Tara
_NAHAR_
_09_
Mummy ta ajje wayar ta na cewa Zunnurain "yawwa dama jiran ka nakeyi tun dazu muyi magana a ina ka tsaya",Mummy akwai wani conference call din da mukayi da Dr's daga India ne" Bai ko karasa ba Mummy tace ok Samu wuri ka zauna ta nuna gefen gadon ta,tana dauke papers din wurin.
Cire glasses din idonta tayi sannan ta kalli Zunnurain din tace mishi "maganar da zanyi maka ka maida hankalinka sosai domin babu wasa a cikinta,kanaji na ko", "yes mummy I am with you" yace Othman ya fada mata.
Gaban Zunnurain ya fadi sosai Domin dama yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki,Jin abinda mummy din tace mishi.
"Wai bakajin abinda nake fada ne",naji Mummy,ni banga alamar kaji ba,Allah naji kince naje kano next week wurin yarinyar Mummyn kano ita ce kika zaba min . Sai Mummyn tayi murmushi "dats good of you my boy" saura Kuma idan Excellency ko Hajiya suka kiraka ka chanza min zance sai naci mutuncin ka Allah.
"Amma Mummy ni banida da wata damuwa da abinda kika zaba,kawai yarinyar ce batada kunya Sam Sam,Kinga last time da mukaje gidan har fa Gorilla ta kirani da shi" inji Zunnurai ya fadi yana bata rai. Dariya Mummy tayi tana janyo shi jikinta tace "haba my baby kayi hakuri ka ji I am just trying to make the right choice for you uhm,zanyi mata fada Kuma insha Allah zata gyara" tashi yayi kawai ya fice Bai sake cewa komai ba,yana fita Mummy ta sake Kiran Umaimah suka dora wayar tasu daga inda suka tsaya.
Chef Shola tana dauke da jug su Kuma sauran yaran ta da suke tayata ayyukan girkin wasu na dauke da flask wasu plates su nata Kai kawon shirya lunch a dining,bayan sun jera ita suka Bari a karshe ta gama kenan ta juya taji Nahar ta Fado jikinta da gudu,ta bude baki zatayi magana kenan kawai taga Amir ne ya biyo ta,murmushi kawai tayi ita Kuma Nahar din tace "Anty Shola Dan Allah kice Kar Yaya Amir ya rama kinji" Sai Amir din yayi saurin cewa "aikuwa yarinya sai na rama Ina fa zaman zamana tazo ta baya tayimin dundu" murmushi chef Shola ta sakeyi tace musu "Kai Amir ta girman ka ka biyewa wannan karamar yarinyar babu ruwana idan Her Excellency ta sauko ta ganku" aikuwa da sauri Nahar ta sake falfalawa da gudu sai dakin su. Amir ya kalli Chef yace "ai kin huta tunda kin korar min me tayani hirar" sorry sir ta fada tana barin wurin.
Da dare wurin karfe 9 Nahar ta bude kofar parlor din su Amir tayi saa kuwa Gogan yana zaune a parlorn yana conference call a system iPad nashi,wuri ta samu a kasa ta zauna tana jiran ya gama wayar da yakeyi har tayi bacci a zaune, yana kallonta ta gefen idon shi har tayi baccin,sai da ya gama wayar sannan ya dauke ta ya dora ta a saman kujerar shi,yana sauketa tayi saurin mikewa zaune tace Yaya Zunnurain,oh my God ya fada a ranshi ya juyo,what is it ya tambayeta zamanta da Chef Shola sosai take gane turanci Kuma take karantawa tunda gdn ba hausawa bane. Yaya Dama so nakeyi ka sakani a makaranta tana raurau da ido kmr zatayi kuka,shi abinne ya bashi haushi don baiga wani abin kuka ba anan ,yace mata "waye ya aiko ki,Kuma idan kuka zakiyi ki tashi ki tafi",Yaya Amir ne da Anty Shola,tashi kije kiyi bacci "malama shi Amir din menene ya hana shi saki a makarantar"anan wurin ya Barta ya shige dakin shi,haka ta tashi tana hawaye ta fice.
*******************
Isma'il ne Akan gadon shi yana sana'ar da ya saba kullum,wayar shi ce a hannun shi yana kallon hoton su,a haka bacci ya dauke shi.
"Hello hauwa,karki manta goben zan shigo da safe domin mu karasa tattauna karashen zancen namu" ok matsalar aminiyar kwarai sannna sukayi sallama.
Tana kashewa hauwan tayi tsoki tace shashasha kawai banyi aure ba kije ki auri Yaron da shi ne burin kowacce Budurwa ga kudi ga kyau kiyi tunanin zan barki ki zauna a gidan....
Da safe Kiran wayar mama ne ya tashi ismail ya dauka tare da sallama "ta amsa sallamar sannan tace babana ba dai ko sallar asuba bakayi ba" yace mama "nayi sallar bacci ya sake daukeni saboda Ban samu bacci da wuri ba jiya".
#Rufaidayusuf
#Aeshakabir
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro