Sha biyu
_NAHAR_
_12_
Asalin su
Muhammadu haifaffen garin river ne yanada matarshi guda daya me suna Iyaa Hadiza,shi maaikacin gwamnati ne sun Haifi yara uku,Hajiya Fatima ita ce ta farko,Sai Faiza da take bi mata sai kuma Adetola shi ne karaminsu.
Sun rayu cikin rufin asiri daidai misali Amma Malam Muhammadu ba kudi gareshi ba,ita Kuma mahaifiyar Adetola tana Yan sanao'in mata a gidanta duk domin rufin asirin su.
Abu daya da Malam Muhammadu yafi maida hankali a kanshi shi ne ilimi,baya wasa da saka yaran shi a makaranta ko kadan.
Daga matan har namijin.
Iyaa Hadiza ya saka ta tayi NCE anan Rivers din Bayan ta gama ta samu ta fara koyarwa tana taimakawa mahaifin nasu,ta auri wani Dan kasuwa me rufin asiri sosai haka ita ma. Ta sanadiyyar hakan ne ya saka kanwar ta Fatima a University Bayan tagama NCE nata a garin Lagos achan ta hadu da wani lecturer din su ya aureta.
Adetola da ya sakance shi ne karami Kuma namiji dukka sun maida hankali sosai wurin karantun shi.
Bayan ya gama secondry school babu yawa Allah yayi wa Mahaifinsu Malam Muhammadu rasuwa,mutuwar ta taba Yan unguwar tasu sosai saboda mutum ne na kwarai.
Bayan rasuwar tashi Yayyin shi biyu mata suka dauki nauyin shi ya cigaba da makarantar gaba da secondry,Adetola yanada kokari matuka Amma yafi maida hankali wurin Iya zance,da jagoranci wanda hakan yasa suna zaunar da shi suyi mishi fadan ya maida hankali Akan karatun shi,Amma duk da haka abu idan aka ce wannan kungiya ce to fa insha Allahu shi ne zai shige gaba,a haka har ya gama degree din shi ya tafi bautar kasa.fafur yaki aiki ya maida hankali Akan siyasa tun suna yi har suka Gaji suka bar shi.
Allah ya saka mishi lidifi sosai a harkar siyasar Kuma ya samu iyayen gida,a haka ya fara rike mukamai Bayan sun Kuma bashi aikime kyau sosai a gwamnatin tarayya,daga nan rayuwar tasu ta fara chanzawa.
Babbar yayar shi Hadizan bata taba samun haihuwa ba,ita Kuma Fatima tanada yara guda hudu,maza uku mace daya.
A kwana a tashi Shi Adetola yaje Sudan wakiltar Nigeria a wani taro da aka gayyaci Shugaban maaikatar tasu shi Kuma yaje a madadin Nigeria,bayan sun gama taron ne sai babban su ya gayyace su dukka gidanshi dinner,a chan ya hadu da yar mutumin ya Kuma nuna yana son ta,Hajiya Hairah Haifaffiyar Kasar Sudan ce gaba da baya Kuma mahaifinsu Al-Mustapha yanada matukar dukiya sosai, matanshi hudu ne yanada yara sun Kai Talatin da doriya.
Bayan Adetola ya dawo Nigeria ne ya sanar da mahaifiyar shi ya gano wacce yakeso,anan fa ta ce ita bata yarda ba saboda akwai cousin din shi da takeso ya aura,an sha wahala kwarai da ita kafin a shawo kanta da shared sharadin idan sai ya auri cousin din tashi Bayan ya auri Hairah,Kuma haka akayin Bayan auren su da shekara uku ya Auri yar uwar tashi.
Wanda a yanzu Adetola Muhammad shi ne Gwamnan garin Rivers Kuma Her Excellency Hairah ita ce first Lady wacce sun haifi yaro Daya da ita Othman-Zunnurain ita Kuma Yar uwar tashi ta haifi yara biyu mace ce ta farkon wacce taci sunan mahaifiyar shi sai kuma namijin shi ma sunan mahaifin nashi ne Amma Ana ce mishi Amir.
***********
Kano
Alhaji Auwalu Maso Aljanna shi ne cikakken sunan mahaifin Isma'il Mutum haifaffen kano Kuma attajirin Dan kasuwa ne da ya shahara a kasuwanci daban daban daga cikin wannan kasar har da wajenta.ya auri mahaifiyar su ismail din wacce mahaifinta fulani ne mahaifiyar ta Kuma shuwa ce shiyasa tayi kyau sosai haka ma yaranta sunfi na duk matan gidan kyau,Hajiya Falmata akwai addini matuka sannan ita ce matar shi ta farko sannan tanada yara 5 ne maza biyu sai matan uku,Isma'il shi ne babba Kuma ya dauko halin mahaifiyar sak wurin hakuri da addinin,sai mata uku masu bi mishi sai kuma namiji karamin su,sai kishiyar maman shi wacce take opposite hali da maman shi tanada yara 7 ita mata 6 ne sai autan ta namiji.
Isma'il yayi aure da wuri ne yana 28yrs ya auri Aisha anan gaban layinsu ya ganta Kuma yake masifar sonta.........
#Rufaidayusuf
#Aeshakabir
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro