Chapter 2
"Sake sosa keyarsa yayi yace Ammi karki damu please ina ganin tunda akwai halin yin hakan kawai ayi,kallonsa tayi cikin fushi tace saboda bakasan darajar kudin ba da zafin nema ko?kun tashi kawai kun tarar da kudi sai akace kuma a dinga annobazazzaranci dashi haka?saukowar Alhaji daga upstairs ya sanya ammi yin shiru tana sake kallon takardar
"Lafiya tun daga sama nake jiyo hayaniyarki?yayi tambayar yana kallon ammi,da sauri ta mika masa takardar hannunta tace duba fisabilillahi wannan kudin ai sunyi yawa saboda batasan darajar kudinba tunda ba saba gani suka yiba shine zasu rubuta wannan zungureriyar takardar suce suna bukatar ayi musu haka?kalli hall dinnan gaba daya inajin sau 10 aka taba yin biki a cikinsa saboda tsabar tsadarsa sai governors da senate ne suke kamawa
"Murmushi Alhaji yayi yace haba hajiya menene abin tayar da hankali ai yanzu zamani ya sanja don an kashe kudade irin wannan a gurin biki ba wani abu baneba ina ganin tunda muna da halin yin hakan,saboda haka nina dauki nauyin komai duk sanda bukatar kudi ta taso ka fadamin ba sai kayi amfani da kudin aljihunkaba ya karasa magana yana kallon irfan....shiru ammi tayi tace toh ai shikenan tunda ka bashi wuqa da naman yin annobazzaranci da dukiyarka Allah ya bada sa'a
"Kallon irfan Alhaji yayi yace gobe inada meeting da managers na wasu companies guda 2 kuma bazan samu dama ba ya kamata kaje da wuri saboda ka hadu dasu...murmushi irfan yayi yace okay dad insha Allah
"Tsaye take jikin tsohon mirror din dakinta wanda rabinsa ma duk ya fashe sanye cikin doguwar riga wacce kana kallonta kasan an kashe kudade masu yawa wajen siyanta,kawarta bilkisu ta kalla dake zaune tana danna wayarta tace beelie ga wata doguwar riga nan ki cire kayan jikinki ki sata
"Cikin mamaki bilkisu ta dago ta kalli nasreen tace bangane in cire kayana ba saboda me zan sanja kaya?
"Haba Beelie meyasa zaki tambayeni bayan kinsan amsar da zan baki,taya zan fita dake da wannan atamfar da yake jikinki wacce bata wuce 4500 ba ko kinaso ayi mana dariya ne?kina matsayin kawar amarya ya zama dole kiyi looking good kinsan na fada miki wajen gyaran jikin nan da zamu gurine na manyan mutane bazai yiwu muje musu ba tare da mun daukowa kanmu mutunciba nasreen ta karasa magana tana sanya lipgloss a bakinta
"Baki bude bilkisu ta kalli nasreen tace wai ke nasreen don Allah yaushe kika chanja ne gaba daya rayuwarki kin dauketa da zafi don kawai zaki auri mai kudi?
"Kinga mallama nifa na fuskanci tunda na samu irfan zan aureshi kike nuna min wasu alamu na bakin ciki sam sam bakyason cigaba na kinfison muyita zama cikin wahala dagani har ke toh baze yiwuba ni kam assalatu na tayi zama cikin kangi da rayuwar qaranta ta karemin don haka idan zaki sanja kayan nan ki sanja in bazaki sanjaba toh kowa ya kama gabansa nasreen tayi magana cikin fushi
"Ganin yanda ran nasreen ya baci ya sanya bilkisu saka rigar data bata a dole sannan ta kalli nasreen tace tashi mu tafi lokaci yana tafiya
"Wai kina nufin uber zan hau?nasreen ta tambayi Beelie a takaice
"Eh mana toh da me muke hawa idan zamu unguwa wannan wacce irin rainin hankalin tambaya ce?bilkisu ta fada tana kallon nasreen
"Bushewa tayi da dariya tace nawawo over my dead body,wai ke don Allah nayi miki kama da masu hawa uber?ai ni dinnan da kika gani matar manyan mutane ce wlh ko aure nayi dole irfan ya ajiye min kamar motoci 5 saboda ita kanta motar ba sosai nakeson maimaici ba,bushewa bilkisu tayi da dariya tace gaskiyane babbar yarinya don yanzu ta fahimci duk abinda aka fadawa nasreen bata taba fahimta gaba daya rayuwarta ta sauya,kiran karasowar driver din da irfan ya turone ya sanyasu dakatawa da hirar sukayiwa umma sallama suka fita
"Cikin farin ciki nasreen ta fito daga gidansu sedai tana kallon motar da tayi parking kofar gidansu taci birki gaba daya walwalar da take fuskarta ta dauke,cikin damuwa bilkisu ta kalli nasreen tace nas lafiya naga kinci birki anan me kike kallo ne?cikin damuwa nasreen ta kalli bilkisu tace beelie kalli motar da irfan ya turo a daukeni.....kalleta fa matrix ce 2019
"Cikin mamaki bilkisu tace and then?
"And then what? bilkisu wannan wanne irin tambayar banzace,bakya kallon motar da irfan ya turo a daukemu a kaimu wajen gyaran jiki ko kuma baki da idone?taya irfan ze turo a daukeni a cikin matrix instead of range rover...ko nayi mishi kama da wacce zata dinga yawo a matrix,bata jira bilkisu ta sake magana ba tayi saurin kara wayarta a kunne da alama irfan take kira
"Hey...idan na fahimceka gaba daya yanzu baka da wani buri sai na tozartani a idon jamaa right?yanzu banda Allah ya taimaka nida bilkisu zamuje pedicure and manicure ai da tuni ka gama zubar min da mutunci irfan,taya zaka turo driver ya daukeni a matrix?bayan na dade da fada maka cewar a yanzu bani da wani buri illah na ganni ina yawo a range rover....kaga wait nifa irfan abubuwan nan sun isheni idan kana ganin auren nan baze yiwu ba kawai a fasa don bazai yiwu ka dinga zubdamin da mutunci ba nasreen ta karasa magana cikin fushi da masifa
"Bata dade tana wayar ba tayi cutting call din cikin fushi sannan ta kalli bilkisu wacce ta bude baki tana kallonta cikin mamaki tace kinga mu shiga wlh banda ya cemin kannensa ne suka fita da range rover din Allah da bazan shiga wannan motar ba wlhi,A daidai LA BEAUTY manicure and pedicure motarsu nasreen yayi parking suka fito suka shiga gurin banda isa da gadara babu abinda nasreen keyi kana ganinta zaka zaci wata yar president dince ko governor,a hankali ta tabo bilkisu tace look beelie kinga waccan matar,da sauri bilkisu ta mayar da hankalinta wajen kallon hadaddiyar mace wacce tasha gwala gwalai hatta sarkar kafarta (anklet)da tasa ta gold ce taci gaba da kallon matar wacce aka dukufa ana yi mata wankin kafa tace naganta nasreen ya akayi?
"Murmushi nasreen tayi tace amaryar sarki ce ba'a fi 5 months ba naga pictures din bikinsu yana trending nasan kema kin gani don haka it's my lucky day yanzu zan tashi in karbi digits dinta,da sauri Beelie ta zaro ido tace ke nasreen matar sarkin zakije ki cewa ta baki number dinta gaskiya tsaurin idon naki yayi yawa karki manta dai ruwa ba sa'an kwando bane,kallon bilkisu nasreen tayi sannan ta tabe baki tace lallai ma beelie idan ita matar sarki ce ni kuma matar billionaire kinga kuwa tafiyarmu zatayi kyau da ita beelie kalli sarkar wuyanta ki kalli wasu awararo duk na gold a jikinta nima nan da kwana kadan zan fara sararawa cikinsu don wallahi muna yin aure zansa irfan ya siyamin gold set....bata jira bilkisu tayi magana ba tayi saurin mikewa ta nufi inda hajiya nafeesah wacce ake kira da kilishi ke shirin fita daga shagon nasreen ta tari gabanta tace "hey"
"Murmushi kilishi tayi tace sannu
"Amm please idan bazaki damu ba inason digit dinki oh sorry i am nasreen muhammad by name...nice wacce irfan kamal ze aura ina gayyatarki bikina on 28th of this month nasreen ta karasa magana cikin tsananin isa da izzah
"Sosai nasreen tayi matukar birge kilishi ganin yanda take abunta babu alamar tsoro tabbas tana matukar son jaruman mata kamar nasreen idan har tayi nasarar kawance da nasreen tasan zata samu duk abinda takeso domin ta fuskanci halinsu yazo daya....karbar wayar tayi sukayi exchanging number sannan ta wuce sukayi sallama
"Gaskiya nasreen ke bala'i ce wallahi ni kin fara bani tsoro ma bilkisu ta fada tana kallon nas...dariya nasreen tayi tace haba kawata meye don nayi kawance da matar sarki kema idan kinaso ina iya hadaku kawance,da sauri beelie ta rike baki tace ke rufamin asiri ban tafasa ba balle na kone kedai da kika ga zaki iya sai kiyita fama
"Sai wajen 6pm suka fito daga wajen gyaran jikin sosai ake yiwa nasreen gyaran jiki duk da ba wannan ne zuwanta na farko ba tafi 1 week tana zuwa,a gidansu nadia aka saukesu a gurguje nasreen ta matsa su karasa saboda ta karbarwa bilkisu Asoebi dinta na ankon bikin,karbar kayan tayi a take tayiwa nadia transfer 80k na ankon data karbarwar beelie tukunna suka fito
"Cikin mamaki bilkisu tace nas ni kam wannan kayan har nawane ankon naga kamar 80k kikayi mata transfer ko?
"Murmushi nasreen tayi tace eh mana kinsan ankon fa duk mutum daya 80k ne each,kinga wannan nadia din da kika gani event planner ce babbar kawarsu zahra buhari ce dasu fatima dangote itace take shirya mana bikin nan yanda ya dace kuma ba sena bata baki na wajen fada miki irin arzikin dad dinta ba
"Haba nasreen wannan wasa da kudin yayi yawa taya za'ace kamar mu ba yaran kowa ba mu fitar da anko har na 80k ina ganin wannan cusa kai ne inda Allah be kaimuba.....da sauri nasreen ta dakatar da ita tace point of correction sedai idan ke kike cusa kanki inda Allah be kaiki ba amma ni kam Allah ya riga ya kaini kuma ya kashe ya bani na amshe kuma kece kike ganin kanki ba yar kowa ba ni kam yanzu yar kowa ce don jira nake kawai na auri irfan senasa ya budewa Abba babban shago me zaman kansa ta karasa magana a daidai lokacin da mota tayi parking a kofar gidansu bilkisu akayi dropping dinta sannan aka karasa da nasreen nasu kofar gidan duk da basu da wani nisa tsakanin gidajen layine kawai
"A gajiye ta shiga gidan ta tarar da umma zaune kan tabarma a tsakar gida tasa radio gaba tana ji,murmushi nasreen tayi tace su umma kenan iyayen jin radio nina rasa me kikeji idan kinsa radio dinnan a kunnenki kina faman ji......murmushi umma tayi tace madhubala wutar kyau kyakkyawarmu kuma kyauta daga Allah har an dawo ne?
"Wlh har mun dawo don ma mun tsaya gidansu nadia na siyawa bilkisu ankon ranar dinner don kinsan yar wahala ce yanzu seta fara karantomin kauli da ba'adi tace yayi tsada nasreen ta karasa magana tana zama kusa da umma,dariya umma tayi tace ku kuka sani dai fadanku kamar na kaji yake tsakaninki da bilkisun taki shiyasa ko da kuna yara babu me raba ku fada idan kunayi,itama Nasreen murmushi tayi tace toh ai beelie dince yar rainin hankali yawwa umma kinsan me?
"Girgiza kai Umma tayi tace a'a wutar kyau na sekin fada
"Umma yau da matar sarki na hadu wajen gyaran jikin nan har munyi exchanging number da ita ma
"Cikin tsananin mamaki umma tace ke nas...nas banason karya matar sarki fa kikace
"Allah umma matar sarki wannan amaryar da ya aura dinnan toh itace yanzu ta zama kawata wlh don yanzu ma naga sakonta a whatsApp tana cewa dafatan na koma gida lafiya
"Ayiriririri Kai jamaa tabbas na yarda arziki a jininki yake nasreen shiyasa ban taba yin hawaye ko bakin cikin samunki ke kadai ba a matsayin yar mu...gyaran muryar Abba ne ya dakatar dasu daga magana a tare suka kalleshi
"Menene yake faruwa naji ana guda a cikin gidan kamar zaa kawo sabuwar amarya abba ya fada yana ajiye butar hannunsa kasa,murmushi umma tayi tace toh ba dole nayi guda ba yau nasreen a wajen gyaran jikin da take zuwa ta hadu da matar sarki yanzu har sunyi musayen number suna gaisawa wannan harkar arziki ba dole nayi guda ba
"Toh ikon Allah nasreen yanzu har daukakar taki ta kai haka kai Alhamdulillah,sannan ya kalli umma yace me zan samu ne aljihuna ba ko sisi inaso zan fita,turo baki umma tayi tace ni ma kam hakan take don sauran chanjina dazun nan na kwashe na bawa dillaliya sedai wajen nasreen nasan baza,a rasaba,da sauri nasreen ta bude jakarta ta kirgo 10k ta mikawa abba tace yayi managing zuwa safiya,daga nan ta dauki jakarta ta shiga dakinta ta fada kan gado ta fara danne dannen wayarta musamman Instagram da TikTok saboda anan ne nasreen ke ganin designers abubuwa wanda suke jan hankalinta sosai
"Tsaye suke kamar zakarun da sukayi fada suka gaji duk da wannan ya zame musu inda sabo sun saba da hakan,cikin fushi tace haba irfan taya zaa dauko abu tun iyaye da kakanni a kawoshi zamaninmu ace wai zaayishi da bikinmu?wannan abun ya zama old model so local gaskiya ni ban amince da hakan ba idan har kai ka amince toh babu inda zani
"Wani gumi ne ya karyo masa cikin tashin hankali yace look nas...try to understand we have no time yau ne kawai damar mu gobe zaa fara bikinmu sannan bani da lokacin da zan zauna yiwa ammi bayani balle ta fahimceni kuma wannan wushe wushe din da kike gani alada ce tasu ammi sannan duk bikin da zaayi a gidanmu sai anyishi saboda haka please kiyi hakuri nas-nas duka duka abin baze wuce 3 hours ba fa anyi an gama meyasa kike damuwa ne haka?
"Of course i have to worry idan kai kana ganin it's normal toh ni it's not normal to me,bani da ra'ayin traditional events a bikina saboda haka akwai sauran lokaci zaka iya yiwa ammi bayani ta fahimcemu gaba daya didn't you tell her that i am a slay queen?i am a model baze yiwu ayi irin wannan abin a taron aurena ba ta karasa magana tana juyi a gaban irfan
"Nas....bamu da lokaci please try to understand me wannan ba lefina bane umarnine ammi ta bamu daga ni har ke yanzu haka suna chan suna shirye shiryensu taya kike tunanin zata fahimceni?irfan ya fada a takaice inda kasan ransa ke matukar yi masa azaba
"Da kyar irfan ya shawo kan nasreen kafin ta amince zataje gidansu irfan din goben saboda ananne aka shirya wushe wushe din wanda aka kashe kudade masu matukar yawa wajen tsarashi gaba daya farfajiyar gidan nasu an mayar da ita kamar hall saboda tsananin decorations
WUSHE WUSHE DAY
"Banda tashin kida irinna sudanese da yan maiduguri da tashin kamshi babu abinda gurin keyi,tuni amarya nasreen da manyan kawayenta sun halarci gurin idan ka hango ango irfan baki har kunne banda murmushi babu abinda yake yi cike da farin ciki,kowa ka kalleshi gurin banda fara'a babu abinda yakeyi....guda kawai ke tashi inda manyan kawayen ammi wasu ma duk daga sudan sukazo suke faman yi suna yaba kyau irinna nasreen suna faman liqa mata kudi,babbar kawar ammi hajiya salamatu ce aka bawa damar tayiwa nasreen kamu inda aka kwaba lalle da ruwan turare zaa sanya mata a hannunta,tuni aka fara guda inda ta karasa gurin amarya zatasa mata lalle,babban abin mamaki nasreen sam taki tsayawa a sa mata lallen banda yatsine fuska babu abinda takeyi kamar irin dan shugaban kasa ya shiga ghetto area lol
"Cikin isa nadia ta karbi lasifikan dake hannun MC hankalin kowa ya koma wajen nadia don jin me zatace kowa dai ya ganta yaga kawar amarya saboda kalar ankon nasu ma dabanne,gyaran murya tayi tace Hey guys i am Nadia Mukhtar zage nasan ko baku sanni ba tabbas zakusan mahaifina saboda he's very popular and he's among the richest billionaires of the world,maganar gaskiya amaryar mu bata kaunar traditional events kuma she's allergic to lalle dan gargajiya and i am sorry to say wannan taron is so local an dena irin wannan kalar abun i don't really know ma ko waye ya bada shawarar ayi irin wannan kalar abun so very boring and annoying,cikin zafin nama ammi ta taso ta karbe lasifikan hannun nadia sannan ta sauke mata kyawawan mari har guda 2.....tuni guri ya hade da hayaniya cikin mamaki kowa ke rike baki
Thank you for reading my story!!!❤️
Heroine 🦋
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro