BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
~
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
~
Dawowar su Ammi an dagata sai karshen January. Ammah kullum saita kira ta tuna mai shi zai dauko su kaman ya ce mata zai gudu ranan da zasu dawo.
Ya yi tunanin yin hakan amma yasan mai raba shi da Ammah da Mami sai Allah.
Duk weekends ya ke zuwa Kaduna, sam baya da hutu. Aiki da Alhaji na tafiya lafiya lau, bai taba tsammanin haka ba. Ya koyi abubuwa da yawa dangane da aikin da A.R.H ke yi wanda a baya bai taba zama ya yi tunani mai zurfi akai ba.
Alhaji na shirin bude branch anan Abuja. Sayf ya san duk wayo ne irin na Alhaji, mai yasa duk shekarun nan bai bude ba sai yanzu?
Duk zuwanshi garin sai ya je wurin bishiyar nan ko Allah zai hada shi da ita amma har yau. Dukda haka bai karaya ba. Ya rasa dalili amma baya ji zai iya hakura har sai ya nemota. Ita ce mace ta farko da ta ja hankalinshi ta hana shi sukuni.
Ya na mamakin kan shi kwarai, bai ga fuskarta ba, bai ji muryarta ba amma duk ya rude akanta.
Yau sun tashi da tulin aiki a wurin ofis, bashi ya baro ofis ba sai bayan sallar magariba. Kitchen ya nufa yana dawowa gida, ya daga kuloli babu komai kaman ya fashe da kuka.
"Yaya? Mai kake nema?" Ya ji muryar Nusayba na tambayar shi.
"Nussy abinci. Mai kuka dafa?"
"Ai kuwa yau dan wake akayi da rana, har ya kare. Gashi ba'a gama abincin dare ba. Amma bara in dafa ma indomie."
"Yauwa, thank you."
Sashen su ya tafi, nan ya watsa ruwa, ya chanza kaya. Ya na zaune a falo Nusayba ta yi sallama, sanye ta ke da dan karamin hijabi da tray a hannunta.
Jin muryarta Hussein ya fito dan bata zuwa sasahen su sosai. Ya na ganinta da tray ya yi dariya dan ya san abunda ya kawota. "Sayf kadai kika sani, kin kyauta. Haka na zo ina neman abinci kika hadani da dumamen tuwo, toh wallahi sai na ci."
Bata rai Nusayba ta yi, wannan abincin dan Yaya Sayf kadai ta yi shi. "Ban dafa da kai ba fa Ya Hussein."
Sayf ya tashi ya karba tray din. "Kai da ka ce bata iya girki ba. Rabu da shi Nusayba, ya je ya dafa da kan shi."
Duk naci Hussein dole ya hakura dan Nusayba ta hana shi ci. Tana nan zaune har Sayf ya gama ci ta kwashe kwanukan. Tana shiga kitchen din ta yi wani irin ihu da tsalle. Mai aikin gidan na mata kallon ko lafiya ta shareta ta wuce daki.
Ranan juma'a da misalin karfe sha daya na dare jirgin da ya taho daga Pakistan ya sauka a airport din Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
Tun bayan isha'i Mami ta kada kan Sayf da 'yan biyu su ka tafi da motici biyu dan ba'a san yawan kayan su ba.
Mutane na ta fitowa daga (terminal) Sayf ya hanga ko zai ga fitowar su. Idonshi na sauka kan mahaifiyarshi ya ji faduwar gaba ya ziyarce shi.
Ba zai iya tuna yaushe ya ganta karshe ba amma ya na iya tuna lokacin da ya mata ganin farko da wayon shi, lokacin ya na da shekara goma.
'Kyakkyawa', abunda ya fara tunani a lokacin kenan. Ko yanzu bata yi kama da ta haife shi ba, in an gansu tare ma za'a sha yayarshi ce.
'Yan mata biyu ne a gefenta sun saka ta a tsakiya. Ko waccen su da yarinya a hannu, sai namiji da ke biye da su a baya.
Hajiya Aisha ta haifi yara uku bayan ta sake aure. Sunan namijin kawai ya ke iya tunawa, Sameer.
Sayf na jin ciwo in ya tuna cewa su sun girma da mahaifiyarsu. Ta san cin su, ta san chan su, ta kula da su lokacin da basu da lafiya, ta damu dasu kuma ta na son su. Shi bai samu ko daya ba.
Da sauri ya girgiza kan shi dan bai son yin irin tunanin. Ya na da Mami, ta ishe shi. Shi ba karamin yaron nan bane da ke kwana kuka ya na kiran mamanshi ta zo ta cece shi. Ya girma yanzu, baya da bukata.
Karamar cikin 'yan matan ta fara ganin shi. Murmushi ta yi ta taba mamanta ta na nuna Sayf. Gaban shi saida ya amsa da suka hada ido da Hajiya Aisha.
Hassan ma ya lura dasu, shi ya fara yin gaba. A baya Sayf ya tsaya 'yan biyu su ka fara gaisawa da su. Kaman sun hada baki a lokaci daya su ka matsa, sai Sayf ya tsinci kan shi daf da mahaifiyarshi.
"Sayfullah," ta furta a hankali kaman mai rada. Ta daga hannunta da niyan shafa mai fuska ya yi baya ba tare da ya san ya yi ba ma.
"Ina wuni. Sannu da zuwa," Da kyar Sayf ya iya furta kalaman. Ji ya ke yi kaman wani abu ya danne mai makokwaro. Hannun shi ya mika ya amsa 'yar karamar jakar matafiya da ke hannunta.
Fuskar Hajiya Aisha ta chanza. Murmushin dole ta kakalo.
"Yaya Sayf ina wuni!" Karamar ta gaisa shi. Ya gane muryarta, ita ce ta dauki waya da ya kira kwanakin baya.
Da dan murmushi a fuskar shi ya amsa, sauran ma suka gaishe shi. Hannu ya mika ma Sameer su ka yi musabaha.
Basu taho da kaya da yawa ba. An sa akwatinan a motar da Hassan ya tuko. Nan Sameer ya shiga, matan kuma su ka shiga motar Sayf.
Shiru babu wanda ya ce komai har su ka isa. Mami batayi barci ba tana jiran isowar su a falo. Tana ganin Ammi ta mike su ka rungume juna. Lokacin Hajiya Aisha na gidan Abdur-Rahman sun yi shiri sosai, zumuncinsu ya samu tangarda bayan rabuwan amma sun gyara shi.
"Masha Allah," Mami ta ce tana karban daya daga cikin yaran da suke 'yan biyu. "Sai suka tuna mun da Hassan da Hussein dina."
Yaran Kyda ne, Huda da Inas.
Sama Mami ta ja su, dakinta ta kai Ammi. Nusayba kuma ta kai Waahidah da Kyda dakinta wanda tuni ta yi musu shimfida.
Shi kuma Sameer ya bi su Sayf bangaren 'yan maza.
"Aisha kwatakwata ba ki tsufa." Mami ta ce tana sake kallon Ammi. "Wannan aka gan mu tare ai sai a ce na girme ki nesa ba kusa ba."
Dariya Ammi ta yi ta na gyada kai. "Fatima har yanzu ba ki daina tsokana ba kenan."
"Dagaske fa. Ko 'yar kiban nan ta manyance banga kin yi ba."
"Hmm, ba saida kwanciyar hankali ake kiba ba."
"Ke kuwa mai zai dame ki har ya daga miki hankali haka."
Tuna yanda Sayfullah ya yi baya da ta yi yunkurin taba shi ta yi. "Sayfullah ya girma, ya zama babban mutum."
Mami ta gane mai ta ke nufi sai bata ce komai ba. Kowa ya yi mamaki da Abdur-Rahman da Aisha suka rabu lokaci daya dan ba karamar soyyaya su ka yi ba kafin su yi aure. Saidai Allah Ya kaddara zaman nasu ba mai tsawo bane.
"Fatima Sayfullah ya tsane ni."
Ajiyar zuciya Mami ta yi. "Bai tsaneki ba, ki bar cewa haka."
Girgiza kanta ta yi. Da ana maida hannu agogo baya da ta koma ta tabbatar ba ta yi kuskuren da zai rabata da danta ba.
"Kina ganin zai yafe mun?"
"Mu bar maganan nan ki kwanta ki huta." Mami ba ta san yanda zata fada mata ita da dan uwanta sun bar tabo babba a zuciyar danta Sayf ba.
Murmushi Ammi ta yi cike da ciwo. Ta yi da nasanin abunda ta yi, ta bari fushi ya rufe mata ido har shaidan ya yi nasara akanta.
A lokacin da ta gano kuskurenta kuma ta bari tsoro ya hanata gyara mu'amalarta da gudan jininta. A wautarta ta zata Sayfullah ba ya da bukatarta tunda ga Fatima. Abunda bata sani ba shine ba'a taba iya maye gurbin uwa.
"Ba zai yi ba ko?" Shikenan ta ja wa kanta. Ta bari cowardice ya sa ta rasa danta.
"Bazan yi maki karya ba in ce abu ne mai sauki," Mami ta ce tana tuna irin dagar da tasha da Sayf kafin ma ya fara sauraronta in ta dago maganar mahaifiyarshi. "Saidai Sayf dina nada kyakkyawa zuciya. Kada ki karaya, in sha Allah komai zai daidaita."
"Allah Ya sa," Ammi ta amsa a sanyaye.
***
Da sassafe Sayfullah ya kama hanyar Kaduna. Shi da baya son zuwa aikin yau har Allah Allah ya ke yi ya tafi. Bai yi wa Mami sallama ba dan ya san hanashi zuwa zata yi.
"Sayf tafiya za ka yi yanzu?" Hassan ya kalle shi alamu sun nuna bai ji dadin abunda Sayf ke shirin yi ba. "Haba mana. Ace Ammi ta dawo amma ka kama hanya ka tafi. Dan dai yau kadai ka bari ba sai ka je ba mana."
"Look, idan Mami ta tashi kawai ka fada mata." Bai shirya jin nasihar da Hassan ke niyar mai ba.
Ganin Ammi ya fama mai ciwuka da yawa da ya sha sun warke. Bai damu da abunda Alhaji ya mai ba, ko banza bai tafi ya barshi ba, ya kuma kula dashi dukda ba yanda ya kamata ba.
Amma Ammi... nata yafi mai ciwo. Uwa ita aka sani da tausayi amma ace tashi uwar ita da kanta ta tsallake shi ta barshi.
Suna UK Mami ta fara yawan maganarta a lokacin ko sunanta ma ba ya son ji. Duk sallah sai ta bashi tulin kaya wai gashi mahaifiyarshi ta aiko mai dasu. Bai taba sa ko daya ba, duka bayar da su ya yi. Ba yada bukatar su.
Duk juma'a Mami ke tsare shi ya kirata ya gaisheta. Haka har ya zame mai jiki. Amma fa bayan gaisuwar nan babu abunda ke kara shiga tsakanin su. A ganin shi ya sauke hakkinta da ya rataya a wuyar shi.
Ko da ya isa Kaduna, gidan Habib ya nufa dan ya san ya dawo weekend. Habib bai yi mamakin ganin shi ba.
"Allah Ya shirye ka," kawai ya ce mai.
Ran Mami sosai ya baci jin wai Sayf ya tafi Kaduna. Kallo daya zaka ma Ammi kasan abun ya soketa sosai.
Kiran Sayf Mami ta yi. "Ba tarbiyar da na baka ba kenan Sayfullah Abdur-Rahman Hambali! Ko mai kake yi ka barshi ka dawo gida."
"Mami ki yi hakuri amma bazan iya dawowa ba."
"Sayf!" Ta daka mai tsawa.
"Mami ki yi hakuri," ya sake maimaita.
"Sayf," ta kira sunan shi a hankali. "Na fada ma you have to let go."
"Na kasa Mami," ya ce muryar shi na rawa. "I tried, amma na kasa."
Da sanyayyar gwiwa Mami ta koma daki. "Allah Ya karkato miki kan shi Aisha. Ki yi hakuri."
Ammi ta san ba ita ya kamata a ba hakuri ba. Duk abunda Sayfullah ya yi bai yi laifi ba, ita ta ja.
Ranan lahadi Ammi su ka tafi Katsina. A Abujan za su zauna amma sai mijinta, Alhaji Nasir Lamido, ya dawo. Ta so sake ganin Sayf amma har su ka taho bai dawo ba.
Ta yi kewar kasarta ta haihuwa, ta godema Allah da mijinta ya gama aikinshi lafiya suka dawo gida.
Tana ganin mahaifiyarta ta fashe da kuka. Hajja Mero ta ruko 'yar ta kwara daya tilo jikinta ta rarrasheta. "Mai ye na kuka kuma Indo? Sai ka ce karamar yarinya."
Sun sha hira har take fada mata abunda ya faru da Sayfullah.
"Kin kwari yaron nan ba kadan ba Indo. Kin hukunta yaro akan laifin da bashi ya yi ba. Ke zuciya, ai ga abunda ta janyo miki nan."
"Hajja..."
"Ai gaskiya ce. Iyaye ya kamata mu rika jin tsoran Allah. Yaran nan amana ce Ubangiji Ya damƙa mana, kuma ran gobe ƙiyama zai tambaye mu akan yanda muka kula da su. Ba iyaye kadai bane ke da hakki akan yara ba, yaran su ma suna da hakki akan iyaye wanda ya zama dole su sauke shi."
Jikin Ammi ya yi sanyi, zancen Hajja ya ratsa ta sosai.
"Yaron arziki, in an kwana biyu ya na lekowa ya gaishe ni."
Ammi ta san shanyo kan Sayfullah abu ne mai wuya amma ba zata karaya ba, ta riga da ta bata lokaci da yawa.
***
Sayf ya cigaba da harkar shi. Ya ji dadi da Mami bata dago mai maganar Ammi ba bayan ya dawo.
Suna ta shirin bude (factory) tare da Habib. Kaya sun gama isowa, ana assembling. Wata takarda ce dai har yanzu ba'a sa musu hannu ba.
"Sayf fa dole ka kaiwa Alhaji ya taimaka mana. In ba haka wallahi babu ranar fara aikin nan. Put your ego aside ka yi abunda ya kamata. Wani girman kai za ka mai? Tunda ya yi sanadin zuwan ka duniya ai magana ta kare."
Harara Sayf ya maka mai amma ko a jikin shi. "In kaga dama idanun su fado dama ba lafiya ne da su ba."
Ya fi minti uku tsaye gaban kofar office din Alhaji da ke gida. Har sai ya daga hannu zai kwankwasa sai ya fasa. Daga karshe dai ya sauke ajiyar zuciya ya shiga da sallama.
Alhaji na zaune da glass a fuskarsa ya na duba wasu takardu. Kamanin su ya kara fitowa musamman da ya sa glasses.
A kujeran da ke gaban table din shi Sayf ya zauna ya gaida shi.
Ya amsa ba tare da ya dago ba. Saida ya gama ya dubi Sayf. "Akwai abunda ka ke so Sayfullah?"
"Babu komai, dama zan fada ma na dawo ne." Hannu ya sa ya gyara zaman glass din shi.
Har ya mike Alhaji ya dakatar dashi. "Dawo ka zauna. Fada mun mai kake so?"
Sayf ya tattaro duk natsuwar shi ya ma Alhaji bayanin abunda su ke ciki.
Wani irin kallo ya ga Alhaji ya na mai, sai chan ya ji ya ce. "I'm proud of you my son." Daga gani bai yi niyar fada a fili ba, maganar zuci ce ta fito. "Ka ajiye file din, in sha Allah I'll see what I can do."
"Nagode, Allah Ya saka da alkhairi."
"Ammah ke fada mun Amminka ta dawo."
Maganar ta zo mai a bazata. "Eh, ta na Katsina."
Kai kawai Alhaji ya gyda. Drawer din jikin teburin shi ya janyo ya fito da files guda biyu. "Da fatan babu wani abu da zaka yi. Wannan files din na ke so ka kai ma Alhaji Saminu a Zaria."
Ya fita daga office din ke nan ya ci karo da Hajiya Zuwaira a bakin kofa. Tana ganin shi ta daburce.
Kai kawai ya girgiza ya yi gaba. Wurin Ammah ya tafi ya fada mata Alhaji ya aike shi. Ta na jin Zaria zai je ta mike.
"Kazo a daidai. Inada sako."
"Ke wa kika sani a Zaria?"
"Makarantan nan ta Sardauna, ya ma kuke ce mata?"
"ABU?"
"Ita. Sako za ka kaima Maimuna a chan."
"Ammah ba fa nan zani ba, cikin gari zan je. Wacece kuma Maimuna?"
"Duk ba gari daya bane. Ka ji mun yaro fa. In baka zuwa ka fada mun."
"Ni na isa in ce baza ni ba."
Daki ta shiga ta dauko ledoji manya guda biyu. "Gashinan garin kunu ne da na dan wake. Wannan...ko kuma barshi zan kirata kar ka je kamun shirme," jarka ta ciro ta ajiye daban. "Wannan dai nono ne saboda haka ka bi shi a hankali kar ya zube. Ka tabbata ka kai mata komai fa."
"Ni Ammah bana jin kin taba bada sako haka an kai mun. Ko wacece wannan kina ji da ita."
"Ungo naka." Dakuwa ta mai. "Duba wayata za ka ga lambarta. In ka je sai ka kirata."
"Ya kika sa mata?"
"Ahalan ce ta yi saving. Ni ban sani ba."
Saida ya kira Ahlaam da wayar shi ta fada mai da 'Maimoon' ta yi saving. Shima haka ya sa a wayar shi.
"Ammah ba ki fada mun wacece ba."
"Ka fiye gulma. Dole sai ka sani? Toh jikata ce."
Dariya ya yi dan jikokin Ammah yawa ne da su. Ko ina ta samo wannan kuma? Daga gani dai ita 'yar gaban goshi ce.
"Toh ni na tafi."
"Allah Ya kiyaye. Ka tabbata ka kai mata fa Saifullahi. Ni dama ka fara mika mata kafin ka je aiken baban naka."
"Oh Ammah!" Ya yi dariya. "Na ji. Sai na dawo."
•
•
•
•
•
•
•
Who's excited? 🥳💃🏻
A cika mun waya da votes da comments in ana son next chapter da wuri.
~Maymunatu Bukar 💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro