Chapter 1
Flash back
"Ya salam umma tun dazu kike faman kirana kinsan na fada miki nan da 1 hour zanyi baqi na fada miki ban shirya musu komaiba....nasreen ta karasa magana cikin shagwaba tana danna wayarta iPhone 13 pro max wacce ta mallaketa cikin sati 2 na haduwarta da irfan,murmushi matar da aka kira da umma tayi tace nas nas dina madhubala wutar kyau zonan yanzun nan zaki tafi kije ki karasa yin shirye shiryen umma ta karasa magana tana janyo katuwar ledar dake gefenta tace duba min laces dinnan sunyi kyau kuwa ko kuma a sako min wasu?
"Cikin mamaki nasreen ke bin laces din da kallo tace wow amma umma wannan laces din sunyi mugun kyau sosai a ina kika samu?
"Gyara zama umma tayi tace dazun nan dillaliya ta kawo minsu na karbesu zanyi fitar biki dasu kin gansu kala 8 ne na karbesu zan dauki guda 4 nayi amfani dasu sena hada da sauran supers dinnan da kika bani sauran guda 4 din na daukarwa su hajiya kareemah ne saboda kinsan halinsu ba iya siyan kaya masu tsada zasuyi ba ni kuma bazan yarda su kunyatamu ba don haka gara a siya musu kawai kayan da zasu sa kinsan bikin manya dole mu dau magana umma ta karasa magana tana sake kallon laces din
"Murmushi nasreen tayi tace hakane umma dama yaushe zan yarda wasu yan wahala su batamin plans dina dana dade inayi,ai wlh duk wanda beyi dressing na daukar magana ba babu inda zashi wlh ko yaya muke da mutum,yanzu umma wannan laces din nawa kenan?
"Gasu nan kowanne daya 80k ne kinga guda 8 ya kama 640k,sai kudin shaddar da babanki ze sanya ranar daurin aure shima atleast yana bukatar 200k har kudin dinki kenan kawai ki fadawa irfan 1 million nake bukata kinga da sauran chanjin sena komawa malamin nan
"Turo baki nasreen tayi tace kai umma nifa ko ba malami irfan yana sona tunda yana yimin duk abinda nakeso meyasa zamu dinga wahalar da kanmu muna asarar cash?dariya umma tayi kadan tace kin fara shirmen naki ko yaro besan wuta ba sai ya taka kinga tashi ki bani guri kuma ki tabbatar anjima idan yazo ki karbar min kudin nan don nacewa dillaliya gobe da safe tazo ta karbi kudinta,murmushi nasreen tayi tace okay ba damuwa zan bashi account number dinki seya tura miki kawai
"Bata wani jima gaban mirror ba tana shiryawa powder kawai ta sanya sai lipgloss wanda yayi matukar dacewa da lips dinta,ko baa fada mata ba nasreen tasan cewa ita kyakkyawace wacce kyawunta baya boyuwa a duk inda ta shiga tana da matukar kyau mai matukar birgewa duk inda nasreen ta shiga sai an tanka yanda take da kyau ko da cikin kawayenta mata ne,ajiyar zuciya tayi bayan ta dauki wayarta ta yafa siririn veil din abaya dinta ta nufi madaidaicin sitting room din gidan inda take saukar irfan idan yazo
"Murmushi tayi bayan ta zauna gefen kujerar da yake zaune a hankali tace "KOH"(king of heart)
"Murmushi shima yayi yace my queen how are you?ya karasa magana dimple dinsa yana lomawa tare da hadadden pink lips dinsa wanda ya dace da fresh skin dinsa
"I am fine honey,tayi magana cikin shagwaba
"Sun dade suna hira kafin irfan ya tambayeta ko ta gama arranging na event din kamar yanda tace ita zata shirya komai yanda ya dace...murmushi tayi bayan tayi mishi wink tace of course love sannan ta mika mishi paper dake hannunta tace yawwa banaso na manta gara na fada maka da wuri umma tana bukatar 1M na fitar biki zasuyi dinki ita da abba
"Wani zazzafan gumi ne na mamaki ya fara zubowa irfan ganin yawan tarin kudin dake jikin takardar da wasu events na banza da wofi....cikin tsananin mamaki yace wannan meye?nifa ban ganeba
"Murmushi tayi cikin shagwaba tace gashinan gaba daya total ne na kudin da zaa kashe wajen bikin,gasu nan da events din da zaayi duka ka duba da kyau and i am sure nasan zai birgeka sosai ta karasa magana tana kallonsa
"Sake kallon takardar hannunsa yayi yace nasreen wannan abubuwan ai sunyi yawa taya za,a jera kwana 10 ana biki...beside ma wannan kudin yayi yawa,are you expecting me to pay for this bill?bata jira ya karasa magana ba tayi saurin dakatar dashi tace of course,wai ma taya zakace events sunyi yawa and you are telling me wai kudaden ma sunyi yawa kasan wahalar da nasha wajen tsara bikin nan?wannan takardar da kake gani event planner na dauko wacce ta shiryawa su zahra buhari bikinsu ya tafi very softly taya zaka cemin wai events sunyi yawa kanaso ka kunyatani gaban kawayenane don kawai zan aureka?
"Zahra buhari....shine sunan da irfan ya maimaita a hankali sannan ya kalli nasreen da tuni tayi kicin kicin yace amma ai ke ba zahra buhari bace right ?
"Of course....amma ina da damar da zanyi duk abinda sukayi a bikinsu saboda kana da halin da zakayi haka irfan
"I am not a president son, and i am not a governor son nasreen i am just a normal person saboda haka wannan kudaden da kikayi listing ya kamata ki rage wasu abubuwan sunyi yawa...mikewa tayi tsaye a zafafe tace irfan wallahi tallahi seka biya wancan kudaden baze yiwu ka kunyatani ba don kawai ina sonka shikenan sai ka dinga yimin abinda kaga dama?tun ina karama nake da burin idan bikina yazo zanyi yanda nakeso dole bikina ya zama world renowned wedding duk duniya ina bukatar tasan zan auri mutum kyakkyawa kuma me kudi kamarka saboda haka ya rage ya naka idan har bazaka biya wannan kudaden ba irfan na fasa aurenka.....
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un shine kalmar da irfan ya fada da sauri don idan babu abinda ya tsani ji a yanzu shine rabuwarsa da nasreen,yana matukar son nasreen fiye da tunaninsa yana matukar kaunarta bazai taba iya rayuwa babu ita ba sedai halayen nasreen a yanzu suna matukar bashi tsoro,da sauri ya kalleta yace it's ok zan biya na yarda
"Murmushi tayi tace really?
"Daga girarsa yayi yace yeah sure
"Lumshe idonta tayi kadan tace Awwwwn that's why i love you darling Muah...basu wani dade suna hira ba irfan ya tafi saboda Ammi tana jiransa don nasu shirye shiryen ta bangarensu
"Cikin sallama ya tura kofar hadadden palour wanda yayi kama dana sarauta kyau da tsaruwa ya tarar da ammi zaune tana shan kunun shinkafa,bayan ya gaisheta ya zauna a kujerar dake facing din ammi yace ammi barka da hutawa
"Ajiye cup din hannunta tayi tace barka dai irfan ai tun dazu nake expecting ganinka bakazo ba sai da hisham yazo yake fadamin kaje gidansu nasreen ne
"Cikin kunya ya sosa keya yace eh wlhi ammi naje ne inji wanne tsare tsaren ya kamata a shirya naga lokaci yana kurewa you knoe it's just 7 days left to us
"Murmushi tayi tace hakane Allah dai ya nuna mana lokaci nifa farin ciki nakeyi Allah ya hadaka da yarinya ta gari wacce ba yar gidan masu kudi ba saboda yaran masu kudin nan sun fiye karya ga rashin tarbiya da anyi musu magana suce ai iyayensu suna da kudi amma kaga wannan lafiya lau zakuyi zamanku
"Gaban irfan ne ya fadi don shi kam damuwar da nasreen ke sanya mishi har gara yar masu kudin ya dauko...bai karasa tunaniba yaji maganar ammi ta sauka a kunnensa cewar yanzu me suka tsara ta bangarensu?
"Jikin irfan sanyaye ya mikawa ammi takardar yace ammm ehhh wannan sune events din da zaayi ta bangarensu bansaniba ko kema zaki kara wani akai.
"Ta dauki 2 minutes tana duba takardar kamar wata makauniya take sake bin takardar da kallo,cikin tsananin mamaki ta dago ta kalleshi tace irfan wannan kuwa itace takardar daya dace ka mikomin kuwa kodai kayi kuskurene ka mikomin wannan don wannan takardar tafi kama da ta office
"Murmushi yayi yace itace ammi ya karasa maganar gabansa na faduwa
"Irfan kana da hankali kuwa?billions din kudade nake gani fa bama millions ba...wai ma ba ka fadamin cewar yarinyar mallam shehu bace ba?
So finally here is the update...❤️
Heroine 🦋
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro