Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

BABI NA ARBA'IN DA SHIDA











~
BABI NA ARBA'IN DA SHIDA
~







Jirgin kasa da ya taho daga Abuja ya iso garin Kaduna da misalin karfe hudu da rabi na yamma. Tuntuni motocin da zasu dauke su su ke filin jirgin, jiran isowarsu su kawai su ke yi.

Motoci uku ne tunda gayyar 'yan kawo amaryan ba su da yawa. Iyaye maza sun ce ba sai an taho da yawa ba. Anti Maryam da Anti Rukayya ne tare dattijai biyu daga dangin Jaddati da dangin mahaifin su Baffa sai su Adda Salma.

Gidan Alhaji Abdur-Rahman Hambali cike ya ke da jama'a da suka taru domin murnar auren tilon dan sa namiji Dr. Sayfullah Abdur-Rahman Hambali.

Tun daga bakin titi yara su ka biyo (convoy) din motocin kasancewa a hankali su ke tafiya. Dalleliyar Marsandi ce a tsakiya wanda amarya ke ciki. Mutane sun zagaye motar tun kafin su tsaya sai dai babu mai iya hango kowa a ciki sai dai kan su dalilin (tinted glasses) din motar.

Tuni gurin ya karade da guda. Anti Maryam ce ta riko Maimoon da ke lullube da haddadiyar laffaya kanta a rufe. Mami ta yi musu jagora su ka isa sashen Ammah. Nan dinma cike ya ke da mutane amma ta waje, cikin babu cunkoso wurin a gyare a tsabtace.

Tun isowarsu Ammah ke ta murmushi. Ta sha gayunta cikin atamfa ja da babban mayafi fatarta na sheki kaman ba na tsohuwa ba. Zaune a kusa da ita kuma 'yan uwanta ne da 'yan uwan mijinta marigayi.

"Masha Allah! Masha Allah, maraba sannun ku da zuwa."

A kan lallausan kafet din da ke shimfide a falon Anti Maryam ta zaunar da Maimoon. Manyan su ka zauna kan kujerun yayin da 'yan matan amarya su ka zauna a kasa.

Gaisawa aka yi cike da girmama juna da karamci. Bayan an gama gaisuwa kuma aka yi addu'a inda aka roka ma ma'auratan zaman lafiya da zuri'a dayyaba.

"Alhamdulillahi da Allah Ya nuna mana wannan rana. Allah Ya sa rai aka wa. Allah Ya ba su zaman lafiya mai daurewa." Anti Maryam ta yi addu'a duk aka amsa da Ameen. "Ammah ga diyar ku nan mun kawo muku domin kuwa Maimunatu yanzu ta zama ta ku..."

"A'a," Ammah ta katse ta tana dariya, "ni dama chan Maimunatu tawa ce. Yanzu dai Saifullahi ya samu ta zama ta shi. Kinga ma matso nan kusa dani Maimunatu."

Duka aka yi dariya Maimoon ta matsa kusa da ita aiko Ammah ta rungumota jikinta. "Saifullahin ma ya yi wasa sai in hana shi ita, Maimu ai tawa ce."

Anti Maryam ta cigaba da cewa, "Alhamdulillahi hakan ma ya yi daidai. Maimunatu dai 'yar ku ce duk abunda aka ga ta yi ba daidai ba a gyara mata. In na fada ne a tsawatar mata domin yarinya ce sai da kwaba."

"Duk an zama daya," daya daga cikin dangin ango ta ce. "Yanda za mu yi wa sauran duka haka za'a yi mata, ai da na kowa ne."

"Hakane kam," Ammah ta jinjina kai. "Tun haduwarmu ta farko na yaba da halayenta nagartattu. Aure dai ibada ne yanzu kin baro karkashin iyayenki kin dawo karkashin wani. Yi na yi bari na bari. Sayfullah ya zama ke kin zama shi ku yi kokarin tafiyar da rayuwar ku cikin tsari, so, kauna da mutunta juna. Ku hada kan ku kar ku yarda wani ya shiga tsakanin ku, ku adana sirrikan ku. Ku zama abokai aminan masu neman shawaran juna. In zama ya yi zama dole wani ya sabawa wani wani ya hakura domin shi aure idan babu hakuri baya kai labari. Ku din mutane ne kuma dan Adam ajizi ne saboda haka sai an yi hakuri da juna. In ke ce da laifi kada ki ji nauyin bada hakuri. Kar ku yarda ku kwana kuna fushi da juna. Allah Ya yi muku albarka, Allah Ya kare ku daga dukkan sharri. Allah Ya bada zaman lafiya mai daurewa."

Ana haka ne Hajiya Zuwaira mai dakin Alhaji Abdur-Rahman ta shigo. Sama sama ta gaisa da mutanen wurin ta samu wuri daga gefe ta zauna dan ko cikin falon bata ida shiga ba.

Wata da ta ke kanwa wurim Jaddati ta ce mata ta matso kusa ta ga fuskar amarya. Yatsine fuska ta yi ta tabe baki. "Ai Gwaggo da ya ke fuskar ba bakuwa ba ce a wurin mu, da ai kitso ta ke yi mana."

Wurin ya yi tsit da furucinta. Ita ko ki a jikinta sai ma hura hanci da ta ke yi. Mami ta girgiza kai cike da takaici, cikin son karkata zance ta ce Ahlaam da Nusayba su kai amarya da kawayenta masaukin su. Ita kuma ta mike ta ce wa su Anti Maryam bismillah su biyo ta.

Ahlaam ba ta zauna cikin su ba da suka isa saboda kunyar abunda mahaifiyarta ta yi. Nusayba ma ta bita saboda wani dalili nata itama.

"Amma matar chan an yi 'yar rainin wayo," Safara'u ta yi kwafa. "Ki ji 'yar duniya."

"Maimoon mai za'a miko miki? Ga abinci chan kan (dining table)." Adda Salma ta tambaya saboda kar maganar da Safara'u ta dauko ta yi tsawo. Itama abun ba karamin haushi ya bata ba amma yanzu ba lokacin yinta ba ne.

"Ina so in shiga bayi," ta bata amsa. Sam abunda Hajiya Zuwaira ta yi bai dame ta ba. Dan wannan ba komai bane a wurinta.

Daya daga cikin dakuna biyu da ke sashen ta shiga.

Alamu sun nuna gidan sabon gini ne da ba'a taba shiga ba. Ta gefen gidan ya ke da get din sa ta waje sai kofa da ke sada wurin da (main house) din.

A hankali ta warware laffayan ta shiga bayi, bayan ta gama abunda za ta yi ta koma falo. Kuloli ne guda biyar dauke da abinci kala daban-daban sai wasu kulolin masu nama da kifi a ciki.

Waina da miyar taushe ne ya ba Maimoon sha'awa. Sosai ta ci abinci dan rabonta da abinci tun da safe shima ruwan tea kawai ta sha. Bata san yunwar da ta ke ji ta kai haka ba saida ta fara loma. Har saida ta yi kari sannan ta kora da kunnu aya mai sanyi da ya ji kayan hadi.

Da zata samu dama gado kawai zata bi ta kwanta dan a matukar gajiye ta ke ga kanta da ke ciwo saboda kuka kashi-kashi da ta yi.

"Maimu ta shi a gyara laffayan dan yanzu za ki ga an fara zuwa ganin amarya," Habiba ta fada. Ta na ko rufe baki sai ga bugun kofa. "Kin gani ko."

Adda Salma da ke kusa da kofar ta bude. Daga sama sai ga Kydah, Anwara, Mimi, Sadiya Nanah da Waahidah sun shigo. Da mamaki su ke kallon su Adda ta ce, "Ku kuma daga ina haka?"

"Tare da ango mu ke," Sadiya ta amsa daga inda ta samu wuri ta zauna. "Bayan kun tafi Hamma ya zo, da zai tafi ya ke tambayar mu ya bamu bi ku ba ko bamu san da budan kai da za'ayi ba. A wayance mu ka ce eh babu daman fada mai Baba ya hana. Aiko ya ce idan muna son zuwa mu shirya mu tafi tare da gudu kuwa mu ka hado kaya. Su Baba ba su hana tunda shi ya ce."

"Saura kiris a baro Ya Wara." Nanah ta yi dariya.

"Hmm! Ke dai bari da ina chan bakin ciki ya gama kasheni kowa na nan banda ni."

"Me ya faru?" Habiba ta tambaya.

"Mama mana. Wai ban tambaya Babe ba kuma wai banda lafiya. Ai da sauri na aika mai text. Da ya so shima ya kawo mun ƙabli da ba'adi na nuna mai sam ban yarda ba, dan babu yanda za'ayi ayi shirin biki da ni tun daga farko kuma a ki karasawa da ni. Da kullun naga hotuna sai na yi mita kuwa."

Suna ma Anwara dariya Maimoon ta bar falon ba tara da sun lura ba. Dakin da ta shiga dazu ta koma ta zauna a madaidaicin gadon da ke tsakiyar dakin.

Kiran Sayf ne ya sake shigowa wayan. "Assalamu Alaikum Matar Sayfullah."

Hannu ta sa ta rufe fuska ta na mai jin kunya. "Wa'alaikumus salam Habibi kun iso lafiya?"

"Eh Alhamdulillah, mu na gidan Habib. Gamu nan zuwa bayan isha'i. I can't wait to see my beautiful wife."

Falo ta koma ta same su suna hira ana kyakyata dariya. Dadi ne ya mamaye ta da tuna duk sun taru ne a nan don tayata murna a ranan da ta ke da matukar muhimmanci a rayuwarta.

Adda Salma da ke zaune kan kujera Maimoon ta kalla. Tabbas shigowar baiwar Allah nan alkhairi ne a rayuwarta.

Kiran sunanta ta yi Adda Salma ta dago kai tare da mika ma Maimoon hankalinta. "Na'am?"

"Uhmm dama ya ce zasu zo bayan Isha'i."

Kai Adda ta gyada. Habiba ta tsare Maimooon da ido. "Waye shi da ya ce zasu zo? Baida suna?"

"Habiba ki kyale mana Adda Moon din mu." Anwara ta fada. "Kin sa mata ido."

"A'a wai dan mu ji. In ta ce 'shi' ta ya zamu gane wa take nufi? Ko ba haka ba?" Ta ce tana kallon Maimoon.

"Mijina," ta fada tana fur da idanun nan nata manya. "Mijina ya ce zai zo anjima."

Me Habiba za ta yi in ba dariya ba. Sauran su ka ce mata to ta ji sai ta kyaleta haka nan. Maimoon ta yi dariya itama.

Bayan ta yi sallah ta sa kaya. Leshi ne (blue) da aka tsantara mai dinki mai matukar kyau. Rigar (fitted) ce sai dai ba'a yi ta yanda zata kamata sosai ba har surarta ta bayyana.

Nanah ce ta gyara mata fuska. Fuskar nan sumul babu komai fatar ta tafi ko gargada babu saboda tsantsan gyara da ta sha. Kwalli aka sa ka mata da ya kara fito da kyawun idanunta da Sayf ke matukar so.

Waahidah ta daura mata dankwali sannan aka yafa mata lullubi daga kai har kasa.

Jin karan motoci ya sanar da isowar su. A daki suka barta kan gado lullube su ka fita falo.

Ango Sayfullah ya iso tare da Habib da 'yan biyu. Shi ba mai tari abokai bane, bayan su ukun nan duk sauran yana mutunci da su ne kawai, sai dai na wani ya fi na wani.

Kaman hadin baki shima (blue) din shadda ce a jikin shi ta sha aikin hannu. Sai dai na shi ya fi nata duhu. Ga hular zannan Bukar da ta sha rini ta shiga da kayan zaune das a kan sumar shi. Kayan sun kara haska farar fatar shi sosai.

Ango yana ta baza kamshi su ka shiga falon bakunansu dauke da sallama.

Gidan nan kyauta ne daga wurin Alhaji. Ya ga ana gyara amma bai san na me ye ba sai da aka gama Alhaji ya kira shi ya mika mai mukullan gidan. Komai an saka a gidan sai dai abunda ba za'a rasa ba.

Kyautar ta bashi mamaki matuka. Da ya sanar da Mami ta ce mai wannan kyauta ta nuna cewa mahaifinsa yana son ya rika zuwa gida, yana son dan sa a kusa da shi.

Bai taba tsammanin haka daga gare shi ba. Sai dai bai samu damar zama ya yi dogon nazari a kai ba.

Falon sai kamshin turare da ba shakka Maimoon ta hada ya ke. Zazzaune suka same su sai dai babu fuskar da Sayfullah ke ta daukin gani.

Gaisawa aka shiga yi Sayf na ta kallon kofa yana jira ya ga fitowarta.

"Baba Sayf daina waige-waige ba ganinta za ka yi ba," Adda Salma ta fada tana murmushi.

"Tabbas, sai ka biya kudi masu tsoka kafin za ka ga amarya." In ji Safara'u.

"Nawa?" Hussein ya tambaya.

Budan bakin Habiba ta ce. "Miliyan goma ne ba tsada."

Baki Hussein ya bude. "Haba baiwar Allah. Miliyan goma fa?"

"Kwarai kuwa. Tambaye shi ka ji ya san tafi haka ai."

Murmushi kawai Sayf ya yi. Hussein ya dage wai su yi ciniki da Habiba. Shi Sayf so kawai ya ke ya yi tozali da kyakkyawan fuskar matarsa.

"Amma dai miliyan goma ya yi yawa Hajiya. Mun san Antin ta mu tafi haka amma a taimaka Yayan na mu talaka ne."

"Toh miliyan tara da rabi, mun rage."

Hussein ya rike haba. "Amma dai ke 'yar Kano ce ko?"

"To wa ya sani? Mu ajiye batun Kano a gefe, kawai ku saki kudi idan kuna son ganin amarya."

Haka su kai ta yi su biyun kaman su kadai ne a dakin daga karshe Habib ya ce zasu bada daidai gwargwado a basu akant lamba. Sai aka ce ya tura a na matarsa kawai tunda ita ce babba.

"Toh alert ya shigo, Baba Sayf kana iya shiga ka ga matar ka."

Sayfullah bai tsaya jin wani karin bayani ba ya shiga dakin da zuciyarsa ke ce mai ta na ciki. A nan ya yi kyakkyawan gamo.

Zaune ta ke a tsakiyar  gadon ta rungume kafafuwanta. Kamshin turaren shi ne ya sanar da ita ya shigo dakin tun kafin ya yi sallama. Take bugun zuciyarta ya kara tsananta.

"Assalamu alaikum wa rahmatullah Raihanatul Qalb."

"Wa'alaikumus salam wa rahmatullah," ta amsa a hankali.

Bata dago kanta sai ji ta yi ya kama karshen mayafin ya daga a hankali. Dukda haka bata dago ba saida ya sa hannunsa kan habarta ya dago mata kai.

Dukkan su sai da tsigar jikin su ta tashi da idanuwansu su ka sarke da na juna. Ita ta yi saurin janye idanunta saboda ba zata iya cigaba da kallonsa haka ba.

Hakan ya ba Sayfullah damar kallon fuskarta tsaff. Daga girarta zuwa hancinta komai saida ya tabbatar ya haddace.

"Fatabarakallahu ahsanul khaliqin," ya furta har yanzu idanun shi ba su bar yawo a kan fuskarta ba. "Mahnoor dago ki kalle ni."

A hankali ta dago kanta sai dai idanunta a runtse su ke. Murmushi ya yi bai ce komai ba har ta bude su a hankali.

Sayfullah ba zai taba gajiya da kallon idanunta ba. Su ya fara gani su ka rikita mai kwakwalwa su ka hana shi sukuni har sai da ya gano mai su. Yau gashi Allah Ya amsa addu'ar shi ta zama matarsa.

"Hi, Mrs Sayfullah," ya furta a hankali kaman mai rada. Hannunsa biyu ya mika mata ta saka nata a ciki ya rike su gam yana shafa lallenta da manyan yatsun shi. "Maimoon ban san da wasu kalamai zan yi amfani da su ba dan yi miki bayanin irin farin cikin da na ke ciki. Kawai abunda na sani shi ne ban taba tsintan kai na a wannan yanayin ba. Allah Ubangiji ya bamu zaman lafiya. Allah Ya bani ikon rike ki yanda ya kamata, Allah Ya bani ikon sauke nauyinki da ya rataya a wuyana."

Tuni hawaye sun fara zubowa daga idanunta tana amsawa da Ameen. Babban yatsar shi ya sa ya share mata hawaye.

"Allah Ya bani ikon yi maka biyayya. Allah Ya bamu hakurin zama da juna Ya kuma kare mu daga dukkan sharri."

A hankali ya mike ya tallabo fuskarta da hannuwansa sannan ya duka ya sumbaci goshinta. "Ameen Noor."

Hannun shi cikin nata su ka fita falo. Nan fa aka fara tsokanarsu mussaman Hussein da Habiba. Sayf ran shi kal baki ya ki rufuwa. Maimoon ko kunya ta lullubeta ta boye fuskarta a jikinshi.

Wahidaah ta ce su tsaya a yi hoto. Nan aka yi musu dan karamin (photoshoot) dama Hassan ya taho da (camera) ya barta a mota dan haka  ya dauko. Bayan an yi musu su kadai sauran suka shiga.

Bayan an zazzauna Habib ya yi addu'a. Yana taya abokin shi murna sosai kuma yana fatan kwanciyan hankali da natsuwa da bai samu a baya ba ya same su yanzu.

"To Anti Amarya ga amanar yayan mu nan mun baki," in ji Hussein. "Ki kullan mana da shi sosai dan Allah. Ina son in ga ya yi tumbi nan da 'yan watanni. Kuma dai nasan an yi ta fada miki haka amma zan kara maimaitawa,  a yi hakuri da shi."

Hannu Sayfullah ya sa ya talle mai keya. Ana ta dariyar barkwancin Hussein. In banda kama babu abunda na su ya zo daya da Hassan. Shi daga gani bai da hayaniya amma Hussein tunda ya shigo ya ke zuba babu kakkautawa.

Badan Sayf ya so ba suka tafi. Gashi kowa na wurin babu daman yi mata sallama yanda ya so. A mota Hussein sai kwasarsa ya ke yi amma ko a jikin shi. Babu wani abu a yanzu da zai iya gusar da farin ciki da ya ke ciki.

Itama Maimoon din kusan haka ne. 'Yan uwanta sun sa ta gaba da tsokana. Anwara ta bada labarin lokacin da Sayf ya kawo sakon Ammah.

"A nan fa aka kulla abun. Zama a iya cewa ni ce sila dan ni na yi (insisting) ta kai mai (cake) din da mu ka yi baking ranan."

"A'a fa Ya Wara," Nanah ta girgiza kai. "Ba ke kadai ke da (credit) ba, ni fa na yi (cake) din."

Adda Salma na jin su tana girgiza kai.

"Kin tuna sanda ya zo Zaria bata da lafiya...."

Ita dai nata murmushi kawai. Duk bama jin su ta ke yi ba tana chan tana tunanin mijinta.




****


Washegari da karfe sha daya aka yi budan kai. Wurin ya kayatu sosai ya sha (decoration). Mutane sun yi kara sosai domin gidan cike ya ke da jama'a. Maman Adda Salma tazo tare da kannen Adda, 'yan gidan su Habib ma sun zo. Haka ma 'yan gidan su Habiba da 'yan gidan su Safara'u duk sun zo.

An yi budan kai kaman yanda aka saba a al'adance. Dangin ango sun nuna bajintarsu sun bada kudade masu tsoka domin a bude musu fuskar amaryarsu.

Farin ciki wurin Mami da Ammah ba'a cewa komai.

Duk hidimar da ake yi babu keyar Hajiya Zuwaira a wurin hakan kuma bai damu kowa ba.

Ikram da Amira da suka zo tare da kakarsu na makale gefen amarya akan gadon karfen da aka tanadar mata a matsayin wurin zama. Tunda su ka zo basu matsa ba.

Wasa wasa dangin su Sayf yawa ne da su dan tun tana rike fuska da suna har ta daina.

Ta sadda kai kasa tana duba waya ta ji an zauna gefenta. Daga kai da zata yi ta ga Jasrah zaune a wurin.

Mamaki ne ya hanata rungume Jasrah kaman yanda yarinyan ta yi har saida ta fara janyewa tukun ta ankara. Hannu ta sa ta riketa tana farin cikin ganinta.

"Ina wuni Adda Moon." Ta gaisheta murya na rawa. Sake rungumeta ta yi kafin ta janye ta ce, "Kin yi kyau sosai."

Yau (lemon green) din leshi ta saka mai manya-manyan zane. Lullube ta ke da laffaya da ya shiga da kayan.

"Lafiya lau Jasrah. Ya gida? Ya karatu?"

"Alhamdulillah. Adda na yi missing din ki sosai."

Jikin Maimoon ya yi sanyi ta ji babu dadi dan rabon da su yi magana har ta manta. Take ta yi alkawarin gyara hakan. "Nima na yi missing din ki Jasrah."

Chan sai ga Sadiya da Mimi sun yi murna sosai garin Jasrah dan kwata-kwata ba su yi zaton za ta zo din ba.

An yi taro lafiya an tashi lafiya. Su Anti Maryam jirgin karfe hudu za su bi. Duk yanda su Mimi su ka so a bari su sake kwana Anti Rukayya ta ce sam hakan ba zai yi yu ba dan har an siya wa kowa (ticket).

Da suka zo tafiya sai da aka yi koke-koke. Da daidai da daidai su ka rungume ta su ka yi mata sallama. Kydah ce karshe, a kunne ta rada mata, "To Adda Maimoon a kulla mana da yayan mu."

Tana ji tana gani duka su ka tafi su barta a nan. Wurin karfe shida bayan sun koma masaukin su su Habiba su ka fara hada kayan su suma.

"Ba dai tafiya za ku yi ba?"

"Tafiya za mu yi mana." Safara'u ta bata amsa. "Mai kuma ya rage Maimu? Ai biki ya kare."

"Haba Sapare ku bari sai gobe mana." Ta ce tana marairaice murya.

"Babu wannan zancen." In ji Habiba. "Kar ki damu mijinki na kan hanya."

Banza ta yi da Habiba ta juya wurin Adda Salma. "Amma Adda ke ba yau za ki tafi ba ko?"

"Ni ma mijina na chan ya na jirana."

"Kaiii dan Allah yanzu dukan ku tafiya za ku yi ku barni."

"Yanzu ma kuwa." Habiba ta ce tana zuge (zip) din jakarta.

"To at least ku bari sai ya zo mana."

"Ba fa zai zo ya same mu ba a nan Maimoon." In ji Adda Salma.

Haka suma tana ji tana gani su ka tafi su ka barta. Allah Ya so ta Ahlaam na nan. Itama ana kiran isha'i ta gudu.

Haka ta zauna jungum-jungum a gidan ita kadai. Bayan ta yi sallah ta gyara wurin duk da ba wani datti ya yi ba. An taho mata da turare dan haka ta kunna turaren wuta sannan ta sa wa kofar parlor din mukulli ta shiga bayi.

Wannan karon atamfa ta saka abun ta riga da sket dinkin ya zauna sosai a jikinta. Tana cikin daura dankwali ta ji a na kwankwasa kofa.

Dankwalin ta ajiye a gefe dan dama ta rasa ta ina zata fara daurawa. Gyale ta dauko ta yafa a kanta sannan ta nufa kofar ta murda mukulli ta bude.

Wani irin sanyi Sayfullah ya ji ya ratsa shi da ta bude mai kofa fuskarta dauke da murmushi.










🥹🥹🥹🥹🥹❤️❤️❤️😩






~Maymunatu Bukar💕

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro