BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
Dazu ina cikin typing hannuna ya danna publish button din, ina lura na maza na cire sai dai har notification din ya tafi🙈😹 Na san na sa muku rai (inata ganin comment chapter 28 baya budewa🤣) shi yasa na dage na gama typing, ko editing banyi ba. So enjoy 🎉
~
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS
~
Zafi a ke yi na fitan hankali, gashi an tara su a cikin lab sun fi su dari.
"Wai su malaman nan in sun san baza su zo ba ai sai su fada tun wuri. Yanzu ba abun ka fita ba ya zo." Rukayya ta ce ta na tsaki.
Dariya Maimoon ta yi ta cigaba da danna waya. Kiran sunanta aka yi ta dago, wata abokiyar karatunta ce. "Akwai Khumra da Kajiji?"
Ciro su ta yi daga cikin jaka ta mika mata, a nan ta ke ta yi mata transfer. Godiya ta mata.
"Nima fa Khumra na ya kusan karewa." Inji Rukayya.
"Sai ki zo ki siya wani ai kafin su kare."
Lecturer dai bai zo ba sai ana saura minti talatin lokacin shi ya kare. Sai da ya yi awa biyu da ya kamata ya yi tun farko. Awannin su hudu kenan a zaune. Kafarta har zugi ta ke yi, ga bayanta da ya rike.
Da kyar ta isa daki, wata irin yunwa ta ke ji na fitan hankali. Ta yi rashin sa'a babu kowa a dakin kuma babu sauran abinci da ta bari da safe. Daya daga cikin su ta dawo dan ga plate nan. Indomie ta maza ta daura ko neman albasa da attarugu ba ta yi ba, haka ta dafata ita kadai.
Ta na gama ci ta hau gado, a nan barci ya dauketa. Cikin barci ta jiyo karan buga kofa. Tsaki ta yi ta tashi ta bude, bata ma ga waye ba ta juya.
"Sorry," Anwara ta ce. "Na manta key dina."
Duk yanda ta so komawa barci ya gagareta, ta dai yi kwance ta rumtsa ido. Ta na ji Anwara na hidimar daura tukunya, a gajiye ta ke da ta taya ta.
Adda Salma ta kirata, shi ya ida farkar da ita. Sun yi hira sosai. Hutun da taje ma ba su hadu ba saboda ta yi tafiya.
"Yauwa Maimoon muna da maganar da zamu yi ma."
"Magana akan me Adda?"
"Ba zata yiyu a waya ba, sai mun hadu."
"Toh shikenan, Allah Ya kaimu. A gaida su Ikram."
Ganin kwanciyar ba zai amfane ta ba, ta mike ta hau gyaran daki. Da yake yau kowa tun safe ya fita ko ina kacha kacha. Anwara ta tattara tarkacen da ke tsakiyar dakin, shara kawai ta yi ta goge dakin.
Dakin su na burgeta, su kadai babu wata kazamta. In ta je dakin su Rukayya har Allah Allah ta ke yi ta fito dan ita kam bata yi sa'a 'yan daki ba, gasu su takwas ne a dakin. Tulin kaya ba'a magana.
"Moon sauko mu ci abinci."
Tsam ta tsaya jin sunan da Anwara ta kirata da shi. Da sauri ta girgiza kai dan kar ta fada tunanin da baida amfani.
"Haka na ji Sadiya na ce miki, Adda Moon. Kin san kuwa idanunki na resembling moon din."
Dariya ta yi. Spoon ta dauko ta zauna su ka fara cin shinkafar da Anwara ta dafa.
"Waye wannan?" Anwara ta tambaya ta na nuna ma Maimoon hoton Hamma Ashmaan a wayarta da ta dauka.
A hoton sanye ya ke da jeans da t shirt, ya sa bakin glass. Ta goge duk hotunan shi da ke wayarta, wata kila bata lura da wannan ba.
"Ohh! He's handsome! Moon ko dai saurayin ki ne."
"Cousin dina ne."
"Kuma saurayin ki? Idan ba haka ba me kike yi da hotan shi. Anya bazan cewa Ahmad ya hakura ba. Kema auren gida za ki yi kaman ni kenan."
Yake kawai ta mata, ta cigaba da cin abinci. Hudubar da Safara'u ta yi mata ta fara yawo a kanta kaman an kunna rediyo.
Babu komai cikin zancen face gaskiya. Ita ta dade da hakura amma zuciya bata da kashi, akwai wani bangare chan kasa da ke fatan sauyi. Amma abunda ya faru da saukan Jasrah ya hure wannan (hope) din gaba daya.
Tun ta na karama su ka dauki karan tsana su ka daura mata. Har kazafi a ka yi ma mahaifiyarta akan ta je ta dauko 'yar wani ta kawowa Baffa. Dan ba'a shawara da zuciya da bata fara son Ashmaan ba.
"Iyayenshi ba su so."
"Ba cousin din ki bane. Duk gida ne ai."
"Ke kika san wannan."
"Amma me yasa?" Kafada kawai Maimoon ta daga. "That's sad. Allah zai kawo wanda ya fishi. Ni kam iyayenmu har murna su ke yi in muka daidaita kan mu. I can remember lokacin da muka fara relationship da Ahmad, maman shi was so happy."
Wata miyar sai a makwabta. Wa yaga Hajiya Suwaiba na murna Ashmaan da Maimoon sun daidaita kan su. Sai ranan da jaki ya yi kaho hakan zai faru.
"Zumuncin ku na da karfi."
"Ah sosai. Abu daya da iyaye da kakanni su ka dage a kai shi ne zumunci. Duk bayan wata biyu iyayen mu ke meeting dan jin matsololin juna. Kuma duk karshen shekara muna reunion saboda asan juna duk da muna da yawa gaskiya, ba lalle ka san kowa ba. Wasu dai za ki ga kamanni ki san you're related."
"Masha Allah. Allah Ya bar zumunci."
"Ameen."
"Mu kam opposite din ku ne. Bamu da yawa amma abun sai a hankali. Matsalolin yau daban, na gobe daban."
"Muma akwai problems fah. Babu dangin da babu wannan, amma zan iya cewa na mu bai yi tsanani ba. Ana haduwa dan gannin an magance matsololin duk da dai wasu mutanen ba'a iya musu."
"Baffa kadai ke kokarin ganin an gyra. Kin san abu kai kadai, gajiya za ka yi."
"Sosai. Babanki seems like a nice person." Anwara ta ce da murmushi a fuskarta.
Itama murmushin ta yi. "He is. In na zama half the person Baffa is, da na ji dadi."
Daga nan shiru ya ratsa su, amma irin shirun nan ne da ake kira (comfortable silence). Anwara ta cigaba da kallon hotuna a wayar Maimoon, harda tura wasu.
Ranan juma'a da yamma Maimoon ta samu sakon da ya tayar mata da hankali. Dawowarta daga aji kenan ita da Rukayya, kiran Mimi ya shigo wayarta.
Ta na amsawa ta ji Mimi na kuka ta san babu lafiya. "Me ya faru? Mimi, Baffa ne ko?"
Mimi ta kasa bata amsa sai kuka da ta ke yi. Daka mata tsawa ta yi. "Ki fada mun me ke faruwa mana!"
"Baffa ya fadi a wurin aiki, yana asibiti."
Kuka ta fashe da shi itama. Anwara da Rukayya su ka yi kanta suna tambayanta lafiya.
"Baffa...Baffa..." kawai ta ke maimaitawa ta na dauko jaka. Karkarwa hannuwanta ke yi sai Anwara ce ta amsa ta hada mata kayan.
"Dare ya yi Maimunatu. Ki bari sai gobe."
Maimoon da Anwara a tare suka watsa ma Rukayya harara. "Dan Allah matsa mana." Anwara ta ce ta na dauko takalmi.
Har yanzu Maimoon ba ta bar kuka ba. Oh Baffa! Abun ya mai yawa. Gashi dama zuciyar ta shi ba lafiya ne da ita ba. Addu'a kawai ta ke yi, wasu ma bata san abunda ta ke cewa ba.
Har tasha Anwara ta kai Maimoon. "Ina da test gobe, da tare zamu tafi. Amma in sha Allah, ina gamawa za mu taho."
Wata karamar purse ta mika ma Maimoon. Kudi ne a ciki. Sai lokacin ma Maimoon ta tuna bata da ko sisi a hannu. Niyarta da dare ta je ATM ta ciro kudi.
"Nagode Anwara."
"Ki bar kuka haka nan. In sha Allah babu abunda zai samu Baffa. Sai mun iso."
Anwara na komawa daki ta kira mahaifinta. Kira hudu ta mai bai dauka ba. Sai safa da marwa ta ke a cikin daki. Mamanta ta kira itama bata dauka ba kaman ta kurma ihu.
Wayarta ta yi kara, hannunta har rawa ta ke yi ta amsa. "Anwara?"
"Baba ina wuni," ta ce da fillanci. "Baba kana ina? Kai kadai ne?"
"Lafiya Anwara? Ina gida."
"Baba zan turo maka wasu hotuna dan Allah ka duba yanzu."
Zuciyarta duka ta ke yi da tsananin sauri. Da taga Baffa saida gabanta ya fadi, dan kaman an aje mahaifinta ne a wurin. Kamanninsu ya baci. A dangin su babu wanda bai san labarin dan Jaddati da ya bata ba tun yana karami. Kullum addu'ar Jaddati ta ga danta kafin ta koma ga Allah.
Ko ba'a fada ba ta san Baffa shi ne wanda iyayenta har yau ba su gaji da neman shi ba.
Ranan da Anwara ta fara ganin Maimoon ta ga ta yi mata kama da wani amma ta kasa cewa ga wanda ta ke kama dashi. Saida ta ga Baffa, ta sake kallo Maimoon din sosai ta ga ai da kakarsu ta ke yanayi. Har kalar fatarsu kuwa.
Akwai ranan da wata kawar Nanah ke cewa da ita ce da kalar fatar Maimoon da tuni ta yi bleaching. Ranan ran Anwara ya baci ba kadan ba. A nan ne ma ta ke fada ma Maimoon kalar fatar su daya da Jaddati. A lokacin ne ta sake ganin kamanni amma sai ba ta yi wani dogon tunani a kai ba.
Sake kiranta Baba ya yi. "Anwara! Ina kika samo hotunan nan? Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!"
"Shi ne Baba?"
"Muhammad ne Anwara. Shi ne. Wallahi shi ne. Ya Hayyu Ya Qayyum!"
Duk yanda aka yi Anwara ta kwashe ta fada ma Baba. Da niyarta sai ta tattaro bayani daga wurin Maimoon sai ta sanar da su. To amma Maimoon din bata cika magana akan danginta ba, ta na yawan maganan Baffanta da Umminta da kannenta amma sauran 'yan uwan sam bata dauko zancen su. Sai ranan ne ma da Anwara ta ke tambayanta akan hoton saurayin nan da ta gani.
"Gobe in sha Allahu za mu biyo jirgi. Ya Arhaman Rahimin."
"Saidai wani abu Baba. Dazu ya samu heart attack."
****
Maimoon ba ta san yanda aka yi ta isa asibitin ba. Tuni ta kira Mimi, ta na waje ta na jiranta. Mimi na ganin Addarta ta sake fashewa da wani kukan. Rungumeta Maimoon ta yi, ita idanuwanta sun bushe, hawayen sun daina zuba sai kukan zuci da ta ke yi.
Baffa na barci da karin ruwa a jikinshi. A watannin nan ya koma kaman ba shi ba. Duk ya rame, ya lalace.
"Ummi me likitan ya ce?"
"Ba su ce komai ba tukun. Tunda suka sa mai ruwa ba su dawo ba. Ya kusa karewa ma a na ta zuwa babu kowa wurin."
Itama Maimoon din saida ta je wurin nurses din sau uku kafin su ka zo su ka cire ruwan, har ya fara zugo jini.
Har dare babu likitan da ya zo ya duba Baffan. Ya farka amma bai ce komai ba, sai dai ya daga kai ko ya girgiza in an tambaye shi me ya ke so.
Ummi ta kirata waje ta mika mata katin ATM dinta. "Gashi ki je ki ciro duka kudin da ke ciki. Mun dai biya kudin yau. Amma ba mu san nawa za'a bukata ba."
POS ta je, itama ta ciro sauran 'yan chanjin da ke account dinta. Ta koma ta samu likita na duba sauran yan dakin bai iso kan Baffa ba tukun.
"Sannun ku, ya me jiki?" Likitan ya fada ya na gyara abun aikin shi da ke rataye a wuya.
"Da sauki Alhamdulillah." Ummi ta amsa.
"Allah Ya kara sauki." Ya duba abunda zai duba, ya wa Baffa wasu yan tambayoyi. Bayan ya gama ya ce daya a cikin su ya zo ya karba takardar maganin.
Mimi aka tura, Maimoon ta bata kudi ta siyo maganin a pharmacy. Mutum daya ake bari ya kwana, Ummi ta ce duka su tafi ita zata kwana dashi.
Daren ranan babu wanda ya iya barci a cikinsu. Washegari da sassafe su ka koma asibitin. A lokacin da suka isa lokacin likitan ke duba shi, likitan jiya ne. Da ya gama ya nemi Maimoon ta biyo shi office din shi.
"Damuwa ne ya ma mahaifin ki yawa." Likitan ya sanar da ita.
Dama ko bai fada ta san hakane, dan tun ranan da Hajiya Suwaiba ta fasa kwan kwanciyar hankali da natsuwa su ka yi ma Baffa sallama.
Likitan ya cigaba da cewa, "Yanzu dai an samu maganin ya daidaita zuciyar."
"Alhamdulillah," Maimoon ta furta.
Mikewa likitan ya yi, ya tsaya a bayan kujerar da ya ke zaune a ita da. "Baiwar Allah zan fada miki gaskiya. Idan da hali ku kai mahaifinki babban asibiti. Nan za su yi ta wahalar da ku ne amma basu da kayan aikin da lalurar shi ke bukata."
Gabanta ta ji ya fadi. "Ban fahimci me kake nufi ba."
"Kin ga nan karamin asibiti ne. Za su yi ta rubuta muku maganin da zai sa ya samu sauki ne na karamin lokaci. Amma abunda ya ke bukata shine a mai heart bypass surgery, saboda jijiyoyin da ke kai ma zuciyar shi jini a toshe su ke."
"Aikin ya na kai nawa? Kuma a ina ake yi?"
"Manyan asibitoci na kudi, sai kuma shika da Aminu Kano. Kudin ya danganta da asibitin da kika je amma na san ba zai yi kasa da dubu dari biyar ba."
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Ji ta yi lumfashinta ya tsaya cak! Hasbunallahu wa ni'imal wakeel.
"Baiwar Allah kar ki tada hankalin ki fa. Magungunan za su yi aiki, amma mudun ana son waraka mai daurewa aikin shi ne mafita. Ban fada maki dan in tayar miki da hankali ba. Sauran likitocin ba lallai ne su fada mu ku ba."
Gwiwa a sake ta bat ofishin likitan. Oh Allah! Allah Ka duba lamarin mu. Tsit ta yi bata fada ma kowa abunda likitan ya ce mata ba. In ma ta fada tayar musu da hankali kawai za ta yi.
Kiran Anwara ne ya dauke mata hankali. Yanzu ta sake tabbatar da kirki irin nata. Ta kirata ya kai sau goma tun dawowarta.
"Maimoon ya jikin Baffan?"
"Da sauki alhamdulillah. An rubuta mai magunguna. Sun ce zuwa gobe za su sallame mu."
"Masha Allah, alhamdulillah. Ki yi hakuri ba mu samu tahowa yau ba. Amma gobe in sha Allah za mu taho."
"Wallahi ba sai kin zo ba Anwara. Da kin barshi kawai, nagode, nagode."
"Ki bar mun haka Maimoon. An riga da an zama daya."
Nanah ma ta kirata, Rukayya ma haka. Da rana sai ga Safara'u da Habiba.
Likitan da ya karbi aiki da yamma ya sallame su bai bari sun wayi gari ba ma.
Har yanzu Baffa bai cewa komai, ko da yaushe ya na cikin tunani mai zurfi. Allah kadai Ya san mai ya ke tunani. Duk yanda su ka so dauke mai hankali abun ya ki.
Ko da su ka koma gida mutane na ta shigowa dubiya. A lokacin ne Adda Salma ta kirata. "Dazu Mimi ke fada mun. Yanzu ya jikin Baffan?"
"Da sauki," Maimoon ta ce. Kaman ta fada mata abunda likitan ya ce. Sai kuma wata zuciyar ta bata shawaran da ta yi shiru.
Maimoon ta kasa boye abunda likitan ya fada mata. Da dare ta ja Ummi gefe ta sanar da ita komai. Ummi fashewa ta yi da kuka Maimoon na bata hakuri.
"Ummi ba wai urgently ya ke bukatar aikin ba fa. In sha Allah za mu samu mafita kafin abun ya yi tsanani. Dan Allah ki daina kuka."
"Allah Ya sa Maimunatu, Allah Ya sa."
Washegari, ya kasance lahadi. Suna zaune a tsakar gida sai ga Baffa ya fito. Da sauri Maimoon ta mike ta riko mai hannu. Murmushi ya mata, ta maida mai martani bakinta na karkarwa.
"Baffa da ka kira mu baka fito ba." Sadiya ta fada ta na gyara mai wurin zama.
"Na gaji da zama ciki ni kadai." Ya ce murya a dashe.
Ciki ta shiga ta dauko tabarma. Sun zagaye Baffa Sadiya sai zuba ta ke yi, wannan karan Mimi na biye mata. Baffa na ta murmushi abun shi.
Da ana tsayar da lokaci da Maimoon ta tsayar da wannan.
Sallamar Anwara su ka ji daga sama. Maimoon ta mike ta isa wurinta. "Inata kira ba ki dauka ba."
"Sannu da zuwa. Wayar na daki. Nanah ya hanya? Sannun ku da zuwa mu shiga ciki."
Ta yi gaba Anwara ta riko hannunta. Nanah kuma har ta shige ciki.
"Maimoon...." Anwara ta kira sunan da wani irin murya. "Tare mu ke da baban mu."
Kallonta Maimoon ta yi. Da baban su kuma?
"Ban san ya zan fada miki ba. Mu je kawai." Anwara ba ta tsaya sauraron Maimoon ba ta damki hannunta su ka yi waje.
Dattawa biyu ne tsaye jikin wata dankareriyar mota. Maimoon na daga ido ta kalle su ta ji zuciyar ta ta yi wani irin tsalle.
Shin daidai ta ke gani ko idanuwanta sun samu matsala?
•
•
•
•
•
I deserve Votes and comments rututu😭😭
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro