Uku
NAHAR
_03_
Kallon shi take yi, zuciyarta tana kara kuna. Sai da ta samu waje ta zauna sannan ta zuba masa kananan idanuwanta.
"Ka fada min gaskiya Isma'il. Me yasa zaka sa a dauke su?"
Kallon ta shi ma yayi cike da rashin fahimta, da kuma mamakin zarginsa. Amma sai yaji kamar shine bai fahimci me take nufi ba da furuncin ta, so he smiled.
"Darling kar rudewa ta saka kina magana irin haka mana." Ya fadi yana dafa kafadun ta. Matsawa tayi domin ta zamewa rikon da yayi mata.
Murya babu zaki ko walwala ta sake kallon shi. "I'm not a fool Isma'il. I have always been smart ko ka manta ne? Ni da kai mun sani ba'a raina mun wayo. Rashin nuna damuwar ka ma kadai ya isa ya nuna min cewa akwai sa hannun ka a batan nan da suka yi. Ka fada min cikin ruwan sanyi! Ina ka kai mun yarinya?"
Wani numfashi yaja, kamar yana kokarin tattaro duk hakurin sa. Baya so ya fadi abunda zai kara tayar musu da hankali. Ya san halin Aisha sarai amma bai taba tunanin zata tuhume shi da irin wannan laifin ba. Murmushin karfin hali ya sake yi sannan ya dubeta.
"Ki dai nutsu, sai muyi magana anjima. Naga alama har yanzu hankalin ki a tashe yake. Amma ina tabbatar miki da cewa za'a gan su cikin lokaci kalilan. Kin bar su Ummah a parlor. Ya kamata ki fito su san kina lafiya." Da hakan ya fita a dakin tana bin shi da kallo da yake nuna tsananin fushin ta.
Isma'il kuwa ji yake kamar kan shi zai tsage gida biyu. Wai ya za'ayi ta ce yana da sa hannu a cikin lamarin? What if in har ta fada yan sanda suka ji? Ya san babu ruwansu take zai shiga jerin prime suspect domin already an zo an dauki mai shagon kusa da gidansu wanda ya shaida cewa ya ga sanda Nahar ta nufi titi dauke da Haifah a hannun ta.
Toh in aka ji kuma matar sa tana fadin cewa tana zargin sa, tabbas shima ya shiga sahun su.
Bangaren sa ya wuce, yana rike goshinsa kamar hakan zai sassauta ciwon kan da yake ji.
Sai da ta tabbatar ba parlor din yaje ba saboda lekan sa da take yi sannan ta gyara fuskarta ta fita zuwa parlorn da murmushin da ko kadan bai kai zuci ba.
"Maimoon, kije ki kawowa Umma lemo." Ba musu ta tashi sannan Aishan ta zauna gefen Ummahn.
Shiru ne ya ziyarci wajen kafin Umman ta hakura ta fara magana. "Ya kamata ki sakawa ranki salama Aisha."
Kamar wadda take jira sai kawai ta fashe da kuka tana kifa kanta a kan cinyar Umman. Cikin kukan take magana mai tsinka zuciyar me sauraro.
"Umma shi ne ya dauke su. Ni zuciyata tana gaya min shine silar batan su. Dama tun jiya nake ji a jikina abu zai faru amma shi ko a jikin sa. Umma dama ba son su yake ba..." wani kukan ya kwace mata, ta cigaba da yin abunta. Umman nata kuwa jikinta sanyi yayi. Abun kuma ya sake daure mata kai.
Kwata kwata bata yi niyyar zuwa gidan ba saboda kunya irin tata amma jin yadda Aishan ta dinga mata kuka a waya ya saka ta zo saboda ta san matsalar ta na hawan jini da ya kamata bayan shekarar ta biyu da aure. Duk da tayi duk yin ta taji dalili a wancen lokacin, fir Aishan taki ta furta menene. Sanin zurfin ciki irin nata ya saka ta hakura musamman ma da taga Isma'il din yana kokarin sa.
"Ya zaki dinga magana irin wannan kamar wata karamar yarinya Aisha! Don Allah yaushe zaki girma ne! Maza tashi ki share hawayen ki." Ta fadi cikin sigar rarrashi.
Ita kuwa Aisha bata da niyyar tashi sai da Umman ta dago ta.
"Ummah baki gani bane? Ko zuwa duba ni Mama batayi ba saboda da ita aka hada baki aka sace min yarinya. Dama basa so na. Ni na san dole watarana sai sun ja ra'ayin sa kuma gashi nan. Ai gashi nan." Jikinta har rawa yake alamar ita da gaske take shi ya dauke mata yarinyarta. Shine don kar a gane aka hada da me aikin ta.
Shiru Ummahn tayi kawai abun yana sake bata mamaki. "Ki saurare ni!" Wannan karan da kakkausar murya ta fada saboda taga alama rarrashi ba zai yi tasiri ba.
"Bana son na sake jin irin wannan munanan kalaman daga bakin ki. Mijin naki da mahaifiyarsa kike jifa da irin wannan kalaman! Ashe kin watsar da tarbiyyar da na miki!"
Shiru ta danyi sannan ta hadiyi wani abu kafin ta sake yin magana. "Wallahi Umma bata sona. Allah..." dukan da Ummahn ta kai wa bayan tane yasa tayi shiru. A gefe guda kuma sai tausayinta ya kama Ummah.
Lallai akwai abunda yasa Aishan take fadan hakan amma dai bata so ta zargi komai. Zato zunubi. Ba tayi magana ba Maimuna ta shigo da tray a hannun ta.
Ba su taba komai ba suka bar gidan in banda kuka babu abunda Aishan take yi.
Tana zaune tana mai da ajiyar zuciya har bacci ya fara fusgarta taji wayar ta na ringing. Ba shiri ta tashi ta tafi ta dauka.
"You're speaking with Inspector Muhyiddeen. Na kira number mijin ki bata shiga. Ki hada ni dashi, an samu wani information."
*****
Kafin kace meye dukka sun ukun sun iso bakin dakin da su Nahar suke har Dr Othman da Dr Ashir suna rige rigen bude handle din,ganin haka sai Dr Ashir ya saki handle din,Zunnurain ne ya fara shiga ciki yaga nurses biyu tsaye Akan Nahar din,ganin shi ya saka suka ja baya shi Kuma Dr Ashir ya matso kusa suka rufa kanta suna ta kokari daidaita komai,bayan kamar minti sha biyu Naga ya matsa daga wurin Yana samun kujera ya zauna,shi Kuma Dr Ashir Yana yi mata allura sannan ya daidaita drip din hannunta,ya juya Yana neman Ina Dr Othman din ya shiga sai ya ganshi gaban gadon baby Haifa Kan kujera ya rufe idon shi Yana kallon sama,ganin haka sai kawai ya fita ya ja kofar a hankali.
Fitar Dr Ashir kenan sai Haifa ta farka daga baccin tana motsi alamun kuka takeson fara wa,Jin motsin ya saka shi bude ido,ya Mike ya karaso wurinta,yana daukan ta kuwa ta saka kuka."oh my God,what did I do to deserve this" cewar Zunnurain.haba mana daga wannan sai wannan tun jiya nake abu daya for godsake yanzu ni gashi Ban samu wani na yaran nan ba ma,sannan taya ma zanyi rainon yarinyar nan.Nurse! Dr Othman ya kwalla kira,tana budewa ya Mika mata yace "please do take care of this baby, ki yi mata abinda kike ganin ya dace Tayi shiru please".
Bakin gadon da Nahar take yaje ya tsaya a kanta ya kalleta na wani Dan lokaci yana Jan tsoki,yace "lakum jamien Sabab dhalik"(you all cause it) da yaren maman shi,wani bangaren na zuciyar shi yana cewa she's pretty though,yayi saurin kawar da tunanin yana zaro wayar shi daga aljihun shi.
"Hello Mummy,how was the meeting?"
"It went well habeeby, Ya masu jikin? Naji alamun gajiya a tattare da kai ko zaka taho ne idan ya so a samu masu kula da yaran nan,kaga tun jiya ma fa ban fadawa Daddyn ka ba,saboda ya dawo late kuma ya gaji"
"No Mummy I can't go anywhere,zan zauna anan har sai Naga abinda hali yayi,Kinga yarinyar nan ma from all indication she looses her memory". Salati Mummy tayi tace " let me get prepared Ina tafe".ok mum!.....
******
*Gare ku masu karatu!* Ya kuke ganin labarin? Mene ne ra'ayin ku game da wannan shafin?
Ga wanda suke so su dinga samun update akai akai zasu iya joining ta wannan link din:
https://chat.whatsapp.com/GuF6mZcV0998DjE8Hngl6P
Ko kuma suyi following account din mu na wattpad in da zamu dora littafin a dunkule. @AeshaKabir.
Mungode.
Rufaidah Yusuf
AeshaKabir.
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro