Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

Chapter 4


""Gabansa na dukan goma goma ya bude kofar cikin mamaki yake bin ammi da mimi tsaye sannan ya sake kallon agogon dakin yaga har 8pm shin menene ya kawo ammi da wannan time din,bakinsa na rawa yace ammi kece?

"Murmushi tayi tace kai dai bari wlh ina zaman zamana kaga wacce ta tasoni kasan duk tayi tunanin wannan week dinne bikinku shine tazo day before yesterday na fada mata har anyi gashi gobe zata koma turkey na rasa wanda ze rakota shiyasa na taso da kaina na kawota taga amarya tunda kai dai ba bakonta baneba

"Sai a lokacin hankalinsa ya kwanta kadan sedai har yanzu zuciyarsa bata dena bugawa ba har ammi taso fuskartar tsoro a fuskar irfan,murmushi yayi yace okay ammi gaskiya naji dadin zuwan mimi sannan ya kalleta yace mutanen turkey ina fatan kin tahomin da tsarabata

"Murmushi mimi tayi tace yaya irfan ni kam ban kawo maka komaiba amma na kawowa aunty na tsarabarta,sannan ta samu guri ta zauna bayan sunyi dariya gaba daya a daidai lokacin da idon ammi ya sauka akan take away na restaurant kana gani kasan abinci aka siyo a ciki

"Mikewa yayi ya kawowa su ammi soft drinks,ganin har kusan 15 minutes babu alamar nasreen yasa ammi kallon irfan tace hala nasreen din bata ji shigowarmu bane ya kamata ka fada mata tazo su gaisa don yanzun nan zamu tashi ba zama zamuyi ba

"Am amm ai nasreen din ma bata nan...irfan ya karasa magana cikin i'ina

"Cikin salon mamaki mimi ta kalli ammi itama ammi ta kalli irfan tace kamar ya nasreen bata nan menene ya faru da nasreen din?

"Cikin tsoro da faduwar gaba yace eh dama dazu ne tacemin bata jin dadi shine taje asibiti ganin doctor

"Haba irfan taya zaka bar yarinya ita kadai ta tafi asibiti?menene amfaninka da bazaka raka taba sedai ka hada yarinya da driver wannan sam be daceba ai sai ka janyo mana zagi wajen iyayenta maza tashi mu tafi asibitin gaba daya muje mu sameta muga ya jikin nata yake

"Gabansa ne ya sake mugun faduwa har wani irin tari yana kamashi yace ah no ammi ai ta dade da tafiya yanzu may be ma suna hanya karki damu ammi all is well insha Allah

"Shiru tayi kadan tace are you sure?

"Da sauri ya daga kansa yace yes ammi i am very sure

"Okay toh shikenan amma ko dan gaba karka kuskura ka sake barin ta taje asibiti ita daya,amma irfan nasreen din ta dade tana rashin lafiyar ne ko tunda tazo bata da lafiya?ammi ta sake jefa mishi tambaya

"Da sauri ya girgiza kai yace a'a lafiyarta kalau dazu ne kawai dai bataji dadiba amma da sauki ma sosai

"Amma meyasa nake ganin take away ko ta ina a cikin gidannan kamar ma ba'a taba yin girki cikin gidan ba ammi tayi magana tana kallon dustbin din dake ajiye a gefen palour din wanda ya cika da ledojin abinci

"Sai a lokacin irfan ya kula da abinda ammi ta gani cikin wayancewa yace ah no wannan hisham ne ya taho dashi yaci anan shine fa muma ya taho mana da abinci bayan ni na fada mishi na tashi daga matsayin gwaro

"A tare sukayi dariya da mimi ammi tace
uhmm lallai wannan shegantakar naku dai bazaku fasa ba,toh mu dai zamu wuce idan ta dawo kayi mata ya jiki sai wani lokacin kuma wannan ma mimi ce ta taso ni

"Har bakin mota irfan ya rakosu ammi suka shiga mota driver ya jasu suka tafi

"Gaba daya street din shiru kamar anyi walkiya an dauke don hatta gates din street's din duk an kullesu hakan yana nufin karfe 12:00am ya wuce,da gudu mai gadi ya bude musu kofa suka shiga gidan bayan securities sun duba motar tasu sannan suka barsu sukayi parking nasreen nata faman tsaki ta shiga gidan

"Irfan ne zaune a palour din daga gani bacci yake ji amma ya kasa kwanciya saboda tsananin tsoro tun dazu yake kiran wayar nasreen amma a kashe,ganinta yasa shi mikewa tsaye da sauri yace nasreen daga ina kike?kina kallon agogo kuwa?tun dazu wayarki kashe wannan wanne irin rashin hankali ne?

"Jefar da handbag dinta tayi akan daya daga cikin couches din dakin sannan tace mr billions of questions me kake nufi ne?bangane wannan kalar tambayoyin ba kamar ina gaban alkali na fada maka birthday naje na kawata toh meye kuma zaka isheni da tambaya sannan maganar waya chaji nane ya kare kuma bani da lokacin sawa saboda hidima tayi min yawa.....saurin katse ta yayi yace har gidan ubanwa kika je birthday din?wai ma nina baki izinin fita ko waye?da har zaki fita ki dawomin karfe 12:30am cikin gidannan a matsayinki na matar aure ai ko yar tasha me nutsuwa bazata kai wannan lokacin a wajeba

"Kaga sauraramin irfan....don Allah saurara min nifa idan na fuskance ka kanaso ka hanani jindadin rayuwata sai ka fa ke da cewa wai ni matar aurece shin su matan auren basu da yanci ne?menene aibu don kawai na fita naje birthday party shikenan zaka tasa ni gaba kana min masifa kamar wacce ta aikata zunubi toh wallahi baze yiwu ba ni macece mai yanci ya zama dole in fita bazan zauna kamar wata akuya ba ko tinkiya wacce ake daurewa a gida toh baze yiwuba...tana gama fadar haka ta nufi hanyar bedroom sedai kafin ta karasa ya janyo hannunta yace wai ba magana nake miki ba?

"Fashewa tayi da kuka cikin tsananin shagwaba tace irfan dama ba sona kakeyi ba?dama ka auro nine don ka cimin mutunci?dama soyayyar tamu duk a wajene daga aurenmu ko sati banyiba zaka fara sanyani zubar da hawaye?

"Gaba daya jikinsa ne yayi sanyi cikin sanyin jiki yace nasreen bani da niyyar cutar dake ko kadan soyayyarki dake raina ina tabbatar miki kullum karuwa take yi bata taba raguwa amma ke kinsan kalar wannan abin da kikayi ai baki kyauta ba taya matsayinki na matar aure zaki kai har 12 a waje ya zama dole na nuna bacin raina akanki saboda ina kishinki....i love you and i really care about you

"Turo baki tayi cikin shagwaba tace i am so sorry honey and insha Allah i will not try it again

"Goodgirl ya fada a hankali sannan ya hade pointed noses dinsu yace my nas nas bakya jin magana sena miki bulala ko?

"Runtse idonta tayi ta bude tace ba nace maka na dena ba ai bazan kuma ba,tana gama fadan haka ta mike ta nufi bedroom don ta gaji sosai tana bukatar watsa ruwa a jikinta,bin ta yayi da kallo a hankali yace nasreen da kinsan masifar da kika jefani wajen ammi dazu da ko kasheki nayi bazaki bude baki kiyi magana ba

"Wanka kawai tayi sannan tayi sallar isha'i ta nemi gado ta kwanta saboda tayi matukar gajiya a wajen birthday party din kilishi ba karamin kudi aka kashe a wajen birthday dinba hatta souvenir din da nasreen ta taho dashi harda Iphone 11pro a ciki sedai sam bata damu da abinda ke cikiba saboda yanzu ta girmi wannan wayar ita kanta iPhone 13 pro max ce a hannunta

"Sai karfe 2 nasreen ta tashi daga nannauyan baccin da takeyi shima wayartane ya dameta da kara,sunan bilkisu ta gani cikin sauri ta daga wayar a hankali tace marar mutunci sai yau ko,murmushi bilkisu tayi tace kinga gani a kofar wannan gidan naki me kama dana shugaban kasa securities sun isheni da tambayoyi daga ina nake,gurin wa zanje,shin ansan da zuwanki kinga sai tambayoyin da suke min kenan saura kiris ya rage bance musu tare da ke mukayi rayuwar wahala ba a ghetto area

"Da sauri nasreen tace haba sweetie don't try me wlhi zan shuka miki rashin mutunci ki basu wayar nayi musu magana,sosai bilkisu ke yaba tsaruwar gidan nasreen don ko me hassada idan yaga gidan nasreen bai isa yace ba,a zuba manya manyan kudade wajen yinsaba,a gajiye ta zauna sannan ta kalli nasreen tace ya na ganki da pajamas kamar wacce ta tashi a bacci yanzu?

"Murmushi nasreen tayi tace ke yanzun nan kece ma kika tasheni daga baccin wlhi don ban tashi ba a gajiye nake kinsan jiya akayi birthday din wannan hajiya nafisah din wacce na karbi number dinta wajen manicures

"Cikin mamaki bilkisu tace kamar ya birthday karki fadamin wai har kin fara fita,toh wai ma irfan dinne ya barki har kika fita wani birthday?nasreen kwananki fa 6 da aure amma kin fara yawo gidan birthday ni wlh kwata kwata wannan matar batayi minba saboda na lura irinsu ne masu batawa yara tarbiya ai kana gani kasan ba sa'arki bace

"Kinga don Allah saurara min bilki kice nan dinma se mun raba hali ko?wai ke don Allah yaushe zaki wayene?ai yanzu kai ya waye an dena wannan rayuwar takura da duhun kai yanzu kai ya waye rayuwa ake irinta yaran Elizabeth(hahah only elegant online writers can relate)ai yanzu zamani ya sauya ba,a wannan zama kamar wata saniya ko tinkiya kana zaune gida ba tare da kasan meke faruwa a duniyaba nasreen ta karasa magana tana danna wayarta bayan notification ya shigo mata

"Amma dai ai wayewar ma akwai kazamar wayewa akwai mai mutunci amma ke yanzu ko dangin mijinki suka samu labarin har kin fara yawon gidan birthday ai dole su sanya miki question mark bilkisu tayi magana a takaice

"Kinga don Allah ki rabu dani nan dinma biyoni kikai ki fara min wa,azin naki kenan toh wlh indai akan fita zaki yimin wa,azi bazan daukaba don ke kanki kinfi kowa sani bana son rayuwar takura don anjima kadan ma gidan biki zanje jiya a wajen birthday wata ta gayyaceni bikinta ita kuma yarinyar senator ce saboda ganin yanda nayi kyau na fito ba karya kinga da bana kwalliya waye zeyi sha'awar ma ya gayyaceni event dinshi nasreen tayi magana cikin gadara

"Baki bude bilkisu take kallon nasreen da tuni tayi nisa bata jin kira da kyar ta bude bakinta tace ikon Allah nasreen daga haduwa da mace jiya ta gayyaceki biki saboda baki da hankali ki kwashi jiki ki tafi idan kuma barauniyar mutanece ko kuma yar kidnapping kuma fa?

"Bushewa tayi da dariya tace uhmm se kiyi kuma toh wai kinsan ma a ina zaayi bikinne?a blue velvet luxury marquee nefa,ke kanki kinsan kaf abuja babu inda yakai haduwar event center dinnan don haka ko don nayi pictures a gurin dole naje

"Karfe 4 nasreen ta shirya cikin hadadden lace dinta wanda ko a duhu ka kalleshi kasan an kashe mahaukatan kudi wajen siyansa da dinkinsa,sai data tsaya a monavee beauty lounge aka mata makeup kafin ta nufi wajen bikin

"Sosai irfan ke mamakin ganin duk inda yake tunanin zega nasreen a cikin gidan amma be ganta ba,sake kallon agogon dake jikin bangon dakin yayi yaga har karfe 10:30pm amma nasreen bata cikin gidan toh ina ta tafi kuma?wajen dispenser ya nufa ya debi ruwan zafi lipton kawai ya jefa ciki ba tare da yasa sugar ba ya fara sha zuciyarsa na matukar tafasa saboda takaici

"Hahahahahha kawata kenan ai kedai ki bari gobe tun 2 sena rigaki zuwa wajen bikin nan don gaskiya yau an cashe na dade banyi rawa irinta yau ba.....shine abinda nasreen ke fada a waya bayan ta turo kofar ta shigo ba tare da tayi sallama ba,murmushi ta sakeyi ta wayar tace kedai bari yanzu na shigo gida mu hade goben kawai bye,tana gama fadar haka ta kashe wayar sannan ta mayarda kallonta ga irfan da ya hade ransa yana kallonta cikin fushi yace daga ina kike?

"Daga gidan biki nasreen ta bashi amsa with her full confidence

"Gidan biki as in how?wa kika tambaya zakije gidan bikin?wai ma zaman kanki kikeyi da zaki bar cikin gidannan ba tare da izininaba irfan ya jefa mata tambayar a fusace

"Don Allah saurara min Allah ya dawo dani kenan zaka fara min masifar taka ko?wai don Allah dama har yanzu ana wannan kauyancin se an tambaya kafin a fita?Wai don Allah meyasa kullum kakeson daga min hankali ne,kamar wacce ta fita wani yawo na fada maka gidan biki naje....ko so kake nayi ta maimaita maka kamar mai rera waka ne?

"Ya kike neman raina min hankali ne da wata banzar wayewarki wacce bata wuce cikin spoon ba,har ni zaki kalla ki cemin wai yanzu baa tambayar miji idan zaa fita shin baki da ilimin addinine akanki?

"Kaga mallam don Allah karka nemi ka zagi iyayena don idan na fuskanceka kana nufin basu sanyani a makaranta ba ko?toh yayi maka kyau irfan na jinjina maka ina kara jinjina maka da tun ba,aje ko ina ba kana shirin cimin mutunci,bata jira ya sake magana ba ta nufi dakinta bayan ta ajiye handbag dintane ta sake fitowa ta nufi dining area sam babu alamar abinci ko takeaway kamar yanda irfan ya saba ajiye mata,fridge ta bude shima hakan take babu komai a ciki sai soft drinks,kallonsa tayi tace ina abincina?

"Shiru yayi mata cikin bacin rai irfan ke kallon nasreen da sam ita babu abinda ya dameta ma

"Ohh kana jina inayi maka magana kayi min shiru ko?kenan dama saboda kayi min horon yunwa kace min chef bazata zo ba sai nan da 1 week ko?tabbas nayi nadamar aurenka tun tafiyarmu batayi nisa ba,tana gama fadar haka ta nufi dakinta....kan gado ta fada sannan ta dauko wayarta ta kira nadia

"Hey nadia ya kike?

"Fine amaryar mu ya komai?

"Hmmm nadia akwai matsala fa mutumin nan gaba daya so yake ya hanani shakatawa besan ni auren nan da nayi saboda na huta nayishi ba,ke kinga duk ba wannan ba kinsan gobe zani gidan bikin nan ko and nifa har yanzu bani da gold ke in fada miki jiya har kunyar kaina na dinga ji don in fada miki ni kadai ce babu sarkar gold a wuyana don haka wlh gobe bazan koma bikin nan ba nadia ba tare da sarka da awararo na gold ba yanzu meye abin yi?

#Thank you for reading my story!!!
#Sending love
#CEO Heroine

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro