Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA GOMA SHA BIYAR











~~BABI NA GOMA SHA BIYAR~~



Kalaman da ya ji ba karamin girgiza shi sukayi ba. Ji yanda suke tsara batawa wani rayuwa babu ko dar a tare dasu.

Ƙafafunshi ya ji suna neman su kasa ɗaukar shi. Bangon kusa da shi ya dafa, ya na maida lumfashi kaman wanda ya sha gudu.

"Kana gani zai yarda?"

"Ko bai yarda ba, zamu gamsar da shi." Wata murya daga cikin waya ta bada amsa.

Me sukayi musu suke neman tarwatsa musu rayuwa haka? Me suka tare musu a duniyan nan?

Zuciyarsa kaman zata tarwatse saboda tsoro da fargaba, ga dacin wai 'yan uwanshi ne ke shirin yi mai wannan abu.


****


Tana zaune Sadiya ta faɗo ɗakin kaman an korota. "Adda...." ta ce tana huci. "Hamma ya ce yana ta kiranki baki dauka ba."

Kai ta girgiza. "Gudun na meye kuma?"

"Ya ce inyi sauri ne."

Da to ta amsa mata sannan ta tashi tana neman wayar. Bata ma san inda ta yarda ta ba tun da safe da sukayi magana da Habiba. Chan kasan pillow ta ganta.

Missed calls sun kai biyar daga wurin Hamma Ashmaan. Sunan shi ta dannan, tana fara ƙara ya kashe. Sai kuma ga kiran shi ya shigo.

"Salamu alaikum Hamma."

"Wa'alaikumus salam, Moon. Wai me yasa baki son ajiye wayan ki kusa da ke? Ayi ta kiran ki. Sometimes, ban ga amfanin wayar ba ma."

Dariya tayi. "Sorry. Lafiya dai ko? Naga missed calls ɗin da yawa."

"Inafa lafiya banji muryar ki ba tun safe ba."

Wani iri taji da furucinsa ya duki kunnenta.

"Yanzu dai me kike yi?" Ya tambaye ta yana kawar da tunanin bashi amsa da take yi.

Kallon dakin tayi ta gan shi a gyare tsaf. Babu kuma aikin gidan da zatayi dan tuni Ummi ta mata retire. Yanzu komai Mimi da Sadiya ke yi sai dai ta kama musu wani abun in zaman ya isheta.

"Babu abunda nake yi."

"Good, shirya mu fita yawo."

"Yawo kuma?" Jin abun tayi wani banbarkwai.

"Yes, yawo. Na ji zaman gidan ya isheni nake son fita shine nazo neman 'yar rakiya."

"Ka nemo abokin ka ya raka ka mana."

"Ni ke nake so ki raka ni."

"Hamma..." sai kuma tayi shiru.

"Moon..." ya ce yana kwaikwayon muryarta. "Shirya kinji, nan da ten minutes zan kara kiran ki."

Yana gamawa ya kashe wayar. Da mamaki ta ke kallon wayar. Ita yarinya ce da zata mai rakiya? Dan jum tayi tana tunani. Kawai sai su tafi yawo dan zaman gida ya ishe shi. Hamma Ashmaan sai shi.

Bayan minti goma sai ka kiran shi ya sake shigowa. "Moon fito mu tafi."

"Hamma sai ka dawo kawai."

"Baza ki ba kenan."

Ta jiyo dan bacin rai a muryar shi sai kuma ta ji ba dadi. "Hamma ba haka bane, kawai dai..."

"Kawai dai kina mun rowa, ba komai."

"Nifa Hamma ba haka bane."

"To yaya ne?"

Shiru tayi ta rasa abun cewa.

"To fada mun me kike so in kawo miki tunda dai kin mun rowan rakiya."

Dariya tayi, tana tunanin me zata ce. "Ka kawo mun gurasa."

"Ki rasa abunda kike so sai gurasa. Wani iri."

"Bandashe mai dadi dan Allah."  Miyaunta har tsinkewa ya fara yi.

Dariya Ashmaan yayi ya ce mata an gama. Kuma ta turo mai Sadiya da Mimi su mai rakiya tunda ita ta kiya.

Su Mimi basu dawo ba sai gab da Maghrib. Sun dawo da ledoji niki niki a hannu. Sadiya sarkin surutu ta zauna sai bada labari take yi.

"Yauwa Adda ga gurasar ki. Hamma ya hanamu ci wai taki ce ke kadai."

Tun kafin ta bude kamshin duk ya cika mata hanci. Bandashe ne da ya amsa sunan shi bandashe. Yaji kuli-kuli da kayan lambu. Ka tsire da aka yanka a kai.

Kasa boye murmushinta tayi. Tana daga kai suka hada ido da Ummi da ke mata wani irin kallo. Da sauri ta dauke kanta.

Da dare kafin ta kwanta ta turo ma Hamma Ashmaan sakon text tana mai godiya. Ko minti daya batayi ba da tura mai sai ga amsar shi ta shigo.

Ba nace babu godiya a tsakanin mu ba? Kina so muyu fada ko. I'm glad you liked it.

Bata bashi amsa ba. Ajiye wayan tayi ta kwanta ran ta cike fal da tunani.


****

Ranar ake kwallawa yau ba kadan ba ce. Duk ta jike da zufa. Tun safe bata zauna ba, yatsun hannunta har zugi sukeyi ga bayanta ya rike saboda zama.

Tabbas neman halal da wuya.

Tana isa gida bata nemi komai ba wanka ta fara yi. Kaso hamsin cikin gajiyar da tayi har ta tafi. Mimi ta kawo mata abinci ta dan tsakuri kadan. Dan bata sha'awan cin abinci yanzu, so kawai take yi ta ganta a kan gado.

A nan bacci ya dauketa.

Hayaniya take ji kaman yara na wasa. Gyara kwanciya tayi ko zata koma baccin amma ta kasa. Daga karse dai ta hakura ta tashi.

Amira da Ikram ta gani a tsakar gida suna wasa abunsu. Suna ganinta suka rugo da gudu suna ihu... "Aunty Maimoon!"

Tsawonta ta rage kafin su iso gareta. Suna zuwa suka fada jikinta. Hannunta tasa ta zagaye su. Yaran kaman Mamansu, akwai shiga rai sosai.

A tsakar gidan ta samu Ummi da Adda Salma suna ta hira. Adda ta taba ce mata in tana tare da Ummi tana ji kaman mahaifiyarta ce ta dawo gareta.

Wuri ta samu kusa da su ta zauna.

"Na kusan zuwa in sheƙa miki ruwa ai," inji Salma. "Wannan barci kaman kasa."

"Na gaji sosai Adda, ba kiji inda bayana ya ƙage ba ga yatsuna har wani zugi suke yi."

"Sannu. Zaman kitso da wahala kam."

Tashi tayi taje ta zubo abinci a kitchen. Gidan yayi shiru, su Amira sun bi Sadiya da ta fita yanzu. Karar rediyon Ummi ne ya yanke shirun da ya gitta.

Labaran yamma akeyi. Rahotanin duk cike suke da abubuwan tashin hankali. Kusan ko ina a duniya yaƙi akeyi. In ba yaƙi ba wani abun tashin hankalin. Na yau daban, na gobe daban.

Duniyar duk ta zama abun tsoro.

A cikin haka ne aka bada rahoton wata mata da ta watsa ma matar danta ruwan zafi. Kafin nan dama sun dade suna samun matsala inda 'yayanta mata suka ma matar dan uwan duka sosai har da ji mata rauni.

"Mutane ba'a tsoron Allah," Ummi ta ce tana girgiza kai jin wannan abun al'ajabin.

"Kwakwata Ummi," in ji Adda Salma. "Ki duba rashin imani a wurin nan. Na tabbata a cikin 'yayan nata akwai masu aure, in ma babu zasuyi. Bata taba tunanin itama haka zai iya faruwa da nata yaran ba..."

"Hakane Salma. Diyarki gidan wani zata, yanda kema gidan wani kika je. Duk abunda baza ki so a yi wa 'yar ki ba kema kar ki wa diyar wasu."

Maimoon na cin abinci tana jin su. Lamarin duniya na matukar tsorata ta. Mutane kaman basu da digon imani a zuciyoyin su. In kaji wani abun sai ka dunga tantama anya?

Saboda wasu abubuwan hankali baya iya dauka. Idan ba zalunci ba, me zaisa ki dauki ruwan zafi ki watsa wa 'yar mutane.

Lamarin mutane na bata tsoro matuka.

"Ummi abun babu dadin ji. Kuma ana samun matsololin nan sosai cikin society din mu. Zaki ga dangin miji sun takura wa yarinya babu gira babu dalili."

"Abun sai addu'a. Allah Ya shirye su. Yaran nan kullum addu'a ta ku samu mazaje na gari. Allah Ya kaiku gidajen da baza'a wulakanta ku ba.

"Ameen," Adda Salma ta amsa.

Sai bayan sallar maghriba Adda Salma da yaranta suka tafi. Maimoon na daki tana ma Mimi karin karatu taji kiran Baffa.

"Kiyi ta maimaita shafin har sai na dawo," ta ce ma Mimi tana mikewa tsaye.

Sallama tayi a bakin kofar dakin, saida aka bata izini ta shiga. Dakin ya chanza mata sosai kaman ba shi ba. Satin da ya wuce aka kawo sabon setin gado aka sa a dakin. Kyautar da Baffa yayi ma Ummi kenan.

Gadon ya zauna das a dakin. Bai cika wurin ba kaman wancan. A kasa kan kafet din da aka kawo tare da gadon ta zauna. Ta samu Baffan yana waya sai da ya kammala.

Bayan ta gaishe shi ya amsa, ya kira sunanta da wani irin murya saida gabanta ya fadi.

"Maimunatu," ya sake kiranta.

"Na'am Baffa."

"Me kika tsarawa rayuwar ki?"

Tambayar tazo mata a baibai. Ta tsorata ta, ta birki ta mata tunani. Neman natsuwarta tayi ta rasa. Baffa ya ga yanda ta rude sai yayi murmushi.

"Affuwan, tambayar bata fito daidai ba. Kina da wani buri da kike so kika kin cika?"

Karatunta ya fara fado mata rai. Tana son ta ga ta koma makaranta ta cigaba da karatu. Ta hada digiri ko zai zaman mata hanyar taimakama iyayenta da 'yan uwanta. Kafin Hamma Mu'azzam ya rasu kullum maganar shi karatu. Ya kan ce musu ko suna ganin ba ze amfane su ba, suyi su aje. Wata rana bukatar shi zai taso.

"Uh, Baffa..." ta fara ce wa sai kuma tayi shiru.

"Fadi mana, ina sauraron ki."

"Makaranta na ke so in koma."

Murmushi Baffa yayi. Ya sani abunda zata bukata ba zai wuce wannan ba amma dan ya tabbatar da hakan ya tambaye ta. An cire ta a makaranta a lokacin da abubuwa sukayi musu muni. Ko sau daya bai taba jin tayi korafi ba. Ko bayan samun lafiyar shi bata taba zuwa ta ce mai ga abunda take so ba.

"Toh Maimunatu. Sai ki fara shiri nan da wata biyu zakiyi jarabawa tare da Mimi."

Idonta cike da hawaye ta kamo hannun Baffa. Ta rasa da wasu kalamai zata gode mai. "Nagode Baffa, nagode. Allah Ya kara budi."

"Ameen Maimu, Ameen." Ya ce yana shafa mata kai.

"Babu matsala ko Baffa?"

Dariya yayi saboda ya gane abunda take nufi. "Babu in sha Allah."

Sallama suka jiyo daga kofar dakin. Baffa ne ya tashi ya fita dan ganin waye. Khalifa dan autan Mommy ya samu tsaye a kofar dakin.

"Daddy ne ya ce in kira ka," yaron ya ce.

"Toh shikenan. Je ka ce mai gani nan zuwa."

Takalman shi ya sa yabi bayan yaron. Bai yi mamakin kiran ba dan ya dade yana tsammanin shi. Sai dai yana fargabar sanin dalilin kiran nasu. Dan yana ji a jikin shi kaman ba kiran alheri ne wannan ba.

A katafaren falon kasa ya same su. Yayi mamakin ganin babban wan su Abdulkarim zaune kusa da Bello. Da sallama a bakin shi ya shiga. Hannu ya basu suka gaisa sannan ya samu kujera ya zauna.

"Sannu da zuwa Yaya," Baffa ya ce. "Ban san da zuwan ka ba shi yasa ban zo mun gaisa ba."

Yar dariya Abdulkarim yayi. "Babu komai Muhammadu, yau nazo da safe wani aiki ya kawo ni. Ban dade da shigowa ba ma. Bello ke ce mun ka samu aiki. Allah Ya sanya alkhairi, sai dai banji dadin rashin fada mun da kayi ba."

Da Ameen Baffa ya amsa, yana share sauran zancen nashi. Shi ya fara turawa text kuma ya kira shi bai dauka ba. Inna ma da kyar ya ci sa'a ta daga wayar.

"Allah Ya sanya alkhairi Baffa." cewar Daddy. "Ina ta so in shigo in maka murna kai da Maman Mu'azzam ban samu lokaci ba."

Murmushi Baffa yayi yana cewa babu komai.

"Ka tuna sanda Ardo ya kama mu mun dawo daga kwallo?" Da mamaki Baffa ya kalli Abdulkarim din. "Ranan jikin mu ya fada mana. Muhammadu kai kadai ka tsira."

"Shi dama ai allazi makaranta ne," Daddy ya ce. "Babu yanda banyi da shi ya raka mu ba amma ya'ki. Ashe bai da rabon shan wahala ne."

Sosai yayi mamakin yanda suke tuna baya. A yanda suke yanzu ya zata sun mance kallar rayuwar da sukayi a baya. Sun mance kallar shakuwar da ke tsakanin su a lokacin. Komai na su iri daya Ardo, mahaifinsu ke musu. Daidai da takalma kala daya suke dashi. Tamkar 'yan uku, haka suke kullum a tare. Tare suke zuwa kiwon dabbobin Ardo, tare suke tafiya makaranta, tare suke cin abinci, tare suke kwana. Tare suke tsara yanda rayuwar su zata kasance.

Kwatswam rana daya komai ya sauya.

Bayan rasuwar Ardo ba dadewa 'yan uwan nashi suka rikide suka zamo wasu mutane na daban. Yayi iyakar bakin kokarin shi wurin ganin ya gyara koma meye ya shiga tsakanin lokaci daya amma bai samu nasara ba.

Lokaci daya komai ya lalace. Abun ya na damun shi sosai, ya na mai ciwo. Har yau yana son ya sani ko wani abun ya musu.

"Allah Ya jikan Ardo," Baffa ya ce a raunane. Ya na kewar mahaifin shi. Tun bayan rasuwar shi komai ya chanza mai. Tun rasuwar duniya ta mai zafi.

Da Ameen duk suka amsa.

Suna zaune ana ta tuna baya har aka kira sallar isha'i. Tare suka dawo daga masallaci. Baffa yayi hanyan sashen shi Abdulkarim ya kira shi.

"Muna da abunda zamu tattauna da kai."

Komawa falon sukayi inda suka samu an jera abinci. Ce musu yayi ya koshi. Robar ruwa kadai ya dauka. Yana nan zaune har suka kammala cin abinci.

"Wata muhimmiyar magana nakeso muyi Muhammadu, ina so ka saurare ni da kunnen basira." Abdulkarim ya ce yana gyara zaman shi. "Wani cigaba ne ya zo maka, sai dai ban san ya zaka dauki abun ba."

"Ina sauraron ka."

"Mun sami labarin cewa mai girma gwamna zai dauki wasu ma'aikata na musamman. Wani abokina na cikin committee din masu screening, so ya nemi in kawo candidate."

"Wannan opportunity ne babba," Bello ya ce. "In har aka dace a abun nan dukan wasu matsalolin ka sun kare."

"Amma sai dai ya bukaci wani abu," Abdulkarim ya cigaba da cewa. "Kafin in fada ma ina son kayi nazarin irin tarin cigaba da zai zo maka kai ma in ka samu wannan aikin. Mawuyacin halin da kake ciki a yanzu zai zo karshe."

"Me ya bukata?" Baffa ya tambaya yana mai jin tsoron amsar da za su bashi.

"Ya nemi auren 'yar ka Maimuna." Daddy ne ya amsa.

Duban shi Baffa yayi. "Auren Maimunatu kuma? A ina ya santa har zai nemi aurenta?"

"Ya zo gidanan kwanakin baya."

"Kar kayi saurin yanke hukunci Muhammadu. Ka je kayi tunani sosai tukun. Ni dai ina mai baka shawaran yin nazari sosai, kar ka manta duk abunda na fada maka."

Gwiwa a sake Baffa ya bar falon. Kukan zuci yake yi, ashe kiyayyar da 'yan uwanshi ke mai har ya kai haka? Abun ya tashi daga kan shi shi kadai ya koma harda yaran shi.

Sai yanzu suka san da mawuyacin halin da ya ke ciki? Tun kafin su kira shi ya gama yanke shawaran abun yi. Abun duniya bai taba tsone mai ido ba da har zai salwantar da rayuwar diyar shi da ya ke matukar so.

Lamarin Abdulkarim da Bello ya wuce yanda yake zato. In har 'yan uwanka da kuka fito ciki daya zasu iya hada baki dan su cutar da kai to dan wani na waje yayi ba abun mamaki bane.

Dakin shi ya nufa ba tare da ya amsa gaisuwar 'yan matan shi dake tsakar gida ba. Yana zaune a bakin gado yaji an turo kofa. Ba sai ya daga kai ba, ya san waye ya shigo.

A gefen shi ta zauna. "Babban Mu'azzam lafiya na ganka ka shigo haka?" Sanyayyar murya Ummi ta daki kunnuwan shi.

Kai kawai ya iya girgizawa. "Akwai matsala Rabi."

"Subhanallahi! Matsala kuma? Wace irin matsala?"

"Ni kai na ban sani ba amma ina ji a jikina. Ku dage da addu'a, dan Allah."

"Addu'a kullum cikin yinta mukeyi. Koma menene Allah na nan Shi ne gatan mu. Wani bai isa ya cutar da mu sai abunda Allah Ya gaddara. Saboda haka ka kwantar da hankalin ka dan Allah. Ka san ba'a so kana yawan tunani da sa abu a ran ka."

"Hakane. Allah Ya kare mu baki daya."

Da Ameen Ummi ta amsa tana daura kanta a kafadar Baffa














Don't forget to vote and comment, dan Allah! 🙏🏽🥺❤️







-Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro