Sha daya
NAHAR
_11_
_"Haba wifey na..." ya fadi yana kallon cikin fuskarta. Sosai son ta yake kara shiga ran shi kamar dama can ya santa, zaka gane hakan ne daga irin kallon da ya ke mata.
Bata rai ta sakeyi. "Ni dai gaskiya na gaji da zama a nan..." bakin ta ta turo.
"Kiyi hakuri mana Nahar dina, the light of my life... kin san in matata ta gane na aure ki na boye ki a nan wallahi babu abunda ba zata iya ba. Saboda haka ki kara hakuri. Kar ma babyn cikin ki yaji kina ma baban sa rigima..." ya fadi, yana shafa cikin nata. Lankwasar da kanta tayi irin wanda yake nuna babu yadda zatayi dinnan. Rungume juna sukayi wanda yayi daidai da lokacin da suka ji a banko kofar. Kafin su ankara aka fara tafi daya bayan daya.
"Your game is over you cheat! Macuci kawai!" A firgice suka dubi Aisha da take tsaye a kansu hannun ta akan kugun ta.
Basu lura da wukar da ke hannun ta ba sai da ta nufo Nahar a guje...
"NAHAR!"_
Firgigit Isma'il ya farka daga baccin da yake, jikinsa ya jike shakaf da gumi. Kallan gefen sa yayi yaga Aisha bata nan. Bai san sanda ya sauke wata ajiyar zuciya ba. Yanzu da taji shi me zata yi?
Rike kan shi yayi, mafarkin na sake dawo mishi sabo a cikin kan shi. Shi wannan wani irin mafarki ne haka? Tsaki yayi sai kuma ya tuna babu amfanin da tsakin zaiyi masa. Maimakon ya koma ya kwanta sai ya tashi zaiyi alwala ko raka'a biyu ce yayi. Daidai lokacin Aishan ta fito daga bandaki da alamar ita ma alwalar tayi. Mamaki ya kama shi, yaushe ta fara sallahr dare?
"Meye kake wani kallo na?" Ta fada ba yabo ba fallasa.
Bai bata amsa ba ta cigaba. "Mama tace babu abunda ya fi samarwa da bawa nutsuwa a zuciya sama da ya kai kukan shi zuwa ga Allah. Ta gaya min sallahr dare tamkar wani mashi ne da baya missing target dinsa..." murmushi yayi amma cigaban maganarta ya saka ya neme shi ya rasa.
"Wallahi da kan ka zakayi kuka Isma'il. Da kan ka zaka zo ka gaya mun inda yara na suke... Yadda na hana ido na bacci haka kai ma zaka tsinci kan ka a makamancin yanayin nan har sai ka fito ka gaya min gaskiya."
Da haka ta matsa a wajen tana fita daga dakin don ta dauko hijabin ta da ke dakinta tayi sallar. Ya dade a tsaye mamaki yana kara kama shi. Tunda abun nan ya faru kullum a cikin zulumi yake sai yan kwanakin nan ya samu sauki kadan a dalilin sassaucin da ya gani daga bangaren ta. Ashe kwata kwata ma bata huce ba. Ashe har yanzu tunanin ta yana kan abu daya ne. Sai yaushe ne zata dawo normal? Sai yaushe ne farin cikinsu zai dawo? Watakila he has to plan a vacation for them to put their minds off the whole saga for a while.
Ajiyar zuciya yayi. Zai shirya musu tafiya wata kasar ko dan zukatan su suyi sanyi.
Alwala yayi sannan ya tayar da sallah, yana rokar Allah yasa ya cinye wannan jarrabawar.
****
Amir ne zaune a gaban mahaifiyarsa fuskarta a daure kamar zatayi duka ta kalle shi.
"Ni fa bana son shishshigi. Naga sai wani makalewa yar tsintuwar can kake yi. Mene ne matsalar ka ne Amir? Of all the classy girls around you sai wani ficikar kake shigewa?"
Kan shi a kasa ya murmusa.
"Oh Mami kenan. Yanzu har kinyi tunanin wani abu? Ni wallahi i only see her as a sister. That's it."
Hnmm kawai tace sannan ta kauda kai tana daukan apple ta gutsira. "Ka mayar dani abokiyar wasan ka ko. Allah ya baka sa'a..."
"Ayi hakuri amaryan his excellency." Yayi bowing sannan yana tashi da sauri don ya kaucewa dukan da ta kawo masa. Dama neman sanadin da sai fitar dashi yake saboda yasan Nahar tana can tana jiran shi yazo su fara video games din da ya koya mata.
Fitarsa ke da wuya Hajiya Hajar ta share wata kwalla da zo mata. Ita kadai tasan dalilin zuwan kwallar tata.
Ko da ya fita, dakin shi ya fada ya debi tarkacen game din nasa sannan ya fita zuwa inda su Nahar din suke. Can ya hange ta zaune tana hadawa Haifah building blocks inda ita kuma Haifahn take rarrafawa tana ruguza ginin sai ta kyalkyale da dariya.
Sosai suka burge shi a wani bangaren na zuciyarsa kuma ya ji wani tausayin su ya kama shi musamman ma ita Haifahn wadda yake ganin a raba ta da mahaifiyarta. Was that not selfish ace ko yunkurin neman ina ne gidansu ba'ayi ba kawai a taho dasu another part of the country? Wai ma meye babban dalilin dauko su din? Ai da kawai sai a kai su police station din Kano ayi ta cigiya har Allah yasa a samu guardians dinsu. Yana wannan tunanin kuma wata zuciyar tace maybe kuma planning batan nasu aka yi ba? Maybe kuma gudowa suka yi... Allah masani.
A hankali ya karasa, da yaga basu gan shi ba sai ya zagaya ta bayan Nahar din yana fadin "Tadaa!" Don kawai ya tsoratar da ita. Ai kuwa ta tsoratan, bata san sanda ta debi blocks din ba ta watsa masa tana kwalla.
"Oh kamfanin kuka. Meye na kukan kuma? Kinsan in ba so kike ku bata da bro ba yakamata ki rage saurin kwallar nan. The choice is yours." Ya watsa hannu. Kafin ta amsa yace guess what? Ita ma shrugging tayi.
"Game time!" Ya nuna mata kayan game din da ya ajiye akan kujera.
"I'm gonna beat you this time around! Nima na fara koya ai sosai."
"Wait wait, ya naji kina wani turanci har haka."
Dariya tayi. "Daddy ne ya gaya mun yadda ake fada ai. Kuma yace zai samo min lesson teacher kafin na shiga makarantar tunda kai da yaya baku so na."
Bai kula ta ba ya jona playstation din suka fara buga game din. In ban da dariyar su da wasan Haifah babu abunda kake ji. Har Zunnurain din ya shigo basu ankara ba sai da yazo ya kashe socket din ran shi a bace.
Nan da nan suka sha jinin jikin su.
"Ka same ni a parlor na... ke kuma zan dawo na same ki." Ya fadi hade da galla mata hararar da tasa cikinta ya kada. Shi kuma Amir din ya sauke kan shi kasa sannan ya fice din.
Daukar Haifah tayi tana kankame ta. Shi kuma daidai lokacin ya mika mata hannu. Ba shiri ta mika masa ita.
"Zan dawo and ki sani ba zaki sake ganin ta ba sai sanda kika yi hankali. Kalle ta a wurin, fool kawai..."
Bai sake kallon ta ba yasa kafa ya fice...
AeshaKabir
RufaidahYusuf
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro