BABI NA GOMA SHA TAKWAS
~~BABI NA GOMA SHA TAKWAS~~
"Ni Muhammadu zai watsa ma kasa a ido? Ni Bello duk abunda na mai!"
"Ai Allah Ya kara."
A fusace Bello ya juyo ya kalla matar shi da ke kwance kan gado. "Au Allah Ya kara ma zaki ce. Kin san yanda muka rabu da Ambasad kuwa? Kin san irin tarin kudin da na rasa saboda kawai talakan chan ya ce ba zai bada auren 'yar shi ba. Me ye ban yi wa Muhammadu a rayuwa ba?"
"Mutane mutunci ne da su a ka ce ma" Hajiya Suwaiba ta ce ta na taɓe baki. "Ka sa su inuwa su jefa ka rana. Bare kuma mutumin talaka, talakan ma mai girman kai kaman dan uwanka. Ai kadan ma ka gani. Gwara tun wuri ka dauki mataki dan nan gaba abun sai ya fi haka. Ba ya giga ba har ya samu aiki, ai yanzu jin shi ya ke yi daidai da kai."
Kai Bello ya kaɗa ya na tuna yanda su ka yi da Muhammad. Muhammad ya same shi a office ɗin shi da ke independence way. A lokacin Amsada Audu na tare da shi a office ɗin. Bello ya yi zaton buƙatar shi za ta biya, be yi tsammanin Muhammadu zai yi hakan ba, a gaban Ambasadan kuma.
Baffa ce musu ya yi be shirya yiwa 'yar shi aure ba, kuma in ma ya shirya aurar da ita toh ba zai ba mutum irin Ambasada Audu ba. Fadan irin cin fuskar da hakan ya jawowa Daddy bata lokaci ne. Baram baram su ka yi da Audu bayan Baffa ya fita. Dan ya na gama magana bai tsaya sauraron komai ba ya juya ya tafi.
Tun a hanya Daddy ke zage zage har ya shigo ɗaki ya sami Mommy kwance kan gado.
"Ai ko zan yi maganin shi," ya ce ya na kumfar baki. "Har ni za'a wulakanta? Ni fa? Sai ya kwamace bai zo duniya ba, sai na nuna mai na fi karfin a mun wulkanci."
Nan Daddy ya yi ta fada ya na barazana. Bayan wani dan lokaci Ashmaan ya yi sallama. Saisaita kan shi Daddy ya yi kafin ya bashi izinin shigowa.
Saida Ashmaan ya tattaro duk wata natsuwa kafin ya tura kofar ɗakin. Domin ya bukatar ko kwarin gwiwan shiga filin daga. Ya ma kan shi ba zai bar ɗakin nan ba har sai ya samo yardar iyayen shi kaman yanda ya ma Moon alƙawari.
Sati biyu kenan da abun ya faru sai yau ya samu courage din tunkarar iyayenshi. Tabbas da gaskiyar Moon da ta ce akwai matsala kuma amincewar iyayenshi abu ne mai wuya. Amma ya yarda duk wani abu mai muhimmaci a rayuwar dan Adam ba ta hanyar sauƙi a ke samu ba. Dan haka har sai inda ƙarfin shi ya ƙare dan ganin ya mallaki Moon a matsayin matar shi ta sunna.
A ƙasa ya samu wuri ya zauna sannan ya gaishe su cike da ladabi. Daddy ne ya dan ja shi da magana inda ya ke tambayan shi yanayin aikin na shi in kuma ya na jin ɗaɗi.
"Aiki Alhamdulillah Daddy. Ma'aikatan na da kirki sosai. Babu wata matsala."
"Madallah, haka nake son ji. Sai ka maida hankali, kasan dai irin wahalar da na yi wurin samo maka aiki a ma'aikata babba irin wannan."
"In sha Allah, Daddy. Allah Ya kara girma."
"Ameen. Lafiya dai ko Ashmaan? Na ga kaman da magana a bakin ka."
"Nima abunda zan ce kenan Alhajj," in ji Mommy da yanzu ta ke zaune kusa da mijinta. "Ashmaan lafiya? Da fatan ba wata matsala ba ce?"
"Eh to, a wurina ba matsala ba ce amma sai dai ban san yanda za ku dauki abun."
"Faɗa abunda ke tafe da kai, muna sauraron ka." Daddy ya ce ya na gyara zama.
Lumfashi Ashmaan ya ja sannan ya sauke a hankali, a zuciya ya na addu'a Allah Ya sa abun ya zo cikin sauƙi.
"Daddy, Mommy kafin in faɗa muku dan Allah ina neman alfarman da ku fahimce ni kafin ku yanke hukunci."
"Wai meye ne Ashmaan ka ke ta wani kwana-kwana. Me ka ke son faɗa? Ko ma meye a shiryi muke dan ganin farin cikin ka." Mommy ta ce, dan ta fara tsorata.
Kai a ƙasa, ya na sosa ƙeye, ya ce. "Akwai yarinyan da muka daidaita da ita ne amma ina tsoron yanda za ku dauki abun."
A take murmushi ya bayyana a fuksar Mommy. "Au to, ni har ka fara bani tsoro. Alhaji ka na jin dan ko?"
"Ina jin shi. Ashmaan girma ya zo. Shine ka tsaya kana kame-kame. Kwantar da hankalinka, ko 'yar gidan waye ni da kaina zan je in nemo maka izini. Wacece ita? Na santa ko iyayenta?"
Da zuciya na iya barin kirjin mutum da ta Ashmaan ta dade ta fita saboda matsanancin bugun da ta ke yi. Har yanzu kan shi na ƙasa ya kasa dagowa. Sun zata kunya ce ba su san tsanin fargaba bane ke dawainiya da shi.
"Eh Daddy, Maimoon ce 'yar gidan Baffa Muhammad."
Shiru ne ya biyo baya bayan furucin sa ya daki kunnuwan su, saida Ashmaan ya daga kai dan ganin ko su na nan. Ko wannen su dauke da expression daban daban. Daddy kallo shi ya ke kaman zai karya shi, Mommy kuwa a firgice ta ke kallon shi.
"Ka ji abunda kunne na ya ji mun Alhaji? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Sai na ji kaman ya ce 'yar wurin Muhammadu."
"Eh Mommy, ita ce."
Firgit! Hajiya Suwaiba ta mike ta na kallon Ashmaan cike da bacin rai. Daddy ko fuskar shi a turnuke ta ke kaman bai taba fara'a a rayuwarshi ba. Kafin Mommy ta ce wani abu ya yi kan Ashmaan inda ya dauke shi da lafiyayyun maruka har biyu.
Ko gezau Ashmaan be yi ba, kan shi na nan a kasa kaman dazu.
"You are very stupid! Ashe ba ka da hankali. Dama ina ganin take-taken ka amma na yi shiru na kyale shine za ka zo mun da maganan banza da wofi. To wallahi, ka kiyaye ni dan zan dauki mummunan mataki a kan ka. Shasha wanda bai san abunda ya ke yi ba. Kai har ka yi girman da za ka tunkare mu da irin wannan maganan. In har ka na son zaman lafiya kar in sa ke ji ko da wasa."
"Daddy..."
"Yi min shiru mutumin banza kawai. Ka rasa wanda za ka kawo sai 'yar gidan Muhammadu. To wallahi ba zan taba hada jini da mara asali ba. Ashmaan ka kiyaye ni in ba haka ba wallahi na lahira sai ya fi ka jin dadi."
Da karfi Daddy ya buga kofan bayan ya fita. Fuskar Ashmaan ta yi jajawur sakamakon marin da Daddy ya mai. Mommy na tsaye ta na kallo shi da wani expression da ba zai iya cewa meye ba.
"Sai Rabi ta zuba ruwa a kasa tasha. Aikin malamai ya yi kyau."
Da gwiwowin shi ya rarrafa har inda ta ke ya ruko hannunta. "Mommy dan Allah ki yi mun rai, ki ganar da Daddy. Wallahi Mommy zan iya mutuwa idan na rasa ta."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!" Mommy ta ce ta na rushewa da kuka. "Shikenan sun gama da kai Ashmaan. Akan wannan mai idanun mujiyan kake wannan abun."
"Mommy dan Allah..." Ashmaan ya ce ya na kara rikon da ya ma hannunta.
"Wallahi zan tsinse maka in ba ka shiga hankalin ka ba. Ba kai babu yarinyan nan har abada, kai ba ita ba kadai ba ma. Ba kai babu su har abada, na rabaka da su in har ni ce na tsugunna na haife ka. Ko bayan raina Ashmaan ka aure ta wallahi Allah Ya isa, bazan taba yafe maka ba."
Wani abu Ashmaan ya ji ya duke shi a tsakar kan shi har lumfashin shi na daukewa. "Mommy...."
"Zaman su yazo karshe dan ban san mai zasu ma nan gaba ba." Fincike hannunta ta yi daga na shi ta yi fita ta bar shi a tsugunne, zuciyar shi na radadi kaman zata fita.
~~~
Maimoon na zaune a tsakar gida ita da Mimi, Sadiya da Jasrah su na mulmula gullisuwa. Hira su ke yi amma kwata-kwata hankalinta ba ya kan su. Tun ranan da Hamma Ashmaan ya fada mata sirrin zuciyarsa natsuwa ta bar ta. Tabbas magangannun shi su zo mata a bazata. Ba ta taba kawowa a rai ba Hamma zai ce ya na son ta.
Murna ya kamata ta yi, saboda Hamma Ashmaan mutum ne. Amma sai dai ita kunci ta ke yi saboda tasan kancewa da shi kama zuba ruwa ne a cikin mai.
Dole ta hakura ta ture shi bawai dan bata son shi ba. Saidai so ya yi kadan a circumstance irin na su. Akwai abubuwa da yawa da a ke la'akari da su kafin mace da namiji su yarda za su kasance tare da juna har karshen rayuwarsu. Bayan son da ke tsakanin su, babu wani abu da Hamma zai iya bata.
Daga sama su ka ji an fado gidan kaman daga sama. Kafin ta san ko meye ta ji an finciko ta ana ja har saida su ka bar bangaren su. Wulli aka yi da ita ta je ta daki bango ta buga kai. Ba anan abun ya tsaya ba, duka kawai ke sauka a jikinta ko ta ina.
"Kin yi kadan, kin yi kadan...." Abunda muryar ke maimaitawa kenan.
Wani abu ta ji ya mata rumfa kaman jikin mutum. Ta na daga kai suka hada ido da Hamma Ashmaan.
Me ke faruwa?
"Ka matsa a wurin Ashmaan!"
"Mommy ki natsu dan Allah." Ashmaan ya ce ya na kare Maimoon da bata san abunda da ke faruwa ba a bayan shi.
Wani irin ciwo kanta ya ke yi kaman zai tsage. Kokarin gano abunda a ke ciki ta ke yi amma ta kasa. Mutanen gidan ne cirko-cirko a tsaye suna kallon Ashmaan ya na rike da Mommy ta na hargowa akan ya saketa.
Ummi ta fito idonta ya saukan Maimoon da ke tsugunne dafe da kanta. Da sauri ta isa gaban 'yar ta Sadiya da Mimi na binta a baya. Tare su ka kamata ta mike.
Kallon Mommy Ummi ta yi, "Na bar ki da Allah Suwaiba, zai karban mun hakkina."
"Ni da ke wa zai bar wani da Allah? Kin je kin asirce mun yaro ya fita daga hayyacin shi. To wallahi kin yi kadan, ko bayan raina ban yarda ya hada zuri'a da ke ba."
"Ko ni bazan so hada zuri'a da ke ba Suwaiba. Ki kwantar da hankalin ki, danki ko shine autan maza ba zai taba auren 'ya ta ba."
"Ummi," Ashmaan ya ce a tsorace.
"Sai ki ce mata ta daina like mai kaman cingam," Mommy ta ce. "A zahiri ka ganta kaman mutuniyar kwarai amma kowa ya san yawon banza ta ke yi."
Ido Maimoon ta runtse, kalaman Mommy na sukarta.
"Suwaiba!" Ummi ta daka mata tsawa. "Ya ishe ki haka. Ke har kina da bakin da za ki ce yaran wasu na yawon banza?"
"Mommy dan Allah ki yi hakuri, mu koma ciki." Kokarin janta ciki Ashmaan ya ke yi amma ta ki.
"Ki fita ki bar mun gida. Ku fita ku bar mun gida."
A haka Baffa ya shigo ya same su. Idon shi kan iyalin shi ya fara sauka ya ga Ummi, Mimi da Sadiya rike da Maimoon da ke a fige kaman wanda ta tashi daga ciwo. Jini ne ke bin fuskarta.
Baffa ya taka inda suke tsaye a rude. "Rabi me ka faruwa haka? Me ya same ta?"
Ummi kasa bashi amsa ta yi saboda wani kuka da ta saki. Bai taba jin bacin rai irin haka ba. Abun har ya kai a rika zubdawa yaranshi jini.
"Muhammadu ka tattara ka bar mana gida." Muryar Mommy ta karade wurin. Ta na magana ta na huci kaman wanda ta yi dambe.
"Gida dai ko? Shikenan zamu bar muku gidan ku Suwaiba. Mun gode da irin halaccin da kuka nuna mana irin na 'yan uwantaka."
"Wani 'yan uwantaka? Lokaci ya yi da zaka san babu wani dangantaka ta jini a tsakanin mu."
"SUWAIBA." Daddy ne ya fito jin abunda Mommy ke cewa. "Ba ki da hankali?"
"Ai gaskiya ce, ku fada mai ba ku hada komai da shi ba. Dan tsuntuwa ne mara asali."
•
•
•
•
•
Dun! Dun! Dunnnnnn!!!
Hehe 😜
Jama'a yau juma'a kar a manta a karanta Suratul Kahf💕
-Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro