BABI NA ASHIRIN
~~BABI NA ASHIRIN~~
Kwance ya ke kan kujera a mike ya daura hannun shi na hagu a kan fuska. Tunani ya ke yi mai zurfi. Idanunta kaɗai ya ke gani in ya rufe ido. Bai taɓa ganin idanu masu kyau haka ba, kaman madaran da aka diga ma tawada.
Bature ya yi gaskiya da ya ce: eyes are the windows to the soul.
A cikin idanunta ya hango duhu mai rudarwa. Har yanzu ya na iya jiyo sautin kukanta cikin kunnuwanshi. Yana cikin mota a lokacin, bai yi yunkurin hanata ba saboda shima da zai samu dama da ya yi irin kukan da ta yi ko zuciyar shi za ta daina mai radadin da ta ke yi.
Bai ji sanda aka bude kofar falon a ka shigo ba sai ji ya yi an daka mai duka a kafa.
"Lafiya ka ke kuwa? Tunda ka dawo garin nan ka ke tunanin kaman matar da aka ce za'a mata kishiya?"
Matasa biyu ne masu fuska iri daya tsaye kan shi. Mikewa ya yi ya jingina da kujeran da ya ke kwance a kai.
Wanda ya yi magana dazu ya sake cewa. "Hassan ko baka lura ba? Tunda Sayf ya dawo daga KD kullum ka gan shi ya na tunani. Ko dai wata ta gama da kai ne ba mu sani ba?"
Bata rai Sayf ya yi. "Kai kam ka na da matsala. Kowa irin ka ne aka cema? Kai dai ka je ka ji da tarin 'yan matan ka."
"Jiya wata ta kira ni ta na kuka wai sati daya bai dauki wayarta ba," Hassan ya ce daga zaune. Juyawa ya yi ya kalli dan uwanshi. "Wallahi ka sake basu number na sai na ci maka mutunci. Ya Sayf ka san akwai sanda wata ta watsa mun ruwa lokacin a school ta na sha shi ne."
Dariya Sayf ya yi yana kallon 'yan biyun su na musu. Mikewa ya yi ya shiga daki dan ya chanza kaya. Ya na dawowa daga office ya kwanta kan kujera ya na tunani.
Ko me ya sameta ta yi kuka haka? Kukanta ya taba mai zuciya ba kadan ba, cike ya ke da kunci da ciwo. Bai san meyasa ba amma haka kawai ya ji ya na son cire duk wani abu na bacin rai daga rayuwarta ko idanun nan za su yi haske kaman watan da su ke kama da.
Hassan kadai ya samu a falon. "Ya je amsa waya," ya ce ya na nuna mai daya daga cikin dakuna.
"Mu je ya taho, lokacin sallah ya kusa." Sayf ya ce yana balle agogo a hannun shi na hagu. Manyan kaya ya saka, farar shadda da hula sannan ya maida gilashin da ke ta ya shi gani.
Motar Hassan su ka shiga dan shi bai cika san tuki ba. Hassan na tada motar Hussein ya fito da gudu ya bude baya ya shiga. "Da tafiya za ku yi ku barni?"
"Gani na yi baka shirya ba ai." Hassan ya ce ya na reverse.
A National Mosque su ka yi sallar juma'a. Bayan an sauko su ka nufo gida. A hanya su ka hadu da go slow. Dama garin Abuja ba baya ba wurin cinkoso.
"Ni wallahi yunwa na ke ji," Hussein ya ce daga gidan baya ya na rike ciki. Kan shi ya turo tsakanin kujerun ya na kallon Sayf murya a marairaice. "Ya Sayf ka siyan mun ko biscuit ne."
"Dole ka ce mun Ya Sayf tunda abu ka ke nema ai."
"Ai kai ne babba, shekara biyu ai ba wasa ba ne."
Tsaki Hassan ya yi. "Ko dan shekara goma ba zai yi abunda ka ke yi ba Hussein. Ya dai kamata a san an girma, shekara talatin da hudu ba nan ba."
"Yunwa bata san wani shekaru ba, Hamma Sayf ka taimaka. Beran masallaci ya fini arziki, ko sisi ban da shi."
"Ina za ka yi sisi dama Hussein ana kashe ma 'yan mata kudi," Sayf ya ce dukkan su su ka yi dariya. Daga karshe sai da ya siyan mai biscuit din saboda ya cika musu kunne da magiya.
Sayfullah Abdur-Rahman Hambali matashi ne mai shekaru talatin da shida a duniya. Yana aiki da US Embassy a garin Abuja. Mutum ne mai saukin kai da sakin fuska.
Sunfi minti talatin cikin go slow din kafin su isa gida. Cikin gida su ka nufa dukkan su uku a jere. 'Yan biyu sun sa Sayf a tsakiya, sun fi shi duhu saboda haka farar fatar shi ta kara haske. Kowanne cikin su ya sha shadda sai walkiya su ke yi.
"Walking skyscrapers," su ka ji an ce ana dariya. "Wai, tsawon kun nan ya yi yawa."
Dariya su ka yi, suka samu wuri a kasa suka zauna. "Ina wuni Mami," su ka ce a lokaci daya.
Wacce aka kira da Mami ta yi murmushi. "Lafiya lau. Ku je dining table Nusaiba ta hada muku abinci." Har sun mike ta dakatar da Sayf. "Idan ka gama cin abincin ka same ni a dakina."
Kai ya sosa ya ce to dan ya san dalilin kiran. Hussein har ya yi zubi ya na kai loma.
"Yaya ga shi har na zuba ma," wata budurwa mai kimanin shekara ashirin ta ce ma Sayf ta na nuna mai kujerar da ta janyo.
"Thank you Nussie," ya ce ya na murmushi. Masa ce da miyar taushe sai zobo mai sanyi. Zama ya yi ya ci abincin sosai. "Ya yi dadi, ke ki kika dafa?"
"Wa? Wannan din? Haba Sayf kaima zancen ka ke nema," Hussein ya amsa kaman shi aka tambaya. "In banda kona abinci wannan me ta iya?"
Kumbura fuska Nusaiba ta yi ta na kallon yayanta, Hussien. Sayf ta juya ta kalla a shagwaba ta ce. "Yaya ka gan shi ko?"
"Ai gaskiya ce. Gwara dai a dage a koyi girki yarinya kar mu kai ki a koro mana ke ace ba ki iya abinci ba." Ya na gamawa ya fice dan Sayf ya dauki roba zai jefe shi da shi.
"Rabu da shi," ya ce yana kurbar zobo. "Amma dai na san ke ki ka yi zobon nan."
Murmushi ta yi kanta a kasa. Hannu ya tura cikin aljihun shi ya ciro kudi. "Gashi tukuici da kuma barka da juma'an ki."
"Nagode Yaya."
Kai kawai ya daga mata sannan ya nufi dakin Mami a sama. A hankali ya tura kofar bakin shi dauke da sallama. A kasa kan carpet ya tarda ta. Gaishe ta ya sake yi bayan ya samu wuri ya zauna.
"Sayf." ta kira sunan shi murya babu alaman wasa. "Mai ya faru tsakanin ka da Baban ka da ka je Kaduna?"
"Mami na ce maki babu komai."
"Wato ban isa da kai ba shi yasa ba zaka fada mun ba ko? Jiya Yaya ya kirani ta inda ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba, wai ni ke hure ma kunne."
Ran shi ya ji ya baci. "Haka ya ce miki?"
"Ban ce ka je ku kara samun matsala ba. Me ya faru Sayf?" Ta kara maimaitawa.
Ajiyar zuciya Sayf ya yi yana kallon kanwar mahaifin shi da ta ke tamkar uwa a wurin shi. Da ana zaban iyaye ba shakka Mami zai zaba. Ita da mijinta sun mai abunda iyayen da su ka kawo shi duniya su ka kasa.
"So ya ke yi in ajiye aikina in koma karkashin company din shi, ni kuma na ce bana so."
"Mai ya sa baka so?"
"Mami bai tambaye ni me na ke so ba, inada ra'ayin irin aikin ko kuwa, ina aka taba haka? Ina son aikin da na ke yi yanzu, bai san wahalar da na sha ba kafin in same shi kawai daga sama sai ya ce in aje. Ba'a mun adalci ba in aka mun haka. Sanda na ke da bukatar shi bai mun abunda na ke so ba sai yanzu zai za ya c—"
"—ya isa haka Sayf," Mami ta dakatar da shi. Kwantar da murya ta yi. "Bana son inga kana fada da mahaifin ka sam. Yanzu ina so in ka nutsu ka kira shi ka mai duk bayanin da ka mun."
"Ke ma kin san ba zai saurare ni ba." Yaushe Alhaji Abdur-Rahman Hambali ya taba tsayawa ya saurari abunda Sayf ke so? Shekara talatin da yan kai bai yi ba ai ba zai fara yanzu ba.
"Koma me ye. Ka kira Ammie da na ce?"
Ya ga takan shi. 'Yan query ne yau a kan Mamin ta shi. "Na yi mata text."
Rai ta bata ta na kallon shi. "Kiranta ne ce ka yi ba text ba. Sayf ka kiyaye ni."
Dariya ya yi ya taso ya zauna a gefenta. "Yi hakuri Mamina. Zan kira ta anjima in sha Allah."
"Yauwa ko kai fa. Dan Allah ka sassauta fushin ka haka ka ji? Ba shi da amfani ko kadan."
Kan shi ya daura kan cinyarta ba tare da ya ce mata komai ba. Shi kadai ya san yanda ya ke ji in aka mai maganan daya daga cikin iyayenshi. Wasu abubuwan duk yanda ya so manta su ya kasa. Kai ya girgiza dan bai cika son ya na tunani mai zurfi akan haka ba.
Hannun Mami ya ji yana yawo akan shi. Ido ya runtse, ya na tuna sanda ta ke mai haka lokacin ya na karami. Ba zai taba iya biyan akan Mami abunda ta mai ba. Ta ceto rayuwarshi daga halaka, ta bashi kulawa da soyayyar da ya rasa tun ya na karami. Sai dai ya yi ta addu'a Allah ya biya ta.
"Mami nagode." Ya ce a hankali.
"Tashi ka fita ka bani wuri," ta ce ta na ture kan shi daga jikinta. A duk sanda ya mata godiya haka ta san me ya ke tunani. Sam ba ta shirya yin kuka ba.
Ya na dariya ya fita ya rufe mata kofa. A falon kasa ya sami Alhaji Ahmad ya dawo daga wurin aiki. Gaishe shi ya yi.
"Lafiya lau, Sayf. Wata wainar ku ka tuya kai da Fatima yau?"
Dariya ya yi. "Baba babu wata wainar da muka tuya." Shakuwar da ya yi da Baba Ahmad, bai yi da mahaifinshi ba. Tsakanin su kullum abu daya ne.
"Ai nasan hali ne." Baba ya ce ya na dariya shima.
Barin shi ya yi ya ci abinci ya nufi sashen 'yan mazan gidan. Flat ne mai dakuna hudu, falo da dan karamin kicin. Bai samu kowa a falo ba, dakin shi ya nufa. Kayan jikin shi ya chanza ya sa jallabiya sannan ya dauko laptop din shi dan ya karasa aikin da ya fara a office yau.
Saida ya ji bayan shi ya fara amsawa sannan ya aje gefe. Nan ya tuna ya ma Mami alkawarin kiran Ammie. Shi a ganin shi text din ya yi mata ya isa, tunda har ta yi mai reply.
Bata dauka kiran farko ba, ya sake dialing. In bata dauka ba wannan karan shikenan, ai dai ya kirata. Har ta kusan tsinkewa ya ji an dauka. Zuciyarshi ta fara bugawa da sauri. Bai san mai ze ce mata ba.
Kafin ya yi magana, ya ji an ce, "Yaya Sayf ina wuni," cikin Hausar da bata kware ba.
"Lafiya lau, uhmmmm...." kokarin tuna sunan yarinyar ya ke yi.
"Waheeda, Waheeda ce Yaya."
"Waheeda," ya sake maimaitawa. "Ina mamanki?"
"Ammi na waje, bari in kai mata."
"No, ba sai kin kai mata ba. Ki ce mata Sayf ya kira kawai." Yana kai nan ya kashe wayar.
Falo ya koma, ya samu 'yan biyu na buga FIFA a Ps4. Wuri ya samu ya zauna. Hussein na ta kunkuni Hassan na cin shi. Sayf ba ya da wasu abokai da su ka wuce su, sai amininshi daya Habeeb.
"Ban yarda ba Hassan, a sake bugawa. Anya ma baka taba min controller ba ma da na fita."
"An cika kawai malam," Sayf ya ce ya na amsan controller din daga hannun shi.
Hussein ya dage Hassan bai ci shi ba sai an sake. Yana cikin zuba aka kira shi a waya. "Hello baby..." ya ce ya yi hanyar waje.
Kai Sayf ya girgiza. "Haka dai zaka kare."
Da dare suna kan table suna cin abinci duka gidan Sayf ya tsaya ya na bin kowa da kallo. Familyn na burge shi, inama shima haka ya taso cikin iyayenshi da 'yan uwanshi. Bai taso haka ba, amma tabbas yaran shi ba za su rasa abunda shi ya rasa ba.
Muryar Mami ya tsinta ta na cewa. "....ku dage ku yi aure ku daina cinye mun abinci."
"Mami ga babban dan ki nan, ai shi ya kamata ki cewa haka. Mu ai yara ne," Hassan ya ce ya na nuna Sayf.
"Da dukkan ku na ke yi. Sayf sai a dage tunda kai ne babba."
"Wani shine babba," Baba ya ce. "Kowannen su ya kai ai. Mu lokacin mu ina mu ke wuce shekara ashirin da biyar gidan iyaye. Amma ka kunan godai-godai da ku babu ko kunya."
Dariya kowa ya yi, Mami ta ce. "To kunji dai. Sai a bada himma."
"Ki cigaba da mana addu'a Mami," Sayf ya ce ya na hango fuska rufe da niqabi mai dauke da fararen idanu a ranshi.
She really had the most beautiful eyes he has ever seen.
•
•
•
•
•
Toh Jama'a 💃🏻💃🏻💃🏻 Who is excited? I know I am💃🏻🥳
Thank you for your support ❤️ nagode sosai.
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro