BABI NA ARBA'IN DA DAYA
~
BABI NA ARBA'IN DA DAYA
~
Mutane da dama suna nunawa mutum kuluwa ba don sun son shi tsakani da Allah ba sai dan suna son wani abu daga wurin shi.
Alhaji Bello da Hajiya Suwaiba ba su taba fahimtan haka ba sai da mummunan lamari ya faru da su. Tunda Daddy ya biya bashin da ake bin shi komai ya chabe ya tawarwatse. Gaba rayuwar da suka saba da ita ta chanza.
Mutanen da suke gani duk duniya sun fi kowa son su, su suka fara janye jikin su. Har Abdulkarim wan Daddy da tare aka ci bashin dashi ya nuna sam bai san labarin ba.
Abokai da aminai da ake sharholiya da su duk sun guje su saboda dalilin da ya sa suke tarayya da su ya kare. Yanzu ba su da wani amfani a wurin su.
Tsakanin Alhaji Bello da Hajiya Suwaiba kwakwata babu kwanciyan hankali. Kullum cikin hayaniya su ke, ita ta saba a bata kudi ta yi ta zubda su yanzu kuma babu. Alhaji Bello yanzu dole ya koyi tattali, ita kuma ta nuna sam bata san wannan zancen ba.
Abun ya yi muni har sai da manya suka shiga ciki.
Haka dai ake lallabawa, yau da dadi gobe babu.
Alhaji Bello na zaune a falon shi na sama ya baza takardu Fauziya ta yi sallama ta shigo. Yatsine fuska ya yi, ko dagawa ya kalleta bai yi ba.
"Dama Daddy kawata zata yi aure shine na zo karban kudin anko?"
Tsaki ya yi a zuciya, yaran nan kaf halin uwarsu su ka kwaso. Kullum bani-bani. "Nawa ne?"
"Dubu ashirin da hudu kudin anko, sai kudin dinki da kudin kwalliya da lalle. Total zai kama dubu hamsin zuwa sama."
Ai Alhaji Bello bai san lokacin da ya ture takardun da ke gaban shi. "Amma ban taba sanin baki da hankali ba sai yau. Dubu hamsin zan dauka in baki saboda wani banzan biki. Toh bikin ma na hana zuwan shi. Fita ki bani wuri shasha kawai."
Cigaba da duba takardun ya yi yana ta mita shi kadai. Yara daga su har uwarsu basu san babu ba, ba su iya tattali da adana abu ba. Gaba daya basu san da kyar ya ke gudanar da gidan ba.
Banko kofar aka yi ba sai ya kalla ba ya san Suwaiba ce. Wato ta kai shi kara, zata zo ta same shi.
"Alhaji wai me ya ke damun ka ne? Babu dama ayi maka maganan kudi sai ka rufe mutum da fada. Idan yaran nan basu zo wurin ka sun karba ba ina kake so su je?"
"Kudi dai na ce bazan bada ba. Idan kuma ke da ita zaku danne ni ku kwata ne sai in gani."
Takaici kaman ya kashe Hajiya Suwaiba. Tsaki ta ja ta bar falon.
"Koma me ye, kudi ne dai bazan bada ba."
Takardun da ya ke dubawa ya dauko ya cigaba. Dukda tun dazu ya ke kallon su amma ya rasa abun yi. In har shekaran nan ta kare a yanayin nan ma'aikatan zata shiga (bankruptcy). Dole ne ya samu wanda zasu sa mai hannun jari a ciki.
Ya bi duk abokan kasuwancin shi amma kowa sai ya nuna ba haka ba. Gaba daya sun juya mai baya abun kaman hadin baki.
Har yau kuma bai samu appointment da Nasir Lamido ba. Ya yi iyakar bakin kokarin shi amma abun ya gagara.
Ko ta ina duniya ta yi wa Alhaji Bello zafi, ba'a cikin gida ba ba wurin aiki ba. Ko ta ina gara shi ake yi. Ga wannan yaron Ashmaan ya ki ya dawo, da yana nan da ya kama mai wasu abubuwan.
Tun barin Muhammad gidan shima ya saka kafa ya tafi, wai ya tafi phD din shi. Da abubuwa suka kwabe ya daina tura mai kudi ya zata zai dawo sai dai ina. Wai ya samu aiki a chan, dama ba shi ke biyan kudin makaranta ba, yana under scholarship ne.
Waya ya dauka ya kira Ashmaan din. Ya gaishe shi, Alhaji Bello ya yi sauri dakatar da shi. "Rike gaisuwar ka, tambaya dama na ke so in yi maka, ni da kai wa ya haifi wani?
"Daddy...."
"In kai ka haife ni sai in ji da zan baka umarni ka ki bi."
"Ba haka bane Daddy. Ka yi hakuri."
"Wani in yi hakuri, kasan irin mawuyacin halin da muke ciki? Amma saboda son kai duk haka bai dame ka ba, kai kana chan kasar turai cikin snow mu ko oho. Sakayyan da za ka yi mun kenan Ashmaan?"
A dayan bangare Ashmaan ya ji jikin shi gaba daya ya yi sanyi. "A'a Daddy, ka yi hakuri ka yafe mun. Inada wani project da zan yi presenting, ina gamawa zan taho in sha Allah."
"Yauwa toh. Allah Ya kawo ka lafiya."
Daga nan su ka yi sallama. Ashmaan ya kifar da kan shi akan pillow. A yanda ya tsara ba zai koma Najeriya ba har sai ya gama karatunsa, wato sai bayan shekara uku kenan.
Tunda ya zo garin nan ya na aiki akan (autopilot) ne. Ci, sha, bacci, karatu, shikenan. Gaba daya duniyan ta daina mai dadi. Ba ya da wani abu kuma da ya ke burin samu ko ya ke wa (fighting), kawai dai gashinan.
Rasa Maimoon ba karamin tabo ya yi wa zuciyarsa ba. Ba ya jin zai taba warkewa daga rashinta, har gobe ba zai taba daina son ta. Ta ya ma zai fara? Itace mace ta farko da taba janyo hankalin shi kanta. Bai taba son wani yanda ya so ta, ba ya ji kuma zai iya. Iyayensa sun sa ya rasa ta.
Sai da ya dage sosai ya iya cireta daga ran shi ya samu sukuni, ya dawo mutum. Amma har yau ya tuna wani irin ciwo na sukar zuciyarsa. Wani lokacin mai niqab zai gani, ko ya ji an yi maganan wani abu da ta ke so shikenan komai zai dawo mai sabo.
Da yana kiran Mimi su gaisa amma ganin haka na maida mai hannu agogo baya sai ya daina.
Shi yasa ma ba ya san komawa Najeriya, komai zai dunga tuna mai da ita ne.
Amma yanzu dole ya koma. Daddy na bukatar shi, duk da ba su jituwa shi mahaifinsa ne, kuma ya yi mai abubuwa da dama da bazai iya taba biyan shi ba ko da zai yi amfani da sauran rayuwarsa dan yin haka.
Tashi ya yi ya shiga bayi. (Studio apartment) ne ya kama da ke kusa da makaranta. In baya da lectures akwai wani restaurant da ya ke aiki a wurin. Suna biyan shi daidai gwargwado, da kudin da ya ke samu ya ke cida kansa a nan.
Shiryawa ya yi cikin riga da wando sannan ya dauko babbar kwat ya daura saboda sanyin watan Janairu. Inda ya ke aiki ya nufa, snow na saukowa kadan kadan.
Ya iske matar da zai amsa aiki a wurinta har ta tafi. Dan haka ya cire kwat din ya nannadd hannun rigarsa ya hau aiki.
****
"Jasrah wallahi kin raina ni. Zan ballaki a gidan nan!"
Jasrah na jin Radhiya ta gama masifanta ta tafi. Abubuwan a gidan su sai kara tabarbarewa su ke yi.
Duk alhakin su Baffa ne ke kama su ba komai ba. Tunda su ka bar gidan matsalan yau daban na gobe daban.
Ajiyar zuciya ta saki. Ta yi kewar su sosai da sosai. Musamman aminanta Sadiya da Mimi. Suna magana a WhatsApp wani lokacin amma ba sosai ba. Tunda su ka tafi ta lura sun janye jikin su. Bata ga laifin su ba, ko ita ce haka zata yi.
Karshe dai da su ka yi magana, Sadiya ta ce mata suna Abuja amma bata yi mata bayani ba. Tana da tambayoyi da yawa amma ta san ba huruminta ba ne.
Kasa ta sauka. Gaba daya gidan babu dadi. Da su Sadiya na nan ai baza'a ganta a nan ba ma. Ta kosa ta fara jami'a, har yanzu Daddy bai ce komai ba.
Tana cikin kicin Fauziya ta shigo. "Jasrah kalla nan, wannan ba Sadiya da Mimi ba ne?" Ta tambaya ta na nuna mata hoto a Instagram.
Karban wayan ta yi, hoton biki ne suna tsaye kusa da amarya. "Sune. Mai ya faru?"
Wani irin ihu Fauziya ta yi. "What?! Sune? Kin tabbata? Ki kalla da kyau."
"Na ce miki sune, ke baki san kamannin su bane."
"No way!"
Jasrah ta yatsine fuska tana kallonta. Radhiya ta shigo kicin din itama, Fauziya ta nuna mata hoton.
"Kai! Me ya kaisu wurin?"
"Wai wani wuri? Me ye kuke cewa? Kun san amaryan ne?"
Harararta Fauziya ta yi. "Ba ki san Anwara Lamido ba? Wurin bikinta ne fah!"
Tabe baki ta yi. "Oho ke kika santa."
Plate din abincinta ta dauka ta yi gaba. Tana jin su suna mamakin yanda aka yi su ka je bikin. Radhiya ta ce tambayan da ya kamata ma su yi shi ne me su ke yi a Abuja.
Jasrah ta girgza kai. Sun bar musu gidan amma har yanzu ba'a kyale su ba.
Palo su ka biyo Jasrah. "Kin san wani abu ko?" Inji Fauziya. "Me ye hadin su da family din Lamido?"
"Oho."
"Kar ki mana wasa da hankali mana Jasrah." Radhiya ta ce a fusace. "Nasan kina magana da su."
"Bana yi, ko ina yi ni ban san mai kuke so in ce muku ba. Su waye wani Lamido family? Ni ban taba jin su, dan haka ku kyale ni. Idan ma suna da hadi dasu ina ruwanku? Ba sun bar muku gida ba koma meye kuke stalking din su a Instagram?"
"Ba ki da hankali," Fauziya ta ce. "Muje Radhiya sai na gano abun nan. It's just not adding up, abun bai yi making sense ba."
•
•
•
•
•
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro