Inna cikin garin Bauchi. Gida ne madaidaici daidai ita. Gidan dauke ya ke da komai mutum zai bukata.

Baffa ya dangana halayyar mahaifiyarshi gare shi da iyalinshi akan rashin wadatar shi. Bai gina mata gida ba, bai fidda ta kasashen duniya yawan shakatawa ba. Bai taba kawowa akan shi cewa dalilinta shine dan ba ita ta haife shi ba.

Bayan ya kimtsa, ya ci abinci a teburin me shayin kusa da gidan ya nemi a mai iso wurin Inna. Yara biyu daga cikin yaran 'yan uwanta ta dauko su ke taya ta zama.

"Baffa bismillah," daya daga cikin su ta ce.

A zaune kan kujera ya sami Inna. Ko meye ya biyo baya ba zai taba chanza matsayin da Inna ke da shi a rayuwarsa ba. Ita ce mahaifiyar shi, babu abunda zai taba chanza wannan.

Bayan gaisuwa babu abunda wani daga cikin su ya kara furtawa. Baffa bai san ta yanda zai dago maganar ba.

"Bello ya sanar da ni abunda ya kawo ka Muhammadu," Inna ta ce bayan lokaci mai tsawo. "Banda masaniya akan abunda ka zo nema. Ni ma na tashi wata rana maigidana ya dawo da kai bayan ya je gona. Bai fada mun daga ina ya samo ka ba nima ban bukaci sani ba. Kayi hakuri da abunda Suwaiba ta yi. Sam ba haka na so kasani ba. Ardo ya sa na yi mai alkwari ba zan sanar da kai ba, ban san dalilin shi na yin haka ba. Har ya koma ga mahaliccin shi bai daina kokarin gano 'yan uwanka ba amma babu nasara. Ina fata wannan ba zai chaza komai tsakanin mu ba."

Tabbas ba amsar da ya so samu daga Inna ba kenan. "In wani abu ya chanza ai na zama butulu. Allah Ya saka muku da alkhairi, Ya biya ku da gidan Aljannah. Allah Ya jikan Ardo."

"Ameen, ameen." Shiru ne ya kara ratsawa na wasu yan dakiku kafin Inna ta ce. "Sai kuma maganar Ashmaan da 'yar wajan ka. Inaga a hakura ko? Tunda iyayenshi sun nuna basu so. Allah Ya hada kowa da rabon shi."

"Ameen. Duk yanda kika ce haka za'ayi Inna."

Washegari Baffa ya koma Kaduna. Saida ya je gidan Bello kafin ya isa gida. Shekara biyar da suka wuce ya siya filin ya fara gini a hankali ba tare da kowa ya sani ba. Ba dan kaddara ba babu abunda zai kaishi gidan Bello ya zauna har tsawon wannan lokaci.

A zaune a kasa Ummi ta same shi cikin daki. Ba ta ce mai komai ba ta zauna kusa da shi. Kanshi ya daura kan kafadarta sannan ya fashe da kuka.











Allah sarki Baffa 🤧

Ku taimaka ku yi commenting dan in san mai ku ke tunani please. No update sai na ga comments rututu🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️

@rukayyatuuuu wattpad isn't letting me tag you, this update is for you. Na tashi da safe naga comment dinki and it boosted me to write, nagode❤️





~Maymunatu Bukar 💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro