BABI NA BIYAR
~~BABI NA BIYAR~~
Yau za'a sallame Baffa kaman yanda likita ya sanar da Ummi. Tunda Maimoon ta iso take ƴan kimtse kimtse. Ta haɗa duka kayan su wuri daya, mota kawai za'a kaisu. Mimi da Sadiya na makaranta.
"Maimunatu?" Baffa ya kirata.
Jakar hannunta ta aje sannan ta taka har inda yake. Hamma Ashmaan ne yayi magana aka maido shi ɗakin mutum ɗaya amma da a ɗakin mutane takwas yake. "Baffa ga ni."
Alhamdulillah Baffan ta ya samu sauki, sai dai ƴar rama da yayi. "Ke ya bakije makarantan ba?"
Ƙasa tayi da kanta. Ranan da zasu gano ba makarantar da take zuwa kashin ta zai bushe. "Baffa nazo in taya Ummi aiki ne."
Dariya yayi. "In banda abinki Maimu, har wani aiki ne mai yawa da sai kinzo taya ta. Baga Ashmaan ba."
"Baffa..." ta faɗa a shagwabe.
"To ya isa, je ki cigaba da aikin ki." Ya ce yana mata dariya. A lokacin Ummi ta fito daga bandaki. "Yawwa Ummin su, babu wani aikin da za'a taya ki? Ga ƴar ki nan tazo taya ki aiki."
Ɗadi ne ya mamaye ranta, lallai Baffan ta ya samu sauki. Dama shi mutum ne mai yawan tsokana da janyo mutane jiki. Zama ta iya cewa yafi Ummin su sakin fuska, kullun fuskar shi dauke da murmushi.
Ummi ta maida idanunta kan Maimoon dake zaune kan daya daga cikin kujerun roba dake ɗakin. "Rabu da ita, yawo ne kawai. Ita dadi mota."
"Kai Ummi." Ta ce tana turo baki.
A haka Hamma Ashmaan ya shigo ya same su. "Moon lafiya ake turo baki?"
"Rabu da ita Ashmaan, shagwaban ne ya motsa." Baffa ya bashi amsa. "Kasan da tana ƙarama shagwababbiya ce, harda laifin Mu'azzam, shi ke biye mata."
Dariya duk suka yi. Ashmaan ya fara ɗaukan kaya ya kai mota, Maimoon na taya shi. Nan da nan suka gama tunda kayan basuda wani yawa. Ashmaan ya taimakawa Baffa ya taka har mota, gidan gaba ya shiga, Ummi da Maimoon kuma suka shiga baya.
Motan shiru baka jin komai sai labarai da akeyi a rediyo amma an rage ƙaran. Ashmaan ya karya kwanan gidan su kenan wata mota ta fito, hakan yasa ya taka birki da ƙarfi, dan bai ji ta ba kuma yayi horn. Sai da yayi reverse, sannan ɗayan motan ta fito ta wuce. Abin mamaki Daddy ne a ciki direba na tuƙa shi amma sai yayi kaman bai gansu ba. Babu wanda yayi mamaki a cikin su, Ashmaan ko kunya yaji. Kai ya girgiza yana fadin Allah ya kyauta a zuciya.
Maimoon taɓe baki tayi. Bata taɓa ganin mai girman kai, tinkaho da dagawa kaman ƙanin mahaifinta ba. Duniya ina zaki damu? Saboda abun duniya mutane suke yanke zumunta, saboda dukiyar da ba wayon ka bane ya samo ma kake wulaƙanta wasu.
"Alhamdulillah," Baffa ya ce bayan Ashmaan yayi parking mota. "Sannu da ƙoƙari Ashmaan."
Jasrah ce ta fito da gudu ta bude ƙofar Baffa tana mai sannu da zuwa. "Yawwa ƴar autar Baffa." Haka yake kiranta kasancewa ita ce karama, Sadiya ta bata ƴan watanni.
Daga nan suka isa cikin gida. Mimi da Sadiya sun dawo har sun dafa abinci. Tabarma aka shimfiɗa a tsakar gida, kowa ya zuba abinci. Baffa wani daɗi ke ratsa shi, ina ma ace shi da ƴan uwanci ne haka. Su uku mahaifiyar su ta haifa, Abdulkarim, Muhammad, sai Bello. Tare suka taso, komin su tare. Amma da suka girma a maimakon su ƙara haɗa kai sai kowa yayi hanyan shi, Bello da Abdulkarim dukiya da mulki su ka rufe masu ido, suka sa suka juyawa ɗan uwansu baya saboda suna ganin yanzu sunfi ƙarfin shi saboda dukiyar da suka tara. Mahaifin su ne mai masu nasiha, toh amma yau ba shi, mahaifiyar su kam bata damu ba, in dai jakar ta da nauyi.
Baffa a kullum mamakin halayen su yake, ya kan zauna yayi ta tambayan kanshi tambayoyin da ba zai iya amsawa ba. Addu'ar shi kullun garesu shi ne Allah Ya shirya su.
Bayan sun gama cin abinci, Jasrah, Mimi da Sadiya suka kwashe kwanukan suka yi wanke wanke. Ita kuma Maimoon ruwan zafi ta ɗaura ma Baffa, yayi wanka sanna ta bashi magani ya sha, ya kwanta. Hamma Ashmaan yana gama cin abinci ya fita, yace yana da aikin yi.
"Wash!" Sadiya ta ce tana faɗawa kan katifar ta. "Ƙugu na."
Jasrah da ke kusa da ita ta kai mata duka. "Kefa dadi na dake you're too lazy, sai shegen son jiki. In kinje gidan ki wa zai maki?"
Hararrata Sadiya tayi. "Ban gane wa zai mun ba. Tare za muyi mana."
Mimi ta kwashe da dariya tana girgiza kai. "Baki da hankali wallahi. Mazan mu na hausawa ne zasu taya ki aiki? Lallai ma, keep dreaming. Ke ni na taɓa saurayin da ya ce mun wai matan shi baza tayi aikin gwamnati ba. Kuma bai yarda a kawo mai mai aiki cikin gida ba. Dole ta kula dashi da yaran shi, kuma shi bazai tayata ba saboda shi namiji ne."
Ido Jasrah ta zaro. "Haka yace maki?"
Kai Mimi ta ɗaga. "Lallai." Sadiya ta taɓe baki. "Ni dai ina ƙara rokon Allah ya bamu mazaje na gari wanda suka san haƙƙin matan su."
"Ameen ƴar uwa!" Mimi da Jasrah suka yi saurin ansawa.
Maimoon na jin su, ita dariya ma suke bata. Duka shekarun su nawa? Suke irin wannan hira, kai ta girgiza. Mimi wai harda saurayi, abun mamaki yake bata. Ita lokacin da take kamansu ai karatunta ne kawai a gabanta, bata da lokacin da namiji zai zo ya cika ta da ɗaɗin baki ya ɓata mata lokaci. Ita ta dawo daga rakiyar maza ai. Wa zai so baƙa mummuna? Tayi kuskuren faɗawa tarkon su, amma ta koyi darasi. Darasin da baza taɓa mantawa ba. Ita da soyyayya haihata-haihata.
Miƙewa tayi ta fita amma kafin ta fita ta juya ta kalli su Mimi. "Toh masu samari ai kwa tashi kuyi sallah ko?"
Kunya duk tabi ta rufe su. Wai dama Adda Moon na ɗakin? Su kwatakwata basu ganta ba. Tashi sukayi suka je suka yo alwala, kafin kowa ya gabatar da sallan shi.
Sai bayan sallan isha'i Jasrah ta koma gida. Tana shiga Mommy ta rufe ta da faɗa. "Ke wai wani irin kunne gare ki? Sai na balla ki a gidan nan wallahi, shashasha mara wayo." Jasrah dai bata ce komai ba, ta daga kai zata tafi ta lura da maihaifin ta zaune yana kallon TV.
"Daddy barka da dare." Ta gaishe shi tana tsugunniya a gaban shi.
"Sannu Jasrah, ya school?"
"Alhamdulillah Daddy."
"Hope babu problem?" Kai ta girgiza. "Okay."
Daga nan ta miƙe, dan ta san ba abunda zai kara cewa. Babu shaƙuwa tsakin ta da Daddy, ita tana gani ma bai taɓa wata daya a gida tare dasu ba.
Mommy tai kwafa. Wato ba zaiwa ƴar shi magana akan zuwa wurin wanchan mutanen ba ko? Ita ta rasa mai yasa har yanzu suke zama a gidan. In tayi magana sai yace tana so mutane su zage shi, yaƙi ba ɗan uwanshi muhalli. In ma sai ya taimake su to ya basu gida daidai da shi mana, dole se sun zauna mata a gida. Ina dalili!
"Suwaiba." Taji ya kirata. Tana gunguni ta zauna kusa dashi. "Mai ya sa kike takura wa Jasrah ne?"
Ido ta juya mai. "Ai ka fini sani. Wai Bello yauce mutanen nan zasu bar mana gida?"
Bai bata ansa ba. Shima ba son zaman su yake ba, amma Abdulkarim yace kar ya kore su. Suda zasu shiga siyasa, in har mutane suka gano basa taimakon ƴan uwansu ai ba wanda zai zaɓe su. Ance ai daga gida ake fara kyauta.
Jasrah na ta isa daki toilet ta shiga ta rage mara. Fitowan da zata yi tashi karo da yayarta zaune a kan gado. Kowa ɗakin ta daban, saboda haka tayi mamakin ganin Fauziya a ɗakin ta dan ba wani shiri su keyi sosai ba.
"Ya Fauziya ya akayi?" Jasrah ta tambaya tana janyo kujeran dressing mirror dinta dan ta zauna.
Kallon ta Fauziya tayi tana yatsine fuska kafin ta bata amsa. "No, ba wani abu bane ba fah, kawai naji Mommy na maki faɗa ne. Jasrah wai what's your problem? Meye matsalan ki? Kullun ai ta maki magana daya, ai ko jaki yaci ace ya gane—
"—please!" Jasrah ta dakatar da ita ta na daga mata hannu. "If you don't have anything better to say, ki tashi ki bar mun ɗakina."
"Jasrah ni kike ce ma haka?" A fusace Fauziya tayo kan ta. "Baki da kunya, ke har kin isa kimun magana haka. Dan ubanki shekara nawa na baki?"
Jasrah bata sake cewa komai ba, sai ma juya mata ƙeya da tayi, in ta gaji ta bari.
"Wawiya mara hankali, ke baki ma ƙyaman zama kusa da su? Sai kinje kin kwaso talauci, stup—"
"Keh Fauziya." Wata murya ta daka mata tsawa. Dukan su saida suka firgita. Hamma Ashmaan ne tsaye bakin kofa, duk abunda ta ce a kunnen shi. "Akwai wawiya mara hankali irin ki? Kina girma amma baki da hankali baki da tunani..."
"Haba Hamma Ashmaan." Fauziya ta watsa hannu sama. "Ya zaka dinga mun haka a gaban ta, ai shi yasa ta raina ni. Gaskiya ka bari."
"Oh rashin kunyan da kika saba zaki mun. Look," yace yana nuna ta da yatsa. "In bakiyi a hankali sai da balla ki a gidan nan, sai na koya mi ki hankali. Useless kawai, wuce ki ba mutane wuri."
Fauziya ta fita daga dakin tana ƙunƙuni. Kwafa Hamma Ashmaan yayi, yana gab da sauya mata kamanni. Saboda takaici ya ma manta abinda ya hayo dashi sama. Yazo wuce wa ne yaji tana zazzaga rashin mutunci iya san ranta.
Duban shi ya maida kan Jasrah. "Kashe wuta ki kwanta, dare yayi." Yana gama magana ya fita.
Ajiyar zuciya Jasrah ta sauke. Allah ya gyara lamarin gidannan. Wanka ta shiga tayi kaman yanda ta saba, tasa kayan bacci, tayi addu'a, sai bacci.
~~~
Tunda Maimoon ta tashi gaban ta ke faɗuwa, ta rasa dalili. Har nafila tayi, amma har yanzu hankalin ta bai kwanta ba.
Inna Lillahi Wa Inna Ilahi Raji'un.
Allah dai yasa lafiya. Yau ma kaman kullun, ta gama gyaran gidan. Baffa Alhamdulillah sauki ya samu sosai. Dan yau har ya fita aiki. Allah ya sa a samu abunda aka fita nema.
Ta shiga kitchen dan ɗaura girki amma sai ta tarar babu kananzir. Ɗaki ta nufa ta bude wata jakar baya, a ciki ta fito da ƙaramin purse mai dauke da ƙudi, dubu biyu ta dauka ta fita, sannan ta nufa ɗakin Ummi.
"Assalamu Alaikum." Tayi sallama, tana turo ƙofa. "Ummi, zan je in dawo."
"Toh Maimoon, sai kin dawo."
Kasuwan dake kusa da gidan su taje. Kananzir ta fara siya, sannan ta nufa inda ake saida kayan lambu. Latas, kabeji, cucumber da tumaturi ta siya. Bayan nan ta siya naman miya da sauran chanji.
Ummi rike haɓa tayi tana kallon kayan da Maimoon ta siyo. "Maimunatu ina kika samu kudin nan?"
"Wanda nake tarawa ne Ummi."
"Banda abinki ai sai ki adana. Mai ya sa baki zo kin tambaye ni ba?" Shiru tayi tana sadda kai ƙasa. "Allah ya maki albarka, mun gode."
Murmushi ya bayyana a fuskan ta. "Ameen Ummi." Ɗaki ta shiga ta cire hijab da niqab sannan ta shiga kitchen ta ɗaura girki. Kafin ƙarfe biyu ta kammala. Shinkafa ta dafa da miya, ta yanka vegetables din da ta siyo. Sannan tasa komai a kula. Wanka ta sake yi, tayo alwala, tayi sallan azahar. Kasancewa yau juma'a, Mimi har sun dawo. Sai da suka je suka gaida Ummi sannan suka shiga ɗaki.
"Adda Moon Ina wuni."
"Lafiya lau ƴan biyun Ummi, ya makaranta?"
"Alhamdulillahi," suka amsa. Sannan ko waccen su ta je chanza kaya.
Tare suka zauna suka ci abincin. Sadiya sai santi take yi. Taɓe baki Maimoon tayi. "Gaki nan sai aikin ci, ci ba ƙiba asaran hatsi."
"Kai Adda!" Sadiya ta turo baki gaba. Dariyar ƙeta Mimi ta mata. "Ai ba ƙarya aka yi ba."
Harara Sadiya ta banka ma saƙon tata. "Dallah matsa, duka da mai kwado ya dara gaya."
Kafin Mimi ta bada amsa abun ya zama fada, Maimoon tayi saurin dakatar dasu. "Toh sabbabu, ya isa."
Chan da yamma sai ga aminiyar Maimoon, Safara'u. Tayi tafiya, taje Katsina gidan ƙanwar mahaifinta hutu. Sosai Maimoon tayi murnan ganin ta dan an kusa wata biyu rabon da suga juna. Sai da ta kai ta gaida Ummi, in da Ummi ta tambaye lafiyar mutanen gidan sannan suka karasa ɗaki.
Kudi ta ba Mimi ta siyo mata soft drink. "Haba Munari, sai kace dai wata baƙuwa."
Wuri Maimoon ta samu ta zauna, sannan suka gaisa sosai. "Mutanen Kt, ya katsinan? Ya kika baro su?"
"Katsina Alhamdulillah, sai zafi." Nan suka zauna sukayi firar yaushe gamo. Nan Safar'u ke sanar mata cewa ansa bikin yayanta.
"Wai, su Najeeb an kusan zama ango. Masha Allah, Allah ya nuna mana."
"Ameen." Safara'u ta amsa. "Ke ni ma Baba karami ya tuso ni gaba dole sai na fito da miji a haɗa bikin."
Kasancewa Safara'u ce babbar ƴa mace a gidansu, kuma yaran ƴan uwa sa'annin ta duk sunyi aure, wasu har da yara, wannan yasa ƙanin mahaifin ta ya sa mata ido. Shi a dole sai ta fiddo miji.
Mutane na mancewa aure nufin Allah ne. In lokaci yayi ba wanda ya isa ya hana, haka in lokaci baiyi ba ba wanda ya isa yasa. Amma sai a dinga gani kaman kaine baka son auren. Ko wace mace burinta ta ganta cikin ɗakin ta tana bauta ma Allah.
"Ki dage da addu'a kinji Safara'u. In sha Allah ko mai zai daidaita."
"Ameen Maimoon, ameen."
Da Safara'u tazo tafiya, turare ɗaya daga cikin wanda Hamma Ashmaan ya kawo mata ta bata. Saida Maimoon tayi da ƙyar kafin Safara'u ta ansa. Har kofar gida ta raka ta, sannan ta dawo ciki.
Bata dade da komawa ba, Baffa yayi sallama. Ita ta amshi kayan dake hannun shi, Sadiya kuma ta kai mai abinci. Suna zaune kawai suka ji an bugo kofa. Salati suka hau yi saboda karfin da akasa aka turo kofan kaman za'a balla ta. Tuni Baffa da Ummi suka fito dan ganin mai ke faruwa.
Daddy ne ya shigo gidan yana huci kaman zaki. Fuskan ci a haɗe babu annuri, daga gani kasan ranshi yayi matukar baci. Dukkan su mamaki ne ya kama su. Mai ya kawo Daddy? Kuma mai ya faru yake huci kaman zakin dake shiryin hadiye su.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro