Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA BIYU







~~BABI NA BIYU~~




Sunan ta da aka kira yasa ta tsayawa. Waye ke kiran ta haka? Dan sam bata ba samarin layin su fuskar da zasu tare ta a hanya ba, bama a layin nasu ƙadai ba, a ko ina. Bata tsaya ba, ta cigaba da tafiyar ta.

"Maimoon?"

Cak ta tsaya, dan taso ta gane muryan. Mamaki ya kamata ganin wanda kwakwata batay yi tsammanin ganin shi ba. Ko yaushe ya dawo ƙasar?

"Maimoon din ce kuwa, ga idanun nan."

Murmushi tayi amma shi ba zai ga hakan ba saboda niqabin ta. "Hamma Ashmaan?"

"Maida idanun kar su faɗo," yace cike da zolaya. "Nasan kina mamakin gani na, jiya da daddare na dawo."

"Sannu da zuwa. Ina wuni, ya hanya?"

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah, ina zaki haka?"

Cike da rashin gaskiya ta bashi amsa akan cewa Ummi ce ta aike ta.

"Muje to in raka ki."

Da sauri ta girgiza kai; "ba sai ka raka ni ba Hamma, ba yanzu zan dawo ba, aiken da yawa."

"Rowa ake mun ko?"

"Ni na isa, ba haka bane."

Murmurshi yayi, yana jinjina kai. "To shikenan, sai kin dawo. Anjima zan shigo muyi hira, nayi missing dinki sosai."

Dariya tayi, kunya na kamata.

Tsare da yayi da idanu. "Ke bakiyi missing ɗina ba kenan?"

Girgiza kai tayi. "Ni bance ba."

Murmushi yayi yana kaɗa kai. "Ƙar in tsaida ki, bye."

Sallama ta mai itama sannan ta juya ta cigaba da tafiya. Ashmaan bai motsa daga inda yake tsaye ba har saida ya bar ganin Maimoon. Murmushin da ke dauke da ma'anoni daban yayi kafin shima ya ƙarasa inda yake da niyan zuwa.

Ta na tafiya tana murmushi ita ƙadai. Duk cikin abokan wasan ta (cousins) sun fi shiri da shi sai ƙanwar shi Jasrah. Rabon da ta ganshi har ta manta, tunda ya tafi makaranta a America ƙaro karatu.

Alhaji Bello (Daddy) da Hajiya Suwaiba (Mommy) na da yara shida, maza biyu da mata huɗu.  Ashmaan ne babba yanada shekaru ashirin da tara, sai Hasina da tayi aure da yarinya ɗaya, shekarun ta ashirin da shida, Fauziya mai shekaru ashirin da hudu, sai Radiya sa'ar Maimoon, sai Jashrah mai shekaru sha shida sannan ɗan auta Auwal da ake kira da Khalifa yana da shekara goma.

Dukkan su halin su ɗaya da iyayen su, har da Khalifa da bai wuci ka ƙaryashi da hannu ɗaya ba. Har ma sun so sufi iyayen nasu, Hausawa na cewa magaji mafiyi.

Hasina halin ta sak irin na mahaifiyar ta, koma fiye da nata. Duk cikin su tafi takura ma Maimoon, musamma bayan wani babban lamari da ya faru tsakanin su. Da yake itama Maimoon ɗin ba kanwar lasa bace, tana taka mata birki sosai.

Mommy na da son yara ba ƙadan ba, duk abun da suke so koda kuwa bai dace ba zata basu dan a wurin ta bataga amfanin dukiyar da uban su ya tara ba in har baza'a basu abunda suke so ba. Sun tashi kuma da ƙiyayyar ƴan uwan su kaman yanda ta koya masu tun suna ƙanana.

Ashmaan da Jasrah ne ƙadai suka fita daban a cikinsu. Mommy tayi faɗan tayi faɗan har ta gaji. Har cewa take Rabi'atu ta asirance mata yara.

Maimoon ba ta dawo daga inda taje ba sai wurin ƙarfe uku. Nan ma ba gida ta nufa ba, gidan su Habiba—babbar aminiyarta— ta wuce dan akwai abu mai mahimmanci da ya kamata su tattauna akai.

Ta haɗu da Habiba a makarantar islamiya bayan sun dawo gidan Daddy da zama, shekara bakwai da suka wuce. Lokaci ɗaya jinin su ya haɗu sosai, suka ƙulla aminantakar da yanzu ta zama ƴan uwan taka.

A yanzu Habiba na shirin gama makarantar jami'a ta jihar Kaduna, Kaduna State University (KASU) inda take karanta pharmacy. Baban ta babban ɗan kasuwane da ya tara dukiya mai dumbun yawa. Sabanin ƴan uwan Maimoon, Habiba bata taɓa nuna mata akwai banbanci tsakin su ba. Tana da kirki sosai, ita da iyayen ta. Sun dauki Maimoon kamar ƴar cikin su.

A palo Maimoon ta sami mahaifiyar Habiba. Bayan sun gaisa da ida sa ɗakin Habiba a sama. "Assalamu Alaikum," Tayi sallama tana tura ƙofar ɗakin.

A tsaye ta samu Habiba riƙe da ƙugu. Habiba bata da tsawo sosai kuma tana dan ƙaramin jiki. Tana da ɗan haske amma ba chan sosai ba.

"Wa'alaikumus salam. Tun ɗazu nake jiran ki, sai yanzu kika ga daman zuwa ko?"

Hararta tayi. "Sai kace baki san daga inda nake ba."

"Haka ne kuma. Toh samu guri ki zauna."

Drinks da snacks ta kawo ta jera a gaban Maimoon. Samosa kaɗai Maimoon ta ci, dan duk ciki ya fi birgeta.

Sunyi hira sosai da Habiba, har take sanar mata Safara'u ɗayar ƙawar tasu tayi tafiya. Su uku ne aminan juna ƙut ƙut, sun ma tashi daga aminai, sun zama ƴan uwa. Safara'u da Habiba dama chan ƙawaye ne saboda iyayan su tare suke ƙasuwanci. A wurin Habiba Maimoon ta san Safara'u. Tun daga lokacin kuma suka saba sosai har haka.

Ita ma Safara'u na shirin gama makaranta, Mathematics take karanta.

Hira tayi ɗadi har Maimoon ta so manta abunda ya kawo ta, tana tunawa ta sanar da Habiba ɗan ta rasa abun yi akan al'amarin, gaba ɗaya kan ta ya ƙulle.

"Kina nufin har yanzu baki faɗawa Ummi ba? Haba Maimoon!"

Ajiyar zuciya Maimoon ta sauke. "Ki bari kawai Habiba, wallahi ni ma ina so in faɗa mata, amma ina gudun baccin ranta."

Tsaki Habiba taja tana girgiza kai. "Tun yaushe? Wajan wata shida kenan fa, ai ban san baki faɗa mata ba. Idan ma ranta bai baci ba akan abunda kikeyi ba to lallai ze baci akan boye mata dakika yi."

"Hmm! Ni yanzu ya zanyi?" Ta tambaya tana tagumi.

A rayuwa tana gudun baccin ran iyayenta, bata so sam! Amma kuma in ta tuna dalilin da yasa tayi hakan sai taga ai bata da wani laifi.

"Kawai kije ki faɗa mata, kar tazo ta sani."

"Haka za'a yi. In sha Allahu zan samu lokaci in faɗa mata, nasan zata gane."

"Allah ya sa." Habiba tace.

Bata bari yamma yayi ba kaman yanda Habiba ta so, ta shirya ta tafi gida tana nazarin abunda suka tattauna. Tabbas ya kamata ta sanar da iyayen ta abunda take yi kafin lokaci ya ƙure a samu matsala. Da wannan shawarar ta idasa gida.

~~~~

Suna zaune a tsakar gida, sun shimfiɗa tabarma suna cin abincin dare sukaji ana sallama, kuma muryar namiji. Da sauri su Maimoon suka maida hijaban su, dan dama anan sukayi sallar isha'i.

Baffa ne ya tashi yaje ya shigo da baƙon, sai gashi sun shigo tare da Hamma Ashmaan. Nan Sadiya ta kawo mai tabarma ya zauna. Suka gaisa da Ummi da Baffa, har Ummi na tsokanan shi.

"Ashmaan kaje chan kayi zaman ka, sai yanzu ka dawo. Ina sha wata ta rike ka ai."

Ashmaan dai dariya kawai yayi, yana sosa kai.

"Hamma Ashmaan ina wuni." Sadiya da Mimi suka gaishe shi a lokaci daya. Fuskar shi dauke da murmushi ya amsa masu. Ita ma Maimoon ta gaidashi, ya amsa.

Nan sukayi hira da Ummi da Baffa kaman yanda suka saba duk sanda yazo. Ashmaan yana girmamasu sosai. Bayan ƴan mintina yace zai tafi. Waje ya fita ya dawo da ledoji a hannu, ɗaya ya mikawa Ummi, ɗaya ya mikawa Baffa. "Ga wannan ba yawa."

"Harda dawainiya haka?" Baffa ya ce yana murmushi. "To Allah amfana."

"Allah saka da alkhairi." Ummi tace.

"Ameen, ameen." Ashmaan ya amsa yana murmushi.

"Mimi," ya kira Amina. "ga naku ke ta Sadiya."  Amsa tayi tai masa godiya.

"Moon kema ga naki." Ashmaan yace, idanun shi a kan ta.

Ji tayi duk ta tsargu, meye zai wani kafe ta da idanu? A hankali ta taka inda yake a tsaye ta amsa ledar hannun shi. "Nagode Hamma Ashmaan, Allah saka da alkhairi."

Lumshe idanu yayi. A sanyaye ya amsa da Ameen tare da musu sai da safe. Har ƙofar gida Baffa ya raka shi, shima ya masa sai da safe sannan ya dawo cikin iyalin shi suka cigaba da hirar su kafin kowa ya tafi makwancin sa.

"Meye a cikin ledar ki Adda Moon?" Sadiya ta tambaya, tana son ganin kwakwap.

Maimunatu bata tanka mata ba, ta cigaba da gyara wurin kwanciyar ta.

Mimi ta zunguri Sadiya, da ido take ce mata tayi shiru. Sadiya ta taɓe baki. Tashi ma tayi ta dauko ledar da Hamma Ashmaan ya basu. Mimi tazo ta zauna kusa da ita suka fara fiddo kayan ciki.

Dogayen rigunane guda biyu iri ɗaya amma akwai banbancin kala. Ɗaya ja, daya blue. Da sauri Sadiya ta dauki blue din tana karawa a jikinta. Rigar nada kyau, A-shape mai dogon hannu an mata ado da fararen stones a wuya da karshen hannun.

"Wow!" Mimi ta yaba ta kyaun rigan.

Sauran abubuwan ciki suka cigaba ta fiddowa.

Kwalaban turare biyu na kamfanin Elizabeth Aden, sai set ɗin man shafawa na beauty shop, ɗankunne kala takwas, kowa hudu kenan, takalma kafa biyu, sai kuma lodin chocolates, kala daban daban.

"Kai Masha Allah!" Sadiya ta ce tana washe haƙora. "Allah wa Hamma Ashmaan albarka, wannan kaya haka."

"Wallahi kuwa sis, Allah ya biya masa buƙatunsa na alkhairi." Mimi tace itama. "Ya fita daban a cikin ƴan uwanshi, baza ki taɓa cewa ƴan uwa ne ba saboda banbancin halayan su."

Itadai Maimoon nata ido. Duk abun suke tana jin su, amma bata ce komai ba. Itama ta yaba da kyan kayan kuma ta kara godewa Hamma Ashmaan.

"Adda," Mimi ta kira a hankali. Idanu kawai ta zuba mata. "Please ki bude bag din mana." Sadiya ta daga kanta. "Muna son ganin kayan ciki.

"Gatanan ku bude." Abun nema ya samu, da sauri suka dauko ledan suka dawo tsakiyar dakin. Wata leda Sadiya ta fara cirowa, ledan na da duhu baza ka iya cewa ga abun dake ciki ba.

Hannu na rawa Sadiya ta bude ledan, jallabiya ce a ciki kallar toka(ash). Da sauri ta mike tana karata a jikin ta kaman yanda tayi dazu. Babu wani kyalekyale jikin ta, an mata aikin hannu (embroidery) mai kyau kala ɗaya da rigar, sai dai zaran da aka yi amfani dashi yafi duhu. An zagaye gaba dayan wiyar rigar har ya sauko tsakiya, hannun rigan ma haka. Sai ɗan madaidaicin gyale.

"Gaskiya Hamma Ashmaan ya iya zabe, sai kace mace." Mimi ta ce tana kallon rigar. "Meye kuma a ciki?"

Wata riga Sadiya ta kara fiddowa, wannan kalar ta Maroon ne. Rigar kaman babbar rigan maza, wuyan round sai dogun hannu. Daga wuyan har hannayen an jera masu golden stones, sai gyale baki shima ƙarshen shi anyi ado da kallan stone din dake jikin rigan.

Itadai Maimoon duk wainar da ake tuyawa nata ido. Sadiya da Mimi sai yaba kyan kayan sukeyi. Sadiya ta kara zaro wata riga.

"Kai Adda!" Mimi ta ce da taga abun yaƙi ƙarewa. "Duk ke kadai? Gaskiya Hamma naji da ke."

Wanna karon baƙar jallabiya ce, bata da wani kwalliya. Harda niqabai masu kyau sosai. Tunda Sadiya ta fara fiddo kayan, niqab din kadai ya dauki hankalin Maimoon. Sunyi kyau sosai, ta kuma ji dadi da Hamma Ashmaan bai manta son da take musu ba.

Niqab ya zama barin jikanta da bata tunanin zata iya rayuwa in babu shi. Tun tana sakawa saboda ba'ar da su Mommy ke mata akan bakinta har yazo ya zaman mata jiki. Ko nan da chan bata iya fita in babu shi.

"Adda ko wace riga da niqab dinta," Sadiya tace. "Kinga irin na larabawan nan ne wanda kike so sosai."

Sauran abubuwan ciki Sadiya ta cigaba da cirowa. Jilbabs, turare, kayan shafa, takalma da lodin chocolates.

Sadiya riƙe da haɓa tana kallon kayan cike da mamaki. "Wannan sai kace saurayi yama budurwar shi siyayya." A hankali tayi maganan dan kar Maimoon taji.

"Nima dai haka nace Sadiya, ko dai?" Mimi ta daga gira. Nan suka kwashe da dariya harda tafawa.

Maimoon bata jin abunda suke faɗi, kuma bata damu ba, dan sun saba. A ranta cewa take wannan kayan sunyi yawa.

"Sadiya kaman akwai wani abu a ciki." Mimi tace tana daukar ledar kayan.

"Ko?" Da sauri Sadiya ta dawo tsakiyan ɗakin ta zauna, dan harta koma kan katifar ta.

"Duba ki gani." Mimi ta miƙa mata ledan.

Sadiya ta dauki ledan taji da ɗan sauran nauyi. Dan madaidaicin kwali ta fiddo. Ita da Mimi suka tsaya kallon juna kafin su kwala ihu. Ihun sai da ya firgita Maimoon. Aiko ta hausu da faɗa. "Wai ku baku da hankali? Bakusan dare ba? Ku dinga abu kaman ƙananan yara."

"Adda waya!" Sadiya ta fadi tana tsalle. Maimoon ta tsaya tana kallon ta. Waya kuma? Wace waya?

"Kalla!" Tare suka haye saman katifan ta suna nuna mata kwalin hannunsu. Saida gaban Maimoon ya fadi. Wayarce ko.

"iPhone ce," inji Mimi tana dariya.

Ita kam kanta ciwo ma ya farayi. Ita ina zata kai wannan?

"Irin ta Jasrah ce," Mimi ta faɗa tana juya kwalin

"Masha Allahu! Ki ce mun samu na portrait." Sadiya ba dai san hoto ba. Mimi dariya tayi har hakoranta na fitowa.

Maimoon da abun duniya ya ice ta, ta fuzgo kwalin ta tura karkashin pillow. "Wuce kuje ku kwanta."

Yanda tayi maganan yasa suka sha jinin jikinsu. Sumi sumi suka koma kan katifar su. Tsaki tayi, girman wayan ya mata nauyi akan katifa. Allah Allah take safiya tayi ta maida wannan wayan. Sam! Bata son abunda zai kawo magana ko ya dagawa iyayenta hankali.

Da safe da suka tashi, Mimi da Sadiya suka kaiwa Ummi kayan da Hamma Ashmaan ya kawo masu. Taji dadi sosai da irin karamcin yaron, tayi ta sa mai albarka. Maimoon ma ta kai nata amma banda wayan. Mimi da Sadiya dai basu ce komai dan sun san hallin yayar tasu, dan haka suka ja bakin su sukayi shiru.

Wurin karfe sha ɗaya, Maimoon ta gama aikin gida har ma tayi abincin rana. Tayi sauri ta sake wanka dan duk hayaƙin risho take yi. Sadiya kan mata dariya, wai in har zata sake wanka bayan ta gama girki to meye amfanin yin shi tun farko. Kawai bazata iya dafa abinci bata yi wanka ba, gani take ƙazanta ne. Tayi wanka ta shirya cikin atampa dinkin riga da zani. Atamfar ƙarama ce amma duk da haka ta mata kyau sosai. Ta dauko hijabin ta tasa, ta rufe fuskar ta da niqabi. Ta dauki jakar ta, sannan ta nufi dakin Ummi. "Ummi na tafi."

"To ƴar albarka, a dawo lafiya." Runtse idanu tayi. Ƙaryar da take ma iyayenta na damun ta amma ba yanda ta iya. Amma In sha Allahu zata sanar dasu, tasan zasu fahimta. Dole ce tasa hakan.

A waje taci karo da Hamma Ashmaan, hakan ya mata dadi dan dama tana son ganin shi. Cike da ladabi ta gaida shi. "Hamma ina kwana."

Shima cike da fara'a ya amsa mata. "Lafiya qlau Moon, amma ina zaki haka da sassafe?"

"Makaranta." Ta ce a takaice. "Hamma kaya sunyi kyau, Allah amfana, Allah ya saka da alkhairi."

"Haba Maimoon, godiyar kuma ai ya isa haka. Ki dauka kaman Mu'azzam ne ya maki."

Zuciyar ta saida ta buga an taɓo mata inda ke mata ciwo. A hankali ta mika mai ledan dake hannun ta. Cike da rashin fahimta yasa hannu ya amsa.

"Ga wannan, nagode. Amma bazan iya amsa ba."

"Saboda mai Maimoon? Ban isa in maki kyauta ki amsa ba kenan?"

Kai ta girgiza. "Ba haka bane Hamma, wannan dai ba zan iya amsa ba."

"Dalili?"

"Kawai dai bazan iya amsa ba. Dan Allah kar kace komai, dan Allah."

Baice mata komai ba, illa kallon ta da yakeyi kaman mai neman wani abu. Sai kuma chan ya daga kai. "Shikenan Maimoon," alamu sun nuna ba haka yaso ba. "A dawo lafiya."

"Sai anjima." Maimoon ta juya ta cigaba da tafiya.

Ina zata amsa waya a hannun shi ƙannen shi da mahaifiyar shi su tozarta ta. Wayan ma ba karama ba, ita Maimunatu ina zata kai wayar dubu dari da yan kai. Ai zancen ma bai taso ba.

Hakan shi ne daidai.





~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro