BABI NA GOMA
~~ BABI NA GOMA~~
Sauri take ta kammala abunda takeyi saboda yau gidajen da zata je kitso da yawa. Tana gama shiryawa, suka karya tare da Mimi da Sadiya. Farar doya ce suka soya, sai kunun tsamiya. Tare suka zauna suka ci abinci, bayan sun gama su ka ma Ummi sallama, Baffa yau da wuri ya fita.
"A dawo lafiya, Allah ya kiyaye, Allah ya bada sa'a." Cike da farin ciki ko waccen su ta amsa da Ameen.
"Adda Moon yanzu ina zaki?" Sadiya ta tambayi Maimoon inda suke tsaye a bakin titi suna jiran abun hawa. "Wannan wani irin kitso ne da sassafe." Mimi tace.
Kafaɗu Maimoon ta daga. "Kaman tafiya zasu yi anjima."
Suna tsaye keke napep ya tsaya, Maimoon ta ce Mimi da Sadiya su shiga, ita zata tare wani. Sallama ta musu tare da musu fatan alkhairi. "A maida hankali."
Bai fi minti biyu ba, wani ya kara tsayawa. "Unguwan sarki zaka kai ni," ta ce, sannan ta mai kwatancen gidan.
A ƙofar wani babban gida aka aje ta sauka tayi sannan ta mika mai kudin. A hankali ta taka gaban get din, dutse ta dauka ta fara bugawa. A ladabce ta gaida tsohon da ya bude mata ƙofa, shi ma ya amsa mata cikin sakin fuska, kasancewar ta ɗan ɗaɗe tana zuwa masu kitson, ya shaidata.
Palon babu kowa a ciki, ta dinga sallama amma ba'a amsa ba. Wajan mintin ta biyu a tsaye kafin wata matashiya ta fito. Ba fara ba ce chan chan, amma da ɗan haskenta. "Haba Maimoon, gidan sai kace bakon ki, ai da kin hayo. Ina ma Amira wanka ne shi yasa banji ki ba. Sannu da zuwa."
Murmushi kawai ta yi. "Ina kwana Anty Salma."
"Lafiya qlau Maimoon, ya su Ummi?"
"Suna nan lafiya."
Murmushi Anty Salma tayi.
Maimoon tayi wata shida tana mata kitso, ita da ƴan matan ta guda biyu. Sun haɗu a gidan ƙawar Anty Salma, tana ganin kitson ta yi maza ta amshi numbanta. Matar na burgeta, babu ruwanta, kullum cikin fara'a take, ga janyo mutum a jiki. Yanda take mata sai ka rantse sunyi shekaru da sanin juna. Dan ma dai miskilancin Maimoon na hanata sakin jiki da ita, da sabon su yafi haka kam.
Palon da ke sama ta kai ta. "Bari in kawo maki breakfast Maimoon."
Da sauri ta ce. "A'a, ki bar shi kawai. Naci abinci."
Ƴar hararar ta tayi, "Ai dama nasan ba ci zakiyi ba, mun kusan faɗa dake wallahi. Ko ruwa ban taɓa gani kin sha a gidan nan ba."
"Ba haka bane Anty Salma," tayi saurin cewa, ta naji a ranta bata kyauta ba. "Kiyi hakuri."
"Dama abunda kike cewa kenan kullum ai. Bari in turo miki Ikram a fara mata."
A hankali ta zare hijab da niqabi dinta. Bayan minti ɗaya a kayi sallama. Yarinya ce ƴar shekara biyar, sanye take da doguwar riga ta kanti me gajeran hannu. Da gudu ta shigo. "Anty Maimoon ina kwana."
Murmushi mai faɗi Maimoon tayi sanda yarinyan ta zauna gefenta. Yaran Anty Salma na burge ta, kullun dagwas zaka gansu, cikin tsafta, da babban abokin nata, ƙamshi. Maman su ma haka, shi yasa bata ƙi tayi awanni cikin gidan ba. Yanzu haka burner dake jikin bangon a kunne take, wani sanyayyan kamshi ya gauraye dakin gaba ɗaya.
"Iki, ya kike?"
"Lafiya qlau, kitso zaki mana ko? Abuja zamu, daga chan Papa ya ce zamu hau jirki mu tafi UAE."
"Dagaske?" Ta zaro idanun ta kaman yanda Ikram tayi. Kai ta daga, murmushi kwance a fuskarta. "Wurin Papa zamu, dama nayi missing din shi."
"Aiko dole in maki mai kyau dan Papa ya yaba."
"Yay," da sauri ta zare dankwalin, gashin ta mai tsantsi ya bayyana. Kaman in da saura jikinta ya ke, kanta ma kamshi ya ke yi, an feshe da hair spray sai sheƙi yake yi.
"Wani iri zan miki?" Maimoon ta tambaya.
"Anty mai kyau, wanda zaifi na Amira da Maama. Kitson gaba kuma."
Dariya Maimoon tayi, kullun so take nata yafi na kowa kyau. Nan ta zauna ta mata kitso ƴan ƙanana kaman da allura ake tsagar. Shiku biyu ta tsaga zata mata a bayan, sai ta gaban zata zubo shi ta kowani gefe. Har tayi rabi Anty Salma ta dawo tare da Amira, ƙaramar ɗiyar ta mai shekara biyu.
"Inji," Anty Salma ta ce tana dariya. "har kinyi rabi. Sannun ki."
Itama dariya tayi. "Juyo Iki ayi na gaban"
Bayan ta gama ma Ikram kitso, ta sa mata beads. Yarinyar tayi kyau, gwanin ban sha'awa. Kitson kaman inji yayi, kaman yanda Anty Salma ke cewa. Kan ka ce me, Maimoon har ta gama. Anty Salma ta sallameta, godiya sosai Maimoon ta mata, dan kudin da ta bata yafi ƙarfin kitson da tayi. Har ta kai kofar palon taji muryar Ikram na tsaidata.
"Anty Maimoon, Maama na ta ce ki tsaya."
Tana juywa sai ga Anty Salma ta fito hannun ta dauke da leda, Maimoon ta mika ma ledar. "Gashi...kar ma ki fara Maimunatu, ba'a maida hannun kyauta baya." Tayi saurin cewa da taga ta fara girgiza kai.
"Zauna Maimunatu," kan kujera suka zauna, Anty Salma ta kamo hannun ta. "Maimoon, nasan babu wani sabo tsakanin mu, amma ganin ki nake kaman ƙanwata da muka fito ciki daya, like the sister I've never had. Amma kiyi hakuri in na shige miki da yawa."
Da sauri ta girgiza kan ta. Da ɗaɗi mutum ya ce yana son ka fisabilillah, itama Anty Salma ta kwanta mata a rai. Amma saboda kada ta wuce iyakarta, shi yasa take ja da baya.
"Ba haka bane Anty Salma, kawai..."
"Miskilanci ne kalan naki ko?" Cike da zolaya Anty Salma tayi magana. Maganar ta taba Maimoon dariya, amma kawai sai tayi murmushi.
"To in dai dagaske kike zan kira ki in mun isa. So nake ki dauke ni kaman yayar ki. Kina da yaya mace?"
A hankali ta girgiza kanta. "Ni ce babba."
"Kin gani, kin yi yaya, ni kuma nayi ƙanwa."
Anty Salma ta ja Maimoon da hira, hira suka yi sosai kafin ta mata sallama. Gida uku zata je kitso, biyu cikin unguwan nan, ɗayan kuma a unguwar su, shi zata bari karshe.
Ƙarfe biyu da rabi ta koma unguwan rimi, unguwan su. Gidan da zata bai wuci sau uku ta taɓa musu kitso ba. Ita kwatakwata ma bata son zuwa gidan, mutane ne masu dagawa da girman kai da raina talaka.
Compound ne babba dauke da part biyu, da yake mata biyu ne a gidan. Uwargidan take ma kitso. Amma in da sabo yaci a ce ta saba da irin wannan ɗabi'a saboda sak irin na gidan Daddy. Ta shiga palon ta samu ɗaya daga cikin ƴan matan gidan na ma wata ƴar dattijuwa rashin kunya, tana gama wa ta wuce fuu! Ta haye sama.
Hannu Maimoon ta sa ta dafa kafadar tsohuwar, takaici ya kama ta ganin har hawaye ta keyi. "Inna kiyi hakuri."
"Yana iya ƴar nan?" Matar tace tana murmushi mai cike da takaici. "Ai dole na nayi hakuri."
"Wata rana sai labari, ki ƙara hakuri." Sam! Bata son ganin ana wulƙanta mutum, ai dan Adam daraja gare shi. "Haka ne, nagode." Tsohuwar tayi murmushi. "Samu wuri ki zauna, yanzu zasu fito."
Ƙananan ta fara wa, sannan manyan. Wacce zatawa karashe tazo mata da extension(attachment) wai ta sa mata. A nutse ta ce. "Ni bana sa attach, Allah Ya tsine ma wanda tasa da wanda aka sawa."
A fusace budurwar ta juyo ta kalle ta. "Keh! In zaki mun kitso ki mun malama. Ban ce ki mun wa'azi ba."
"Zan miki kitso, amma bazan sa miki attach ba." Ta bata amsa tana kallon attach ɗin da ke hannunta. Abun kyama yake bata, taya za'ayi mutum ya dinga jida shi a kai, bayan gashin da Allah Ya hore ma. Har wani wari-wari ƙarni-ƙarni zaka ji yana yi. Tunda ta fara kitso ko zare bata taba ƙarawa wata ba, ballan tana attachment.
Abun na ɗaure mata kai, yana bata mamaki, mussaman in taga yaran musulmai da shi. Abunda Allah Da kan shi Yace Ya tsine ma wanda ta ƙara da wanda tayi ƙarin kuma sallan wanda yayi hakan bata ƙarbuwa. Amma abun mamaki, mutane sun maida shi abun ado da gayu. Wanda in har baki sakawa gani akeyi baki waye ba. Ina waye wa a saɓon Allah? Ina waye wa mutum na janyo ma kan shi tsinuwar Allah, yana ruguza lahirar shi da hannun shi? Abun sai addu'a kawai.
Budurwar taga yanda kitson ƴan uwanta yayi kyau sosai, bazata so a ce nata ya fita daban ba, ba dan taso ba ta zauna Maimoon ta mata kitso.
Daidai sanda ta shiga gida, lokacin Hasina da Fauziya ke fitowa. Tayi mamakin ganinta, tasha ta tafi, dan sati ɗaya kenan da Fa'iz ya tare ta a waje. Da dukkan alamu hutu ta zo. Ko kallon su batayi ba, dan a gajiye take. Da tuni ta dawo, dan ma gidan da taje karshe an bata mata lokaci.
Hasina ta yatsine fuska tana harrar Maimoon, ƴar uwar ta ta juya ta kalla. "Ashe mai idon mujiyan chan na nan."
Taɓe baki Fauziya tayi. "Dama ina zata?" Basu kara ce wa komai ba suka yi gaba. A rayuwarta, Hasina kwatakwata bata son ganin Maimoon, ji take kaman ta kamo ta ta shaƙe ta. Har yanzu tana fargaba kar Fa'iz ya ce zai sake aure, dan har yau bai mance da Maimoon ba.
Watanninta na farko ta wahala, dan ko kallo bata ishe shi ba, ballan tana aje da kwana wuri daya. Saida ta kai shi ƙara wurin mahaifiyar shi da kuma mai iƙirarin yana danne mata haƙƙi ta samu ya fara kulata, haka har ta samu ciki. Haihuwar Nihal shi ya kawo sauyi cikin zaman su, dan Fa'iz na matuƙar son diyar shi. Sai dai har yanzu ko digon san Hasina bai taɓa ji ba, saboda ita ta raba shi da abunda ya fi so duk duniya. Ya kamata tana ba kawar ta labari yanda akayi auren, bai nuna mata yaji ba amma tun ranan ya ma kan shi alkwarin sake aure, ko ba Maimoon ba, zai aure wacce yake so, koma take son shi tsakaninta da Allah.
A tsakar gida ta samu Ummi da su Mimi kan tabarma, Ummi na taya Sadiya tsifa. Tana da gashi Masha Allah, sai dai bai da cika. Ita da Mimi haka kan su yake. Maimoon ce mai cikar gashi da tsawo ɗan a kan ƙugun ta ya tsaya, shi yasa ma bata kitso.
"Yanzu Ummi wannan ƙatuwar yarinyan kike kunce ma kai." Mimi ta ce tana taɓe baki.
Da wasa Ummi ta harare ta. "Ina ruwan ki? Auta ce, ko goya ta sai inyi."
"Mu kuma ko oho." Mimi ta turo baki gaba.
Dariya Sadiya ta yi, tana kallon Mimi ta wutsiyar ido. Maimoon ita ma dariya tayi dan Mimi kawai kishi take, ita ma gani take auta ce tunda shekara biyu ne tsakanin su. Amma sai suna fada kiji tana cewa, wai ban girme ki ba, shekara biyu wasa ne? Amma yanzu da yake fada take nema, an aje shekarun a gefe.
Gefen Ummi ta zauna, sannan ta gaishe ta. "Ummi ina wuni?"
"Lafiya qlau Maimu, an dawo lafiya?" Ummi ta amsa tana murmushi.
"Adda sannu da dawowa." Sadiya ta gaishe ta.
"Yauwa auta." Ta amsa tana dariya. Mimi idanu ta juya kaman da ita ake. "Adda Moon harda ke?"
"Ko ke za'a fara cewa autan ne Mimi?"
"Allah ya kiyaye, shekara biyu fa na bata, harda watanni."
Dariya dukkan su suka yi. Ledar da Anty Salma ta bata ta nuna ma Ummi, Ummi tayi godiya ta sa mata albarka. Turaren wuta ne har kala uku a ciki, ɗaya an rubuta 'na kaya' a jiki, sai coal dinnan na zamani, sai humra da colakca.
Maimoon ta ji dadin kyautar sosai, ga su da kamshi. Mimi ta tura ta dauko mata kasko da ashana ta kunna. Ɗakin su Ummi ta fara kai wa, sai da ya kama sosai, kafin ta kai dakin su.
"Adda Moon kamshin so cool wallahi." Mimi ta ce sanda ta shigo dakin.
Murmushi Maimoon tayi, ta ƙara zuba turaren a kan coal din. Wanka taje tayi, sannan Mimi ta kawo mata abinci. Tasan in tayu bacci yanzu da kyar ta iya yi da dare, shi yasa ta hakura duk da gajiyar da ke nukurkusanta.
~~~
Washe gari Jasrah tazo da yamma tare da diyar Hasina, Nihal. Ummi tayi mamaki, dan tunda aka haifi yarinyar ta je barka bata sake ganinta ba, sai dai a hanya in sun zo. Dan Hasina bata taɓa tako ƙafarta cikin gidan ba da sunan sunzo gaishe su. Bata dai ce komai ba, amma tasan ba da sanin mamanta aka kawo ta nan ba. Da kaman da ma Jasrah magana ta maidata, sai dai tayi shiru.
Sadiya da farko taƙi daukan yarinyan, amma yaro da shiga rai, sai ta kasa daurewa, nan ta dauke ta ta dinga mata wasa, yarinyar harda dariyarta. Kamanninta ɗaya da baban ta, sai dai hasken mamanta ta dauko, dan ga ta nan kaman ka taɓa jini ya fito.
"Adda," Jasrah ta ce kira. Maimoon dake gyara kayan ta ta juya ta kalle ta. "Na'am, Jasrah ya akayi?"
"Daman Hamma Maan ne ya ce in zo in duba ki, yayi tafiyan da bai shiryawa ba kuma yana ta kiran ki wayan a kashe."
"Wayar ce ta samu ɗan matsala, amma na kai gyara. Zan kira shi In sha Allah."
Suna zaune suka ji an bankaɗo kofar ɗakin da ƙarfi, Hasina ce ke huci kaman zaki. Jasrah ta jefa da wani mugun kallo. "Keh! Uban wa ya ce ki kawo mun yarinya kazamin wurin nan? Ina wasa da ke?"
Jasrah ta turo baki, tana gunguni. "Wuce muje dallah, sai na mata wanka," ta fada tana yatsine fuska kaman taga kashi. "Allah kadai yasan abunda ya taba ta, eww."
Tunda ta fara haukanta Maimoon ko daga ido ta kalle ta batayi ba, har suka tafi. Ummi na ɗakin ta tana jin abunda ke faruwa, girgiza kai tayi. "Allah ya shirya."
Ranan da daddare su uku suna dan taɓa hira, sai Sadiya tayi shiru. Maimoon na lura da ita, chan sai taga ta fara hawaye. Da sauri Maimoon ta miƙe. "Subuhanallahi, Sadiya me ya faru? Me yasa kike kuka?" A lokacin Mimi ta lura da ba abunda ke faruwa, zama suka yi gefen ta suka sa Sadiyar a tsakiya. Maimoon ta dinga tambayanta mai ya faru, sai da kyar tana kuka ta ce. "Hamma Mu'azzam na tuno."
Nan jikin su yayi sanyi ainin. Maimoon tayi murmushin ƙarfin hali, dan ita ma ƙirjinta wani zafi ya keyi. "Addu'a zaki mai Sadiya, duk sanda kika ji kina missing ɗin shi, ki mai addu'a, ita ya fi buƙata."
"Ina yi Adda, kullun sai na mai addu'a. Kawai yau, I miss him so much, it's painful." Mimi ba ta iya ce wa komai ba, sai hawaye da ke zuba a fuskarta.
"To ku tashi muje mu yi arwala, kowa yayi nafila, sai mu mai addu'a."
Suna fita daga dakin, hawaye suka fara zubowa daga idanun Maimoon. Bata goge su ba. "Allah sarki Hammana, Allah ya jikan ka da rahama, Allah kai haske kabarin ka. Muna kewar ba kadan ba."
Mu'azzam yayansu ne, shi ne babba a gidan. Kamannin shi ɗaya da Baffa, babu inda ya bar shi. Mutum ne mai hazaƙa, da sanin ya kamata. Sa'an Hamma Ashmaan ne, dan kusan tare aka haife su. Yana son ƴan uwan shi sosai, su ma haka.
Allah ya mai rasuwa shekara hudu da suka wuce. Ya kwanta bacci, aka waye gari babu shi. Washegarin ranan da zai mutu, da daddare sun ɗaɗe suna hira sosai shi da ƴan uwan shi, da iyayen su, har wajen karfe biyu na dare kafin kowa ya tafi ya kwanta. Farkawar da beyi ba kenan.
Mutuwar Mu'azzam ta girgiza ahalin Baffa ba ƙadan ba, dan shi Baffa ma sai da yayi jiyan wata da watanni. Ummi kuwa, ita kadai ta san yanda ta ke ji. Ga rashin ɗa, ga a lokacin miji ya kwanta ba lafiya, ga yara mata har su uku. Da yardar Allah, da amincewar Sa, komai ya dawo daidai. Sai dai a kullun suna kewar Mu'azzam ba ƙadan ba, kullun su na mai addu'a Allah ya jikan shi da rahama, ya gafarta mai.
.
.
.
.
.
.
Allah ya azurta mu da karshe mai kyau😢
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro