BABI ARBA'IN
~
BABI ARBA'IN
~
Gidan cike ya ke da mutane ko ta ina. Duk fadin farfajiyar gidan an jera kujeru da mutane ke zaune a kai. A gefe masu abinci suna ta aikin su.
Amarya Anwara da 'yan uwanta da kawaye suna bangaren 'yan mazan gidan. Nan suka koma tunda aka fara biki.
Jiya ta yi bridal shower din ta a gidan Kydah. Komai ya tafi lafiya yanda ta dade ta na tsarawa tare da 'yan uwanta.
Da misalin karfe sha daya aka daura auren Anwara da dan uwanta Ahmad. Anwara harda hawayen farin ciki buri ya shiga, ta sha tsokana sosai wurin 'yan matan amarya.
Maimoon ta taya ta shiryawa dan yanzu Aunty Rukayya, kanwar su Baffa, za ta zo ta shiga da ita ciki wurin iyaye.
Da Aunty Rukayya ta zo tafiya da amarya, Anwara ta yi saurin kamo hannun Maimoon kuma ta ki saki dole ta bisu. Ita da Anwara sun yi wani irin sabo sosai, kafin ta nema shawara wurin sauran ta zo wurin Maimoon ya fi so goma. Kusan komai tare su ka yi.
Guda kawai ke tashi da suka shiga ciki. Wurin Jaddati aka fara kai ta. An yi mata nasiha sosai. Daga nan kuma aka zagaya da ita wurin wanda ya kamata.
A halin zagayen ne 'yan uwa ke ta tsokanar Maimoon. Duk inda su ka bi sai an ce; "toh takwarar Jaddati ke ce next." Ko kuma "saura ke."
Maimoon dai jin su kawai ta ke yi. Ko ita ta ce musu ta kusa aure ne, oho!
An sha hotuna da amarya. Ana cikin hoton ne Maimoon ta samu ta gudu. Dakin da su ke zaune ta koma, yunwa ta ke ji kaman zata ci babu.
Irin gajiyar da ta yi kai ka ce ita ce amaryan. Babu kowa a falon duk ana waje wurin dauka hoto. Masa ta zubo ta dauko zobo mai sanyi sosai. Ta ci sosai harda kari. Daga nan kuma ta mike a kan kujera.
Sai a lokacin ne ta lura da missed calls guda biyu a wayarta. Daya Sadiya ce dayan kuma Sayf ne ya kira wurin awa hudu da suka wuce. A lokacin kai ya dauki zafi bata ma san inda wayar ta ke ba.
Kan sunan shi ta latsa, wayar na fara ringing ya kashe sai ga kiran shi ya shigo. Bai taba dauka idan ta kira shi, sai ya kashe ya sake kira.
"Mahnoor."
A hankali ta lumshe ido. Sunan na yi mata dadi sosai. "Na'am."
"Kin gama assistant bride duties din na ki?"
Dariya ta yi. "Ina fah, na dai gudo yunwa na ke ji."
"Kin dai abincin ko?"
"Gani nan ko hannu ban wanke ba."
"Uhm kin yi magana da Baffa ko Ummi?"
"Magana? Wace irin magana?"
"Ba ki yi ba kenan. Shikenan."
Abun ya daure mata kai amma ta share. Maganan su bai tsawaita ba su ka yi sallama.
Maimoon bata taba tsammanin haka zai kasance da ita ba, bata taba tunanin Sayfullah zai zama bangare na rayuwarta ba. Ba su dade da sanin juna ba amma ta na ji kaman suna tare tun farkon rayuwarta.
Ya yi wa kansa wuri a zuciyarta. Bata jin kuma zai fita.
****
Bayan isha'i aka kai Anwara gidanta a nan Gwarimpa. Su Nanah an sha kuka za'a rabu da 'yar uwa. Maimoon ma duk yanda ta so daurewa sai ta zubda kwalla. Ba karamin kewar Anwara za ta yi ba.
Suna kai ta Aunty Rukayya ta kado kan su, ba a bar kowa a gidan ba. Da Anwara taga da gaske tafiya za'a yi a barta ta sake fashewa da kuka. Tun a na lallashin ta sai da Aunty Rukayya ta yi mata fada. Kafin a kai ta gidanta an kai ta gidan Aunty Maryam da yanzu ta tashi daga matsayin kanwar mahaifinta ta koma uwar miji, duk da sam ba haka ya ke a wurin ta ba.
Sun fito wajen gidan wata abokiyar wasan (cousin) su Baffa ta sa ke maimaitawa Maimoon kalaman da aka yi ta damunta da su dazu.
"Sai nan da wata biyar zamu da dawo na Mamana in sha Allah."
Kydah ce ta ce. "Aunty me kika ce?"
"Oh, ba ku sani ba? Bayan an daura auren yan uwanku aka sa ka ranan Maimoon da yayanki."
"Ya Sameer?!" Kydah ta zaro ido waje.
"A'a ba Sameer ba, dayan yayanki, Sayfullah."
Da sauri Kydah ta juya ta na kallon Maimoon da ta daskare a wurin. Har su ka shiga mota Maimoon ta kasa ko tunani da kyau.
"Maimunatu Muhammad Lamido!" Kydah ta ce ta na kallonta cike da mamaki.
Nanah ke tuki, Sadiya a gaba, baya kuma Kydah, Mimi da Maimoon.
Mimi da Kydah sun saka Maimoon a tsakiya, hakan ya ba Kydah daman juyawa gaba daya ta fuskance ta.
"Yanzu ki na tare da yaya na shi ne ban sani ba? Ina kika san shi, yaushe kuka hadu? Tell me everything! Oh Allah!"
Ajiyar zuciya Maimoon ta saki. Har yanzu kwakwalwarta ta kasa daukan zancen. Abunda ya ke nufi kenan dazu da ya tambaye ta in ta yi magana da Baffa.
"Maimoon!" Kydah ta taba ta ganin bata bada amsa ba.
"Ya Kydah!"
Dariya Kydah ta yi, daga karshe ta rungume Maimoon din. "Na ji dadin wannan hadin sosai."
Har suka isa gida hirar da ake yi kenan. Nanah, Sadiya da Mimi su ke amsa tambayoyin Kydah, har yanda ya je Zaria lokacin da bata da lafiya sai da Nanah ta bada labari, Maimoon kaman ta nutse.
Ko da suka isa gida dakin da su ke kwana ta wuce. Tunda aka daura aure dama rabi da kwatan bakin duk sun tafi sai daidaiku.
Zama ta yi bakin gado ta dafa kirjinta inda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Shin mafarki ta ke yi ko dagaske ne?
Arwala ta yi ta gabatar da sallah raka'a biyu. Ta yi addu'a mai tsayi a sujada. Sai da ta ji ta samu natuswa sannan ta yi sallama. Dukda haka bata bar kan abun sallahn ba, ta cigaba da addu'a Allah Ya tabbatar musu da alkhairi. Idan wani abu ya sake faruwa bata san ya zata yi da kanta ba.
Son da take ma Sayfullah ya dushe sauran, sauran kamar ba komai bane in aka hada da irin son da take masa.
"Ya Allah Ka kula da ni, da lamarin ba ki daya."
Ta gama shirin kwanciya kenan sauran su ka shigo dakin. Waahidah ta kankameta ta na ihu. "Adda Moon! Yanzu matar yaya zan rika ce miki."
Ba su sani ba, amma farin cikin da su ke nunawa ba karamin dadi ya yi mata ba.
Washegari sauran baki duk sun tafi. Gidan ya koma kaman ba shine a cike ba. Nanah ta fada mata su Baba na kiranta a sashen Ammah. Da hijabinta har kasa ta tafi. Bayan ta gaida su ta samu wuri a kasa ta zauna.
Baba Nasir ne ya yi mata duk bayanin da ya kamata. Sannan ya sanar da ita Sayf ya zo da kan shi neman izini kafin iyayensa su zo. Maimoon bata taba boye wa Ummi halin da ta ke ciki ba, Baffa ya san da haka shi yasa basu nemi Maimoon din ba, su ka samu Ummin kawai. Da bayanin da suka samu da wurin Ummi su ka yi amfani wurin yanke hukunci.
Baba Nasir cikin raha ya ke cewa ai abun ma na gida ne.
"Allah Ya nuna mana da rai da lafiya." Jaddati ta yi addu'a.
****
Duka kayan dake cikin wardrobe din ta fito dasu amma ta rasa wanne zata saka a ciki. Hannu ta sa ta dafe kanta, saura mata awa daya kafin ya iso, gashi ko kayan da zata sa ma bata sani ba.
A irin haka ne ta ke kewar Anwara, da yanzu ta samo mata mafita. Tana zaune cikin kayan kannenta biyu suka shigo dakin.
Mimi ta yi turus tana kallonta. "Adda ba ki shirya ba?"
"Banda kayan da zan saka."
Mimi ta kalla Sadiya, Sadiya ta kalla Mimi sannan suka kalli kayan da ke baje a kasa kaman gwanjo.
"Ba'a rasa abunda za ki saka ba Adda," Sadiya ta ce.
Maimoon ta mike ta koma kan gado ta zauna tana kallon su. Ko minti biyu ba'a yi su ka miko mata wata doguwar riga ta material. Ai bata karba ba ta girgiza musu kai.
"Ta ya zan sa wannan rigan dan Allah!"
Mimi da Sadiya su ka sake kallon juna sannan su ka cigaba da duba mata. Dayake duk yawancin kayan nata dogayen riguna ne, wata suka dauko amma wannan lace ne. Dankareren leshi ne ya sha dinkin kaftan da dogon hannu.
Karba ta yi ta shiga cikin bandaki ta sanyo rigan. Zaunar da ita su ka yi suka gyara mata fuska dukda hoda da man baki kawai ta yarda aka shafa mata.
"Wow! Adda am, kinga yanda kika yi kyau kuwa!" Inji Sadiya ta na gyara mata zaman mayafin akanta. "Hamma Sayf zai manta kan shi idan ya ganki."
Hannu Maimoon ta kai mata ta kauce ta na dariya.
Kallon kanta ta yi a madubi, ba wata kwalliyan azo a gani ta yi ba amma tabbas ta chanza. Aikin Mimi ne da ta zambada mata kwalli a idanu, hakan ya sa suka kara haske sosai kuma su ka yi kaman sun kara girma.
Wayar ce ta yi kara amma saida gabanta ya fadi.
"Hamma ya iso." Mimi ta ce tana dariya ta mika mata wayar sannan su ka bar dakin.
"Mahnoor?"
"Na'am."
"Kin shirya? Ga ni nan a falo."
"Toh gani nan fitowa."
A hankali ta furzar da iska daga bakinta, zuciyarta na wani irin bugu kaman zata fita daga kirjinta. Satin da ya wuce Sayfullah ya ce ta shirya zai zo ya dauketa su je gaida Mami. Tun ranan gabanta ke faduwa, bata san ji wani irin tarba za'ayi mata ba.
Dan karamin (pep talk) ta yi wa kanta sannan ta fita, har ta kai (stairs) ta tuna ta yi mantuwa. Da sauri ta koma dakin ta dauka jakar turare da za ta kai wa Mami da Nusayba.
Ta kawo karshen (stairs) din sai dai wurin a boye ya ke yanda wanda ke palon ba zai hango ka ba. Jin kanta ta ke yi kaman tsurara saboda rashin niqabinta.
Sunan Allah ta kira sannan ta fita.
Sayfullah ya daga kofi zai kai baki kenan ta fito. Chak ya tsaya ya kasa motsi. Ashe ganin da ya yi mata gidan Habib bai kalleta da kyau ba. Duk yanda ya so kada ya kura mata ido ya kasa, haka ya yi ta binta
Girgiza kan shi ya yi. Ya samu kan shi a yanayin da bature ke kira da 'tongue tied,' sai da ta sake gaishe shi ya dawo hayyacinsa.
Ranan da Baba ya sanar da Sayf cewa an bashi Maimoon kasa bacci ya yi. Nan da 'yan watanni Mahnoor din sa zata zama ta shi halak malak. Tare zasu gina rayuwar mai cike da so, kauna da fahimtar juna. Tare za su gina rayuwar da ya dade ya na bege, rayuwar da ya rasa da ya na karami.
Ummi ta sauko sun gaisa. Daga nan su ka mike za su tafi. A waje Maimoon ke tambayan shi ba zai shiga su gaisa da Ammi ba. Ce mata ya yi ta bari sai ya dawo da ita sai su shiga.
A mota shiru babu me cewa komai. Sayf ya lura a takure ta ke shi yasa ya yi shiru kada ya kara takura ta.
Cikin ikon Allah ba su hadu da hold up a hanya ba, saboda haka babu dadewa su ka iso. Mami tun safe ta ke shirin tarban Maimoon, Allah kadai Ya san abinci kala nawa ta sa aka dafa.
"Bismillah," ya ce mata. Shi ya yi gaba tana bin shi a baya. Tun a kofa Sayf ya san Mamin na shi ba karamin shiri ta yi ba.
Sun same ta a falo tana ganin shigowar su ta mike tana musu maraba. Maimoon ta duka gaisheta Mami ta janyota jikinta ta rungume.
Duk wani fargaba da ke tare da Maimoon ya bace gaba daya. Sayf sai murmushi ya ke yi.
Mami ta janye Maimoon daga jikinta, tana rike da ita ta ce. "Tubarakallah Masha Allah!" Ido su ka hada da Sayf ta gyada mai kyan irin ka iya zaben nan.
Dariya Sayf ya yi har sautin na fita. Maimoon kunya ya kamata.
"Ina wuni Mami, mun same ki lafiya?"
"Lafiya lau Alhamdulillah diyata. Ya wurin su Ummi da Baffa."
"Suna nan lafiya."
"Masha Allah, bari in yi wa babansu magana ko. Ga snacks nan ki ci fah. Kai kuma," ta nuna Sayf. "ban ce ka dauka ko daya ba, ba kai aka yi wa ba."
Dariya su ka yi gaba daya, Sayf ya ce; "Noor kin kwace mun fada wurin Mami."
Murmushi ta yi. Baba Ahmad ya sauko sun gaisa. Shima faram-faram ya ke. Gaba daya Maimoon ta ji sun burgeta sosai. Sun tarbeta cike da mutunci da kulawa.
Nusayba ta sauko sun gaisa dukda sama-sama gaisawar ta su ta kasance. Sayf ke sanar da ita 'yan biyu sun yi tafiya.
Mami ta ce su hau sama. Sosai ta rika janta da hira duk dan da saki jikinta.
Sai yamma Sayf ya ce za su tafi. Maimoon ta ba Mami turaren da ta taho da su. Sosai ta yi mata godiya sannan itama ta hadata da sha tara da arziki.
Wannan karon sun yi hira sosai a hanyar su ta komawa.
Da suka iso Maimoon na sha zasu shiga su gaida Ammi sai dai ba haka ya faru ba. Ya na ajiye ta ya juya bai ma bari ta dauko zancen ba.
Washegarin ranan da aka daura auren Anwara Ammi ta kirata bata yi magana ba amma idanunta kadai sun fada ma Maimoon abunda ta kasa furtawa.
A take Maimoon ta kuduri niyan gyara (relationship) din Sayfullah da Ammi.
•
•
•
•
•
•
•
~Maymunatu Bukar💕
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro