Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ASHIRIN DA UKU





~~BABI NA ASHIRIN DA UKU~~





Bakin glass ne a fuskarshi saboda iska da akeyi. Tsaye ya ke ya na jiran a kawo mai mukullin motarshi. Agogon da ke daure a tsintsiyar hannunshi ya kalla, karfe hudu da rabi.

"Alhaji gashi," wani saurayi ya ce ya na mika mai mukulli.

"Yauwa Yunusa nagode. Komai ya gyaru ko?"

Da eh Yunusa ya amsa mai. Kudi ya ciro daga cikin aljihu ya mika mai, da sauri Yunusa ya girgiza. "A'a Alhaji da ka bar shi. Kudin da ka bada dazu ma basu kare ba."

Dan bata rai Sayf ya yi. "Amsa Yunusa. Wannan daban ne."

Karba Yunusa ya yi ya na ta godiya. "Nagode, nagode. Allah Ya saka alkhairi. Allah Ya sa ka gama da iyayenka lafiya." Ya bude ma Sayf murfin motan sannan ya rufe bayan ya shiga.

Hannu Sayf ya daga mai kafin ya tada motarshi ya bar wurin aikin. Har ya dauki hanyan gida ya tuna sun yi da Habib za su hadu yau.

Kiran shi ya yi a waya dan ya tabbatar ya na gida. Bayan minti ashirin ya kashe motar shi ya nufi daya daga cikin gidajen da ke jere a compound din. Ya na tura kofan yara biyu su ka yi tsalle su ka dane jikin shi. "Baba Sayf!"

Hannu ya sa ya ruƙo su sannan ya yi juyi dasu. Ihun su da dariya ya cika wurin. Ikram da Amira na hannun shi ya ƙarasa cikin gidan.

"Ina jin ihun su nasan ka iso," Habib ya ce ya na girgiza kai.

Gyara ruƙon da ya ma Amira ya yi dan ya gaisa da babanta ba tare da ya sauke ta ba.

"Baba Sayf mai ka kawo mana?" Ikram ta tambaya ta na kallon shi.

Mukullin motar shi ya basu ya ce su je su dauka ledar sweet. Da gudu su ka fita suna murna.

"In hakoran yarana ya rube kai zan kama."

Dariya Sayf ya yi sannan su ka sake gaisawa, aka dan yi hira kafin su fara tattauna abunda ya kawo shi.

"Na yi magana da Mr. Wei shekaran jiya. Machines din are ready zuwa next month za'a yi shipping din su. Transformer kuma sai nan da wata biyu." Habib ne da bayanin nan.

Sayf ya gyada kai alamar gamsuwa. Sun fara harkan noma tun suna samari yan secondary school. A hankali aka rika samun cigaba. Yanzu haka suna shirin bude mill ne inda zasu rika sarrafa shinkafan da suke nomawa da kuma masara. Gonar tasu na nan cikin wata karamar hukumar jihad Kaduna.

"Zuwa yaushe kake gani komai zai kammala?" Sayf ya tambaya.

"Eh toh. In sha Allahu ba zai wuce zuwa March na shekara mai zuwa ba. Amma Sayf baka gani Baba ba zai ji dadi ba?"

Kai ya dago ya kalli Habib. "Ba zai ji dadi ba akan me?"

"Akan order din machines din da mu ka yi mana."

"Habib ba fa mota mu ka siya ba. A.R.H motors ba su dealing da irin wannan. Kuma ai kasuwa ce, bai zama lallai sai mun bi ta hanyan shi ba. It's not a must."

Ganin ranshi zai baci ya sa Habib ya chanza maganar. Sun cigaba da tattaunawa har aka kira sallar magriba. Bayan sun dawo masallaci su ka samu an jera musu abinci a kan dining table. Tuwon shinkafa ne da miyar taushe. Sayf ya ci ya koshi ya yi hamdala.

Chan sai ga matar Habib ta fito sanye da doguwar hijab har kasa a hannunta kuma tray ne dauke da kayan shayi. Habiba ya tashi ya amsa tray din ita kuma ta zauna a kujerar da ke kusa da mijinta.

"Baba Sayf ina wuni." Ta gaishe shi da dan murmushi a fuskarta.

"Ina wuni Maman Ikram. Ya gida? Ya yara? Abinci ya yi dadi Masha Allah. Gaskiya a yi mun packaging sauran in tafi dashi."

"Ka ma isa," inji Habib ya na dariya. "Ai sauran dumame na ne na gobe in Allah Ya kaimu. In kaji haushi kuma kaima matar ka ta ma."

Dariya Salma ta yi. Sayf ya gyada kai. "Abun harda gori."

"Harda shi. Na ga alama Sayf so ka ke yi in hada ka da Ikram in aurar."

"Ka bar ganin ka riga ni aure Habib, na fa girme ka."

"Wani girma? Ai girma ya dawo wurina malam. Anya ma ka taba budurwa? Kin ganshi nan," Habib ya ce matar shi. "matan su da kansu ke bin shi amma ya ki maida hankali. Seriously Sayf, ya kamata a ce kaima ka yi settling down."

"In banda abunka Babe, ai aure lokaci ne." Inji Salma.

"Rabu da shi Maman Ikram."

"Na sani lokaci ne amma kwatakwata baya ma making effort. Na ce miki ko budurwa bai taba yi ba. Kinga kuwa baya da shirin yin auren."

Dariya Habib ya ba Sayf. Bai taba jin wata mace ta burgeshi ba ko ta ja hankalinshi. Sai mai kukan nan, zuciyar shi ta ce. Sayf bai san sanda murmushi ya subuce mai ba.

Murmushin nan kan idon Habib ya faru. "A'a dai abokina, ya da smiling? Ko dai wata ta yi nasara ne?"

Girgiza kan shi ya yi sannan ya mike. "Kaga tafiya ma zan yi. Yanzu dai Maman Ikram dagaske ba za ki bani sauran abincin ba?"

Dariya Salma ta yi ta ce mai ya yi hakuri.

"Babu zancen in yi hakuri. Ke da mijin ki kun shiga blacklist. Ranan da zan rama na nan zuwa."

Har mota Habib ya raka shi. Kafin ya tada motar sai ga Ikram dauke da leda mai takeaway.

"Baba Sayf gashi in ji Mamana."

"Ki ce mata nagode kuma ita kadai zan cire a cikin list din banda baban ki."

Saida safe su ka ma juna sannan ya tada motar shi ya tafi. Ko da ya isa gida ciki ya nufa dan ya sanar da Mami ya dawo. Ya samu har ta kwanta saboda kanta da ke ciwo.

Washegari ya tashi da sakon da ya tarwatsa mai duk wani shiri da ya yi na satin. A schedule din shi babu zuwa Kaduna, rabon shi da garin tun kiran da mahaifinshi ya mai. Gashi kiran Ammah ne bai isa ya tsallake ba.

Ammah na da muhimmanci kwarai a wurin shi, ta taka rawar gani babba dan inganta rayuwar shi. Bayan Mami da Baba Ahmad, Ammah ce kadai ta damu dashi, ta ke son ganin cigabanshi.

Kasancewar juma'a ce bai dade a office ba. Ya shirya akwati duk da baida niyan kwana amma ya san Ammah na iya hana shi tahowa yau.

"Da banda aiki da na bika." Hassan ya ce daga kan kujera inda ya ke zaune.

"Ka shirya mu tafi kawai."

"Dan kar ya yi tukin ya ke son ka je ba wani abu ba." Hussein ya ce ma dan uwanshi ya na dariya.

Cikin gida ya shiga ya wa Mami sallama. "Tafiya daga sama haka. Ammah bata fada ma dalilin kiran ba."

Kai ya girgiza. "Kawai ta ce tana son ganina."

"To ka bari sai gobe ka tafi da sassafe mana. Yanzu ai dare ya yi."

Duka karfe biyu yanzu amma Mami ke cewa dare ya yi. Ita duk inda sha biyu ta wuce bata son a tarki wani tafiya.

"Saura ka ce yau zaka dawo, na san halinka. In kaje garin kaman ana cizon ka. Allah Ya kiyaye, ka gaida su. And Sayf please bana so inji komai ya faru kaji."

"In sha Allah Mami."

Ya isa garin Kaduna ana kiran sallar la'asar. Zuciyarshi a cunkushe ta ke tunda ya karyo kwanan gidan da ya girma. Ganin gidan na tuna mai abubuwan da inda ya na da hali da ya goge su daga kwakwalwan shi gaba daya ya huta.

Bai san ko mai gidan ya san zai zo ba, bai san kuma yanda za'a tarbe shi ba. Ya na tunanin fara shiga wurin Ammah ya ji an yi kara an dane jikinshi.

"Yaya! Ba ka ce mun zaka zo ba. No wonder Ammah ta sa akayi ta girki ashe dan lelenta ne zai zo."

Dariya ya yi, ya dan tureta daga jikin shi cikin wasa. "Ahlaam yaushe zaki girma wai?"

Dariya ta yi itama. "Yaya Sayf ina wuni? Ya hanya?" Bude motar ta yi ta dauko mai jakar shi ta nufi cikin gida.

Kaman ya ce mata ba'a nan zai kwana ba sai ya fasa ya bita. Falon ya chanza, ba'a haka ya same shi wancan zuwan ba. Da alama matar gidan ta yi tafiya ta dawo.

Bai yi zaton mahaifinshi na gida ba dan bai lura da motocin da ke ajiye ba. Bai shirya haduwa da shi ba. Alhaji Abdur-Rahman Hambali na zaune a katafaren falon shi ya na kallo labarai.

Sayf babu inda ya bari a kammanin mahaifinshi. Duhun shi ne kawai bai dauko ba, ya dauko farar fatar mahaifiyarshi. In banda wannan kaman Abdur-Rahman ya yi kaki.

"Baba baka fada mun Yaya zai zo ba." Ahlaam ta ce.

Shiru bai bata amsa ba idonshi na kan Sayf. Wuri Sayf ya samu kan carpet ya zauna ya gaishe shi. Ya amsa babu yabo ba fallasa. Daga nan shiru ya ratsa wurin kowa da abunda ya ke sakawa a ranshi.

A wurin Sayf Allah Allah ya ke yi ya tashi ya bar wurin. Dukkan rayuwarshi ba ya jin ya taba awanni biyu cikakku tare da mahaifinshi, babu sabo da shakuwa tsakaninsu kwata-kwata.

Karan takalma su ka ji ana saukowa daga matakala. Mace ce sanye da dankareren leshi sai walkiya ya ke. Fuskarta cike da kwalliya kaman yarinya 'yar shekara sha takwas. Ta na ganin Sayf duk wata fara'a da ke fuskarta ta bace kaman an aiko mata da sakon mutuwa.

Da sauri ta saita kanta ta dauko murmushi ta yaɓa. "Wa nake gani kaman Sayfullah. Lale marhabun, sannu da zuwa. Ai ban san za ka zo ba da na sa anyi maka special tarba."

Murmushin yake Sayf ya yi. "Ina wuni Hajiya."

Ya na ganin yanda ranta ya baci jin abunda ya kirata amma babu mai ganewa. "Lafiya lau Sayf. Ya aiki? Ya ka baro su Fatima? Da fatan kowa na nan lafiya. Ban ji dadi da baka sanar dani ba zaka zo Sayf. Gashi yanzu zan fita. Ahlaam dan Allah ki tabbata an dafawa Yayanku abinci hadadde, kuma aje a share mai daki."

Hmm! Matan nan bata daina ba Sayf mamaki. Idan ka ganta a haka sai ka rantse ta damu dashi amma duk duniya babu wanda ta tsana irinshi. Ganinta zaune kusa da mahaifinshi kugu da kugu na sa ran shi radadi.

Duk wani abu da ya samu dan Adam mukaddari ne. Amma duk wani wahala da kalubale da Sayf ya fuskanta Hajiya Zuwaira ita ce sila.

Nan ta tashi ta fita tare da ce ma Ahlaam ta biyota.

"Har yanzu ba ka shirya fara aiki a A.R.H ba?" Sayf ya tsinci muryar mahaifinshi na tambaya.

A.R.H motors kamfanin ne da ke aiki akan sassan mota da na'urorin haɗi, tallan motoci, ayyukan kasuwancin motoci. Ya na daya daga cikin manya a jerin irin kamfanonin a Nigeria.

Shiru ya yi ya sadda kai. Shi mutum ne da baya son hayaniya ko tashin hankali. "Alhaji ka yi hakuri."

"Ba za dai ka daina kirana Alhaji ba ko Sayfullah? Mamanku ma ina ji ka ce mata Hajiya."

Ji ya yi kaman ya ce mai ba Maman shi ba ce. Saidai shi ba mara kunya ba ne.

"Ka yi hakuri."

"Kullum abunda ka ke cewa kenan amma har yau ban ga chanji ba. Kai ne babba amma kai kadai ke sa mun ciwon kai. Sam ba haka kannenka ke yi ba, su da suke mata ma. Ga Malika nan, ta gama master dinta. Next week zata fara aiki. Haba Sayf mai ka ke so ayi ma ne? Ka tattara ka koma Abuja, wato ubanka bashi da gida ko."

Kan shi na kasa har Alhaji ya gama fadan shi, wanda kullum abu daya ne. Ya tattara ya koma Abuja sai yanzu da ya ce bai shirya aiki da A.R.H motors ba. Alhaji ya manta sanda ya ce mai baida wuri a gidan shi, ya manta lokacin da matar shi ta sa aka fitar dashi daga gidan kaman barawo.

Mai aiki ce ta shigo da abinci ta jera a gaban shi. Wani irin murmushi ya yi. Wai yau shi a ke ba abinci a gidan nan, bayan an hanashi a lokacin da ya ke da bukata. Ruwa kawai ya sha ya ce ma Alhaji zai je wurin Ammah.

Ya na fita ya sauke ajiyar zuciya. Shiga bangaren Ammah ya goge duk wani bacin ran da ke tare da shi. Murmushin da ke fuskarta kadai ya ishe shi. Zama ya yi kusa da ita ya daura kan shi a kafadarta.

"Kai Saifullahi daga ni kar ka karya mun kafada."

"Haba Ammah ba haka ake taran mai gida ba fa."

"Wani mai gida? Mai gidan ba ya ke wata da watanni bai zo ba."

Murmushi ya yi dan ya san korafi ta ke mai. Janye jikin shi ya yi, sannan aka gaisa da kyau. Abinci aka kawo mai ya zauna ya ci sosai. Ya na ci ya na tuna sanda Ammah ke sa hannunta ta bashi abinci da kanta.

"Ammah kin tuna sanda kika dawo garin nan?"

Ya mutsa fuska Ammah ta yi. "Kai ni ban tuna ba. Na dawo saboda kai kuma ka gudu ka barni ba."

Dariya ya yi. "Na ce ki zo mu koma Abuja kin ki."

"Ni rabani da garin nan. Kullum mutane na kunshe cikin gida. Gwara nan ka na ganin giccin mutane amma chan kai kadai kaman maye. Sam garin nan na ku ba'a zumunci."

Babu yanda ba'ayi da Ammah ba lokacin ta baro Katsina ta dawo ta kiya. Wani zuwa da tayi ta ga halin da Sayf ke ciki a gidan ya sa ta tattaro kayanta ta dawo. Shine sanadin dawowarta Kaduna.

Da daddare Ammah ta kirawo Sayf da Alhaji falonta. Ta nemi karin bayani daga wurin su gaba daya. Wannan ya ba Sayf daman fadan dalilinshi na kin karbar aiki.

"Dole sai ya ajiye aikin da ya ke yi yanzu?" Ammah ta tambaya.

"Eh Ammah," Alhaji ya amsa.

Ammah ta gyara zama ta maida hankalinta kan Sayf. "Ka ji abunda Babanka ya ce. Ina so ka je ka kara tunani akai. Ka sani, kyan da ya gaji mahaifinshi. Ka dau iya lokacin da kake bukata dan yanke shawara. Amma kafin nan zaka rika zuwa karshen mako tunda naga Baban ku har lokacin ya na aiki, saboda haka zaku rika zuwa tare ka ga yanayin aikin da sauran su. Idan daga karshe shawarar ka bata chanza ba toh shikenan ba za'a sake dago maganar ba. Da fatan kowa ya fahimce ni."

Magana ta zauna babu wanda ke da abun cewa. Ammah ba ta fiye shiga cikin al'amarin su ba. Tunda ta yi magana sun san an kaita makura.

"Mamin ku ta fada ma su Aisha sun kusa dawowa?" Ammah ta tambaya Sayf bayan Alhaji ya fita.

"Wata Aisha?"

Dakuwa ta mai. "Ka ci gidanku. Aisha uwar ka mana."

Sosa kai ya yi. "Ohh! A'a, bata fada mun ba."

"Toh ni ai yanzu ina fada ma ko. Zasu baro chan Pakistan din gaba daya su dawo gida. Ita da yaran za su fara dawowa, kai zaka dauko su daga airport."

Sayf bai san sanda ya yi ihu ya ce. "Me?" Tun kafin tafiyan ta zo ma har an yanke shawarar wanda zai dauko su.

"Kwarai kuwa. Ka kirata ka tambayeta yaushe ne zasu iso dan ka sani."

"Amma Ammah..."

"Bana son jin komai Sayf. Ni na tafi in kwanta."

Ya na zaune ta tashi ta gama hidimanta sannan ta shiga ciki. Kan shi ya jingina jikin kujerar. Ammah ta kira shi ne kawai ta hukunta shi a wayance. Bayan sa shi aiki da Alhaji yanzu kuma shi zai dauko....

Iyayenshi sun rabu ya na da shekaru uku a duniya. Tun lokacin rayuwar Sayf ta lalace. Mahaifiyarshi ta tafi ta barshi, mahaifinshi kuma bai damu da shi ba harkar kasuwancin shi  kawai ya sa a gaba. Bayan rabuwar su Ammi ta yi aure ta bar kasar gaba daya. Tunda ta tafi bata sake waiwayan Sayf ba. Alhaji ma ya kara aure, ya auri Zuwaira wanda tun zuwanta ta takura ma Sayf. Ko nishi mai karfi bai isa ya yi ba.

Sam bata kula dashi, bata san cin shi ba bata san shan shi ba. Mami ta so daukan Sayf bayan rabuwan iyayenshi amma Alhaji ya hana. A lokacin kuma baya zama kullum ya na yawon kasashen duniya dan bunkasa kasuwancin shi.

Sayf baya ma son tuna irin rayuwar da ya yi da Hajiya Zuwaira. Rayuwa ce cike da keta, hantara da mugunta.

Hajiya Zuwaira ta so haihuwar 'ya'ya maza amma Allah bai bata ba. Ko ta haife su ba rai su ke zuwa, ko kuma su rasu bayan watanni. 'Ya'ya biyu Allah Ya bata. Malika mai shekaru ashirin da shida. Ita ake kira da 'yar mamanta dan babu inda ta baro Hajiya Zuwaira daga kamannin har halayen. Sai kuma Ahlaam mai shekaru ashirn.

Ko abinci Sayf baya samu a gidan da baida tamkar shi sai dai ya je gidan su Habib. Ko kuma in Mami ta zo yi musu hutu a bashi saboda ganin idonta. Duk da aurenta haka ta ke baro gidanta ta zo gidan yayanta da sunan hutu duk saboda ta kula da Sayf.

Sayf bai sake ganin mahaifiyar shi ba saida ya shekara goma. Shima Mami ce ta dauke shi ta kai shi Katsina jin Aisha ta zo hutu.

Haka ya taso cikin rashin kula da soyayyar iyayenshi. Mahaifiyar shi ta watsar da shi saboda fushin da ta ke yi da mahaifinshi, shi kuma Alhaji ya ture shi gefe gaba daya baya shiga lamarin shi.

Dawowar Ammah gidan ya sa Sayf ya samu chanji. Haka Sayf ya rayu har ya tafi aji daya a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya ke karantan International Relation. A wannan shekaran aka tura Baba Ahmad mijin Mami UK wani course.

Mami ta nemi da ta tafi da Sayf saboda a lokacin ya fara biyewa abokan banza. Saida Ammah ta yi da gaske kafin Alhaji ya yarda. Ya kammala degree din shi a chan sannan su ka dawo. Bayan ya yi NYSC shi da 'yan biyu suka koma UK dan karo karatu. Shekarar su biyar a chan su ka kammala Masters din su da PhD.

Dukiyar mahaifinshi bata taba tsokanewa Sayf ido ba. Ya dage dan ganin ya gina kan shi. Ya dade bai samu aiki ba saidai ya buga nan ya buga chan, da kuma harkan noma da su ke yi da Habib. Haka har Allah Ya sa ya da ce ya samu aiki da US Embassy. Yanzu shekarar shi shida ya na aiki a wurin.

Sai yanzu ne iyayenshi su ka tuna suna da da mai suna Sayfullah. Sai yanzu ne su ke nuna sun damu dashi bayan sun watsar da shi lokacin da ya ke da tsananin bukatar su. Alhaji na so ya dawo gida kuma ya yi aiki a kamfaninsa. Ita kuma Ammi ta na nuna ta na son shi kuma ta damu dashi wanda bata yi hakan ba a baya. Sun makara, dan bakin alkalima har ya bushe.



****



Bai san iya lokacin da ya dauka tsaye a wurin ya na jiran wucewarta ba.

Kaima in banda abunka ta ya zaka gane ta? Wata zuciyar ta tambaye shi.

Shima bai sani ba amma ya na da tabbacin ya na ganinta zai ganeta. Haka Sayf ya gama zaman jira amma yarinyar da ya ke nema ba ta wuce ba. Gashi gobe zai koma.

Dole ya hakura. Amma ya dauki alkawarin nemota tunda Ammah ta maida garin wurin zuwan shi.













Phew 😮‍💨 it's a long one! 

So, what do you think about Sayf and his life story?

Don't forget to
VOTE
COMMENT
SHARE

~Maymunatu Bukar 💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro