BABI NA ASHIRIN DA HUDU
~
BABI NA ASHIRIN DA HUDU
~
Allah Mai Yanda Ya so. Yau ita ce zata tafi jami'a, wanda a baya ta cire rai gaba daya. An sa komai a mota sai tafiya. Ummi ta riketa ta ki saki kaman an ce mata in Maimoon ta tafi bazata dawo ba.
"Oh Allah. Ummi ki sake ta mana." Baffa ya ce ya na kallon ikon Allah. "Wannan in akace aure aka yi mata ban san ya za ki yi ba."
Kowa a wurin ya yi dariya. Maimoon duk yanda ta so daurewa saida Ummi ta sata kuka. Adda Salma ce ta bada motan da za'a kaita, tare za su tafi da ita da su Mimi.
Da kyar Baffa ya lallaba Ummi ta saketa sannan su ka hau hanya. A cikin motar suna ta wa Ummi dariya.
"Zanga yanda za ta yi in Maimoon ta yi aure," Adda Salma ta ce.
Mimi da ke gidan gaba ta karkato ta na fuskantansu. "Ai Adda mun dade da sanin Ummi ta fi son Adda Moon, mu 'yan kallo ne."
Maimoon na jin su bata ce komai ba. Itama wani iri ta ke ji, yau ta bar gida zata tafi wani gari. Wanda bata taba sati daya bata ga iyayenta da 'yan uwanta ba. Amma duk da haka murnar da ta ke yi bai gushe ba.
Rayuwa na tafiya mata daidai babu laifi. Sana'ar turarenta sai kara gaba ya ke yi, duk da an 'yan watannin nan an samu gargada wanda ba komai bane saboda sana'a—da rayuwa ma gaba daya—ya gaji haka.
Binciken Baffa da ke yi na 'yan uwanshi har yanzu ba'a samu wani cigaba ba. A wurin aiki kuma an bashi gurbin aiki na dindindin (permanent job). Kuma ya yi kokari an saka ceiling a dakunan kuma an janyo wutar lantarki. Sauran ginin kuma a hankali za'a cigaba da yardar Allah.
Da riban da ta samu ta yi wa kanta siyayyan makaranta. Bata bari Baffa ya kashe ko kwandala ba sai dai katifa da risho da ya sammace ta ya siyo. Amma komai ita ta yi wa kanta tunda su biyu ne kada nauyin ya mai yawa.
Kafin su taho Baffa da Ummi su ka kirata daki. Sun yi mata nasiha da iyaye ke ma yaran su in zasu tafi makaranta. Sun gargadeta da ta ji tsoron Allah a duk inda ta ke. Yanzu za ta yi nesa dasu ba za su san abunda ta ke yi ba amma Allah na kallonta. Sun kuma ja kunneta akan biyewa abokan banza, karatu ta je yi saboda haka ta maida hankali ta kuma dage da addu'a.
Sun ciro kudi 'yan daidai sun bata duk da ta so su barshi. Sai da Baffa ya mata jan ido. "Hakkin ki a wuyana ya rataya har sai ranan da ki bar karkashin ikona."
Sun isa Zaria karfe sha daya na safe. Sanyin farkon shekara sai kadawa ya ke yi. Mutane sai hidimarsu su ke yi cikin makaranta. Wasu jambitos ne kaman ita gasu nan da lodin kaya.
Sati biyu da suka wuce tazo ta yi clearance din daki, ta samu bedspace a Amina Hall. Tare da taimakon wasu mata ma'aikatan hostel din su ka shiga da kayanta. Dakinta a kasa ya ke basu sha wahalan hawa sama ba.
Dakin mutane hudu ne da alama kuma ita ta fara zuwa saboda dakin duk kura. Daya daga cikin matan ta ce zata share musu sai su biyata.
Bayan ta share ta goge su kuma suka shirya kayan. Tun zuwanta clearance ta zabi gadon kasa da wardrobe karama da ke kusa da gadon.
"Adda me yasa baki dauki babban nan mai murfi biyu ba?" Sadiya ta tambayeta suna cikin shirya mata kayan sawanta.
"Wata ta riga ni."
"Yanzu haka za ki zauna da mutanen da baki sani ba har na tsawon shekara daya, hmm mm. Nima gaskiya KASU zan yi kaman Adda Mimi, ina gida ba inda zani."
Adda Salma ta yi dariya jin abunda Sadiya ke cewa. "Zaman hostel wani karatu ne daban mai zaman kanshi. Akwai dadi, akwai wahala. Saboda mutane ne zaki hadu dasu daban daban, wasu al'adarsu ma baki taba ganinta ko jinta ba. Kuma sai kin kai zuciya nesa, dan rabin shi zaman hakuri ne."
Mimi ta tuntsire da dariya. "Adda yau dai sai kace ana miki nasihan gidan miji. Harda su zaman hakuri."
Dariya duka su ka yi, Adda Salma ta cigaba da cewa. "I'm serious. Wata in ta miki wani abun kaman ki daura hannu a ka ki yi ta ihu. Amma in kika hadu da nagari za ku yi forming dangantaka mai karfi har karshen rayuwanku. Kinga kaman Laila, a aji daya muka hadu a BUK kuma har yanzu ana tare."
"Toh Allah Ya sa yan dakin namu su zama mutanen kirki." Maimoon ta ce suka amsa da 'ameen'.
Wurin karfe biyu su Adda Salma su ka shirya komawa Kaduna. Kaman ta bi su haka ta ke ji. Sadiya harda kwalla zata yi kewar Addarta. Adda Salma ta kara mata pocket money, da Maimoon ta ki karba ta ce mata ai Habib ya bada in kuma so ta ke yi ta maida mai shikenan.
Maimoon ba ta yi mamaki da ta hadu da mijin Addar ba, shima haka ya ke faram-faram kaman matarshi. Kirki irin na Adda har gida ta kawoshi ya gaida su Ummi.
Ita kadai tsuru cikin daki, gashi bata san kowa ba. Dan ma da waya, its ta debe mata kewa. Daren ranan bata iya barci ba. Washegari ta tashi da wuri dan a group an turo suna da lecture karfe takwas. Tun jiya matar da ta share dakin ta cika mata drum da ruwa. A risho ta daura ruwan, sanyin garin ya wuce yanda ta ke zato.
Yau ake yinta dan Maimoon ba ta san ko ina cikin makarantar ba. Kara duba wayan ta yi, a yanda aka turo FSLT ne sunan wurin. Cire kunya ta yi ta tambayi wasu mata biyu da ta gani nan tsaye.
Sun mata kwatance ta yi musu godiya ta cigaba da tafiya. Ta na ta tafiya kawai ta ganta wani wuri daban, wurin bai yi kama da akwai azuzuwa ba ma. Kam bala'i! Ba dai da gangan wa'incan matan su ka batar da ita ba?
Da kyar ta samu ta maida kanta daki, zuwa ajin da bata yi ba kenan. A rana na uku ne Allah Ya hadata da wata 'yar albarka ta kaita har wurin. Ta yi mata godiya sosai. Ashe wurin da ta ke nema a nan ta tambaya matan nan amma su ka ce ta kara gaba. Kai amma wasu dai babu Allah a ran su.
Maimoon ta yi kawa a aji mai suna Rukayya. Sai abun ya zo mata da sauki tunda hostel da ya su ke, in akwai lectures Rukayya zata biyo mata su tafi tunda ita ta san gari.
Satin ta daya a dakin sauran basu zo ba, tun bata iya barci har makaranta ta fara wahalar da ita. Da dare ya yi barci ke dauketa. Har ta fara sabawa da makarantar, abu daya ne dai kawai bata saba dashi ba, bayi. Kazanta ake yi wurin nan kaman babu gobe.
Ranan Alhamis ta dawo daga aji wurin karfe sha biyu ta samu daki a bude. Su biyu ta samu zaune kasa sun shimfida abun sallah. Farare ne dukkan su marasa jiki, kammanin su ya nuna fulani ne.
Sallama ta yi ta shiga ciki ta zauna kan gadonta. Saida ta cire niqab din fuskarta sannan ta yi musu sannu.
"Sannu, ke ce mai gadon?" Daya daga cikin su ta tambaya. Da eh ta amsa mata. "Sannun ki, sunana Nanah Fatima, wannan kuma yaya ta ce sunanta Anwara."
Murmushi Maimoon ta yi, daga gani tanada surutu. Sai ta tuna mata da Sadiya. "Ni sunana Maimunatu."
"Ashe sunan tsofi gare ki," Fatima ta yi dariya. "Sunan grandma dina kenan."
Dariya Maimoon ta yi. Daga nan shiru ya ratsa. Kaya ta chanza ta saka marasa nauyi. Taliya ta dafa saboda tafi sauki dan yunwa ta ke ji bata samu ta ci abinci da safe ba kafin ta fita. Dama Ummi ta yi mata miya hadardiya saboda haka fara ta dafa taliyar.
Ta yi ma su Fatima bismillah amma su ka ce sun koshi.
Maimoon ba tada saurin sabo saboda haka tsakaninta da su Fatima gaisuwa ce. Fatima ce karama wannan ce shekarar ta farko a makarantan kaman Maimoon, ta na karanta Medical Laboratory Science (MLS), course din da Maimoon ta so a bata. Anwara kuma tana aji uku a department din pharmacy.
Ranan ta na jin Fatima na fada ma kawarta da su kadai za su kasance a dakin dan dai ita Maimoon ta yi clicking da wuri, da za'a chanza musu Babansu ya ce a barshi kawai.
Tsakaninta da Rukayya kuma karatu ne, da sun dawo daga aji ta ke komawa daki babu inda ta ke zuwa. Ba yanda Rukayya bata yi da ita ba akan su zagaya cikin makaranta amma ta ki. Saida ga baya kuma ta ga ya kamata ace ta san wurare kar a je a kara batar da ita.
Rukayya ta ja ta wurare da yawa, harda wanda ta tabbata har ta gama makarantan babu abunda zai kaita wurin. Ta nuna mata kasuwa, library da ake kira KIL, da sauran su.
Maimoon ta dage da karatunta dan ita kadai tasan irin gwagwarmayan da tasha kafin ta ganta a nan. Kullum da dare ta ke zuwa library bayan sallan isha'i sai goma ta ke dawo lokacin da ake rufe library kenan. Wata rana su je tare da Rukayya, wata rana kuma ita kadai.
Yau bata da lecture sai karfe biyu, ta na zaune kan gado wayarta ta yi kara. Habiba ce ke kiranta video call.
"Ahh ahh! Jamabites!" Habiba ta ce cike da tsokana. "Kaga su Moon a bunk bed. Ya baki dauki gadon sama ba?"
"Mara mutunci, hakan in je in fado."
Dariya Habiba ta tuntsire da shi. Sun sha hira sosai. Ita ta gama result su ke jira sai bautan kasa.
"Toh Mango Pak an gama boko yanzu ai sai maganar aure."
"Maimoon ki kiyaye ni wallahi. Wai ni ya maganan turare, dozen nawa kika saida?"
"Ko daya," ta bata amsa tana dage kafada. "Kin gansu chan cikin locker ko ciro su banyi ba tunda na zo."
"Ke haka ake yi?" Habiba ta yi tsaki. "Idan ba ki yi talla ba ta ya za'a san kina saidawa. Ke sana'a ba'a mata haka, fita da su zaki rika yi duk inda kika ga taron mata ki tallata musu."
"Ai har a rika nuna ni."
"Sai me to? Ke dai ba kudi ki ke so ki cika jaka dashi ba. Bango-bango ma ya kamata ki bi hostel din na ku ki lika, haka ake yi."
Ta gani kuwa dan har a bayi. Sun yi sallama Habiba ta sa ta yi mata alkawarin aiki da abunda ta ce. 'Yan dakin ta fara nunawa aiko Anwara ta siya na jiki gudu hudu manya kwalba. Abun ya yi ma Maimoon dadi.
"Ki ce shiyasa dakin ke wani irin cool kamshi," inji Anwara. "Scent din is nice sosai."
Tun ranan ta ke sa gudu uku zuwa biyar cikin jaka in zata fita. Ba laifi an dan samu ciniki.
Ranan assabar weekend bata tashi da wuri ba sai wurin karfe goma, abunda bata saba yi. Hayaniyar su Anwara ce ma ta tada ta. Fulanci su ke yi sai war-war ke tashi. Ta na ji Anwara ta ce ma Fatima ta yi a hankali kar ta tada ta.
"Ni dai Yaya ki yi mun kitso dan Allah," Fatima ta cigaba da damun yayarta da yaren su.
"Ke ni ki kyale ni. Ba abun in yi miki ba ni kuma in rasa mai mun. Dan asara ko tsaga ba ki iya ba Nanah."
Haka su ka cigaba har Anwara ta yarda ta yi mata kitso.
Da rana Anwara ta dawo salon da ta je kitson su bai mata, sai mita ta ke yi ta rasa mai kitso. Kaman Maimoon ta ce ta zo ta yi mata sai kuma ta yi shiru dan kar taga kaman ta yi mata shishigi.
Har rana Anwara bata daina mita ba. Abun har ya ishi Maimoon bata san lokacin da ta ce mata ta zauna ta yi mata ba.
"Kin iya kitso ne?" Anwara ta tambaya ta dan kallon Maimoon.
"In baki so shikenan."
Mai ta ji mai ta gani, ta dauko kayan kitson ta zauna. Kanta ba ya da cika kuma tsawon dan daidai a cikin minti talatin Maimoon ta gama mata shuku yan matsakaita.
"Amma Maimunatu kin iya kitso haka shine kina ji ina magana ki ka yi shiru."
Dariya Maimoon ta yi. "Toh ba gashi na miki ba."
Wannan kitso shine sanadin sabawarta da 'yan uwan. Ranan da su ka san itama bafullatana ce sun yi mamaki sosai. Daga lokacin shakuwa ya shiga tsakaninsu.
Ranaku nata ja har lokacin hutun tsakiyar semester ya zo. Su Nanah su ka fara tafiya an aiko mota daga Abuja ta zo daukan su. Yaran daga gani daga babban gida su ka fito.
Satin Maimoon daya a gida. Ta je gidan Ammah ta gaisheta. Kamar ko yaushe saida cikinta ya kulle dan dariya. Ta yi ma Ammah kitso inda ta yi ta jaje wai tunda Maimoon ta tafi kanta duk ya lalace.
Hutunta na karewa ta koma makaranta aka cigaba da gashi. Karatu ya yi zafi Maimoon ba'a jin kanta, sunyi test kuma ta ji dadin sakamakonta duk da akwai wasu courses din da saita dage.
Maimoon na cikin karatu Nanah ta dawo wujiga-wujiga daga gani ta wahala yau.
"Ina dalilin wannan makarantan! Wallahi na gaji," wurgi ta yi da jakarta ta fada kan gado. "Maimunatu dan Allah kina da abinci?" Ta tambaye ta kaman zata yi kuka. "I am so hungry, banda karfin zuwa cafeteria."
"Duba tukunya na akwai macaroni, ban san ko kina ci ba."
Da sauri Nanah ta mike. "Mai zai hana." Plate ta dauko a locker din su ta zuba.
Maimoon bata taba gani sun yi girki ba. Sai dai su siyo ko su sha kayan madara irin su cornflakes. In sun daura tukunya toh indomie zasu dafa dukda kuwa locker din su cike da kayan abincin da ya isa cika karamin shago.
Ita kuwa bata taba rasa abinci, in babu to akwai miya. Dan tana karewa ta ke zuwa comm market ta yo chefane.
Tun ranan Maimoon ta kara yawan abincin da ta ke dafawa, duk wanda ke jin yunwa ya dauka ya ci. Sai abincin su ya zamana ma tare su ke ci a plate daya in kowa na daki. In suna cin abincin sai ta ji ta kaman ta na gida tare da Mimi da Sadiya.
Da dare bayan ta dawo karatu ta same su suna cin Mac-D. Bredi ne da ake samai tsire, kabeji da mayonnaise a tsakiya sai a gasa.
"Sannu da zuwa Maimoon," Anwara ta ce mata. Miko mata wata bakar leda ta yi. "Ga naki, sai dai ya huce."
"A'a, ki barshi nagode," ta ce ta na girgiza kai.
"Ba na fada maki ba Yaya," Nanah ta zumburo baki gaba. "Maimoon ko dai baki yarda da mu ba?"
"Ba haka bane ba Nanah."
"Hakane mana. Mu mun iya cin naki amma ke baki taba karban abun hannun mu ba. Shikenan muma zamu daina cin abinci ki."
Hakuri ta basu. Sau da yawa haka za su siyo fruits ko kaza su deba su bata amma bata taba karba ba. Ganin fuskokinsu sun chanza ya sa ta karba.
Suna cikin ci wayar Nanah ta yi kara. Wani irin murmushi ta yi sannan ta dauka. Nanah mai yawan kwaratsi ta bace bat! Murya ta koma chan kasa-kasa.
Anwara da Maimoon na hada ido suka fashe da dariya. Da gudu Nanah ta bar musu dakin.
"Kin gani har Nanah na da saurayi banda ke Maimoon."
"Wannan ai sai ku manya."
"Ni miji gareni ba saurayi ba."
Dariya Maimoon ta yi. Da ya ke Anwara an sa ranan bikinta shi yasa ta ke cewa haka.
"Ko in nemo miki? Ina da yayye da yawa fa."
Girgiza kai Maimoon ta yi. "Rike kayan ki bana so." Dan ita yanzu sam! Bata da lokacin namiji, karatu ne a gabanta.
•
•
•
•
•
•
VOTE
COMMENT
SHARE
Inda na dage da update kuma dan Allah ku dage da votes da comments
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro