BABI NA ASHIRIN DA SHIDA
~
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA
~
Kwanaki na ta gudu. Maimoon ba ta da lokacin kanta, jarabawa sai kawo kai ta ke yi. Yanzu ta saba da rayuwar makaranta, tasan yanda zata tsara lokacinta komai ta bashi hakkin shi.
Rabonta da gida tun hutun tsakiyar semester, sai dai kusan kullum sai sun yi waya da yan gidan. Mimi na chan itama karatunta ya dau zafi.
Ranan wata asabar ta yi wanki da sassafe ta na idar da sallar asuba. Fita ta yi ta tafi aji sai bayan la'asar ta dawo, ta je kwaso kayanta su ka ce daukan mu inda kika aje. Jilbabs dinta biyu da niqabi aka dauke mata, harda kwallarta saboda takaici. Gashi cikin sabbabin da ta dinka ne da zata taho makaranta.
Tun ranan aka mata hankali bata sake barin kaya ta tafi ba.
Harkar turare kuma sai abunda ya yi gaba. Dan har aiko mata kayan hadi akayi daga gida, wanda ta taho da su sun kare. Kitso ne dai ta daina yi. Anwara da Nanah kadai ta ke wa, su kuma bata karbar kudinsu. Ta na jin yin kitso kuma yazo karshe sai dai ta yi wa 'yan gida.
Yau saura wata daya a fara jarabawa. Ta na son zuwa kasuwan Samaru saboda kayan abincinta sun kare. Ba lallai ta samu lokacin zuwa ba nan gaba
"Maimoon in zo in raka ki?" Nanah ta tambaya. "Ban taba zuwa kasuwan ba."
Murmushi ta yi mata ta ce ta shirya su je. Rigar material ce a jikinta mara nauyi. (Sky blue) din jilbab ta saka, ta hadata da niqab din da ya fi kalar jilbab din cizawa.
"Kin yi kyau." Nanah ta ce mata. Ranan ta tambaye ta ko dan saboda sanyi ta ke shiga haka. Abun ya ba Maimoon dariya. Duk mun zafi shigarta ba ta chanzawa. Ita bata ma jin zafin da mutane ke cewa.
Kasuwar da su ka je siyan yan kaya kadan, Nanah tai ta jan su shago-shago ta na lodan kaya. Wanda wasu Maimoon ta tabbata bata bukatan su. Harda su kayan cake su ka bige da siyowa.
Sun dawo sun iske Anwara ta yi musu girki. Dama ko ita ko Maimoon ke yi, Nanah aikinta ci.
"Na gaji!" Maimoon ta ce ta na zama a kasan dakin da suka sawa leda.
"Allah Ya kara," Anwara ta yi dariya. "Wa ya fada miki ana jan Nanah kasuwa?"
"Ai ban sani ba! Kin ji bayana."
"Kai Maimoon banda sharri. Ba mu wani dade ba fa. Ya Wara, cake zan yi."
Ido Anwara ta zaro. "Da wani oven din?"
"Na gani a YouTube ba saida oven ba. Ana iya yi akan gas. Sai dai banda babban tukunya."
"Aiko naga Rukayya da katuwar tukunya." Maimoon ta ce. Ta cire kaya ta sa wata riga cotton, wanda su na zaman hostel ne.
"Ki aro mana dan Allah."
Tare da Nanah aka amso tukunya. Dukda ta gaji, sai taji tana son taga yanda Nanah zata hada cake din. Tare su ka yi kwabin, Maimoon na rike duk abunda aka yi, wanda ta ga zata manta kuma ta rubuta.
Nanah ta daura tukunyan a wuta ta dauki zafi, ta kuma sa gishiri da yawa a ciki. Harda (cake pan) su ka siya. Maimoon ta juye a ciki sannan aka sa cikin tukunyan da ta dau zafi.
"Minti nawa zai yi?" Maimoon ta tambaya.
"Forty minutes ko thirty haka." Nanah ta bata amsa.
A zaman jiran cake din ya yi barci ya yi gaba da ita. Allah Ya so ta gama lectures din ranan. Cikin barci ta ji wayarta na kara. Lallubota ta yi, ba tare da ta bude ido ba ta amsa ta kara a kunne.
Firgit ta mike jin muryan namiji har tana yarda wayar. Anwara ta kalleta irin 'lafiya kike kuwa?'
"Assalamu alaikum," ta ji an sake cewa da wani irin (deep voice). Haka kawai taji zuciyarta ta fara dukan uku-uku. "Salamu alaikum?"
Da kyar ta saita kanta sannan ta iya amsa sallamar.
"Dan Allah da Maimoon na ke magana?"
"Eh, ita ce."
"Uhm, Ammah ce ta bani sako in kawo miki. Gani nan na kusan shigowa makarantan, a ina zan same ki?"
Saida ta yi dan tunanin kafin ta gano mai yake nufi dan kwakwata ba tayi zaton hakan daga Ammah ba. Oh Allah! Ammah ba dai kirki ba. Bayan ta fada mai tana hostel ta ajiye wayar, har yanzu kirjinta bai daina duka ba.
"Bako za ki yi?" Anwara ta tambaye ta tana daga gira da wani shu'umin murmushi a fuskarta.
"Allah Ya shirye ki." Maimoon ta fada tana girgiza kai.
Bayan minti talatin wayarta ta sake kara, ya kira ya fada mata ta isa. Kayan da ta cire ta sake maidawa har ta yi nisa taji Anwara na kwala mata kira. Komawa ta yi dakin ta ganta tsaye da (takeaway pack) a hannu.
Mika mata ta yi, Maimoon ta tsaya tana kallonta. "Mai zan yi dashi?"
"Ba bako kika yi ba? Ki kai mai."
"Kawai sai in fara kai ma mutumin da ban sani ba cake. Kalau kike kuwa? Kuma fa sako aka bashi ya kawo mun."
"Ko ma meye. Ke baki san ana bada tukuici in kawo maka sako ba. Ke gaki da sunan tsohuwa amma baki san al'adarsu ba. Toh Jaddati ko goro aka kawo mata sai ta bada tukuici."
Gasake Maimoon ta yi tana sauraron Anwara. Daga karshe dai dole ta karbi cake dinnan saboda nacin Anwara ba nan ba. Yarinyar akwai kafiya da taurin kai.
A gaban hostel ta ciro waya ta kira lambar. "Salamu alaikum, na fito."
"Wa'alaikumus salam. Sorry ban karaso ba amma gani nan zuwa."
Juya idanu ta yi, wato dan kar ya jira ya sa ta fito tun kafin ya iso. Tana tsaye wata bakar mota kirar Mercedes Benz ta tsaya a gaban hostel din, windows din na da duhu ba'a ganin cikin motar.
Wani security a wurin ya nufi motar, ko mai ya fada mai, mai motar ya tada ita ya shiga wurin parking da ke gaban wurin buga basket ball.
Maimoon ta zuba ido tana jiran isowar mutumin. Kara wayarta ta yi. Shine ya ke tambayarta tana ina. "Ina gaban hostel."
Matashi ta gani yana tunkaro inda ta ke tsaye. Fari ne da gilashi a fuskar shi. "Assalamu alaikum," muryar shi ta daki kunnenta. Duk da tsawonta sai da ta daga kai ta iya kallon shi. Suna hada ido zuciyarta ta harba. Da sauri ta kauda kai. "Maimoon?" Ya ce kaman mai son tabbatar da wani abu.
Kai ta daga mai. "Wa'alaikumus salam. Ina wuni."
"Lafiya lau. Ya makaranta? Gashi wannan Ammah ta ce in kawo miki."
Hannu ta sa ra karba. "Nagode, Allah Ya saka da alkhairi."
"Ameen. Toh sai anjima."
Ya juya zai tafi ta dakatar dashi. Roban cake din kawai ta mika mai dan batasan abunda zata ce mai ba.
Karba ya yi. "Sako ne?"
Kai ta girgiza. "Uhm.....naka ne..."
"Nawa kuma?" Mamaki karara a muryanshi.
Kaman ta nitse dan kunya. Kar ya ce ta yi iyayi. Mai ya sa wai ta biyewa Anwara tun farko?
Sautin dariyan ta ji chan kasa-kasa. "Toh nagode. Jazakillahu khairan."
"Wa iyyaka. Nagode nima. Ka taya ni yi ma Ammah godiya."
Ta na tsaye har ya shiga motar shi. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke, harda dafa kirji saboda yanda ta ke bugawa. Kai ta girgiza sannan ta dauki kayan ta yi gaba.
Tana shiga daki ta kira Ammah. Maimoon ta yi ta godiya. Tabbas mutane irin Ammah kalilan ne a duniya.
"Babu komai Maimunatu. Allah Ya bada sa'a. Ki maida hankali wurin karatun ki kinji?"
"Toh Ammah. In sha Allah."
Har sun yi sallama, Ammah ta ce, "Allah Ya sa Saifullahi bai ya baki nono."
Saifullahi? Ba dai shine abokin Habib ba? Baba Sayf din su Ikram ba?
"Ya bada Ammah."
"To, to, madallah. Sai anjima."
Anwara da ke zaune kan gadonta a sama ta duro. Tare su ka shirya kayan cikin locker. A babban locker su ka saka, dayake yanzu kayan na su duk sun hade.
"Allah Ya yi wa Ammah albarka, kaman ta san ina marmarin dan wake. Maimoon ki yi mana yau dan Allah. Zanje kasuwa in siyo vegetables, akwai sauran kwai?"
"Da sauran Nanah ta yi cake."
Anwara ta zo ta tsaya kusa da ita kaman mai shirin yi mata rada a kunne. "Tunda sai na yi magana, fada mun ya yake."
"Anwara kina da matsala wallahi, ni matsa mun in cigaba da abunda na ke yi."
Wani irin ihu Anwara ta yi, ta tsaya gaban Maimoon ta kura mata ido. "You're blushing!"
Tureta ta yi, kumatunta sun yi dumi. Anwara ta tuntsire da dariya, harda rike ciki. "Is he handsome? Yana da kyau? Ya yake? Fari ne ko baki? Gajere ko dogo?"
Kamannin shi ne suka gitta a idanuwanta. Banza ta yi da Anwara. Nanah ta shigo dakin, ganin yayarta na dariya ya sa ta tambaye ta, "Dariyar muguntan na meye Ya Wara?"
"Kakarki ta yi saurayi."
Nanah ta zaro ido. "Dagaske?"
"Kar ki biyewa yayar ki Nanah. Bata san abunda ta ke cewa ba."
Anwara sai dariya ta ke yi. Nanah ta fada mata ta maidawa Rukayya tukunya kuma ta kai mata cake din.
Cake din ya gasu, ya yi laushi babu wanda zai ce a tukunya aka yi.
Da dare bata fita karatu ba. Tunda ta gwada karatu a daki so daya ta ji dadin shi, shikenan ta daina fita, dama ba wai tana son fitan ne ba. Kuma yawanci Nanah da Anwara ba su nan bare su dauke mata hankali. Yanzu haka sun fita, ita kadai ce a dakin.
Physics ta ke dubawa, dan shi ya fi bata wahala. Ta gani a group ma za'ayi tutorial, tana son taje dan ta kara ganewa. Lecturers dinne sun fi su dari ba komai kake ji ba, balle ka gane.
Tana cikin karatu wayarta ta yi kara, alamar shigowar sakon SMS.
Hi,
I want to properly thank you for the cake. Ya yi dadi sosai.
-Sayfullah Abdur-Rahman Hambali.
Daskarewa ta yi a wurin, idanuwanta na yawo akan sakon dake rubuce.
****
Maimoon.
Sunan ya dace da ita. Tabbas Allah na son shi. Bai taba zaton sake ganinta zai zo mai a saukake haka ba.
Jikinshi ya bashi ita ce ya dade ya na nema tun daga nesa. Da niyar shi ya mika sakon Ammah sai ya zo ya sameta. Ganin ta na ta kallon hanya ya sa ya gane ita ce ke jiran shi.
A take zuciyar shi ta yi harbawan da bata taba yi ba. Bai sake tabbatar wa ba saida ya matso kusa ya yi tozali da kyawawan idanuwanta.
Tabbas ba zai taba manta su ba.
Saida ya yi dagaske, ya tattaro dukan natsuwarshi dan kar ya je ya yi (embarrassing) kan shi a gabanta.
Har ya iso gida murmushin fuskar shi bai gushe ba. Har wata yar dariya yake yi kaman saban kamu. Ko dai akwai wani abu da ya same shi ne? Me yasa yake yin hakan? Ko dai ya haukace ne? Watakila amma ya tabbata bai taba jin haka akan ko wani dan Adam ba.
Cake din da ta bashi ya ci a matsayin abincin dare tare da shayi. Ba tare da tunani mai zurfi ba, ya dauki wayar shi ya tura mata text. Bayan nan ya tafi neman Ammah.
Ya sameta tana cin tuwo. Zama ya yi har ta gama, hankalin shi akan labarai da ke kunne.
"Duk wanda bai gane duniya ta kusan tashi ba yana da aiki ja a gaban shi," Ammah ta fada. "Tashin hankalin yau daban, na gobe daban. Allah Ya sa mu gama da duniya lafiya.
"Ameen Ameen," Sayf ya amsa. Bayan wasu mintuna ya ce, "Na kaiwa jikar ki sakonta. Ta ce in yi miki godiya."
"Allah sarki Maimuna. Ai tama kirani. Nagode, Allah Ya yi maka albarka."
Bayan ya amsa ya dan yi murmushi. "Ammah ba ki fada mun ina kika santa ba."
Salati ta yi tana rike haba. "Oh ni! Wai Saifullahi yaushe ka koyi gulma ne. Ina ruwanka da inda na santa."
Dariya ya yi ganin ganda ta yi kicin-kicin da fuska ta hada rai. Magiya ya rika mata kaman karamin yaro. A gaban Ammah da Mami kadai ya ke iya sakin jikinshi haka.
"Wannan yaro, wannan yaro. Kai da maye ne da an bani. Salma ce ta hada mu."
"Salma?" Ya ce da mamaki. "Salma matar Habib."
"Kasan wata Salman ne bayan ita?" Nan Ammah ta kwashe komai ta fada mai, tun daga haduwar su har zuwa yanzu. "....tunda naga yarinyar na ji ta kwanta mun a rai. Akwai hankali da natsuwa. Iyayenta sun bata tarbiya mai kyau. Kullum cikin shigarta ta mutunci ce, ni shi ya fi burge ni ma."
Tunda Ammah ta fara bayani bakin Sayf ya kasa rufuwa. Abinda Ammah ta ce ya kara bashi karfin gwiwa akan niyar da ya yi.
"Masha Allah," kawai ya ke maimaitawa.
Wani kallo Ammah ta mai, Sayf ya ji kunya ta kama shi. Da sauri ya bar falon Ammah na mai dariya. Ya na ji tana cewa, "In tayi tsami zamu ji."
Sayfullah bai kwanta ba saida ya yi sallar Isthikara, ya nemi taimakon Allah akan shawarar da ya yanke.
•
•
•
•
•
•
•
VOTE
COMMENT
FOLLOW
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro