Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA BAKWAI















~~ BABI NA BAKWAI ~~













Subuhanallahi, Maimoon ta faɗa a zuciya tana kallon sararin samaniya. Hadari ya taru sosai, Allah Allah takeyi ta isa gida. Dan daga gani ruwan da za'ayi mai karfi ne. In ko ya tare ta a hanya akwai matsala, dan ba shakka sai tayi mura da zazzabi.

Da izinin Baffa yanzu take zuwa yin kitso, zama hakanan ba dadi. Tun safe ta fita yau, sai yanzu da yamma ta gama. Da yake gidan da taje suna da ƴan mata da yawa ga gashi Masha Allah.

Batayi aune ba taji ruwa ya fara zuba. "Ya ilahi!"  Ta ambata, tana nema inda zata tsaya dan bata da lema, ƙasan wani rumfa ta fake, ruwa kamar da bakin kwarya haka yake zuba. Tana tsaye a wurin, ƴan mashin suka dinga parking a wurin suma. Hankalinta ya tashi ganin ita kadai ce mace ga maza sunyi dandanzo a wurin, wasun su sai warin sigari sukeyi.

Maimoon bai dace ki tsaya a wurin nan ba, ta faɗa a zuciya. Gashi ta lura ɗaya daga cikin su sai binta yake yi da ido. A nan wurin ta yanke shawaran shiga ruwa, komai zai faru sai dai ya faru amma baza ta tsaya a wurin nan ba.

Sai a sannan ta tuna cewa gidan ƙanwar Safara'u anan kusa yake, amma kuma taje mata gida kai tsaye ba sanarwa? Zata gane, wata zuciyar tace mata. A haka ta karasa gidan cikin ruwa.

Cikin sa'a ta iske gidan a buɗe, kuma ta lura ba mota wata ƙila mijin ta ba ya nan. Da karfi ta buga kofan, sai da ta kusan minti daya a tsaye kafin aka zo aka bude. Da mamaki take kallon wacce ta bude mata kofa.

"Safara'u!"

"Maimu!"

Suka faɗa a lokaci ɗaya. Da sauri Safara'u ta buɗe kofa Maimoon ta shiga. Jikinta har ya fara rawa saboda sanyi. "Daga ina haka?" Safara'u ta tambaya.

Da ƙyar Maimoon ta iya magana saboda rawa da bakinta keyi. "Kitso naje rigachikun ruwa ya tare ni a hanya." Gidan duhu, an dauke wuta. Lantern Safara'u ta kunna.

"Toh shiga bayi ki watsa ruwan zafi, mai ya kaiki shiga ruwa, kin san baku shiri." Kai ta girgiza. "Ke haka ake yi, ina mai gidan? Daga zuwa sai in shigan mata bayi."

Ido Safara'u ta juya. "In zaki shiga ki shiga, Safiyya na waya, yanzu zata dawo."

Maimoon taƙi shiga saida Safiyya ta shigo ɗakin. Daga Safara'u sai ita, bara tayi aure. "Wai yau kice manyan baƙi gare mu, Adda Moon sannu da zuwa."

Murmushi tayi har haƙoranta na bayyana. "Yawwa Maman twins." Ta amsa cike da zolaya. Safiyya tayi nauyi, duka watan cikin hudu amma girman shi kaman na wata bakwai, shi yasa suke tsokanan ta da Maman twins.

"Adda Moon shiga ki watsa ruwa, kar mura ta kama ki." Tana rufe baki Maimoon tayi atishawa. "Kin gani ko." Safara'u tace. "Shiga ga ruwan zafi." Zani Safara'u ta mika mata kayan sa wa.

"Nazo taya ta kwana, mijin ta yayi tafiya." Safara'u ta ce da taga kallon da Maimoon ke mata. Da sauri Maimoon ta shiga bayi ta zare jiƙakƙun kayan jikanta. Sai da taji ta daina rawa sanna ta daina watsa ruwan zafi a jikinta. Ta fito ta samu Safara'u ta shirya mata abinci, Safiyya kuma bata dakin. "Sannu da ƙoƙari Safara'u."

"Yawwa, zauna ga abinci." Kan sofa dake ɗakin Maimoon ta zauna, har yanzu jikinta karkarwa yake yi, dama ita ba dama ruwa ya buge sai tayi zazzabi. Bayan hannun ta tasa ta taɓa kanta, yayi zafi, gashi ya fara ciwo.

"Ai da kinbar abincin kawai, amma in akwai ruwan zafi zan sha."

Baki Safara'u ta taɓe. "Ai dama na sani, sai da na cewa Safiyya ba ci zakiyi ba. Shi mutum ace bai son cin abinci, ina dalili." Nan Safara'u tayi ta mita, Maimoon dai gum tayi. In dai Safara'u ce ta saba, tun suna makaranta maganar ta kenan, Maimoon bata son abinci.

"Naga dai ba siririya bace ni kaman Habiba, duk da ban cin abinci ina da kuzari." Ta faɗa da taga mitar Safara'u taƙi ƙarewa.

Safara'u ta fashe da dariya tana girgiza kai. "Haka ne kuma, at least ana gani a jikinki in kinci."

"Ah toh."

Nan suka zauna su uku suna ta hira cikin nishaɗi. Maimoon tayi ta gwada numban ƴan gidansu amma duk basa shiga. Network, tace a zuciya tana tsaki.  A taƙaice dai sai bayan sallar Maghriba ruwan ya tsaya, tana yin sallah ta ce zata tafi. Duk yanda Safiyya tayi ta tsaya, taƙiya, hankalinta na gida.

"Yanzu dai baza ki jira kici abinci ba ko Adda Moon?"

"Kiyi hakuri Maman twins, in sha Allahu nan ba da daɗewa ba zaki sake gani na."

"Hmm," Safiyya ta ce. "Toh shikenan Adda Moon, muje mu miki rakiya."

"A'a," ta girgiza kai. "Yi zaman ki, kinga garin da sanyi, kar mura ta kama ƴan biyu." Murmushi Safiyya tayi, sannan ta mata saida safe. Safara'u ce ta raka har bakin titi, nan ta shiga keke napep.

"Toh saida safe Safara'u, nagode." Ta ce tana daga mata hannu.

"Sai da safe Maimu, sai munyi waya."

"Okay, toh shikenan." A hankali napep din yake tafiya saboda go slow da ya taru a hanya. Ajiyar zuciya Maimoon ta sauke, its da isa gida ba yanzu ba.

Ana kiran isha'i ta na shiga gida, ta tarar da ɗaya daga cikin ƴan matan gidan cikin mota tana taɗi, da farko tana sha Radiya ce, dan ita ce sarkin hira a kofar gida, amma sai taga ashe Fauziya ce.

Bata ƙara kallon wurin da suke ba, ta tura ƙofa ta shiga. Saurayin dake tare da Fauziya ya ga shigan Maimoon cikin gida. Shafa kan shi yayi, ya juya ya kalla Fauziya dake sanye da atampa rike da siket, sun kamata sosai kaman a jikinta aka ɗinka kayan. Babu komai a kanta sai dan ƙaramin gele da ta daura.

"Fauzee, wacece waccan mai niqabin da ta shiga gidanku? Ina yawan gannin ta, ƴar uwarki ce?

"Allah ya kiyaye baƙar chan ta zama ƴar uwata, kawai wasu mayunwata ne dake zama a gidan mu." Wani baƙin ciki Fauziya taji ya tsaya mata a zuciya. Ta tsani yaran wan mahaifinta, mussaman Maimoon. Bata son ganin ta ko kaɗan.

Saurayin ya jinjina kai. "Tana burge ni though, daga gani bata da hayaniya, she's always calm. I love girls like that."

Kambu! Lallai Fawaz ya raina mata wayo, a gaban ta zai dinga cewa wata na burge shi, watan ma mummunar chan, baƙa? Lallai ma!

Fawaz bai ankara ba kawai yaji ruwa a jikin shi, Fauziya ta watsa mai lemun dake hannunta. "Ni zaka ciwa mutunci, Fawaz."

Fawaz mutum ne mai saurin zuciya. "Keh! Who the hell do you think you are? Wacece ke, kin manta ko ni waye."

Harara ta banka mai mai cike da takaici. "Sai me? Kai waye? A gabana zaka dinga cewa wata na burge ka?"

"Ke ɗin banza! Kin san ƴan mata nawa ke bin Fawaz? Amma ya share su ya ce ke yake so. Me akayi aka yiki, nasan zan samu mata dubu da suka fiki komai! Nonsense! Get out of my car!"

Fauziya kaman ta kurma ihu. Tana son Fawaz, tana son shi sosai. Ya tara duk abunda take nema a namiji, kyau, ado, class, uwa uba dukiya. Tasan muddun tayi sakaci ita zata kwana ciki.

"Haba baby," Fauziya ta faɗa murya chan ƙasa. "Ba haka bane, you know I get jealous. Wallahi ban son abunda zai shiga tsakanin mu." Tana magana tana juya idanu, tana salon da tasan na tafiya da hankalin Fawaz.

Nan ta samu ta shawo kanshi. Sun dade sosai suna hira, sannan ta fito daga mota. Fawaz ma yafito ya mata rakiya har kofar gida. Hannu biyu yasa ya rungume Fauziya a jikinshi, itama ta sa hannun ta zagaye ƙugun shi. "Sai da safe." Ya raɗa mata a kunne.

A haka Hamma Ashmaan ya fito ya same su, suna jin motsin shi suka ja da baya. Fauziya ta tsaya tana kallon shi a tsorace, shikenan kashinta ya bushe yau.

Shi ko mutuwar tsaye yayi. Mai ze gani haka? Har tarbiyar gidansu ta lalace haka? Har Fauziya zata iya fitowa haka ba mayafi, kuma ta rungume wani namiji a ƙofar gida kanta tsaye. Ya salam!

Kallo ɗaya kawai ya mata ta sha jinin jikinta, da gudu ta ruga cikin gida. Ya maida idanun shi kan saurayin. "Idan ba kana so kayi kwanan cell ba kar in sake ganin ka tare da ƙanwata. Get lost!"

Bai jira yaga abunda Fawaz zaiyi ba ya juya ya shiga cikin gida. Yau zai koya mata hankali. A parlor ya samu Jasrah na kallo, Radiya kuma na kwance a two sitter tana waya, daga ita sai vest da gajeran wando.

Wayar ya fizge, yayi ending call ɗin. Da sauri Radiya ta mike zaune. Da ƙyar ta haɗiya yawu ganin kallon da Hamma Ashmaan ke mata. Duk gidan ba wanda take tsoro irin shi.

"Wuce kije kisa kayan arziki." Bai bata wayan ba ya haye sama, ɗakin Fauziya ya isa. A kan gado ya sameta, bai tsaya jin bayani ba kawai ya zaro belt din dake jikin shi.

Ido Fauziya ta waro, sannan ta kwala ihu. "Wayyo Mommy kizo ki taimake ni, zai kashe ni!" Da gudu tayi hanyar fita, amma ya tare ƙofar.

Ashmaan ran shi yayi matuƙar uaci, bai san sanda ya fara dukanta ta ko ina ba.

"Ke.har.kin.isa.ki.kawo.mana.namiji.gaban.gida.ki.rungume.shi." Ihu Fauziya takeyi kaman ranta zai fita, farar fatar ta har tayi ja jawur.

"ASHMAAN!" Mommy ta daka mai tsawa. "Baka da hankali?" Ta tambaya a tsawace tana janyo Fauziya jikinta. "Wani irin rashin imani ne zai sa ka kama mun yarinya kai ta duka kaman ka samu jaka."

Hannun shi ya dunƙule saboda bakin ciki da takaici. Ya rasa abunda zaice, ya san ko yayi magana ba abunda Mommy zata yi. Ƙaryata shi ma zatayi, duk laifin ta ne ai. Ta ɓata yaran nan gaba ɗaya, duk abunda ran su ke so shi suke yi. Basa ganin kan kowa da gashi. Wannan wani irin rayuwa ne?

"Nace mai ta maka kake dukan ta?" Muryar Mommy ta katse mai tunani. "Kai ko ta maka laifi, wani irin laifi ne da har zaka sa bulala ka dake ta. Ko ni uwarta da na tsugunna na haife ta ban mata wannnan dukan ba." Ran ta a bace take magana, ta rungume Fauziya dake kuka kaman ranta zai fita.

Ashmaan ji yake kaman ya kamota ya ƙara mata. Ba abunda yake tunawa sai inda yaganta rungume da namijin da ba muharramin ta ba.

"Mommy kar ki manta  arziƙin yara amana ne daga ubangiji, kuma ran gobe ƙiyama zai tamabaye ki akan irin tarbiyar da kika basu."

Baki Mommy ta bude tana kallon shi cike da mamaki. "Iyyeh! Eh lallai, sannu Ashmaan. Ni kake faɗawa haka? Ni kake cewa ban ba yara na tarbiya ba?"

"Mommy ni bance baki basu tarbiya ba, amma ya kamata ki duba, kuma ki san irin abubuwan da suke aikatawa. This stupid girl, har ta isa ta kawo saurayi gidan nan tana rungumar sa? Haba Mommy, da sake wallahi."

Yana gama magana ya juya ya fita, dan yasan tsayawan shi a wurin baya da amfani. Ba ƙaramin aikin Mommy bane ta rungumi bayan ƴarta ba, ba yau aka fara ba.

A pallon ƙasa ya samu Radiya, wacce yanzu take sanye da dogon hijab. Wayar ta ya jefa mata, da ƙyar da iya chapkewa. "Saura ke ma ki biye mata, sai kun raina kan ku a gidan nan." Yana gamawa ya fita daga gidan ya nufi sashen shi.

~~~

Bangaren Maimoon kuwa, ta isa gida daidai lokacin da Baffa ya dawo. Ledojin hannun shi ta amsa ta kai kitchen, sannan ta haɗo mai abinci. "Yawwa Maimu, sannu."

Murmushi ya bayyana a fuskar ta. "Sannu da zuwa Baffa, ya aiki?"

"Alhamdulillahi, me aka dafa mana yau?"

"Baffa ba ni nayi girkin ba yau, ban dade da dawowa ba." Ta bashi amsa tana murmusawa. "Bara in idasa ciki Baffa."

"Toh Maimu, Allah ya maki albarka."

A hankali ta lumshe idanun ta. "Ameen Baffa, Ameen."

A ɗaki ta samu Sadiya da Mimi kwance suna kallo. "Ku kuma ina kuka samo laptop."

Sai da tayi magana sannan suka san ta shigo ɗakin, hankalin su na kan movie ɗin da suke kallo. "Sannu da zuwa Adda." Suka faɗa a tare.

"Yawwa." Maimoon ta amsa tana zare niqabin daga fuskarta.

"Hamma Ashmaan ne ya ara mana laptop ɗin shi muyi kallo." Sadiya ta bada amsar tambayan da tayi da farko.

"Lallai," Ta jinjina kai. "ƴan gayu. Ina Ummi?"

"Ummin maman Nafisa ke naƙuda aka kirata." Mimi ta amsa, hankalin su ya koma kan kallon da suke yi.

Kai ta girgiza. Ta sha faɗama Ummi ta daina zuwa karbar haihuwa, taƙi taji. Akai yarinya asibiti ba za'a kai ba, sai wani abu ya faru a fara wayyo wayyo. Allah ya kyauta.

Ta na chanza kaya ta kwanta, kanta ciwo yakemata, dauriya kawai takeyi. Allah yaso tana da panadol cikin jaka, shi tasha kafin ta samu bacci ya dauke ta.

~~~

Kwanan ta uku tana jiyar zazzabi da mura saboda shiga ruwa da tayi. Tasha faɗa sosai wajan Ummi, Maimoon tasan tun tana ƙarama basa shiri da ruwan sama, akan wani dalili zata shiga har ta ɗaɗe haka.

Yau ta tashi jikin yayi sauki, kaman batayi rashin lafiya ba. Yau ya kasance lahadai, kowa na gida. Baffa bai cika fita ranan lahadi ba sai ya zama dole, yace shima ya zauna ya huta.

"Adda Moon, mai za'a dafa yau da rana?" Mimi ta tamabaya Maimoon dake zaune kan tabarma a tsakar gida.

Yatsine fuska tayi. "Ke baki san abinda ya dace ki dafa ba? Je ki duba mai ake dashi ki ɗaura girki."

"Kai Adda Moon!"

"Meye wani Adda Moon," ta ja ɗan ƙaramin tsaki. "Inda bana nan fa? Kije ki ɗaura abinda kika ga ya dace, kar ki dame ni."

Mimi ba haka taso ba, haka ta koma kitchen din tana kumbure kumbure. Baki Maimoon ta taɓe, kya yi kya gama. Ta gyara zama ta cigaba da tsefe kalabar dake kanta. Kitson ta baya wuce kalaba dama. Bayan ta gama kunce kan tsab, tasa comb ta taje. Amma a maimakon ta sa ribon sai ta raba gashin gida biyu ta kitsa shi. A ƙugunta jelar gashin ya tsaya.

Mimi daga karshe shinkafa da wake ta dafa, sai stew. Sadiya taje wurin Baffa amsa kudin kayan lambu. A hanyar dawowar ta gida taga ana sauke akwatina daga cikin mota ana shiga dasu cikin gida. Suwa suka zo kuma, Sadiya ta tambayi kanta.

Babu mai bata amsa dan haka ta cigaba da tafiyan ta. Ta wuce ta gefen motan taji an kira sunan ta. A hankali ta juya dan ganin wa ke kiranta. A take ranta ya baci, taji wani baƙin ciki ya rufe mata ido. Mai zai cemata yake kiranta?

"Ina wuni." Ta gaishe shi a daƙile, badan Ummi na yawan jaddada musu kan gaida mutane ba, da wucewar ta zatayi.

"Lafiya qlau Halimatou. Ya kike?" Mutumin ya amsa cike da fara'a. Shi kadai ke ce mun Halimatou, Sadiya ta yatsine fuska amma bata bari ya gani ba.

Matashi ne da bazai wuce shekara ashirin da tara ba. Bashi da tsawo sosai amma baza'a ce mai gajeraba, fuskar shi na dauke da dogon hanci da sajen da ya kwanta, farin fatarsa ba mai haske bane sosai.

"Alhamdulillah." Sadiya ta amsa tana murmushin yaƙe. Ita ya bar ta ta shiga ciki dan Allah. Da taga baya da niya sake cewa komai, ta juya. Har ta turo ƙofan ta ji yace. "Ina take?"

Da sauri ta waiga ta kalle shi dan jin yanda muryar shi ta chanza, ta raunana. "Halimatou ina take? Ina Maimoon ɗina ?"





~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro