Chào các bạn! Vì nhiều lý do từ nay Truyen2U chính thức đổi tên là Truyen247.Pro. Mong các bạn tiếp tục ủng hộ truy cập tên miền mới này nhé! Mãi yêu... ♥

Hudu


NAHAR
_04_

"Inspector ka fada min kawai, bacci yake yi." Ta fadi tamkar yana kallonta ne. Sai da ya danyi jim kadan sannan yace,

"Mallam Hamisu me tireda ya sheda mana cewa yaga sanda suka tsallaka titi. But unfortunately babu wanda ya gansu domin masu zaman majalisar kan titi ma basu fito ba lokacin. Haka kuma shi Malam Hamisu babu yadda za'ayi ace ya hango su."

Tsaki tayi. "And you call this an information? What a disgrace to your profession inspector! Abun kunya ne wallahi a gareka ace ka kira wannan bayanin naka da wani information. Wannan shirme ne! Toh wallahi naga alama bakin ku daya kai da shi. Dole ku fito mun da yarinya ta! Wallahi..." ta fadi, wani sabon kukan yana kwace mata. Wannan karan har ji tayi kamar numfashin ta ma baya shiga yadda ya kamata.

Shiru yayi sannan ya gyara murya. "What are you trying to say Mrs Isma'il Gaya? Kamar baki gane ni ba. MJ ne fa abokin mijin ki. Dazu ma I'm being professional ne saboda maganar aiki ce ta hada mu. Amma ya zakiyi ki jefe ni da irin wannan ka..." katse shi tayi.

"Akan me ba zan tuhume ka ba! Bayan kowa ya sani yadda ku ke yan sanda! Kowa ya san ku da rashin gaskiya. Da an baku chanji sai ku rufe gaskiya! Toh wallahi kunyi kadan. Ni da kai ne zan zo na samu DPO!"

Tana gama surutun ta ta kashe wayar wanda yayi daidai da fitowar Isma'il daga dakin sa yana dubanta. Ya san rigimarta amma akan kishin sa kadai ya sani, bai taba tunanin zata dinga wannan haukar ma da sunan tashin hankali saboda yarinyar su ta bata ba.

Tana jin motsin sa ta juyo gare shi.

"Bar ganin kana da connection, ai nima ina da yan uwa ko? Kar ka bari na maka ka a kotu Isma'il. Akan Haifah babu abunda ba zanyi ba."  bata jira amsar sa ba ta bar wajen. Yadda ta bar shi a wajen haka ya tsaya, hannun sa a aljihu. Shi bai ma san ta inda zai bullowa lamarin ba.

Tabbas yayi kuskure da ya nuna rashin so ga Haifah ba tun farko. Yanzu gashi nan tana nema tayi using din wannan abun against him. Ba wai fa ta fi shi jin ciwon batan su bane, kawai dan ita mace ce amma shima jin Haifahn nan yake watakila fiye da yadda take jin ta din a ranta.

Kamar ya kira Mama sai kawai ya fasa. So yake ma ya fita ya bar mata gidan amma yasan duk inda zai je hankalin sa ba zai kwanta ma. Hannu yasa yana barbaza gashin kan shi cikin rashin abunyi.

Duk ba ma tuhume tuhumen Aisha ba, babbar matsalar sa itace na sakacin kula da yar aikin da babu wadda yake ta ita. Me zai ce idan aka tambaye shi game da lamarinta? Ko kuma aka buka ci ganin ta?

Tsaki yayi yana kallon agogo sannan ya tafi masallaci. A can ma zaiyi zaman sa yayi ta tilawa har sai ya samu sauki domin yasa ni da ambaton Allah zukata suke samun nutsuwa.

****

Bowl din fruits aka sauke a gabanta, sai da wadda ta sauke din ta dan jira taji ko akwai wani umarnin don ta samu ta koma ta kammala aikin ta. Shirun da taji yasa ta juya zata tafi sannan ta matar ta ajiye tablet dinta a gefen table din gabanta sannan ta daga gira.

"Sophy!" Ba shiri ta dawo tana dan rissinawa alamar girmamawa ga matar wadda ko kadan bata tolerating raini ko wargi.

"Yes Ma." Ta amsa tana jiran umarni.

"Zaki iya zuwa gida amma kwana daya." Da yake bata yi zaton zata bar ta ba, sai ta durgushe a wajen tana ta zuba mata godiya. Kusan kwana uku kenan da ta nemi a barta tayi fashin kwana biyu da nuna yardar cewa a cire a albashinta saboda an kwantar da mahaifiyarta a asibiti amma her excellency tayi biris da ita kamar ma bata ji ba. Sai yanzu kuma ta amsa mata.

Godiya ta dinga yi har sai da aka daga mata hannu sannan cikin kula ta bar wajen.

Tana barin parlor din ta sauke ajiyar zuciya sannan ta nuti bangaren ma'aikatan gidan ran ta fes saboda yau zata samu damar zama da mahaifiyarta.

Her excellency, Hajiya Hairah kuwa daukan grapes tayi tana tsinkan daya ta jefa a bakin ta ran ta a bace. Haka kawai tana zaman zaman ta Othman zai jawo mata magana mara amfani. Ta sha jan kunnen shi akan ya dena zuwa Kano da sunan wani voluntary visits amma yaki ji. Yanzu da ya kade yaran nan sun mutu da shikenan abokan adawa sun samu abun yi! Tsaki ta sake yi tana taunawa a hankali. Ran ta a bace yake shiyasa ma har yanzu bata sanarwa mahaifin sa ba wanda baya ma kasar gaba daya. Shi ma kuma Othman din bata nuna mishi bacin ranta ba saboda tsoran kar ma magana ta fita.

A hankali ta mike. So take taje Kano amma ba tare da an gane ba. Da wannan tunanin ta mike, takalmin kafar ta yana bada sauti ta fice a parlor din ta nufi dakin ta domin ta dauki wayarta ta kira Captain Hassan taji if the jet is available.

Tana isa, ta zare zobuna da awarwarayen gold din da ke hannun ta ta zube su akan vanity table. A hankali ta dauki wipes ta na goge foundation din da ke kwance a fuskarta. Sai da ta gama duk wani night routine nata, ta yi brush da watsa ruwa sannan ta dauko wayar.

Tana shiga Captain Hassan ya dauka kamar jira yake. Limshe idon ta tayi sannan ta fara magana kai tsaye. "Ina so zan je Kano gobe. As early as 7."

Sai da gyara murya sannan yace, "Sorry to disappoint you ma'am amma Mrs Haajar is on a trip."

Cikin wata fusata amma da yake ita bata cika fada a waje ba ta kashe wayar. Lallai ma, yaushe aka fara daukar jet din ba tare da izinin ta ba! Wai har ma matar his excellency ta dauka. Yaushe ma aka kawo ta? Ita bata son raini ko kadan kuma bata son hayaniya amma tunda Haajar ta takale ta zata gane kurenta. Ta bar ganin wai ita ce amarya!

Da haushi fal a zuciyarta, ta kira driver tace masa zai kai ta Kano gobe. Bata bukatar wasu escort saboda bata so kowa ya sani. Bari wannan matsalar da Othman ya janyo musu ta wuce, zata dawo ta samu Haajar ne.

*****

Kamshin ta ne ya fara sanar da shigowarta dakin asibitin, Dr Othman na biye da ita. Kamshin nata ya zarce yadda shari'a tace mace ta sanya amma ita bata da masaniyar haramcin yin haka. Ko ma ta sani, bata damu ba.

Da sauri Nahar ta ajiye Haifah tana mika mata toy din da Dr Othman ya kawo mata dazu.

"Ina wuni." Ta gaishe da matar tana kallonta. Sanye take cikin leshi baki me adon tsuntsu ja a jiki, wanda yayi matukar haska fatar ta. Hannayenta kamar ko yaushe dauke da zobuna da awarwarayen English gold.

Tabe baki tayi, ba tare da ta zauna ba saboda ba ta jin zata iya zama a kan plastic chair din dake dakin.

"Yaushe ne sallamar?" Ta juya tana tambayarsa.

Bata fuska yayi. "Mummy gaishe ki tayi fa." Sanin halinsa yasa ta kalli Nahar din sannan tayi wani guntun murmushi.

"Sannu ko? Allah ya kara sauki."

Da haka ta juya ta fice, Dr yana bin ta a baya.

"Of all hospitals Zunnurain. Don Allah jibi yadda ka kaskantar da kan ka. Ba zan iya ba. Zan je na huta a hotel din da na sa aka kama mun. Ka duba sanda zaa yi sallama sannan kuma bana so ka bar ko file din ta daya a asibitin. Ka san duk yadda zakayi hakan ta faru. Da ita zamu koma Portharcout."

Da wannan kalaman ta zaro dark shades din ta ta saka. Drivern ta ya bude mata kofar motar Mercedes Benz GLK ta shige tana yatsina fuska. Ba shiri suka bar wajen.

Dr Othman kuma ya koma da zimmar aiwatar da umarnin ta.

****

Assalamu alaikum. Readers, how far? Ya kuke ganin tafiyar tamu? Har yanzu ba'a fara komai ba ma tukunna!

Ga masu son joining group din mu, ga link:
https://chat.whatsapp.com/GuF6mZcV0998DjE8Hngl6P

Ko kuma follow us on wattpad @AeshaKabir domin karanta wasu littafan daban.

#Aeshakabir
#Rufaidahyusuf

Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro