Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ARBA'IN DA UKU








~
BABI NA ARBA'IN DA UKU
~












"Yauwa Sayfullah kai na ke nema. Zo ka duba laces dinnan ka ta ya mu zaba." Cewar Mami ta na fito da kaya daga cikin leda babba.

Sayf da shigowarsa gidan kenan ya amsa da toh. Salma matar Habib na nan zaune a kasa tana ta ya Mami fito da kayan. Tare da ita ake hada lefen. Mami ta ce kar ta je ta zaban ma amarya kalolin 'yan da.

Zama Sayf ya yi ya tankwashe kafa aka miko mai laces din. Kala uku ya dauka wanda ya san za su yi daidai da kalar fatar Noor. "Maman Ikram babu wasu designs din ne? Materials fah? Su an siyo su? Jiya naga wasu voiles a Instagram zan tura miki link din, sun yi kyau sosai, a zaba kaman guda biyar haka."

Salma ta yi murmushi ta ce, "Toh Baba Sayf, duk yanda ka ce haka za'a yi. Wannan amaryan 'yar gata ce."

"Ahh, sosai!" Inji Mami. "Sai kin ji sharuddan da aka saka mun, banda kala kaza, bata son wannan, tafi son wannan."

Maganan Mami ya ba shi kunya. Nan ya barsu ya wuce daki. 'Yan biyu na zaune falo suna buga FIFA a PS5. Hussain na ganin shi ya tsaida wasan. "Allah Ya taimaki ango! Ango ka sha kamshi. Na Maimoon bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya fadi."

"Zan maka rashin mutunci Hussaini, ka maida ni kakanka."

"Allah Ya huci zuciyar ango. Fushi ba naka bane."

Kai Sayfullah ya girgiza. Idan ya biye mai nan zasu yini ana abu daya. "Hassan takardun nan fa?"

"Na ajiye maka kan table a daki."

"Okay to, nagode. Bari in shiga ciki."

"A gaida Anty Amarya!" Hussain ya ce da karfi dan Sayf ya jiyo shi.

Dawowar shi kenan daga site din A.R.H motors. Aikin bude branch anan Abuja yana ta kara gaba. Takardun da Hassan ya ajiye mai akan aikin ne zai duba ya tabbatar komai na tafiya yanda ya kamata.

Abubuwa suna nema su yi mai yawa, ga aikin shi, ga kamfanin su shi da Habib ga A.R.H motors ga kuma hidimar da ke gabansa.

Dadin shi daya, 'yan uwansa na taimaka mai sosai. Badan haka ba bai san ya zai yi ba.

Yana son komai ya tafi daidai. Dukda dai sha'ani irin haka ba za'a rasa samun matsala ba amma yana so ya kiyaye komai koda an samu matsala abun ya zo da sauki.

Har yanzu maganan inda zasu zauna ne ba'a samu wani cigaba ba. Amma sauran abubuwan suna tafiya yanda ya tsara. Duk wani shirye-shirye da ya kamata ya yi a matsayin sa na ango ya kusa kammala su. Kayan sawa, takalma, hula da sauran su. Harta inda zai sauke baki ya yi (booking) tunda a nan za'a daura aure. Abubuwan da suka rage basu da yawa.

Lefe ne yanzu babban aikin dake gaban shi. Kwata kwata lamarin babu sauki. A haka ma wai dan iyayensa sun taimaka mai kenan. Alhaji da Ammi ma sun turo na su.

Kiran sallan magriba ne ya tayar dashi daga aikin da ya ke yi. Bayan an idar da sallah kuma duka su ka shiga cikin gida domin cin abincin dare.

Nan ya tarar da aminin shi ya zo daukar matarsa. "Za ku biya rike mun mata da ku ke yi."

"Kanwarta ta ke hadawa lefe saboda haka babu wani biyan da za mu yi."

Mami bata bari Habib da Salma sun tafi ba saida su ka ci abinci. Sayf ya raka su mota. Har Habib ya tada motar ya kashe, juyawa ya yi ya ce ma Salma yana zuwa bari su yi magana da Sayf.

"Lafiya?" Sayf ya tambaya.

"Na manta in fada maka. Jiya landlord din estate dinmu ya same ni, mutanen da ke gidan gefen mu zasu tashi karshen watan nan. Ban sani ba ko you're interested."

"Ya situation din gidan ya ke?"

"Eh toh, dole sai an yi dan gyara amma na san ba da yawa ba. Kuma gaskiya suna kokari, maintenance da sauran su, kuma rent din is fair."

"Nagode Habib, zan yi magana da Noor sai in sanar da kai abunda muke yi deciding. Structure din gidan daya ne da naku?"

"Eh. Daki uku a sama da karamin falo sai kasa falo, kicin, store, da kuma karamin daki."

Kai ya gyda ya yi musu sai da safe. Yana isa daki ya dauki waya ya kirata bata dauka ba, ya kara kira bata dauka ba. Sai ya kyaleta wata kila wayar bata kusa da ita.

Bayan 'yan mintoci sai ga kiranta ya shigo. Katse kiran ya yi ya kira da kan shi.

"Salamu alaikum,"

"Wa'alaikumus salam. Noor lafiya na ji muryan ki haka? Me ya faru?"

Muryarta ta dashe bata fita da kyau.

"Lafiya lau. Mun je kasuwa na shaki kura."

"Please ki rika kula da kan ki. Je ki kwanta ma kawai."

Dariya ta yi. "Duka karfe takwas yanzu, ina da sauran aikin da zan y—" tari ya hanata karasa magana.

"Gashi kina tari kuma kin cewa lafiyan ki kalau."

"Dagaske. Kaman allergic reaction ne."

Bayanin da Habib ya yi mai ya mata. Kafin ma ya gama fadin abunda zai ce ta katse shi.

"Ya yi."

"Ba ki bari na gama bayani ba Hajjaju."

"Ba sai ka yi bayani ba, ya yi babu matsala."

"Da bakin ki kaman babu matsala. Ai ko be yi ba tunda kusa da su Habib ne za ki ce ya yi."

"Sosai! Da dadi a ce akwai wanda ka sani a kusa. Ka ga idan shiru ya mun yawa zan dauko su Ikram su tayani hira."

"Ban yarda ba, za su cinye mun lokacina," ya gyara zaman shi a kan gadon. "Ya shirye shirye? Da fatan babu matsala ko? If there's anything just let me know please."

"Babu wata matsala, komai lafiya lau."

"Mahnoor..."

"Dagaske babu matsla, idan akwai zan fada maka."

"Mhmm," jin ta kawai ya ke yi. "Yanzu dai ki tafi ki kwanta sauran aikin a bar shi sai gobe dan Allah. Bana son kina gajiyar da kan ki."

"To, duk yanda ka ce haka za'ayi. Sai da safe."

Ko bayan kiran ya katse bai motsa daga inda ya ke ba.

Bai san da wasu kalamai zai yi amfani da su ba wurin kwatanta irin son da ya ke ma Maimoon. Da tunaninta ya ke kwanciya barci, da shi ya ke farkawa. A shirye ya ke ya yi koma me ye dan ganin farin ciki da walwala a tare da ita.







***



Yau saura wata daya cif a daura auren Sayfullah da Maimoon. Daga amaryan har angon kowa kai ya dauki zafi.

Duk wani shiri da dangin amarya ya kamata su yi tuni an gama, lokaci kawai ake jira ya yi.

Maimoon takan rufe kanta a daki ta yi kuka. Kukan farin ciki da hamdala. 'Yan uwan Baffa ba su bari ya yi komai ba. Duk wani abu da uba zai yi wa 'yar sa sun yi mata. Abun sun maida shi kaman gasa a tsakanin su. Yanda su ke wa 'ya'yan cikin su haka su ka yi mata babu banbanci, nata ma har yafi nasu.

Baffa kuwa bai yarda ba ya ce za su kwashe duka ladar. Tsohuwar ajiya da ya dade yana tarawa ya fito ya damka ma Ummi ya ce ayi hidimar biki da ita.

Kaman yanda bikin Anwara ya kasance daurin aure da walima kadai itama haka na Maimoon din zai kasance. Sai henna party da za su yi a gidan Kydah. Hakan ya fi mata dan ita kam event din biki bai taba burgeta ba.

Hajiya Laila da kanta ta iso birnin tarayya domin gyara amarya Maimoon. Ko nan da tsakar gida bata fita. Fatarta ta yi kyau sosai ta murje ga laushi har wani tsantsi ta ke yi. Gashi shima gyara na mussaman ake mai. Kamshi kuwa ba'a magana abu ya zo ga ma'iya.

Hajiya Ummi uwar amarya itama tana ta nata shirye-shiryen. Tare da Maman Anwara su ke komai, ita ce idonta a garin.

Yanzu haka dawowar su daga kasuwa kenan. Daki ta nufa ta yi wanka. Fitowarta ta samu Baffa zaune a bakin gado.

"Ahh ahh Ummi ya na ga sai kyalli kike yi sai ka ce ke ce amaryan?"

Ummi ta sadda kai cikin jin kunya. "Banda zolaya Baban Mu'azzam."

"Dagaske na ke yi."

Hakan ya kara bata kunya ta yi murmushi. Bayan ta shirya ta samu wuri kusa dashi ta zauna. Baffa ya mika mata jaka dake dauke da takardu. "Iyayen amarya har sun bugo kati."

"Masha Allah, abu na ta matsowa. Allah Ya kai mu da rai da lafiya, Ya nuna mana na 'yan baya."

"Ameen. Zuwa jibi zan tura wasu Kaduna idan Allah Ya yarda."

Ummi ta jinjina kai. "Sai ka bada guba biyar akai gidan Bello."

Da mamaki Baffa ya kalleta. "Gidan Bello kuma?"

"Kwarai dagaske," Ummi ta gyada kai. "Ai ba zai yi yu ba a ce ba'a fada musu Maimunatu za ta yi aure ba."

Baffa ya dan yi jim bai ce komai ba daga karshe ya ce, "Kina ganin idan an yi haka ba zai janyo wata matsala ba? Kin san halin su, bana so su zo su bata  mana taro. Su batawa Maimunatu ranan farin cikin ta, sun kuntata mata da yawa."

"Kwantar da hankalinka Baban Mu'azzam duk hakan ba zai faru ba. Da kenan. Da da yanzu kuma ba daya ba, komai ya chanza."





***



A hankali matafiya ke fitowa daga jirgin da ya sauka a tashar jirgin (Kaduna International Airport) da ke Kaduna. Minti goma kenan da isowarsa daga (Murtala Muhammad International Airport) dake Lagos.

A cikin fasisjojin da ke fitowa daga (terminal) akwai wani matashi sanye da wando (chinos) kalar kasa da riga mai dogon hannu. A kafadar hagu ya rataya jaka sai kuma akwati da ya ke ja da dayan hannun.

Babu wanda ya san dan zuwan shi dan haka babu mai tarbarsa a waje. Wurin masu motoci ya nufa, bayan sun gama ciniki a ka sa kayan shi cikin mota su ka hau hanya.

Sam bai shirya dawowa kasar nan yanzu ba. A yanda ya tsara sai ya gama karatun PhD dinsa na shekara uku sannan ma ya fara tunanin dawowa.

A kofar gida aka ajiye shi ya fito da kayan ya shiga ciki bayan ya sallami mai motan. Ya na shiga idanunsa su ka nufa bangaren BQ din da ke gidan. Take ya ji wani irin daci a ransa. Wurin a kulle duk ya yi kura. Kai ya girgiza ya cigaba da takawa.

Yana shiga falon ya ji an yi ihu. "Hamma Ashmaan!"

Da gudu Jasrah ta zo ta rungume shi, sai kuma ta sa kuka. Hannu ya sa yana dan bubbuga bayanta. Nema ta ke yi ta sa shi kukan shima. Da kyar ya samu ya lalleshe ta ta yi shiru.

Ihunta ne ya sa sauran 'yan gidan fitowa. Sun yi mamakin ganin shi, nan wurin ya dauki ihun murnan. Dan uwa ko ya ke da dadi.

Mommy ma harda kwallanta dan ta yi kewar danta sosai. Daddy ya fita amma nan da awa uku su ke tsammanin dawowarsa.

Jasrah ce ta je ta gyara mai dakin shi cikin gaggawa. Fauziya da Radhiya kuma su ka shiga kicin don saman mai abunda zai ci.

Bayan ya yi wanka, ya ci abinci sannan ya hau gado domin hutar da gajiyar da ke tare da shi.

Tare da Daddy su ka tafi masallaci sallar magriba. Daddy ma sosai ya ji dadin zuwan Ashmaan din dan sam bai taba tsammanin zai zo nan kusa ba.

Da suka dawo Daddy ya haye sama ya barsu a falo ana hirar yaushe gamo. Ashmaan ya aiki Jasrah daki ta dauko mai jaka ya ba kowa tsaraba.

Takalmin da ya siyowa Jasrah ashe kala uku ya siyo a maimakon daya. Ya saba idan ya tashi iri daya ya ke siyan mata ita da Mimi da Sadiya.

Sai kawai ya mika mata duka ukun ba tare da ya ce komai ba. Fauziya da Radhiya suka dungure mata kai ita kuma tana ta yi musu dariya wai itace 'yar gaban goshin Hamma.

Bayan minti talatin sai ga kiran Daddy Ashmaan ya same shi a sama. A ofis dinsa ya same shi. Ba tare da bata lokaci ba Daddy ya sanar da Ashmaan komai da ake ciki duk da ya fada mai wasu abubuwan tun ya na chan.

"Daddy kana ganin Lamido group ne kadai mafita?"

"Kwarai kuwa," Daddy ya gyada kai. "Domin kuwa na yi bincike akan sauran kamfononin da ke haka, Lamido group kadai ne su ke barin tsoffin CEOs din su cigaba da aiki kuma percentage din da suke karba baya da yawan na sauran. Abunda su ke yi shine za su saka ma'aikacin su aiki ta bayan fage tare da ni kenan a misali, har sai na gane yanda suke gudanar da kasuwancin su. Bayan nan zan cigaba da aiki na yanda na saba ina fitar musu da na su (percentage) din. Idan an kwana biyu za su waiwayo dan yin bincike da sauran su."

Kai Ashmaan ya jinjina. Tabbas hakan ne kadai Daddy zai tsira da abun arziki. "Har yanzu ba ka samu appointment din da su ba?"

Kai Daddy ya girgiza cike da takaici. "Har yanzu fa. Bin ka'ida ne da su."

Hakan ya ba Ashmaan dariya amma ya dake. Daddy ya saba bada cin hanci a biya mai bukatun shi ta ke yanke. Ya san tabbas mahaifinsa bai bi ka'idar ba shi yasa har yanzu shiru.

"Me zai hana muje mu ga mai su ke so ayi. Gwara a yi yanda su ka ce din dan lokaci na ta tafiya kan ka ce mai an makara lokaci ya kure."

"Hakane. Idan ka huta sai ka shirya mu je."

Kwanan shi uku cikin gida baya fita ko ina. Kullum a falo ya ke yini tare da 'yan uwansa. Ya zauna sun yi magana sosai ta fahimta, duka ya ji matsalolin su kuma in sha Allahu zai yi kokarin magance musu su. Musamman Jasrah, shekara mai zuwa zata fara makaranta da yardan Allah.

"Hamma yaushe za ka koma?" Radhiya ta tambaya.

"To, har kin kosa in tafi ne?"

"A'a, kawai dai ina tambaya ne."

"Yawancin classes dina zan iya yin su online, so ba yanzu ba tafiyata gaskiya."

"Hakan ma ya fi." Inji Mommy.

Sallamar namiji su ka jiyo daga waje. Ashmaan ya fita dan ganin waye. Bai dade ba sai gashi ya dawo da bakar leda a hannu.

"Sako ne daga Abuja. Akwai wanda ya ke tsammanin sako?"

Kowa ya girgiza kai. Mommy ta ce, "Bude ka gani menene a ciki."

Da envelope ya fara cin karo. Irin envelope din da ake saka katin biki a ciki. Hakanan ya ji bugun zuciyarsa ga tsananta. Hannu na rawa ya ciro guda daya.

Komai ya dauke mai a lokacin da ya karanta abunda ke rubuce kan katin. Bai san lokacin da ya yarda ledar ba. Yana jin Mommy na lafiya amma ina bai ma gane abunda ta ke cewa.

Wani irin sara ya ji kan shi na yi mai. Da sauri ya samu wuri ya zauna dan falon ya fara juya mai.

"Wai me aka rubuta haka?" Mommy ta sake tambaya.

Jasrah ce ta yi saurin daukan katin da ya yarda. Itama saida gabanta ya fadi.

"Kema kin yi wani shiru. Wai menene?"

"Katin daurin aurene." Jasrah ta ce tana kallon Ashmaan.

"Daurin auren wa?"

"Adda Moon."












🌚🌚🌚 jama'a!

Mu hadu a chapter na gaba💃🏻



~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro