BABI NA ARAB'IN DA BAKWAI
~
BABI NA ARAB'IN DA BAKWAI
~
A hankali ya taka ya shiga cikin falon idanun shi a kan ta. A yanzu da kallonta ya halarta a wurinsa ba ya jin zai iya dauke idon shi daga kanta. Bare bai saba ganin fuskarta haka ba babu niqabi ba.
"Sannu da zuwa."
Hannu ya mika mata kaman yanda ya yi jiya. A hankali ta daura a kan tafin hannunsa. Hannunta ya kasance karami akan na shi. Yatsun su ya hade wuri daya ya ja ta zuwa falo.
"Ina zuwa," ya ce mata sannan ya shiga dayan dakin. Kayan shi na nan saboda haka watsa ruwa ya yi ya saka jallabiya mara nauyi.
Mota ya je ya dauko ledoji ya dawo ya shiga kitchen ya dauko (tray), (plate) da kofi. A kasa ya zauna ya tankwara kafafuwan shi ya bude ledojin da ke fitar da kamshi tun dazu.
Gassashiyar kaza ce a cikin leda daya, sauran kuma tsire ne mai hade da bandashen gurasa sai balangu da kuma (fresh milk). A kofi daya ya tsiyaya madaran sannan ya dauko (plate) din ya diba komai a ciki.
Bismillah ya yi ya sha madaran sannan ya mika mata kofin. Bai fi kurba biyu ba ta yi ta ajiye.
"Oya Noor sauko," murmushi ya yi jin bata amsa ba. Tunda ta yi mai sannu da zuwa ba ta sake magana ba ta zama kaman wata kurma. Zama ta yi kaman yanda ya yi tana wasa da yatsunta.
"Ahhh," ya ce yana mika mata gurasar da ya dibo da hannunsa baki. Ya lura yanda hakan ya bata kunya amma ya share. A hankali sai ya cire mata kunyan nan gaba daya.
Sai da ta dauki dan lokaci kafin ta bude bakinta ya sa mata. Haka ya cigaba da bata a baki kaman karamar yarinya. Yafi bata gurasan saboda yasan yanda ta ke so sosai.
Kai ta girgiza mai bayan wani dan lokaci alaman ta koshi. "Last one, ci wannan shikenan."
Madaran ya sake bata. Sai kuma ya langwabar da kai yana marairaice fuska. "Wayyo ni, ni kuma ko wa zai bani a baki?"
Bata san lokacin da ta yi dariya ba. Gyalenta ta janye ta sa hannu ta dibo ta mika mai. Har ya bude baki ya rufe. "Wannan wuya na sai ya kage kin yi nisa, dawo nan," ya ce yana buga gefen shi.
Dan nesa da shi ta zauna. A nutse ta bashi amma fa duk a takure ta ke dan kallonta ya ke yi ba ya ko kiftawa. "To ka daina kallo na," ta ce cike da shagwaba.
"Kallon ki ya fi mun a kan cin abincin," ya ce da dariya.
"Ba wani nan," ta turo baki gaba ta cigaba da ba shi. Bai ci da yawa ba ya ce mata ya koshi. Kafin ta motsa ya kamo hannunta na dama ya side shi tas.
Wani irin lumfashi ta zuga. Ya na sakin mata hannu ta yi kitchen da sauri kaman zata kifa, daman kwanon na hannunta.
Ta na isa ta saki wata ajiyar zuciya tana dafe kirji. "Wayyo Allah!" Zuciyarta na bugun da bata taba yi kaman zata balla kirjinta ta fito.
Sai da ta dan saita kanta ta koma falon dukda har yanzu bugun zuciyarta ya ki ya dawo daidai. Ga cikinta da ke mata wani iri kaman ana yamutsa mata 'ya'yan hanji.
Sayf ma ya shiga bayi ya wanko hannunsa. A dan nesa da shi ta zauna, fiye da na dazu. Bai ce komai ba sai ma hira da ya dauko irin hiran da ake kira da (small talk) dan ta saki jikinta.
Hakan ko ya faru ta saki jiki su ka yi hira kaman yanda su ka saba. Ganin tana hamma ya ce to su tashi su je su kwanta. Sai dai da suka isa kofar dakin da ta kwana bai shiga ba ya tsaya a bakin kofa.
"Sai da safe Noor."
Daga gani ba haka ta zata ba saboda yanda ta dan zaro ido. Murmushi ya yi kawai ya share.
Maimoon ba gajera ba ce amma duk da haka Sayfullah ya fita tsawo sosai. Dan durkusowa ya yi ya sumbaci goshinta. "Mu kwana lafiya."
Ta dade kafin bacci ya dauketa. Idan ta rufe ido abunda ya faru kawai ta ke tunawa kaman tana kallon bidiyo.
Saboda gajiya tunda baccin ya dauke ta ko juyi bata yi ba. Hakan ya sa ta makara sallar asuba. Ji ta yi kaman ana shafa mata fuska, firgita ta yi ta mike da sauri.
"Sorry, I didn't mean to startle you," ya ce. "Tashi ki yi sallah."
Kafin baccin ya sake ta har ya fice. A daddafe ta yi sallah, tana idarwa ta haye gado ba ita ta farka ba sai wurin karfe goma. Wanka ta yi ta shirya cikin atamfa. Har ta kai kofa ta dawo ta yafa gyale ta fita.
A falo ta same shi yana kallo. Bai lura da ita ba dan haka ta yi amfani da damar ta kalle shi sosai. Gilas din shi na zaune kan karan hancinsa. Sajensa ya kwanta luff luff a fuskarsa.
Fatabarakallahu ahsanul khaliqin.
Ganin yana shirin juyowa ya sa ta yi sallama da sauri dan kar ya ganta tana kare mai kallo.
Sayf da tun dazu ya ganta tsaye ya yi murmushi ya mika mata hannu kaman yanda hakan ke son zaman mai al'ada. Zaunar da ita ya dab da shi, ga kungunsa ga nata.
"Raihanatul Qalb, kin tashi lafiya?"
Kai ta gyda mai. "Ina kwana."
"Lafiya lau. Ga abinci Ammah ta aiko mana dama ke na ke jira ki tashi...a'a zauna abin ki." Ya ce da ta yi yunkuri mikewa.
Wainar da ta ci ranan da su ka zo ne aka sake kawowa. Labarin dadin wainar ta ba shi yayin da ya ke zubawa. "Idan na ci na ji ba dadi ni da ke ne."
"Impossible! There's no way ba zai maka dadi ba."
Sayf ya ji dadin wainar sosai harda kari. Maimoon ta rika mai dariya. Janyota ya yi jikinshi zai mata chakulkuli. Tana kokarin kwatar kanta tana dariya lokaci daya kuma su ka yi shiru suna kallon juna.
"Wa na kama?" Ya furta a hankali ya na janye gyalen da ya rufe mata fuska. Dan runtse ido ya yi yana shakar daddadan kamshi da ke fita daga jikinta.
Bugun kofan da aka yi ne ya zabarur da ita ta yi sauri kwace jikinta. Mayafinta ta gyara ta nufi kofar domin budewa.
Jingina ya yi da kujerar da ke bayan shi yana furzar da iska. Da ya yi niya su yi kwana biyar a nan saboda Ammah amma da dukkan alamu tattara matarsa zai yi su tafi.
Tun daga lokacin mutane su ka yi ta shigowa. Da yawa ganin amarya su ka zo yi. Daga karshe ma barin gidan ya yi gaba daya. Wasu mutane sai a hankali, sai a ce wai sai an leka ko ina an gani.
Zuwa yamma yawan mutanen da ke gidan sun ragu, yawanci wanda su ka rage 'yan uwa ne. Sashen Ammah ya nufa inda tsoffin nan su ka yi ta tsokanar shi.
"Ba dai baro ta ka yi ita kadai ba Sayf?" Mami da shigowarta kenan ta tambaya.
"A'a, Ahlaam da Nusayba na chan."
"Yauwa. Mu gobe zamu koma idan Allah Ya kaimu."
"Ina ga muma gobe za mu tafi kawai."
"A'a fah Sayf," Ammah ta ce. "Ba haka mu ka yi da kai ba."
"Ammah in sun zauna nan me za su miki? Ki bari kawai su tafi. Ko mai gidan na ki kike so a kusa da ke." In ji wata 'yar uwarta.
"A'a ni me zan yi da wannan. Su kama hanya su tafi Allah Ya kiyaye."
Bai dade ba ya tafi. Ya shiga ya samu su Ahlaam suna goge falo. Tambayan su ya yi ina Maimoon su ka ce mai tana daki. Ya sameta ta na linke kaya.
"Ka dawo, sannu da zuwa."
"Yauwa," ya amsa ya na zama a bakin gado. "Bakin sun kare?"
"Mmm duk sun tafi."
"Gobe in Allah Ya kaimu zamu koma Abuja, da fatan hakan ya yi mi ki?"
"Ya yi, Allah Ya kaimu."
A daren ranan su ka shiga gaida iyayen Sayfullah. A lokacin ne Maimoon ta fara ganin Alhaji Abdur-Rahman ido da ido. Kaman da Sayfullah ya ke da mahaifinsa ya baci. Sai ta ji kaman tana kallon Sayf ne nan da wasu shekaru.
Ya karbe su hannu bibbiyu, mutum ne mai cike da dattako irin na manyan mutane. Babu shakka Alhaji Abdur-Rahman ya gane kuskuran shi kaman yanda Ammi ta yi. Tunda su ka zauna ya ke ta kokarin jan Sayf din da hira. Sai dai mijin nata ya kasa sakin jikin shi yanda ya kamata. Yanda kasan ya na magana da ogansa wurin aiki haka ya rika amsawa.
Sai da suka kusan tafiya Hajiya Zuwaira ta sauko. Yanayin yanda ta karbe su sam bai damu Maimoon ba. Dan za'a iya cewa in da sabo ta saba da irin mutanen nan. Bata dauketa a matsayin mutum mai muhimmanci ba da har abun zai yi mata ciwo. Tsakaninta da ita kawai girmamawa ne a matsayin ta na matar surukinta amma bayan nan babu abunda ya dame ta da ita. Ciwo ta ke ji idan ta tuna abunda ta yi ma mijinta yana karami lokacin ba ya da ikon kare kan sa.
Da zasu tafi Alhaji Abdur-Rahman ya yi wa Maimoon kyauta irin ta manyan mutane. Shi ya bata izini da ta bude ta gani a wurin. Saitin dan kunne mai hade da sarka, zobe da abun hannun guda shida. Daga gani ba sai an fada ba gwal ne.
Kyautar ta zo musu a bazata. Sayfullah ya yi ma mahaifinsa godiya.
"Nagode Baba, Allah Ya saka da alkhairi Ya kara budi." Maimoon ta ce cike da girmamawa.
Addu'ar ta yi mai dadi. Ya amsa da Ameen sannan ya sa musu albarka.
Da dare su ka je gidan su Habib su gaida iyayensa. Sannan su ka je gidan su Adda Salma. A hanyar su ta komawa su ka wuce ta gaban gidan Daddy. Tana ta kallon gidan har ya bace mata tana tuna rayuwar da su ka yi a ciki. Oh duniya! Abun ya wuce kaman ba'a yi ba.
Safiyar ranan da za su tafi su ka zo yi ma Ammah sallama. Tsohuwar harda kukanta, "Allah na gode Ma ka da ka nuna mun wannan rana." ta ce tana share kwalla.
Maimoon ta kasa daurewa sai da ta yi hawaye. Sayfullah ya mika mata (handkerchief) ya kalli Ammah da kukan nata ke taba mai zuciya, "Ammah zan ci ki tara kin sa mun mata kuka."
"Kaniyanka Sayf." Ta yi mai dakuwa. "Allah Ya yi muku albarka. Allah Ya baku zaman lafiya." Nasiha ta yi musu mai ratsa jiki.
Su Mami fitan sassafe su ka yi dan haka su kadai su ka hau hanya. Hirar su su ka yi hankali kwance. Hannu shi daya na rike da hannun Noor din sa ya tuka har su ka isa garin Abuja.
A hankali motar ta tsaya a harabar gidan. Sayf ya fara fita sannan ya zagaya ya bude mata kofa. Hannunta ya kamo ya taya ta fitowa sannan ya ja ta har su ka isa kofar gidan. Tsaye su ka yi suna kallon kofar.
Maimoon har yanzu ta kasa gasgata al'amarin. Dagaske wai ta yi aure nan kuma gidansu ne. Gidan da zata gina kyakyawar rayuwa tare da mijinta abokin rayuwarta, gidan da zata karasa sauran kwanakin da suka rage mata a duniya, gidan da zata haifa yara ta tarbiyantar da su.
A bangaren Sayf ma kusan haka ya ke tunani. Satan kallonta ya yi zuciyarsa na harbawa.
A tare su ka shiga gidan da kafafun dama bakunan su dauke da sallama. Hannu ya mika ya kunna wutar lantarki, nan da nan kwayayen su ka haskaka wurin.
Maimoon ta zuga lumfashi tana karewa falon kallo. Wurin ya matukar kayatuwa da kayan alatu na zamani. A haka suka zagaye gidan gaba daya. Bata da abunda za ta ce ma iyayenta sai Allah Ya saka da alkhairi.
Dakin da babu shakka nan ne (master bedroom) su ka shiga karshe. Dakin gyare ya ke tsaff an shimfida zanin gado kamshin turare na ta tashi. An jera mata turarruka da kayan kwalliya a kan madubi. Wardrobe din ma jera ta ke da kayanta a ciki. Wannan kuma duk aikin Adda Salma ne da Kydah.
Nan Sayf ya barta ya ce ta kimtsa idan ta gama ta same shi a kasa. Wanka ta yi ta saka doguwar riga mara nauyi sannan ta rufe kanta da hula. A (dining table) ta same shi ya na fito da kuloli daga wani kwando.
"Yanzu Habib ya tafi. Yana gaishe ki."
"Ina amsawa, mun gode."
Da dare Adda Salma su ka shigo. Su Ikram nata murnan ganin Baba Sayf da Anti Maimoon.
Hankalinta na kan Sayf da ke wasa da Amira bata ji abunda Adda ke cewa ba saida ta taba ta. "Na'am?" Ta ce tana juyawa.
"Na ce arrangement din ya miki?"
"Komai ya yi Adda Allah Ya saka da alkhairi."
Ba su dade ba su ka yi musu sallama. Har bakin get su ka raka su.
Kwanan su uku su na baccin gajiya. Babu ruwan su da girki kullum daga gidan Adda ake kawo musu abinci safe, rana da na dare. Ba su yi baki ba sosai a kwanakin.
A hankali Sayf ke bi da ita yanda zata saki jikinta sosai da shi. Kullum suna tare sai dare ya yi ya mata sai da safe a bakin kofa. Ya bar mata (master bedroom) shi ya dauka wanda ke gefe. Sai ya ga ta saba da shi kafin zai koma chan din shima.
Maimoon ta yi waya da 'yan gidan su, sannan ta kira iyayenta da surukanta, Ammah, Baba, Mami da Ammi. Suna zaune a falo kamar kullum ta ce da shi, "Ni ko ka kira Ammi?"
"Ammi?"
"Mm, Allah Ya sa baka kirata ba tun tuni ni ina nan." Shirun da ya yi ya tabbatar mata da bai kira ba. Wayar shi da ke kan (centre table) ta dauko ta mika mai sannan ta zauna kusa da shi. "Kira mun ita dan Allah ni banda kati."
Bai ce komai ba ya yi dialing numban amma sai ya mika mata wayar. Amsa ta yi ta kara a kunne, ta na jin alamun ta dauka ta mika mai da sauri ta shiga bayin da ke na kasa kaman irin fitsari ya matsota dinnan. Sai da ta dan dade ta fito. Yana ganinta ya ce gata ya mika mata wayar.
Murmushi ta yi ta zauna kusa da shi. "Assalamu alaikum Ammi, ina wuni?"
"Wa'alaikumus salam beti, ya kuke? Ya sabon wuri?"
"Alhamdulillah. Ya su Waahidah?" Sun gaisa jiya saboda haka maganar ta su bata yi tsawo ba. Sai dai Ammi ta sake maimaita abunda ta ce mata jiya. Kada ta ji nauyin kiranta, tana nan a duk sanda ta ke bukatan wani abu.
"In sha Allah Ammi, nagode. A gaishe da Baba."
"Zai ji 'yar albarka. Sai da safe."
Maida wayar ta yi inda ta dauke ta idon ta ya sauka kan farantin fruits da ta yanko musu, bai taba kankanan ba. Kallonsa ta yi, "Baka sha watermelon din ba."
"Bana sha."
"Watermelon din? Yana cikin favorite fruits dina. Amma me ye baka so, taste din?"
"Texture din na mun wani iri a baki."
Kai ta jinjina. "Ban yi mamaki ba amma," ta ce tana daukan plate din. Gyara zamanta ta yi ta jingina da kujeran sosai.
Dubanta ya yi a gefen shi. "Me ya sa ba ki yi mamaki ba?"
"Ammi ma bata sha kankana. Ranan da na yi fruit salad na kai mata tsincewa ta yi. Gado ka yi kenan."
"Probably," ya ce yana daga kafada. Daga nan su ka maida hankulan su kan akwatin telebijin. Ita kuwa sai murmushi ta ke yi.
****
Ranan da su ka cika sati daya da dawowa Sayf ya tashi da kiran ogan shi yana son ganin shi an samu matsala a wurin aikin a na bukatar shi da gaggawa. Ogan ya bashi hakuri tunda hutun da ya dauka bai kare ba.
Har mota ta raka shi ta mika mai jakar shi tana mai a dawo lafiya. Sai da motar ta bar gidan ta koma ciki.
Zuwa yanzu Maimoon da Sayfullah sun yi wani irin sabo mai ban mamaki. Yanzu ne ta ke kara fahimtar waye Sayfullah Abdur-Rahman Hambali. Mutum ne mai saukin kai da yawan tsokana. Ta maida hankali sosai wurin gane abunda ya ke so da wanda baya so.
Gaba daya ta ji gidan ya yi mata girma. Tunda su ka dawo sallah kadai ke fitar da shi. Agogon da ke like a bango ta kalla. Awan shi hudu ta fita amma tana ji kaman ya yi awa goma.
Ajiyar zuciya ta yi. Ta gama gyara gidan bata da wani abun yi. Waya ta dauko ta dan yi chatting shima nan da nan ya fitan mata a kai.
Zumbur ta mike kaman an tsunguleta. Waya ta dauko ta kira Adda Salma. "Maimoon kin ji ni shiru ko, yanzu zan turo Adama."
"Dama abunda ya sa na kira ki kenan. Ba sai kin aiko mana da abinci ba, tun tuni na ke fada miki ki daina hakanan za ki sangarta ni."
Dariya Addan ta yi. "Ai bai kamata amarya ta daura tukunya ba."
"A'a Adda, ba wani nan," ta yi dariya. "Dama ya fita yau an kira shi a office shine na ke son in yi mai abinci kafin ya dawo."
"Da kyau kanwata. Me kike bukata?"
"Vegetables din yin miya sai kwakwa da dabino." Su kadai ta ke bukata dan a gara an tanadar mata da komai. Sauran chefane kuma washegarin ranan da su ka dawo Sayf ya bada aka siyo.
Adda ta ce to zata turo Adama mai aikinta ta kawo mata.
Sayfullah na san tuwo sosai saboda haka tuwon shinkafa zata yi da vegetable soup. Sai kunun aya da gas meat.
Ba'a dade ba sai ga Adama ta iso. Adda kuma ta ce ta tsaya ta tayata aikin.
Da yake abincin ba na mutane da yawa bane nan da nan ta gama. Kitchen din sai kamshi ya ke yi. Set din kuloli masu kyau ta dauko ta jera tuwon a daya sannan ta zuba miyar da ta ji kaza a dayan. Wani hadadden kwano ta dauko ta zuba gas meat din a ciki. A dining table ta ajiye sannan ta dawo yin Kunun aya. A blender dinta ta nika komai ta tace. Shi ba mai son sugar ba ne, itama ba so ta ke ba dan haka ta saka kadan. Ta saka a jug dinta mai kyau ta sa a fridge.
Tare da Adama su ka gyara kitchen duk da ma 'yar kallo ta zama. Wanke wanke kawai Maimoon ta bari ta yi mata. A (basket) ta saka komai ta ba ta ta kaima Adda.
Daki ta koma ta yi wanka ta feshe jikinta da turare. Turaren hadi ne na musamman da ta yi wa kanta. Kamshin shi masha Allah kawai. Daidai ta gama shiryawa cikin riga da sket na atamfa ta ji karan tsayuwan mota.
Ita ba ma'abociyar daura dankwali ba ce wahala ya ke bata, da sauri ta yi daurin ture ka ga tsiya dan ya fi mata sauki. Daurin ya sa jelar gashinta da aka yi mata shuku da biki saukowa. Har ta dauki mayafi ta cillar da shi kan gado.
Daidai ta na saukowa Sayfullah yana rufe kofa. Juyowan da zai yi ya daskare a wurin. Idon shi a kanta tana murmushi har ta iso gaban shi kamshin turaren nan da ya ke matukar so ya daki hancinsa.
Maimoon ta yi tsammanin zai kamo hannunta ne kaman yanda ya saba sai kawai jinta ta yi a jikinshi ya rungumeta. A tare su ka saki ajiyan zuciya.
"Mahnoor...." ya furta da wani irin murya ya na kara rungumeta. Janye jikinshi ya yi hannun shi akan kafadunta ya kare mata kallo. "Kin yi kyau Mrs. Sayfullah."
Kunya ta ji tana neman boye fuskarta ya kara janyota jikinshi. Sun dade a haka kafin ta kama hannun shi su ka isa falo su ka zauna. "Abinci zaka fara ci ko zaka fara watsa ruwa?"
"Ke kika dafa abincin?" Kai ta daga mai. "To, ina son in watsa ruwa sannan kuma I'm eager to taste abunda kika dafa gashi kuma ban gaji da kallon ki ba. So ya za'ayi?"
"Yanzu ka fara watsa ruwa sai ka zo ka ci abinci."
"Kallon ki fa?"
"Ka na yi kana cin abinci."
"Yanda kika ce haka za'a yi."
Jakar shi ya dauka ya nufa sama ita kuma ta koma dining table ta kara gyara wurin duk da komai a kimtse ya ke.
Da jallabiya a jikin shi ya sauko wanda ta lura ita ya ke son sawa idan ya na gida kaman dai yanda itama ta fi son zama da doguwar riga mara nauyi.
Kujera ya janyo ya zauna. Ita ta zuba mai komai ta koma kujerar da ke kallon shi yanda zata kalla (reaction) din shi da kyau. Zuciyarta sai bugawa ta ke yi da sauri.
Bismillah ya yi, ya na saka lomar farko ya dago kai da sauri ya kalleta. "Mahnoor! Wow! Wow! Wow! Mai kika sakawa abincin haka?"
"Ya yi dadi?"
"A hundred out of ten. Yanzu za ki saka abincin wasu ya daina mun dadi. Masha Allah"
Ta ji dadin hakan sosai sosai. Tana ta murmushi mai cike da farin ciki.
Dama Sayf ya kwaso yunwa dan haka ya ci abincin sosai, ya ci nama sannan ya kora da kunnun aya. Tuwon ya ce a ajiye mai zai ci dumame da safe.
Ya ba Maimoon dariya ta ce mai to.
Falo su ka koma ya janyota jikin shi yana wasa da gashin da ke kwance saman goshinta. Dukawa ya yi ya sumbaci wurin. "Mai zan bada tukuici?"
"Babu komai."
"Mmm-mmm ban yarda ba. Dole in bada tukuicin kwalliya da na abinci."
"Ka saka mun albarka."
Dagota ya yi ya kalla kwayar idanunta. "Allah Ya yi miki albarka Raihanatul Qalb, Ya sa mun ke a aljannah firdaus."
Tuni idonta ya taru da kwalla. "Ameen Ameen."
Su na haka har aka fara kiran sallah. Nan ya barta ya tafi masallaci ita kuma ta tafi daki. Bai dawo ba sai bayan sallar isha'i. Ya sameta a daki tana waya da Adda. A gefen gado ya zauna har ta gama.
"Ki shiga ki yi arwala." Abunda kawai ya ce mata kenan.
Zuciyarta kaman zata harbo ta shiga bayi. Ta fito ta same shi ya shimfida sallaya guda biyu. Salla raka'a biyu ya ja su bayan ya idar kuma ya yi doguwar addu'a.
Juyowa ya yi ya kalleta idanun shi cike da (emotions). Ji ta yi kallon ya yi mata nauyi da sauri ta kauda kai. Hannunta ya kama ya isa da su gado ya zaunar da ita. Tallabo fuskarta ya yi da hanayensa.
A hankali ya matso dab da ita har suna iya jin lumfashin juna. "May I?" Ya furta a hankali. Tana daga kai ya hade bakin su wuri daya. Daga nan kuma su ka bar duniyar gaba daya
•
•
•
•
•
•
Sigh 🥹😻 I hope you enjoyed it as much as I enjoyed typing it. I was grinning through out🤭❤️
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro