Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ASHIRIN DA DAYA






~~BABI NA ASHIRIN DA DAYA~~








Da ana maida hannun agogo baya da Ashmaan ya yi. Saidai bakin alkalami ya bushe, duk abunda ya faru babu mai iya chanza shi duk yanda ya so kuwa. Bai taba tunanin al'amarin zai kai haka ba. Ya san iyayenshi ba za su amince cikin sauki ba amma ya za ta da sannu zai shawo kan su.

Yanzu kam ya san dalilin kiyayyar da su iyayenshi ke ma iyalin Baffa, musamman ma Mummy. Ganin yanda ta fusata ta na ikirarin tsine mai ya san dole ya hakura. Amma bai san ta ya zai lallabi zuciyar shi ta daina son Maimoon ba.

A sati biyu ya yi duk abunda zai iya dan ganin ya cire ta a ran shi sai dai kaman ana kara rura wutar soyayyarta ne. Ta ya za'ayi ya daina son Moon din sa? Son ta ya dade ya na dakon shi sai yanzu Allah Ya bashi ikon saukewa.

Satin shi biyu cikin daki bai fita ko da tsakar gida ba. Aiki ma Daddy ce mai ya yi ya samon mai leave duk dan kar ya fita ya bi bayan su Moon. Ya zama kaman wani prisoner a cikin gidan. Ko masallaci ya je ya dade Mommy ta dinga kiran shi kenan, duk da tasan ba ya zuwa da waya masallaci.

Washegarin ranan da duniyar shi ta juya Mommy ta kira shi daki ta mai tas! Ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba. Bai san wani irin tsana tai musu ba, tsanar da babu gaira babu dalili.

Yana zaune a kasa ya ji an turo kofa. Ganin Jasrah ce ya sa ya saki fuska, saidai murmushin ma da kyar ya ke yi. Duk ya yi baki, ya lalace.

"Hamma ga abinci," ta ce sannan ta samu wuri ta zauna kusa da shi.

"Ki maida kawai, na koshi."

"Ko romo ne kasha please Hamma. Ba ka ga yanda ka yi ba, zama da yunwa ba shi zai kawo maka sauki ba. Dan Allah ka ci abinci."

Cewa ya yi ta zuba mai. Turawa ya dinga yi ba dan ya na jin dadin shi ba. Kadan ya sha ya ajiye sauran.

Wata brown envelope Jasrah ta zaro daga cikin hijabinta ta mika mai. Ya na gani ya ji kanshi ya fara sarawa. "Bata amsa ba?"

Kai Jasrah ta girgiza. "Ba ka ga yanda ta ji haushi ba Hamma. Ban taba ganin ran Adda Moon ya baci haka ba."

"Mai ya sa ba ki ba Mimi ko Sadiya ba?"

"Su ma sun ki karba. Na rasa yanda zan yi."

Kai ya dafe ya na tunanin me ye mafita. Suraj ya fada mai halin da su Baffa su ke ciki, duk ta inda ya bullowa abun sai ya gagara. Da farko ya so ya kama musu haya amma Baffa ya ki. Yanzu ya bada kudi a ba Maimoon shima ta ki karba.

"Why not ka yi mata transfer? Wurin is awful Hamma, ko wutan NEPA babu." Jasrah ta ce zuciyarta a cunkushe. Da karya ta samu ta fita, Suraj ya kaita gidan dazu. Sam ba ta ji dadin ganin su a wannan yanayin ba.

"Idan na yi transfer zai zama matsala. Nasan yanzu haka Daddy na tracking duk wani move dina."

"Ka ba da a maka depositing ko ta POS ne tunda ga cash anan."

"Hakane kuma amma banda account din da za'a saka."

"Akwai account din su Sadiya da su ke business da shi, sai a sa a ciki."

"Amma in su ka yi kokarin reporting fa? Sunga kudi mai yawa daga account din da basu sani ba."

"To ka ba Ya Suraj ya sa musu."

Ashmaan ya gamsu da shawarar. Kiran Suraj ya yi akan ya zo anjima. Bai san da wani baki zai gode ma abokin na shi ba, ya mai taimakon da ba zai taba mantawa ba.

"Yanzu shikenan mu da su Adda?" Jasrah ta tambaya, fuskarta na nuna alamun damuwa.

"Ban gane shikenan ba?"

"Ba ka ji abunda Mommy ta ce ba, Baffa ba—"

"—wannan shine me? Saboda Inna da Ardo ba su su ka haife shi ba ba ya na nufin shikenan sun tashi daga 'yan uwan mu ba. Kar in sake ji. Haduwar jini bashi kadai ke sa mutane su zama 'yan uwa ba. They are family, and will always be. Kar ki sake ki bari wannan abun ya chanza tsakanin ki da su, kuma kada ki saurari duk wanda zai fada miki akasin haka."

"Toh Hamma," ta amsa a sanyaye. Tashi ta yi ta fita ba ta dade ba sai gata ta dawo da gudu kaman an korota. "Hamma tashi ka tafi yanzunnan Mommy ta fita hankali a tashe. Something about mijin Hasina zai kara aure, ni ban ma fahim.........."

Ashmaan bai tsaya sauraron sauran bayaninta ba ya fizgi mukullin mota ya yi gaba. Dama Suraj ya mai kwatance, bai tsaya ko ina ba sai a gaban gidan.

Zaune ya yi cikin mota ya kasa fita. Babu abunda ya ke tunowa sai fuskar Baffa sanda Mommy ta ce bai hada jini da su ba. Bayan shekaru kusan sittin Baffa ya wayi gari bai san waye shi ba, bai san asalin shi ba. Duk saboda mahaifiyarshi.

Dole ya hakura da Moon ko ya na so ko ba ya so saboda da kunya ma ya kalli Baffa ya ce ya bashi auran 'yar shi bayan abunda iyayenshi su ka mai.

Da kyar ya samu ya saita kan shi sannan ya shiga ciki. Da Maimoon ya fara haduwa, ya na ganinta ya ji idanun shi sun fara cika da hawaye. Juyawa ta yi ta shige ciki da sauri. Ajiyar zuciya ya saki, ya na kallon yanayin gidan.

"Hamma?" Muryar Mimi ta isa kunnen shi. "Sannu da zuwa. Ka shigo ciki."

Ya na tafiya ya na kare ma wurin kallo, a ran shi ya na lissafin abunda ya kamata a yi. A falo ya zauna kan tabarma har Ummi ta shigo ta zauna.

Kusa da ita ya koma ya kamo hannunta. "Ummi," kan shi ya kifa a cinyarta ya fashe da wani irin kuka. "Ummi ki yi hakuri."

"Me ye haka Ashmaan? Kukan na meye? Ya isa haka. Akwai wanda ya isa ya tsallake kaddarar shi ne? Daina kukan haka."

Fuskar shi har ta yi ja, bayan hannushi ya sa ya goge hawayen. Saida ya yi da gaske kafin ya iya samo kan shi. Da ya kalleta sai ya ji zuciyar shi ta karye.

"Duk ka rame, ba ka cin abinci. Sadiya," ta kwala mata kira. "Kawowa yayan ku abinci."

Hakan ya tuna mai da lokacin da suke dawowa daga kwallo shi da Mu'azzam. Abinci Ummi ke fara sawa a kawo musu. Ya ci abincin sosai. Mimi da Sadiya sun zo sun gaida shi. Ko da wasa bai yi maganan masoyiyar ta shi ba amma idanun shi na kan dakin da su Mimi su ka fito.

Suna zaune Baffa ya dawo. Ashmaan bai taba jin fargaba irin wannan ba, bai san ya Baffa zai yi ba in ya gan shi ya zo mai gida. Amma da dayake Baffa mutum ne mai dattako, yanda ya saba ma Ashmaan haka ya mai. Hakan ya sa kunya ta kara lullube shi.

Baffa ya shiga daki ya kimtsa ya ci abinci sannan ya fito. Tuni Ashmaan ya gama tsara yanda zai dago maganan gidan. Ran Baffa ya ba ci sosai har hakan ya kasa boyuwa.

"Baffa ka yi hakuri, ban yi dan in bata maka rai ba."

"Bana son a sake wannan maganan."

Ashmaan ya bar gidan gwiwa a sake. Ya zama lallai ya samu wani hanyan da zai taimake su ba tare da sun sani ba. Suraj ya same shi a gida bayan ya koma, Ashmaan bai yi mai maganan kudin ba dan wannan hanya da alama itama ba mai bullowa ba ce.

An yi hurting pride din Baffa, dukkan su ma, shi yasa su ke kin taimakon shi. Amma ba zai karaya ba. Tun ya na karami Allah ya sa mai son kanin mahaifinshi. Tare su ka taso da Mu'azzam duk da a lokacin sun kan dade ba su hadu ba. Da ya yi wayo kuma ya gane ya je da kanshi ba sai wani abun ya taso ba kaman biki a hadu ba.  Tun lokacin Mommy ta yi iya bakin kokarinta wurin ganin ta datse abutar abun ya gagare ta.

Bayan rasuwar Mu'azzam ya ji kawai responsibility din su ya dawo kan shi. Da dan uwanshi na da rai ya san sai inda karfin shi ya kare wurin ganin rayuwar iyayenshi da kannenshi sun inganta.

Washegari Daddy ya kira shi. Ya same shi a falon shi na sama tare da Mommy. Bayan ya gaida su ya kama bakin shi ya yi shiru ya na sauraron su.

Mommy ce ta fara magana. "Da fatan yanzu ka dawo hankalin ka," kasa ya yi da kan shi. "Kuma I hope ba ka manta duk abunda na ce maka ba. Ko bayan raina ban ya fe maka ba in ka saba umarni na."

Daddy ya gyara murya. "Ashmaan, dole in fada maka I am highly disappointed in you. Ka bani kunya sosai, ban taba zaton haka daga wurin ka ba. Inna ma ta kira ta nuna bacin ranta sosai. Sai dai yanzu komai ya wuce da fatan irin haka ba zai sa ke faruwa ba."

"In sha Allah Daddy," ya ce ran shi na kuna.

"Good. Nasan zuciya bata da kashi, an samu akasi saboda haka na yanke shawaran komawarka makaranta dan ka yi earning phD dinka. Na gama duk wani shirye shiryen da ya kamata, nan da sati daya zaka tafi."

Umarni ne ake bashi ba shawara ba. Kaman ya daura hannun shi a ka ya yi ta ihu haka ya ke ji. Bai san ta ya ya kai kanshi daki ba. Shikenan ya na ji ya na gani an raba shi da abunda ya fi so duk duniya? Wannan wace irin rayuwa ce? Ko wancan karan da ya tafi masters ba da son ran shi ya tafi America ba. Wannan karon ko wani kasa za'a jefa shi?

Arwalla ya yi, ya kabbara sallah. Addu'an shi daya ce a wannan lokacin, in Maimoon alkhairin ce a gare shi Allah ya kawo mai mafita, in kuma akasain hakane Allah ya cire sonta a zuciyar shi.

A Suratul Baqara aya ta dari biyu da sha shida Allah Ya ce; "akwai fâtar cêwa ku ki wani abu, alhâli shi ne mafi alhêri a gare ku, kumaakwai fätar cêwa kuna son wani abu alhâli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kû ba ku sani ba."

Ya barwa Allah zabi. Allah Ya zaba mashi mafi alkhairi duniya da lahira.

Cikin satin da zai koma kullum sai ya je gidan, a chan ya ke yini sai yamma ya ke komawa gida. Duk zuwan shi kalma daya bata shiga tsakanin shi da Maimoon ba. Ya na zuwa gidan zata kunshe kanta a daki.

Ana gobe zai tafi ya ke fadawa Baffa da Ummi maganan tafiyar. Sun yi mai addu'a sosai. Da zai tafi ya ajiye brown envelope, Baffa ya ce ya dawo ya dauka.

"Baffa ko dai hukunta ni ka ke yi?" Ashmaan ya ce rai babu dadi. "Ka dauka kaman Mu'azzam ne ya maka dan nasan shi kam baza ka ki karba ba. Sha'anin tafiya ban san ko zan dawo ko ba zan dawo ba, dan Allah Baffa da Ummi ku yafe mun."

Zuciyarsu tai musu nauyi, su ka ce Allah Ya yafe musu gaba daya. Ko daya basu daura mai laifi ba, Ashmaan yaro ne mai hankali dan albarka. Ya yi iya bakin kokarin wurin ganin ya gyara alakar su da su Bello. Bayan rasuwan Mu'azzam kullum ya na tare da Baffa dan daibe mai kewa.

Da komai lafiya lau, Ummi da tafi kowa farin cikin in ya kasance mijin 'yar ta saboda halayen shi na gari.

Har ya shiga mota ya ji ba zai iya tafiya bai ga sahibar shi ba. Kiranta ya yi a waya, ya ci sa'a ta daga.

"Ba dan ni ba, dan Allah Maimoon ki fito mu yi magana. Bayan yau ban san yaushe zamu kara haduwa ba, watakila wannan ce haduwar mu ta karshe ma ba mu sani ba."

Kashe wayar ta yi kawai. Kan shi ya daura kan steery, chan ya ji an bude kofar motar an shigo. Ido ya runtse sanda sanyayyar muryarta ta da ki kunnuwan shi.

Bai juya ya kalleta ba dan kar ya karaya, babu yanda za'a yi ya iya kallon idanunta ya mata magana.

"Na yi practicing mai zan ce miki amma yanzu duk wata kalma ta gudu ta barni," kallo gaba ya ke yi ya na magana. "Ba zan iya cewa yaushe na fara son ki ba Moon, kawai na tashi wata rana na ji ki kin mamaye ko ina a zuciya da ruhina. Gashi yanzu ina ji ina gani an raba ni da ke. Ban san ta ya zan fara lallashin zuciyata ta hakura ba, zuciyar da ta dade ta na dakon son ki."

Dogon lumfashi ya shaka sannan ya fitar a hankali. "Wani abun na ce mun kawai in ja motar mu je a daura mana aure," dariya ya yi wanda ya fi kuka ciwo. "Amma ba za mu yi haka ba. Albarkar iyaye mu ke so. Allah Ya bamu ladan yi musu biyayya. Ba ma cikin kaddarar juna, haka Allah Ya so. Ina miki addu'an samun wanda zai yaye miki matsalolin ki, wanda zai ba ki wannan peace of mind din da kika dade kina so. Sadly, I'm not that person."

Juyawa ya yi ya kalleta. Bata sa niqab ba, hakan ya bashi daman kare ma fuskarta kallo, ya na memorizing dinta dan ya dinga tunowa in duniya ta yi mai zafi. Zai yi kokarin daina sonta sai dai ba abu bane mai sauki. Kuma ya san ko ya ya dage akwai wani bangare a zuciyarshi da zai so Maimoon har abada. Saboda it was functioned to love her forever.

"Hamma...." ta kira sunanshi hawaye na bin fuskarta.

"Kar ki ce komai Moon. Idan ba haka ba zan gudu da ke. It might sound arrogant, amma ba na tunanin akwai wanda zai so ki kaman ni. In kin tashi fitar da miji, ki zabi wanda zai baki farin ciki. In kinyi wannan kin mun komai. Ina da son kai, na so in zaman wannan a rayuwar ki saidai farin cikin ki yana gaba da komai, har nawa kuwa."

Wata brown envelope ya fiddo daga aljihu ya bata. "Ina son ki yi amfani da wannan ke kadai, use it as a capital. Suraj na nan in akwai wani matsala kar ki ji nauyin yi mai magana. I love you so much Moon, ina son ki sosai. Ina miki fatan alkhairi duniya da lahira. Ki yafe mun duk wani laifi da na yi miki, wanda na sani da wanda ban sani ba. Ni zan tafi, in da rabon zamu kara haduwa toh, in babu kuma sai mun hadu a aljannah."

"Hamma..." abunda kawai ta ke maimaitawa kenan.

Bai hana hawayen da suka gangaro fuskar shi ba. Fita ya yi ya bude mata kofa ba tare da ya ce komai ba. Komawa ya yi ya tada motar ya yi gaba, zuciyar shi na kuna.

"Ya Allah Ka kawo mun sauki cikin al'ammura na."












Ameen

Wayyo Hamma bawan Allah🤧 ya bani tausayi.

So what do think? Let me know in the comments section 💃🏻





~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro