Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA GOMA SHA BIYU





~~BABI NA GOMA SHA BIYU~~





Ranta yayi matuƙar baci amma babu yanda zatayi, ko tayi niya yin wani abuma tasan Ummi zata mata faɗa sosai, ba zata bari ba. Abun ya isheta haka, abun na mata ciwo ba kaɗan ba. Babu ɗan da zai so yaga ana wulƙanta iyayen shi. Bata san sanda hawaye suka fara zuba daga idanun ta ba. Batayi motsin goge su ko tsaidar da su ba, ta haka ne kawai zata ji saukin ƙunar da zuciyar ta ke mata.

Sai da tayi kukan har ta godewa Allah sannan ta tashi taje ta wanke fuska. A madubin dake bayin ta ƙare ma kanta kallo, idanunta har sun ƙara girma, sun yi ja. Da sauri ta kauda kai, bata son ganin fuskarta ma. Bata sake kallon kanta ba har ta bar bayin.

"Ya Allah Ka kawo mana karshen zaman mu anan gidan. Ya Allah!" Ta faɗa a fili.

Akan wani dalili Hajiya Suwaiba zata kira Umminta ta zageta cikin mutune? Kuma ace mutum bazai ce komai ba. Ba wannan karon ne na farko da hakan ya faru ba, ba zama ta iya ƙirga so nawa hakan ya faru ba. Wannan wace irin rayuwa ce? Ta ɗaɗe tana saƙawa tana kwancewa a zuciya.

Chan taji kiran Ummi, sai da gaban ta ya faɗi, dan tunda abun ya faru ɗazu da safe bata bari sun haɗu ba. Dan harga Allah Ummi ta ɓata mata rai. Wani irin haƙuri take dashi? Ace ana ta mata abu ɗaya shekara da shekaru amma ko daga ido ta kalle su bata taɓa yi ba. Gaskiya Allah ne shaidarta, ba zata taɓa iya haƙurin da mahaifiyar ta keyi ba, wannan ya tashi daga hakuri ya zama cutar da kai.

Ta samu Ummi zaune a ɗaki, tana ƴan gyare gyare. Kallo ɗaya Ummi ta mata ta san har yanzu ranta a bace yake. "Maimunatu," ta kira sunanta tare da sauke ajiyar zuciya. "Bance maki kar ki bar abunnan a zuciya ba?"

Maimoon bata san sanda ta fashe da kuka ba, kalaman Mommy na mata yawo a kai kaman yanzu take faɗan su. "Na kasa Ummi," tace tana kuka. "Na kasa. Ummi na gaji, wallahi na gaji."

Ummi ƙoƙarin boye kukan tayi sannan ta janyo Maimoon jikinta tana rarrashin ta. Ita kanta ta gaji, matuƙar gajiya. Amma ya zata yi? Haka Allah ya ƙaddara.

"Maimoon ya isa haka, ya isa. Na san kina haƙuri, ba kaɗan ba amma ki ƙara haƙuri wata rana sai labari."

"In sha Allahu Ummi," ta ce tana share hawaye. Ba taso yin kuka a gaban mahaifiyar ta ba saboda kar ta ƙara mata damuwar da take dashi, sai dai ta kasa dannewa. Abun ya daɗe bai taɓe ta irin haka ba.

"Ya isa," Ummi ta ce tana taya ta goge fuska. "Bana son Baffan ku ko wani ya sani, kin ji?"

Ba dan taso ba ta daga kai. Daman ta san hakan zai faru. Hannu tasa ta taya Ummi gyaran da take yi. Suna yi tana jan Ummin da hira duk dan ta manta abunda ya faru.

Gaba ɗaya yinin ranan bata yi shi cikin jin daɗi ba. Bata faɗa ma kowa ba kaman yanda Ummi ta buƙata. Ko da su Mimi suka tambaye ta mai ke damun kawai ce masu tayi bata jin daɗin jikinta. Bata taɓa jin tsanar zama gidan Daddy ba irin yau, ji take kaman a kan ƙaya take.

Ta son sun taimaka masu, kuma ba zata taɓa mantawa ba. Duk wanda zai baka wurin zama ya ma taimako sosai. Amma hakan bai bashi lasisin wulaƙanta ka ba a duk sanda yaso, sam! Taimakon nan da yama bai bashi dama ba. Babban burin ta a yanzu shine taga sun bar gidan nan, komai ma zai daidaitu daga baya.

Amma taya ma zata fara? Wani mafita take da? Mai zata yi taga burin ta ya cika? Kaman ta ɗaura hannu a ka tayi ta ihu haka take ji.

"Adda," muryar Mimi ita ta fiddo ta daga zurfin tunanin da ta faɗa. "Tunanin me kike haka? Tun ɗazu ake ta kiran ki a waya."

Sai a sanna ta lura da wayar ta dake haske a gefen ta. Ganin sunan Hamma Ashmaan a fuskar wayar ya sa gaban ta faɗuwa. A yanda take yanzun bata son abunda zai tuna mata da Mommy ko na sakwan ɗaya. Har wayar ta gama ringing ba tayi yunƙurin dauka ba.

Mimi na gefe tana kallo ƴar uwar ta da tun ɗazu ta kasa gane kanta. Ta san akwai abunda ke damun ta amma zurfin cikin irin na Maimoon ba zai bari ta faɗa mata ba. "Adda Hamma ne fa ke kiran ki."

"Toh sai me in Hamman ne?" Ta tambaya cike da tsiwa. "Banga damar dauka ba."

Abun ya ba Mimi mamaki. Me ya faru? Ta tambayi kanta. Ganin Maimoon bata da niyan amsa kiran ya sa ta maza ta dauki wayan kafin kiran ya tsinke. Cike da ladabi ta gaida shi. Kamar kullum cikin sakin fuska ya amsa mata.

"Umm..... Addan bata kusa." Mimi taji kunyan yi mai ƙarya amma a yanda Maimoon ta cika dinnan komai zai iya faruwa. Maimoon na jin ta bata ce komai ba sai ma taɓe baki da tayi. Da abun ya ishe ta tashi tayi tabar ɗakin.

Da mamaki Mimi ta bita da kallo tana addu'a a zuciya Allah yasa lafiya.


~~~~


Sanyin da ke ratsa ɗakin ne yasa ta ƙara gyara kwanciya, wani bacci mai ɗaɗi yana sake diɓan ta. Chan kaman an mintsileta tayi sauri ta tashi, ta tuna ba tayi sallar isha'i ba. Bayan ta idar da sallah ta fita waje inda ta samu Ummi da ƙanenta suna mulmula gullisuwa, Baffa kuma na gefe yana taya su hira.

Wani ɗaɗi marar misaltuwa ya ziyarci zuciyarta. A duk sanda taga iyayenta da ƙanenta cikin farin ciki sai taji wani kwanciyar hankali da farin ciki ya mamaye ta. Ta na roƙon Allah ya haɗa su kaman haka a gidan aljanna, tare da Hamma Mu'azzam.

Suna ta hira babu wanda ya lura da ita, sai da Sadiya ta dago kai ta ganta a bakin ƙofa. "Yawwa Adda kin tashi, dan Allah zo ki soya mana gullisuwar. Kin san babu wanda ya iya soyawa kaman ke, wasu ma ƙona ta ƙurmus suke yi," ta ƙarashe maganar tana kallon Mimi ta gefen ido.

Mimi ta san da ita take yi, hararta tayi amma bata ce komai ba. Tun ranan da Ummi ta saro madara su gwada yin gullisuwa ta ƙona wajan soyawa shikenan ta shiga uku wurin Sadiya.

Baffa ɗan murmushi yayi yana kallon Sadiya. "Neman tsokana ko?" Dariya tayi tana sunne kai ƙasa. Da sauri Mimi ta miƙe ta koma gefen shi. "Baffa ka ja mata kunne, tun ranan take tsokana na, so ɗaya ne fa amma kullun sai ta tado zancen."

"Rabu da ita uwar manya, zan gamu da ita."

Kai Maimoon ta girgiza kafin ta samu wuri kusa da su ta zauna sannan ta gaida Ummi da Baffa wanda suka amsa cike da kulawa da fara'a. Hannu tasa aka murza sauran kafin ta tashi taje ta fara soyawa.

Kaman wasa Ummi ta saro madara tace su gwada yin gullisuwa da tuwon madara a gani ko za'a dace. An dace kuwa, dan a rana sai suyi na fiye da ɗubu uku. Alhamdulillahi abun sai ƙara habaka yake yi.

Itama sana'ar kitson ta sai ƙara gaba yake. Anty Salma —wanda a yanzu sun shaƙu sosai, kaman wanda suka yi shekaru da sanin juna. Har gida tazo ta gaida su Baffa, kuma ta kan zo in an kwana biyu, har ta bar su Ikram su yini wasu lokutan—ita ke kai Maimoon gidaje daban daban ta masu kitso, gidajen da ta san ba za'a wulaƙanta taba. Ba abunda zata ce sai Alhamdulillah.

Tana cikin aiki Sadiya da Mimi suka shigo kitchen ɗin. Wuri suka samu suka zauna bayan sun mata sannu, haka ta cigaba da soyawa suna taya ta hira. Wayar Maimoon suka ji tana ƙara a ɗaki, da sauri Sadiya ta tafi daukowa. Ta shigo kitchen ɗin tana magana a waya. "Ina wuni Anty Salma.....Ina su Iki? A basu mu gaisa."

Saida ta gama gaisawa da su Ikram, sukayi hira kaman ba jiran ta ake yi ba. Da yake akwaita da son yara, ta shaƙu da su Ikram sosai, in sun zo ma duk wasu hidimar su a wuyanta suke, bata bari kowa yayi. Saida suka gama shirmen su sannan ta miƙawa Maimoon wayar.

Da harara ta bita, da ido tace masu su cigaba. Ita kuma ta fita tana kara wayar a kunne. "Ina wuni Adda Salma."

Ta kanyi mamaki irin sabawar da suka yi lokaci ɗaya haka. Duk miskilancin ta saida Anty Salma—ko kuma tace Adda Salma kaman yanda ta haƙiƙance su kira ta— ta san yanda tayi dan ta saki jikinta da ita. Mata ce mai matuƙar kirki da son mutane.

"Lafiya ƙalau Moon, ya gida?"

"Alhamdulillah, ina su Amira?"

"Kin gansu chan yanzu sukaji sallamar abokin baban su, Baba Sayf, sun tafi yi mai oyoyo."

"Toh a gaishe su,"

Ƴar hira sukayi kafin chan Anty Salma tace. "Maimoon Allah yasa baby inda zaki kitso gobe."

Zamanta ta gyara a ƙasa kafin ta ba Anty Salma amsa. "A'a, babu inda zani. Akwai inda kike so inje ne?"

"Eh, Amma—kakar Baba Sayf zaki wa kitso. Ta ɗaɗe da mun magana, shaf na manta wallahi. Saida naji sallamar shi na tuna."

"Toh Adda duk yanda kika ce. Kaman ƙarfe nawa, kuma ina ne gidan?"

"Uhhm toh gaskiya ban sani ba, sai na kira ta naji. Duk yanda mukayi zan sannar dake. Zanzo in dauke ki, nima na kwana biyu banje gidan ba."

Da wannan sukayi sallama.

~~~~

Wurin ƙarfe goma Ashmaan ya shiga sashen Baffan shi dan ya gaida shi, kuma ya ga ƴan uwan shi. Sanye yake da farar jallabiyar da ta haska farar fatar shi. Ya sami ƙanin baban shi cikin yaran shi, fuskokin su dauke da murmushin da ka gani kasan suna cikin kwanciyan hankali. Yanda Baffa ke gudanar da rayuwar shi na burge shi, yana ji tunda ya ke Daddy bai taɓa zama dasu kaman haka ba. Babu sabo sam tsakanin su.

Sallama ya sake yi. Murmushin da ke fuskar Baffa ya sake faɗaɗa, a duk sanda yaga Ashmaan sai yaga kaman Mu'azzam ɗin shi ne. "Ashmaan sannu da zuwa, zo zauna."

A kusa da shi Ashmaan ya zauna suka gaisa inda yake tambayar shi ya aiki. "Alhamdulillahi Baffa, ga shi nan muna ta yi."

"Allah ya bada sa'a. A dai dage, kasan dai abunda ya kai ka, banda yin abunda bai dace ba dan Allah. A duk inda kake ka rike gaskiya da amana, ka gama komai."

Har cikin ran shi yaji ɗaɗin kalaman Baffa, inama ace mahaifinshi ne ke mai nasiha irin haka. Sai dai babu komai, ko a hakan ma Alhamdulillah, dan yanda ya dauki Daddy haka ya dauki Baffa.

"In sha Allah Baffa, a taya mu da addu'a."

"Addu'a ai kullum cikin yi muku akeyi Ashmaan. Allah ya maku albarka."

Murmushi yayi mai sauti ya amsa da Ameen. Ummi ya tambaya, Baffa ya ce mai tayi bacci kan ta na ciwo. Saida suka gama gaisawa da Baffa sannan ƴan matan uku suka gaida shi, ya amsa kamar yanda ya saba, fuska dauke da murmushi.

Idon shi ne ya sauka kan Maimoon da tunda ta gaida shi bata sake daga kan ta ba, hirar da akeyi ma tayi shiru wanda yasan tayi hakan ne saboda zuwan shi. Ya kasa gane kan ta, ya rasa mai ya mata ta chanza gaba ɗaya. Ba zai iya tuna rabon da su zauna suyi magana kaman yanda suka saba ba, kiranta da yake a wayan ma yanzu ya daina saboda kullum ya kira sai dai Mimi ko Sadiya ta ɗauka.

Ya rasa me ya mata. Yayi yin duniya ta faɗa mai in laifi yayi mata ya bata haƙuri amma tace bai mata komai ba. Abun ya na damun shi sosai.

"Sadiya me kuke ƙullawa haka?" Ya tambaya yana nuna bokitan da ke gaban su.

"Gullisuwa da tuwon madara," Sadiya ta bashi amsa. Ƙaramin kwanon dake kusa da ita ta janyo ta zuba sannan ta miƙa mai. "Ai dai ka san su ko?"

Da wasa ya harare ta yana amsan bowl ɗin. "Kaji mun yarinya, tun kafin a haife ki muke siya da ƙwandala ni da Mu'azzam. Ni nafi son gullisuwa, shi kuma tuwon madara."

"Da gaske Hamma?" Mimi da Sadiya suka tambaya a lokaci ɗaya. Duk wani abu akan Hamman su suna so su sani tunda basu iya tuna shi sosai.

Zama yayi yai ta basu labarin ƙuruciyar su da Mu'azzam. Sunyi rashin ji ba kaɗan ba. Kewar shi ce da mamaye su lokaci ɗaya, Ashmaan ya lura da yanda fuskokin su suka chanza, addu'a ya ce su mai sai kuma ya dauko wata maganar.

"Mai yasa kuka yi da yawa amma?"

"Hamma baka sani ba?" Sadiya ta tambaye shi.

Kan shi ya girgiza. "Sai kin faɗa."

"Ai ni Adda Mimi mun zama businesswomen," ta ce tana dariya."Mun zama CEOs."

Ɗan ƙaramin tsakin da bata sha kowa zai ji ba Maimoon tayi jin shirmen da Sadiya ke faɗa. Tana daga kai suka haɗa ido da Hamma wanda tun ɗazu idanun shi ke kanta.

Ƙin janye idon tayi, ta tsare shi da manyan idanun nan nata masu ruɗa mutane. Dariya yayi da ya gane abunda take yi, shima sai ya ƙi janye nashi idanun. Ita ta gaji ta kauda kai. Murmushi yayi ya maida kallon shi wurin su Sadiya.

"Sannu CEOs," ya ce yana dariya.

Mimi ta girgiza kai, shirmen Sadiya sai ita. "Hamma Ummi ce ta bamu kayan aiki ta ce mu gwada mu gani, muma mu bar zama haka nan."

Kai Ashamaan ya jinjina. "She's right, yana da kyau hakan. Toh yanzu CEO Sadiya da CEO Mim zan iya investing a company ɗin na ku?"

"Investing kuma Hamma?" Mimi ta tambaya.

"Yes," ya ce yana daga kai. "Zan sa hannun jari, nima ayi kuɗin tare dani."

Wani kallo Sadiya ta mai jin abunda yace. "Kuɗi kuma Hamma? Duk kuɗin da kake dashi."

"Rufa mun asiri, wasu kuɗi gareni Sadiya? Kuma idan ma akwai, ina son ƙari."

"Taya zakayi investing Hamma?" Mimi ta tambaya dan tunda yayi magana wasu ideas suka fara mata yawo a kai.

"Uhhm ke a ganin ki mai ya kamata inyi?"

"Da farko dai muna buƙatan brandname, sunan da zamuyi amfani dashi da kuma logo, sai packaging yanda mutane zasuyi sha'awan siyan kayan mu, irin robobin plastics dinnan masu kyaun da ban sha'awa."

Kai Ashmaan ya jinjina jin bayanin ta. Ya yaba da wayon ta dan abunda ta lissafo shi mai shirin fara sana'a yake buƙata. "Shikenan Mimi? Babu wani abun?"

"Babu, in na tuna da wani abun zan faɗa ma."

"Kuna da sunan da kuke so kuyi amfani dashi?" Ya tambaya yana kallon Mimi da Sadiya. Kai suka girgiza dukan su. "To in kun samo sunan ko faɗa mun sai a fara yin logo ɗin ko?"

Farin ciki ne ya mamaye su, musamman Mimi da tafi maida hankali akan abun. Dama tana da sha'awar yin irin abubuwan nan ko dan ta taimaka da wani abu a gidan. Har ta fara tara kobo da darin ta dan yin jari dasu dan bazata iya tambayan Baffa ba, nauyin dake kanshi ya ishe shi. Hamma Ashmaan ba ƙaramin taimaka musu zaiyi ba, har ta mutu bazata taɓa daina mai addu'a ba. Yanda yake kula dasu ko yayan su da ya rasu sai haka.

"Mungode Hamma," ta ce muryarta na rawa. "Allah Ya saka da alheri."

"Ba nace ku bar mun godiya ba Mimi? Kina so muyi faɗa ko?" Kai kawai ta iya girgizawa.

Maimoon na jin duk abunda ke faruwa amma bata ce komai ba. Kaman ta ce mai ya barshi, ba sai ya taimake su ba, zasu san yanda zasuyi. Sai dai kuma ta ja bakinta tayi shiru. Tasan Hamma Ashmaan ba irin halin Mommy yake dashi ba, amma ta rasa yanda zata daina jin haushin shi ta dalilin abunda Mommy ta ma Ummi kwanakin baya.

Tashi tayi dan shiga daki, taji ya kira sunanta. "Dawo ki zauna."

Kaman tayi banza dashi sai dai rashin kunya ba halinta bane. Hakanan ta koma ta zauna ba dan ta so ba.

"Moon, zauna ki faɗa mun me na miki?"

Janyo hular hijabinta tayi ta rufe fuskarta dashi. "Bakomai." Chan ƙasan maƙoshi tayi magana.

"Maimoon, tell me the truth. Akwai abunda ya faru, there has to be something. Ki taimaka ki faɗa mun, ko ma meye zamu magance shi. Amma ignoring dina ba shi bane mafita ba."

Ita dai ta rasa me zata ce mai. Ce mai zatayi mahaifiyar shi ta wulaƙanta tata ko me? Ko ya yake supporting dinsu Mommy mahaifiyar shi ce, ba koda yaushe zai so ya dinga jin laifinta ba.

"Hamma dagaske ba komai."

"Maimunatu."

Bata san sanda ta daga kanta ba, rabon da ya kirata da sunan har ta mance. Tana daga kai suka haɗa ido. Da sauri ta dauke kanta.

"Baza ki fada mun ba? Uhmm?" Duk ya bi ya wani marairaice murya kaman mara lafiya.

"Da gaske Hamma, ba komai. Kawai dai..." sai kuma tayi shiru dan bata san abunda zata ce ba. Ita ma tayi mamaki yanda take treating din shi, ta san Hamma yafi karfin haka. Saboda shi kadai ne ke taimakon su a gidannan, zata iya cewa ma basu da kaman shi duk duniya.

Ajiyar zuciya ta sauke. "Kayi hakuri Hamma. In sha Allah, hakan bazai sake faruwa ba."

"Baza dai ki fada mun ba ko?"

"Kayi hakuri," ta sake fada.

Badan yaso ba, ya bar maganan ta wuce. Ya san abunda ya faru nada alaƙa da ƙannenshi ko iyayenshi. Ya san kuma abunda ya faru ba kaɗan bane in har zaisa Moon tayi reacting haka.

"Toh shikenan, ya wuce. Yanzu dai ki mun dariya, wannan tsumewan da kike yi zai sa fatar ki ta saki, kiyi wrinkles."

Maimoon bata san sanda dariya ta kubce mata ba. Shagala Ashmaan yayi da kallonta dan ba karamin kyau Moon din shi keyi ba in tana dariya.

A take a nan ya daukan ma kanshi alkawarim bata farin ciki mai daurewa.


.
.
.
.
.
Salamu alaikum 🙈

Anyi sallah lafiya? Allah Ya maimata mana. Da fatan na same ku cikin koshin lafiya. Barkan mu da dawowa, again😂

Ku kasance tare dani, I won't abandon this book again In sha Allah 🙈



Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro