Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

Shida

*NAHAR*

_ 06 _

Jumuat Mubarak everyone.

*****


Tukin sa ya ke a hankali saboda tunanin da yake ta faman yi. Ko dai ya sabawa umarnin mummy ne? Ko dai yaje can inda ya kade yarannan ya tambayi ina ne gidan su? Ya san dole za'a samu wanda ya san su idan ya siffanta su. Ko dai, ko dai? Yana ta tunani karshe zuciyarsa ta amsa amsa a'a gara kawai su tafi dasu din. Gara ya tafi dasu a inganta rayuwar su. Duk da bai ga alamar suna wahala ba sam a tare dasu, bai ga alamar farin ciki a tare da Nahar din ba. Gara ma ita Haifah tana rahar ta musamman in taga Nahar din. Ko shakka baya yi sun shaku sosai duk da baya tunanin akwai wata alaka ta jini a tsakanin su.

A wajen Dr Ashir ya bar su saboda baya so wani abun ya fitar dasu ma har wani ya gan su. Da farko da su din zai fita sai kuma ya fasa.

Da isar sa government house din, ya yi parking motar a gefe sannan ya kira mummy ya fada mata ya iso amma ba zai shigo ba saboda kar a mishi wulakanci by the gate.

"Sun san da zuwan ka ai." Haka kawai tace. Ba don yaso ba haka ya shiga. Ya fara tunanin yadda zaiyi kenan ya hango wata yarinya da ba zata kai shekara ashirin ba tana tahowa inda yake. Sanye take da riga da wandon pakistan a jikin ta. Fuskarta ba kwalliya ko kadan balle murmushi.

"Mummy tace ka shiga."

Kamar ba zai amsa ba amma sai yace, "ke ba a kowa miki gaisuwa bane?"

Ita ma ba ta amsa ba tayi wucewarta bangaren ta.

Ran shi ba kadan ya baci ba amma sai ya danne ya nufi kofar da zata sada shi da makeken parlor din da yafi na maman shi girma. Bai tashi sanin girman da kyaun parlor ya kai haka ba sai da ya shiga dauke da sallama a bakin sa. Can ya hangi Mummyn da kawarta suna hira. Cikin tafiyarsa me cike da nutsuwa ya karasa wajen yana sake wata sallamar.

A tare suka amsa masa suna mishi maraba.

"Good evening mum, sannu da hutawa." Ya gaishe da kawar mummyn. A take taji ya sake kwanta mata a rai.

"Evening my son. Ashe haka ka hadu da accident? Allah ya tsare. Please feel at home. Karasa balcony, Teetee zata kawo maka drinks."

Mikewa yayi, kan shi a kasa yana godiya. Yana wucewa Hajiya Nafisah ta kalli Hajiya Hairah.

"Indeed your son, well trained. Allah sa su hada kan su. In ma taki, zan yi forcing dinta. Nayi nayi taki rabuwa da yaron nan da take kulawa dan talakawa na karshe."

Dariya Hajiya Hairah tayi. "Yaran yanzu ai sai a hankali." Nan dai suka cigaba da hirar su musamman ma akan yaran nasu.

Othman na karasawa ya zauna a patio chair din wajen. Wasu wooden chairs ne daga ganin su kaga kirar turkey, a gefe kuma ga wani artificial water fountain da ya burge shi sosai ba kadan ba. Iskar wajen ma daban take saboda yan shuke shuken da suke kewaye da wajen. Yayi nisa a kallon wajen Teetee ta karaso ta zauna ta cigaba da amsa wayarta.

"Zee, can you imagine? Wai mummy ni ta saka entertaining guest din ta. Zan miki magana anjima." Sannan ta kashe wayar taba satar kallon sa ta gefen ido.

"Ba laifi, amma not my type." Ta fada a ranta amma a fili sai ta gyara murya.

"Hi, chimpanzee!" Ta fada da karfi, cike da tsokana da son bata masa rai amma ita ma tasan ko makaho ne ya shafa fuskar Othman yasan kyakkyawa ne. Fatar sa fara ce kamar ta mahaifiyarsa, ga manyan idanuwan da bata ji zata iya kallon su na sama da mintuna biyu ba tare da ta tsorata ba. Dan mitsitsin bakin sa ya sanya ta fara tunani anya yana iya cin abinci kuwa ya koshi? In yana ci, awa nawa yake yi? Sai hancin sa da bata san yadda zata kwatanta shi ba, shi ba dogo ba shi ba gajere ba. Ta hancin ne kadai zata ce yayi kama da mahaifinsa wanda ta gani a hoto few minutes ago bayan mummyn ta ta gama gaya mata zasuyi bako kuma dan gidan governor din Rivers state ne.

Duk wani information da taso ta samu wanda zata batawa Othman rai dashi, bata samu ba.

Shi yasa ta bullo mishi ta nan.

Ba shiri ya juyo kuwa! Shine birin? Goggon biri? Ganin yadda ya fusata ya sa ta sheke da dariya kamar ba zata dena ba.

*****

Sai da ta ajiye mug din tea din a kan table din gaban su sannan ta kalli Aisha tayi wani murmushi mai sauti. "Wallahi kar ki yarda, duk yadda zakiyi ki tabbatar kinyi saboda maza ai basu da amana. Dama naga wautar ki tun farko ai."

Aishan ce ta sa hannu biyu ta dafe fuskarta sannan ta jijjiga kanta. "Wai me yasa kike min haka ne Hauwa? Kin fi kowa sanin ni kadai ba zan iya reno ba."

"Duk ba wannan ba. Ai gashi yanzu kinyi biyu babu. Shawarata dai ita ce ki cigaba da tayar masa da hankali har sai ya fada miki gaskiya. Kuma ki binciki wayarsa, dole ki samu hint." Zaro ido Aishan tayi saboda bata taba tunanin ta duba wayar ba. Ai da tuni ta gano inda ya kai mata Haifah. Ko ma ina ya kai Nahar din matsalar sa ce. Shi iyayenta suka sani ba ita ba.

Sai da ta yi ajiyar zuciya sannan ta kalle ta. "Kina da gaskiya, zan duba."

Gyada mata kai kawai Hauwan tayi sannan suka cigaba da shan tea har mintuna suka ratsa kafin Hauwan tace,

"How far with doctor Hafsah? Kina shan maganin da take baki kuwa?"

Murmushi Aisha tayi. "Toh guardian dita. Ina shan maganin balle ma ki balbale ni da masifa!"

"Toh Allah ya kara lafiya. Kar dai ki bari ya san kina sha tunda last time ya hana ki."

"Dan Allah ji yadda kike dictating rayuwata kawai don ina kiranki best friend. Mtsw yarda ke zanyi.." Aishan ta fada tana dariya. In dai irin wannan ne sun saba.

Dariya sukayi tare sannan suka shiga wata hirar daban. Aishan tana ji kamar karshen matsalar ta yazo tunda Hauwa ta kawo mata mafita. Yanzu ne ma Isma'il zai san hankali bai ishe ta ba har sai ya fito mata da yarinyar ta!

*****

Kwanan Nahar da Haifah biyu a hotel din tare da Hajiya Hairah kafin su fara shirin tafiya. Har yanzu Nahar din bata saki jikinta da Hajiya Hairah ba. Ita kuma Hajiya Hairah kallo ne kawai yake hadata da yarinyar. Ba zata ce tana son yarinyar ba amma kawai dai taji ta kwanta mata a rai. Yara basu cika burge ta ba balle ma Haifah ta burge ta.

Su na zaune a dakin ne, Nahar tana bawa Haifah Cerelac Hajiya Hairahn shigo.

"Ki tashi, tafiya zamuyi." Hakan kawai tace cikin muryarta mai nuna isa da izza.

Ba shiri Nahar din ta tashi tana kade kayan ta kamar a datti ta zauna. Kallon yadda sabon kayan suka yi mata kyau Hajiya Hairah tayi sannan ta kauda kanta gefe.

Tana tsaye, Othman ya shigo ya mata alama da ta fito. Harararsa tayi kafin ta sake kallon Nahar din da ta dauki Haifah tana neman goya ta. Sai da ta goya ta sannan ta fara kokarin daukar cup din da gwangwanin cerelac din.

"Oh please. A nan zaki bar shi. Ki zo ku tafi."

Kafin Nahar ta amsa, Othman din ya ja hannun mamansa waje. "Mummy don Allah meye in kun tafi tare a jirgin? In wani hatsarin ya same mu a motar fa?"

Sai da ta bata rai sannan tace, "Zunnurain fitinar ka ta fara isa ta. Wallahi zaka koma..."

Da sauri ya kama hannunta. "Sorry your excellency."

Kafin tace komai Nahar din ta fito tana jijjiga Haifah a bayan ta. Kallon su kawai take yi ba tare da tace komai ba don babu abunda take fahimta zuwa yanzu. Ki take yi kamar yau din aka haife ta. Komai sabo take jin shi banda yarinyar hannunta da kuma wani suna da take ji yana mata yawo a kan ta.

"Ke," taji Hajiya Hairah ta taba ta, cikin sanyin murya ta bude bakin ta.

"Suna na Maryam." Hajiya Hairah da Othman ba su san sanda suka dube ta ba. Cikin wani irin mamaki ya matsa kusa da ita.

"Me kika ce?"

"Suna na Maryam." Juya kan shi yayi ya kalli Hajiya Hairah wadda ita ma kallon sa take kafin ta bude baki ta fara magana,

"Are you lying to me Othman?"

Girgiza kan sa yayi. "No, mummy. Wallahi I'm shocked as you are. Zan gwada tambayar ta naji ko zata tuna wani abu."

"Bana so ta tuna komai. Kayan ta da ta cire ma, ka dauko sai na kona su a dakin nan na zubar da ash din a toilet sannan zamu bar Kano." Ba ta jira amsar sa ba ta fice tana girgiza kanta.

Shi kuma kallon Nahar din yayi sannan yace. "Maryam, zo mu tafi."

Shiru tayi amma bata motsa ba.

"Maryam." Ya sake maimaitawa yana mika mata hannu alamar ta taho su tafi.

Makale hannun ta tayi a baya.

"Mummy tana jiran mu. Zo mu tafi gida, okay?" Daidai lokacin Haifah ta tsala kuka. Ba shiri Nahar din ta shiga jijjiga ta hade da sauko da ita daga bayan ta. Tana kunce ta kuwa tayi shiru ta sa yatsan ta a baki tana sha kamar yadda ta saba.

"Kawo babyn ki na rike miki mu tafi."

"Ba baby sunan ta ba, sunan ta Asma."

Maimakon yaji mamaki yanzu, sai yaji ya dan tsorata. It didn't look like she got some memories back, shi ji yake kamar akwai wanda yake fada mata wannan sunayen. Anya kuwa? Ko dai tana da aljanu ne? Kamar wanda aka ce da gaske aljanun gare ta, kawai ya fice a dakin ita kuwa Nahar din ta biyo shi kamar bata fahimci komai ba.

A mota suka tarar da mummy tana ta jiran su. Ba shiri suka nufi airport inda Captain Hassan yake can yana jiran su. Basu samu wani cunkoso ba suka karasa airport din. Ba shiri driver ya mika kayan su zuwa jirgin, shi kuma zai koma a motar.

Sai da ta suka shiga, Othman ya zaunar da Nahar ya karbi Haifah sannan jirgin ya tashi.

*****

Aiki yake a laptop din sa amma kwata kwata hankalin sa baya kai. Kwana biyun nan ma daga gida yake aikin nasa baya zuwa office din saboda nutsuwar sa bata tare da shi.

Idon shi yana kan laptop din Aisha ta shigo parlor din. Kamar ba zai kalle ta ba, sai ya daga ganin sa yace mata sannu. Bata amsa ba ta samu waje ta zauna ta kunna tv ta fara kallo.

"In ka gama za muyi magana." Haka ta fada bayan wasu mintuna da zaman ta. Shi daman ya san ba wai kallon ne zatayi ba. Kawai dai so take ya fara magana. Shi ma kuma ya gaji da halin da suke ciki, so sai ya rufe all files ya kashe laptop din yana kallon ta.

Sai da ta danyi shiru sannan ta tabe baki. "Me police suka ce so far?"

Ajiyar zuciya yayi yana fatan ta cigaba da yi mishi magana cikin sanyin murya irin wannan kamar yadda ta saba kafin faruwar wannan al'amarin.

"No trace of her. Amma sun ce sun fi tunanin wani ne ya dauke ta tare da amincewarta. Domin in da ace babu amincewarta ko yaya ne sai wani yaga alama."

Cikin rashin fahimta Aishan ta ke kallon sa.

"Wallahi bani da masaniya akan batan su, kinji nace wallahi. Addu'a ce ta mu a yanzu." Yana gama fadan hakan sai wayar sa ta dan yi haske, alamar text ya shigo wayar sa. Zai sa hannu ya dauka kenan, Aishan ta fusge wayar. Nan take sakon ya bayyana.

_ Isma'il ka dena yiwa Aisha karya, in baka fada mata da kan ka ba, zan rage ma aikin gaya mata. _

****
*Yaya zakiyi idan kika wayi gari kika tarar yar aikin ki ta gudu da yarinyar ki y'ar wata bakwai?*

*Yaya zakiyi idan aka shud'e tsawon lokaci basu dawo ba?*

*Yaya zakiyi idan kwatsam ta kawo kanta gidan ki da yarinyar a hannu da ikirarin cewar yar ta ce ba taki ba?*

*Ya zakiyi idan likitoci suka ce sakamako ya nuna tana dauke da wata cutar kwakwalwa saboda haka ki bar mata yarinyar har sai sanda ta warke sannan ki karbi yar ki? Ya zakiyi idan mijinki da kotu suka saka hannu akan wannan yarjejeniyar?*

*Shin sace su akayi ko kuma dai guduwar tayi da ita?*

*Tabbas a karon farko, da wahala ki samu amsar abunda zakiyi din. Ku biyo mu a labarin mu domin samun amsoshi!*

AeshaKabir
Rufaidah Yusuf

Join our group via:

https://chat.whatsapp.com/GuF6mZcV0998DjE8Hngl6P

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro