Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA GOMA SHA DAYA























~~BABI NA GOMA SHA DAYA~~







"ADDA!"

Ƙaramin tsaki Maimoon taja, wata sa'ain Sadiya ba isasshen hankali gareta ba. Meye na kwala mata kira haka, sai ka ce bata san inda take ba. Hularta ta maida ta fita dan ganin wani dalili ne Sadiya ke kwala mata kira kaman makauniyar da tayi batan hanya. A kitchen ta same ta ita kaɗai. Ko ina Mimi?

"Ya akayi?"

"Adda na cika sugar a kunun, kuma Baffa baya so. Adda ya zanyi? Wallahi zai mun faɗa." Ta karashe maganan kaman zata yi kuka.

Da idanu Maimoon ta bita, sai wani kwalo ido take waje. "Ruwan ki kuma wannan."

"Kai Adda, yanzu ya za'ayi?"

"Yanda za'ayi?" Ta tambaya. Da sauri Sadiya ta daga kai. "Mai kwatan ki yau sai Allah. Ke baki ji, so nawa za'a ce miki ki dinga sa sugar kaɗan, amma ba kya jin magana. Yau sai kin ansa query."

Sadiya tayi raurau da fuska kaman zata yi kuka. Abun ya ba ma Maimoon dariya, amma sai ta danne ta haɗe fuska. In kana so kuyi faɗa da Baffa, to cika mai gishiri ko yaji a abinci, ko kuma sugar a kunu, nan zaku hau sama da shi. Sam! Baya so.

"Adda Moon dan Allah."

"Ke rabu da ni, yau baku kuke girkin ba? Ni meye nawa a ciki?" Har ta juya zata tafi, sai taji Sadiya ta bata tausayi. Dan faɗan Baffa abun fargaba ne, kwatakwata bai iya fushi ba. Komawa tayi, ta ce ta daura wani ruwa ɗan kaɗan. "Wani za'a dama, amma daidai nashi. Mu ma sha sugarn haka, ya muka iya?"

Dariya Sadiya tayi, sannan ta daura ruwa a risho.

Yau Alhamis, dukan su azumi suke yi. Dama ko wace litinin da alhamis azumi suna yi, sai dai in ɗaya na da lalura, ko kuma dai wani abun, saboda yau da gobe.

Yau Mimi da Sadiya Ummi ta sa yin kayan buda baki, ta ce ma Maimoon ta je ta kwanta, tayi wani abun, ko lazumi tayi. "Naga yaran nan wani kyuya ke son kama ku, bakwa komai, sai dai ku bar wa Addan ku ko? Toh taje hutu, ku zaku dinga komai."

Murmushi Maimoon tayi, ta ce ma Ummi babu komai. Ummi ta dakatar da ita, "In bakya nan wa zaiyi? In kika tafi sai nayi musu sabon training fa, a'a, a'a. Kuma in basu iya ba yanzu sai yaushe? Ko yau za'a aurar dasu su zauna."

Kunya Ummi ta bata, ji yanda take magana kaman nan kusa zatayi aure.

"Adda ruwan ya tafasa." Muryar Sadiya ta tsinke mata tunanin da takeyi. Wani kunun ta damawa Baffa, babu tsamiya, sai lemun tsami ta matsa. Bata sa sugar ba, kar taje itama hannun ta ya kubuce. In an kai mai yasa sugan da kanshi. A flask ɗin shi ɗan madaidaici ta juye.

"Ina Mimi?"

"Taje kai niƙa."

"Zan iya tafiya ko?" Sadiya ta sadda kai tana murmushi.

Kai Maimoon ta girgiza, sannan ta koma ciki. Dan karamin Qur'ani ta dauko, zatayi tilawa. Alhamdulillah, ta sauke duka izu sittin shekara biyu da suka wuce, tare da Safara'u da Habiba. Tana son komawa islamiyan ta sauke wasu littatafan, tana rokon Allah ya bata ikon yin hakan. Suratul Yusuf ta budo ta fara karantawa da ƙira'a mai dadi.

Gab da Maghriba Baffa da Ummi suka dawo, sun je dubiya wani abokin Baffa bai da lafiya. Lokacin Sadiya da Mimi har sun kammala aikin su, su Ummi basu ɗaɗe da shigowa ba aka kira sallah. Maimoon ta kai ma Baffa dabino.

"Barka da shan ruwa Baffa."

"Barka kadai Maimu."

Dabino uku ya ci sannan ya fita masallaci. Mimi ta kawo musu abinci shi da Ummi ta jera. Kosai suka soya sai kunu da aka dama. Ita ma arwala taje tayi. Tare suka zauna su uku suka ci abinci. Sadiya ta kalla Maimoon. "Adda ya kika ji abincin namu?"

Ƙaramin murmushi tayi tana kallon Sadiya da ke daga kafaɗa, ita a dole tayi abun arziki. "Ina sha Mimi ta soya kosan?"

"Ni ce," Mimi tayi saurin amsawa. "Adda kunu kawai ta dama, kunun da ta cika sugar, sai da nace ta bari in dawo dan hannun ta sai a hankali. Bata iya sa gishiri da sugar ba, zanbadawa take yi."

Hararar Mimi Sadiya tayi. "So ɗaya ne fa, sai wannan."

Maimoon na jin su bata ce uffan ba, ganin abun naso ya zama faɗa ta ce ma Sadiya ta dauko mata ruwa. Mimi kuma ta kwashi kayan da suka gama cin abinci ta fita da su. Wayar ta dake cikin jaka taji tana ringing, bata son matsawa. Ko waye ke kiranta a wannan lokaci? Ta gama shan ruwa yanzu yanzu, bata son takura, ai a bari ta huta. Wayan ta tsinke aka sake kira, dan karamin tsaki taja sannan ta tashi ta dauko. Sunan Hamma Ashmaan ta gani.

"Assalamu alaikum." Ta faɗa bayan ta kara wayan a kunnen ta na hagu. Wuri ta samu ta zauna, ta mike ƙafafuwan ta.

"Wa'alaikas salam, Malama Moon. Sai kinga daman amsa mun waya ko?"

Dariya tayi, sautin har cikin kwakwalwan Ashmaan.

"Ba haka ba ne Hamma."

"To yaya ne? Kullun na kira sai a ƙi daukar waya ta. Ko sai na cika form kafin zan iya magana da ke?" Ya tambaya cike da zolaya.

Bata san abunda zata ce mai ba, dan haka ta kawar da zancen ta hanyar gaishe shi. "Ina wuni?"

"Lafiya qlau Moon, ya Kaduna?"

"Alhamdulillah, ya aiki?"

"Aiki gashinan, mun gode Allah. Nasan baki ma san inda na tafi ba, to ina Lagos."

"Waya ce ma ban sani ba?"

"Hmm," kawai ya ce. "Ya su Baffa da Ummi? Ki ce ina gaishe su."

"Zasu ji." Nan Hamma Ashmaan ya dunga jan ta da fira har suka kusan minti talatin a waya. Kiran sallah Isha'i ne ya sa ya mata sai da safe. "And Moon, dan Allah a taimaka a dinga daukar waya ta."

Dariya ya bata sosai. Hamma Ashmaan na tuna mata da Hamman ta, komai nasu tare sukeyi. Harta kayan su iri ɗaya suke sawa, kowa ya gansu sai yasha ƴan biyu ne, saboda har kama sukeyi. Tana ganin Hamma Ashmaan kaman Hamma Mu'azzam, in yayi wani abun sai taga kaman yayanta ne ya dawo. Sai sa take girmama shi ba kaɗan ba.

"Toh Hamma, in sha Allah."

"Yawwa Moon, good night."

***

"Maimoon ya kika yi shiru? Ke me kike gani ya dace in yi?" Safara'u ta jefa ma Maimoon tambaya. Maimoon ta ɗan ja lumfashi kafin ta gyara zaman ta.

Su uku ne zaune a cikin dakin, Safara'u, Maimoon sai Habiba. Habiba da Maimoon sunzo duba mahaifiyar Safara'u da bata ji dadi ba kwana biyu. Sosai Maman Safara'u ke son su, ta dauke su kaman 'ya'yan da ta haifa, mace ce mai kirki, da daraja mutane.

Yanzu haka suna zaune a dakin Safara'u inda take fada musu kanin mahaifin ta ya sata gaba a dole sai ta fiddo miji an hada da na yayanta Najeeb.

"Me Baba ya ce?" Maimoon ta tambaya. Ajiyar zuciya Safara'u tayi, idanun ta duk sunyi ja saboda kukan da ta sha. Tausayin ta ya kama Maimoon, kowa da irin tasa jarabawar. Fatan kawai Allah ya sa muci.

"Me fa ya ce? Ba abunda ya ce Maimoon, ni gani nake kaman shi ma goyon bayan shi yake. Auren nan fa in lokacin ya zo babu wanda ya isa ya hana, haka in lokaci be yi ba babu wanda ya isa yasa a yi. Amma sunƙi gane hakan. Duka nawa nake, ashirin da uku fa, amma sai kace wanda ta shekara talatin a gida."

"Addu'a zakiyi Safara'u, kuma kiyi isthikara. Allah ya zaba mana mafi alkhairi."

"Ameen ya Rabbi," Habiba ta amsa. Nan suka dauko wata firar daban dan su kwantarwa da Safara'u hankali. Basu bar gidan ba sai bayan sallan la'asar. Maimoon ta kalli Habiba tana murmushi. "Sai anjima, ki gaida mun Mama."

"Ai baki isa ba," Habiba tayi magana tana hararar Maimoon. "Yamma fa yayi, ki bari zan ƙara dawowa." Maimoon ta ce mata

"Wa? Ke din? Da dai ban san hali ba. Ke fa kifin rijiya ce, baki zuwa ko ina sai ta kama."

Ba yanda Maimoon ta iya, gidan su Habiba suka isa. Nan ta cika mata gaba da abinci. Hararta Maimoon tayi. "Idan ba so kike na fashe ba, wannan abincin ina zan kai shi?"

"Sai kin cinye kuwa."

Juya manyan idanun ta tayi, amma bata ce komai ba. Sai chan Maimoon ta kalla kawarta ta, ta faɗa mata ko kuwa? Chan wata zuciyar ta bata shawara akan ta faɗa mata ko nauyin dake girjin ta zai rage. "Faaiz ya zo."

Da sauri Habiba ta juya ta kalle ta cike da mamaki. "Yaushe?"

Nan ta faɗa mata duk abunda ya faru. Wani sanyi taji a ranta ta faɗa ma aminiyarta damuwarta. Ba ta faɗa a gaban Safara'u ba saboda itama matsalolin ta sun ishe ta.

"Amma bashi da ta ido, in yana da kunya ai ko kallon ki bazai kara yi ba. Amma da yake tantiri ne, ke kika tsaya sauraran shi ma ai. Da baki dauke dan banza da mari ba, da idanun shi kaman gyada."

Dariya ta ba Maimoon, tayi dariya sosai ganin yanda Habiba ta dage sai masifa take yi.

"Kar ki kara sauraren shi dan Allah Maimoon. Wallahi he's not worth even a single second of your time."

"Ina zan kara? Raba ni, harda matar shi yazo, ya kawo su hutu." Tabe baki Habiba tayi bata ce komai ba, duk cikin cousins din Maimoon ta tafi jin zafin Hasina. Da taji labarin auren ta da Faaiz kaman tayi hauka.

Kafin Maghrib Maimoon ta isa gida. Gabanta ne ya fadi ganin Daddy, kan ta a ƙasa ta gaishe shi. Bata damu da rashin ansawar shi ba, dan ita gani take ma bai taba ansa gaisuwar ta ba.

"Adda sannu da dawowa." Mimi ta fada tana murmushi. Murmushi itama tayi, sannan ta ta nufi dakin Umma dan ta sanar da ita ta dawo.

Da daddare Sadiya ta samu Maimoon ta mata kitso. "Adda dan Allah, ko guda goma ne. Gobe Monday, wallahi naje makaranta baza su barni in shiga ba, Adda Moon ki taimaka."

Ko kallon ta batayi ba, sai yanzu ta daddare kawai zata ce ta mata kitso. "Sadiya ki rabu da ni, sai yanzu kika san zakiyi kitso? Sai kije ki nema wanda zai miki."

Sadiya ta zumburo baki gaba kaman zatayi kuka. Tasan in ta je ta samu Ummi fada zata mata, zama ta iya cewa Maimoon kar ta mata, in taje makarantan su mata duk abunda zasu mata, gobe ba zata kara ba. Gashi Mimi ko tsagar kirki bata iya ba.

Suna zaune wayar Maimoon tayi kara, ta riga da tasan wa ke kira. Tun ranan Alhamis da ya kira ta kullun sai ya kira da daddare sunyi hira. Kafin hannun Maimoon ya kai kan wayar Sadiya tayi saurin daukewa, da mamaki ta tsaya tana kallon ta.

"Hamma Ashmaan, ina wuni....Lafiya qlau...gata nan, Hamma Maan danallah kace ma Adda Moon ta mun kitso....wallahi Hamma duka na za'ayi a school gobe fa...ta ce ba zata mun ba...please Hamma, kaji, ka mata magana...yay! Thank you. Gata."

Wayar ta mika ma Maimoon fuskan ta dauke ta murmushi, ganin kallon da Maimoon ke mata yasa tasha jinin jikinta. Ƙin ansan wayar Maimoon tayi, Sadiya ta faɗa ma Ashmaan ya ce tasa shi a speaker.

"Haba Moon din Baffa," muryar shi ta ratsa gaba daya dakin. "Ki taimaka ki mata kitson kinji. Moon? Ki na ji na?"

"Ina jin ka Hamma."

"Good, ki taimaka. I promise you bazata kara ba, nasan kin gaji but please for me." Cikin kwantatcciyar murya yake magana.

"Amma tsakani da Allah sai yanzu karfe tara zata zo ta wani ce in mata kitso."

"Nace kiyi hakuri ai Moon, please."

"Toh naji." Chan kasan maƙogaro tayi maganan, tana hararar Sadiya dake tsaye kaman mutuniyar arziki.

"Yawwa Moon sai sa nake son ki, make my little sister look pretty, zan kira gobe da rana In sha Allah."

"Sai da safe."

"Sai da safe, a gaida mun su Baffa." Da wannan kiran ya katse. Manyan idanun ta maida kan Sadiya. Sadda kai tayi, tana wasa da yatsun ta. "Adda Moon dan Allah kiyu hakuri."

Ƙaramin tsaki Maimoon ta ja. "Ni zo ki zauna." Kan Sadiya dai ya sha zunguri, bata da bakin magana haka ta zauna. Duk yanda taso ta mata manya kitso ta kasa, kalaba ta mata ƴan ƙanana.

"Toh tashi ki bani wuri."

Da sauri Sadiya ta mike, ta juya ta kalli Addar tata. "Nagode Adda Moon."

Yanda tayi maganan ya ba Maimoon dariya, taso ta danne sai ta kasa tayi murmushi. Bata ce mata komai ba, ta fita ta wanke hannu. Sannan ta dawo tayi shirin kwanciya.





~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro