BABI NA GOMA SHA HUDU
~~BABI NA GOMA SHA HUDU~~
Suna zaune a waje zafi ya koro su, da yake an daɗe da dauke wuta. Mimi da Sadiya na taya Ummi tsintar wake, Maimoon kuma na ƙoƙarin kammala tsifar da take yi.
Tana zaune a bakin ƙofa sai ƴan ƙananan tsakin take ja.
Ummi ta dago kai ta harare ta. "Wa ya saki tsifar? Kin bi kin cika mana kunne da tsaki."
Shiru Maimoon tayi dan a cike take. Kuma duk Ummin ta ja mata ai. Daga ce mata ta ɗan lallabe mata kai kawai ta kama ta mata kitso har wurin talatin. Gasu ƴan ƙanana kafin ta kunce ɗaya aiki ne. Ita da kitson ta in yayi wuta ya kai goma.
"Adda in zo in taya ki?" Inji Sadiya.
Da sauri ta ce, "Eh dan Allah, wallahi hannuna har ya riƙe."
Ummi taɓe baki tayi ta cigaba da aikinta. Sadiya ta tashi ta wanko hannu sannan ta kama ma Maimoon.
Gashin nada tsawo sosai da cika, gashi baki sidik dashi. Jelar har ƙugunta in ta daure, gashin gaban kuma har ya sauko kan goshinta. Bata cika yin kitso ba saidai ta gyara shi ta maida ta daure. In an kwana biyu ta shafa mai, in kuma ya isheta ta tsaga ta yiwa kanta kitso biyu ko huɗu.
Suna zaune Baffa ya shigo cike da fara'a. Ganin mahaifinta a yanayi na farin ciki ya sa duk wani bacin ran da take ji gushewa.
Sannu da dawowa suka mai. Mimi ta mike ta amsa ledojin da ya shigo dasu. Guda biyu ya bata ta kai ɗaki sauran kuma ya ba Maimoon ya ce taje ta raba.
Tuni ƙamshi ya cika mata hanci. Kicin ta shiga ta dauko kwanuka guda biyar. Masa ce da tsire a ciki. Rabawa tayi sannan ta kira Sadiya tazo ta kai.
A tsakar gidan suka shimfiɗa tabarma. Kafin su zauna Baffa ya ba Mimi kudi ya ce ta siyowa kowa lemu. Da sauri Sadiya ta ce zata raka ta.
Bayan sun fita Ummi ta kalla Baffa. "Baban Mu'azzam wani abun ne ya faru?"
Dariya Baffa yayi. "Albishiri ne, kin siya?"
Da sauri ta daga kai. "Na siya, koma nawa ne."
"Toh shikenan, bari mu gama cin abinci."
Cikin kwanciyan hankali suka ci abincin su. Kaman Ummi, Maimoon ma ta ƙosa taji albishirin da Baffa ya dawo dashi. Ta san ba ƙaramin abu ne zai sa mahaifinta farin ciki haka.
Sadiya na gama ci ta wanko hannu ta koma ta zauna kusa da Baffa. "Baffa, mun gama. Ka faɗa mana surprise ɗin."
Hannu yasa ya shafa kumatun ta. "To auta," kallon shi ya maida kan Ummi. "Alhamdulillah, yau aka dauke mu aiki."
Sadiya ta yi ihu ta rungume shi. Ummi kuwa kuka ta fashe da shi, Mimi na rarrashinta. Hamdala Maimoon keyi ba iyaka.
Duk abunda kaga bai faru da kai ba, lokaci ne beyi ba. Da yawa muna ƙosawa akan lammuran da Allah Ya ruga Ya rubuta. Mutum mai haƙuri baya taɓa faɗuwa.
"Ba aikin ɗin-ɗin bane, temporary employment ne. Amma muna sa ran samun na ɗin-ɗin nan gaba, sai a taya mu da addu'a."
"Addu'a ai kullum cikin yinta akeyi," Ummi ta ce a tausashe. "Allah Ya sanya alkhairi, Ya kuma bada sa'a."
Da Ameen duk suka amsa.
Bayyana irin farin cikin da suka tsincin kansu a ciki abune mai wuya.
****
Dawowarta kenan daga aiken Ummi taji muryar Habiba na kwada sallama. Da sauri ta fita, tana murmushi.
Habiba na ganinta ta bata rai. "Ya haka?"
"Ban gane ya haka ba?"
"Baki shirya ba? Ke da mukayi da ke zan zo in dauke ki."
Ido ta runtse tana cizan lebenta na kasa. Ta san yau mita wurin Habiba sai Allah. "Da yau ne abun?"
Hararta Habiba tayi. "A'a shekaran jiya ne. Haba mana Maimoon, shi yasa ma fa ban taho da wuri ba dan in baki time ki shirya a tsanake. Shine zaki wani ce mun da yau ne?"
"Allah Ya baki hakuri. Mu je to in shirya. Shirin nawa duka minti nawa ne? Naga dai ba ni ce mai nawa ba."
Tabe baki Habiba tayi. "Ke dai kika sani. Kuma ke da Safara'u, dan tun dazu take kirana kaman na mata sata."
Gaba daya ta manta yau ne walimar bikin gidan su Safara'u. Duk a zatonta sai gobe.
Saida ta raka Habiba ta gaida Ummi sannan suka tafi daki.
A gaban wardrobe ta tsaya hannu a kan kugu, ta rasa wasu kaya zata saka. Tana cikin wannan tunanin Sadiya ta fado dakin da gudu har ta tsoratata.
"Adda Habiba ina wuni."
"Lafiya lau CEO mai gullisuwa,"
"Kai Adda," Sadiya ta ce tana sunne kai.
"Akwai gullisuwar?" Da sauri ta daga kai. "To a bani na dubu uku."
Kaman yanda Hamma ya musu alkawari, washegarin ranan da yazo da daddare ya aiko musu da ledoji da robobin da zasu dunga sa kayan sana'ar a ciki. Ya ce kuma su fada sunan da suke so a saka a stickers din. Daga karshe suka yanke shawaran amfani da A&S Delectable treats.
Hamma da taya bera bari harda waya ya siyo musu wai dan su dunga talla a social media, ana samun ciniki sosai anan. Ranan murna wurin Mimi da Sadiya kaman su zuba ruwa a kasa su sha.
Ya so ba Maimoon waya itama amma ta ƙiya. Ba yanda beyi da ita ba, daga karshe ya haƙura.
"Har yanzu baki ga kayan da zaki saka ba?" Habiba ta tambaya.
Sadiya da ta shigo da leda a hannu ta ce. "Adda ki sa daya daga cikin dogayen rigunan da Hamma ya kawo miki mana."
Da sauri Habiba ta ce. "Nuna mun su."
Maimoon matsawa tayi ta basu wuri. Tana jin su suna kus-kus suna cicciro kaya. Chan Habiba ta juyo da ash din doguwar riga. Miƙama Maimoon tayi tace tayi sauri ta shirya.
Babu musu ta amsa taje bayi ta chanza kaya. Rigar A-shape ce dan haka bata kama mata jiki ba. Tana fitowa Habiba ta zaunar da ita wai zata mata kwalliya.
"Ke ni rabu ni. Ni da zan sa niqab wani kwalliya zaki mun."
"At least ki bari in sa miki eyeliner."
"Ni fa bana so, kwalli na ya isheni."
Habiba ta tura baki tana kallonta kasa-kasa.
Tana son yi mata kwalliya ko dan yanda Maimoon din ke kara kyau, tun balle in ta dage ta mata eye makeup, idanuwan nan nata suka kara fito tar! Da su. Sai dai kash! Kawarta ba mai son kwalliya bace.
Dama ta wanke fuskarta, mai kawai ta shafa sai ta murza 'yar hoda dan dauke maiko. Sannan da zizara kwallinta.
Habiba ce ta dage sai ta yi mata lining ido. Haka dai ta hakura saboda Habiba akwaita da mita.
Tayi kyau sosai. Kayan sun haska kalar fatarta sosai. Niqabin ya fi kayan haske da kadan. Ta daura abunta cike da kwarewa, idanunnan nata farare kal! Kadai ake gani, gashi sun sha kwalli da eyeliner sun kara haske sosai.
"Kai Hamman kin nan ya iya zabe," Habiba ta ce yayin da take daukar Maimoon hoto. "Kayan babu hayaniya amma so classy."
Murmushi tayi bata ce komai ba.
"Hamma naji dake gaskiya," Habiba bata hakura ba ta sake ce wa.
"Sosai kuwa Adda Habiba," Sadiya tayi caraf ta amsa.
Ido Habiba ta ware tana kallo Sadiya, wani shu'umin murmushi kwance a fuskarta. "Kodai kodai..." ta ce tana kada kai.
Girgiza kai Maimoon tayi. "Baki da aikin yi. Ni mu tafi dan Allah."
Sun isa gidan har an fara tafiya, sauran 'yan mutane kadan da yake a hall za'ayi abun. Dakin Safara'u suka nufa, sun sameta ita da 'yan uwanta suna ta shiri.
"Kaya kawai zan saka mu tafi," Safara'u ta ce tana ganin su.
Kallon Habiba Maimoon tayi da ido take nuna mata gashinan suma basu gama shiryawa ba. Yi tayi kaman bata gane abunda take nufi ba.
"Safara'u kawayen ki ne?" Wata matsahiya da ta shigo yanzu ta tambaya tana musu wani irin kallo. A dakile Safara'u ta amsa mata da eh. "Sannun ku."
Maimoon kadai ta amsa. Ita bata taba ganinta, ba kaman Habiba da ta san yawancinsu ba. Zungurinta Habiba tayi.
Kafin ta bata amsa matan ta sake magana. "Ita kam wannan bata cire niqab dinne? Naga dai duk mata ne yan uwanta a cikin dakin."
Da mamaki ta dan daga ido ta kalle ta. Ko me niqabinta ya tsare mata? Oho. Shareta sukayi ta cigaba dan 'yan kananan maganganu.
Mutane na ba Maimoon mamaki. Ko ina ruwanta da shigar da tayi. Kawai mata daga ganinta zata tuso ta gaba. Ikon Allah.
"Na shirya, mu tafi." Safara'u ta ce ba tare da ta tanka mata ba. "Zubaida sai kun iso," ta ce ma daya daga cikin wa'inda suka samu a dakin.
Suna shiga mota Safara'u ta ce. "Sai bakin hali irin na ubanta."
Da mamaki Maimoon ta kalle ta. "Wacece ita?"
"Nafisa ce 'yar gidan Baba Karami."
No wonder. Basu shiri sam da Safara'u, tana dai jin sunanta amma bata taba ganinta ba.
A Arewa House aka hada gagarumar walima dan murnar auren Najeeb da matarsa Sumayya. Babban malamin sunnah ne yazo yayi wa'azi mai ratsa jiki. Bayan ya gama wa'azi akayi serving abinci.
Basu bar wurin ba sai wurin karfe shida. Dama da motar Safara'u suka taho, saboda haka basu wani tsaya neman wanda zai maida su ba.
Habiba ce ke tuka motar, Safara'u na gaba. Maimoon na zaune a baya ta hakimce. Suna cikin tafiya suna hira kawai suka ji mota ta fara wani kara.
"Lafiya?" Maimoon ta taso. "Ko ni kadai ke jin wani kara."
Kafin wani daga cikin su ya amsa mota ta mutu. Allah Ya so babu kowa a bayan su. Da sauri Habiba ta sauka gefen titi.
Sunyi sunyi amma ta ki ta tashi. Dafe kai Safara'u tayi tana salati. "Saida Mama ta ce kar in dauki motarnan."
"Yanzu ya zamuyi?" Habiba ta ce tana kokarin kunna motan. Amma sai tayi wani kara sai ta mutu.
Gashi Magriba ta tunkaro kai. Maimoon ta girgiza kai. Su kam suna yawan fadawa cikin matsala akan abun hawa ana gab da Maghriba.
"Bari in kira Ya Najeeb ya turo wani ya dauke mu," Safara'u ta ce tana fiddo wayarta sannan ta kara a kunne. Chan tayi tsaki. "Shi mutum ayi ta kiranshi ba zai dauki waya ba."
"Ke ma kin san yana chan yana hidima, wata kila wayar bata kusa da shi," Habiba ta ce mata. "Kawai mu tari napep mana."
Hannu Maimoon tasa ta buge keyarta. "To motar kuma fa?"
"Au! Na manta."
Sake gwada kiran Safara'u tayi. A ka ci sa'a ya amsa. "Ya ce ya zai turo abokin shi."
Suna zaune anan motoci na ta wucewa. Har aka kira sallah aka gama babu labarin abokin Najeeb. Har sun cire rai sun yanke shawaran rufe motan su tafi sai gashi sun iso
"Salamu alaikum," ya ce. "Kuyi hakuri mun bar ku kuna ta jira. Bai sanar dani ba sai bayan da aka fito masallaci. Ku shiga mota a bari ya duba motan."
Safara'u suka tura gidan gaba, ita da Habiba suka shige baya. Maimoon din aka fara saukewa. Ta musu sai da safe da Allah huta gajiya ta shige gida.
Washegari bayan la'asar sai ga wani yaro karami dan layin wai an aiko shi ya ce ana sallama da Maimoon.
Ware idanu tayi. Tana tunanin to waye wannan yake sallama da ita da ya har yasan sunanta. Ce ma yaron tayi ya ce bata nan.
Bayan yan mintina yaron ya kara dawowa. "Wai ya ce Mukhtar ne ba dan halin shi ba dan Allah ki fito."
Harar yaron tayi. "Zuwa kayi ka ce mai ina nan ko me?"
Sosa kai yayi ya fice da gudu. Tsaki ta ja tana ta fita ko kar ta fita. Kuma dai daga an ce ana sallama da ita sai ta kwashi kafafu ta tafi. In ya gaji da jira koma waye ya tafi dan babu inda zata je.
Tana zaune ta manta da zancen Mimi ta dawo daga makaranta. "Adda wani na can fa yana jiran ki."
"Au, bai tafi ba? To a gaishe shi."
"Daman kin san da zuwan shi ne?" Banza tayi da ita ta cigaba da aikinta. "Adda fa ba kyau."
"Ki kiyaye ni." Ta ce tana nuna mata yatsa. "Ni na ce ya zo? Ban fa san ko waye ba. In naje yayi gaba dani ai shikenan."
Kai Mimi ta girgiza tana dariya. Wai yayi gaba da ita. Tun bayan Fa'iz idan wani yazo wurinta shikenan ya zama babban mai laifi. Halin ko in kulanta shi yake koransu. Gani suke girman kai gareta. Basu san an ma Addarta tabon da har yanzu take fama dashi ba.
"Yanzu dai kiyi hakuri ki je. In kin je kya ce mai kar ya kara zuwa."
"Na ce miki ban san waye ba. Saboda haka babu inda zani."
"Wani baki ne haka, dan gajere yana da jiki kuma."
Fuska Maimoon ta kara tsukewa. Yanzu haka mutumin da aka turo daukan su jiya ne. Wai ina dalili? Ace dan an kawo ka gida sai an sake dawowa neman ka. Daga yau ta gama shiga motan wani ya maido ta gida.
Tana dacin rai ta fisgi niqabinta da hijabi ta tafi. Zata fita ta ci karo da Mommy da Fauziya zasu fita a mota. Tsayawa tayi suka wuce dan sai a nemi abi ta kanta.
Jingine jikin mota ta same shi yana latsa waya. Jin isowarta yasa ya dago kai. Sai kawai ta ga yayi wani murmushi. Abu taji ya tsaya mata a makoshi.
"Salamu alaikum," ta yi magana chan kasa.
"Wa'alaikumus salam Malama Memuna, sannun ki da zuwa."
Kaman ta ce mai bata so ana kiranta Memuna, sai kuma tayi shiru.
"Kinyi mamakin ganina ko? Ji nayi bazan iya zama ban sake ganin ki ba."
Babba da shi bai jin kunyan yin karya. Mutane ba kunya ko kadan.
"Da farko dai sunana Mukhtar. Ni dan asalin jahar Kano ne amma anan Kaduna na tashi. Ni ne na uku a gidanmu. Nayi karatu anan Kaduna har secondary sannan na tafi Sokoto na karanta Agriculture. Yanzu dai ina aiki da Federal Road Safety."
Ko wa ya tambaye shi takaittacen tarihin rayuwarshi, oho. Tana dai jinsa yana ta zuba dan ba fahimtar abunda yake cewa take yi ba.
Chan ta tsinko muryar shi yana cewa. "...ko zaki daga niqabin inka fuksarki."
Kam bala'i!
Ta bude baki kenan daga sama taji an kira sunanta a fusace. "Maimoon."
"Hamma—" sai kuma tayi turus ganin irin kallon da yake mata.
"Me kike yi a nan?"
Mukhtar ya dan yi gyaran murya. "Bawan Allah mu dan ganawa ne."
Ko kallon shi Hamma be yi ba. "Oya, wuce mu tafi."
"Ah ah. Malam ya zaka ce mata ta wuce?"
"Na ce ki wuce mu tafi. Kai kuma ka koma daga inda ka fito."
Gaba tayi Hamma Ashmaan na binta a baya. Tazo shiga sashensu ya dakatar da ita. "Yi nan," ya ce yana nuna hanyar garden din dake bayan gidan.
Suna isa ya sha gabanta. Kallonta yake kaman wanda tayi gaggarumin laifi.
"Tsayawa da sauri? Moon duka nawa kike? How old are you? Na ce duka nawa kike..."
Jim tayi tana kallon shi. Iko sai a Allah. Ita dariya ma ya bata inda ya dage yana masifa kaman ya ari baki.
"....kuma daga yau na sake ganin ki da wani sai na karya maki kafafu. Kina ji na?"
Kai kawai ta daga mai.
"Wuce mu tafi dama ina son ganin Ummi."
****
Kalaman da ya ji ba karamin girgiza shi sukayi ba. Ji yanda suke tsara batawa wani rayuwa babu ko dar a tare dasu.
Kafafunshi ya ji suna neman su kasa daukar shi.
•
•
•
•
•
Do you also smell something burning?🤭
Kuma na kusan tafiya hutu in har baku commenting. Ko dai baku jin dadin littafin ne?🤧
Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro