Goma
_NAHAR_
_10_
nan mama ta fara mishi fada yaushe ka fara komawa bacci idan kayi asuba babana azkhar din da karatun sun xama abin wasa a wurinka kenan.
"Duk da babu wani ingantaccen hadisi wanda ya nuna cewa babu kyau baccin Bayan sallar asuba,Amma ai kasan Bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka Kuma idan Annabi SAW idan yayi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito haka ma sahaban shi,Allah ya yarda dasu kamar yanda Muslim ya ruwaito a habith number:670,sannan annabi SAW yana cewa Allah ka sakawa alummata albarka a cikin jijjifinta,daga tizmizi" mama ta dora da cewa babana kasan komai Ina Kara tunasar da kai ne karka dinga wasa da lokuta masu muhimmanci"
Insha Allah Mama zan kiyaye na gode da tunatarwa,yawwa" ba komai babana abinda na kiraka na fada maka dama anjima kuzo kai da Aishar Ina nemanku".ya amsa da to mama.
Tunda ta tashi yau taji zaman gidan ya ishe ta. Ba tare da ta batawa kanta lokaci ba ta fada wanka. Tana sakin ruwan akan ta ta fara kuka kamar ranta zai fita. Abubuwa da dama suna damunta wanda babu wanda ya sani a yanzu sai suke ganin kamar batan su Haifah ne yake saka ta wannan halin da take ciki. Ita kadai ta san me yake damunta. Kuka take sosai, tana tuno abunda Dr ta fada mata a waya jiya da daddare amma sai ta yanke hukuncin taje wajen likitar da kanta ba ta dinga bi ta hanyar Hauwa ba don kawai likitar ta kasance yayar Hauwan.
Sai da tayi kukan ta sosai sannan tayi wankan ta fito. Zama tayi a gaban vanity table tana kallon fuskar ta inda idon ta ya kumbura kamar zai shige ciki. Ajiyar zuciya tayi sannan ta fara shafa mai a hankali tana tunani kala kala.
Ta dauki kusan minti goma kafin ta shirya cikin army green din abaya wadda tayi mata kyau sosai. Har ta daga turare zata fesa sai ta tuna kafin rasuwar mahaifinta, shine abunda yafi jaddada mata akan ta bari saboda mugun son turaren da ta ke yi. Ba shiri taji kwalla ta taho mata, ta sa hannu ta goge sannan ta shafa powder kadan sai lip gloss.
Bag hanger din ta ta kalla ta dauko yar karamar jakar da ta hau da kayan. Haka kawai taji wani murmushi ya kwace mata sanadin tuno yadda Isma'il ya siya mata jakar. Online ta ganta, kamfanin Dior ce saboda haka bata ma saka ran siyar ta ba. Tayi mata kyau don kyau amma siya ma bai taso ba. Duk da haka sai tayi adding dinta to cart dinta. Wanda bata san ya akayi ba Isma'il ya dauki wayarta ya gani ba har sai da ya kira ta rannan yana office yace mata akwai me delivery zai kawo mata abu.
Bata kawo wani abun a ranta ba. Ta dauka kawai yayi order abinci ne ya saka a hado mata da nata. Sai da me delivery din yazo taga wani katon box a gabanta sannan ta fara tunanin ko ma meye aka kawo. Nauyin kayan ya sanya sai jan su tayi cikin gida. A take ta gama sakawa a ranta ba nata bane sakon shiyasa ma gefe guda ta ajiye su a parlor din.
Bayan ya dawo ya huta, da yaji shiru sai ya tambaya tace ai kayan nasa yana nan. Da yace ta dauko sai ta bata rai. "Da nauyi fah."
Murmushi yayi wanda bata mantawa. Tare suka dauko suka so suka zauna yace tayi unboxing kayan. Ba musu ta zauna ta fara dayewa. Nan ta fara jin karo da kayan da mamaki yasa ta kasa cewa komai. Duk wani abu da yake cart din ta sai da ya siyo mata shi. Takalma ne, jakunkuna ne, hair dryer da kuma su turare. Bata san sanda ta yi tsalle tayi hugging din shi ba ranar.
Kallon jakar ta sake yi sai kuma ta tuna ashe fa harda saka hannun sa a batan su Haifah. Sai kawai tayi tsaki tayi jifa da jakar a kan gado ta nemi wata fara wadda tayi daidai da zanen jikin abaya din nata sannan ta fito.
Ya gama shan tea kenan, wanda rabon da aba shi wani abu da sunan breakfast ya manta. Aisha ko tana da appointment da clients dinta bata wasa da abincin sa amma yanzu sam ya rasa kan ta.
"Good morning." Ta fada ciki ciki kamar da ba zata gaishe shi din ba. Shi kuwa cike da murna ya taso har inda take yana hugging dinta ita kuma ta tsaya kikam hannunta ko alamar motsawa bayayi balle ma yayi tsammanin zata yi returning gesture din.
Dan kan shi ya sake ta, farin cikin sa na komawa ciki. "Haba Aisha, wallahi na fara gajiya da wannan attitude din naki. It's been a month and more amma har yau kin ki ki dena gani na da bakin tabo."
Jan hannun ta yayi ya kaita kujera ya zaunar.
"Ina tsoran wannan ne karo na karshe da zan roke ki sulhu." Bata ankara ba taji gabanta ya fadi, zuciyarta tayi laushi.
Cike da raunin muryar da yasan zatayi tasiri akanta ya cigaba da magana. "Wallahi Allah ban san inda yaran nan suke ba. Kuma Allah kadai yasan dalilin faruwar lamarin nan. Ina so ki jiginar da damuwarki, kizo mu fara sabuwar rayuwa in har da rabo wallahi har gida zaki ga wani sanadin ya kawo su. Amma wannan halin da kika dauka sam babu inda zai kai mu." Ya gyara zama sannan ya cigaba.
"Ina azabtuwa da rashin kulawar ki, kema kin sani in babu kulawar ki da soyayyar ki a gare ni, to babu Isma'il. Na rasa nutsuwata, a wajen aikin ma babu abunda nake iyawa saboda ke. Ki tausaya min..."
Idon ta yana kan sa, daidai lokacin shima ya zuba nasa a kan nata din. Sosai suka shiga kallon juna har sai da hawaye suka fara sauka daga idon ta.
Ba shiri ya matsa kusa da ita. "Please,"
Kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta mike zata tafi daki. Tana jin takunsa a bayan ta amma bata tanka ba. Sai da ta shiga ta zauna ta fara kuka sosai. Da yayi yinkurin rarrashin ta bata hana shi ba. Sosai ta dinga kukan wanda ita kadai ta san dalilan da ya saka ta kukan.
"I'm so sorry darling." Ya yi ta maimaitawa yana patting back dinta har sai da yasan yadda yayi tayi shiru. Karshe fitar safen da bata yi ba kenan sai wajen azahar bayan tayi mishi girki sannan tace tana son zuwa gida. Ran shi fes yace zai kai ta. A hanya yana ta yi mata hira wanda take amsawa ba laifi saboda rabin bacin ran sa da take dauke da shi ya tafi. Yana sane da yadda take kokawa da son shi da kuma fushin shi a lokaci guda.
Dadi yaji sosai ganin cewa his love overpowers her anger.
********************
Yana fitowa daga parlor dinsu wata kofa ya bi wacce zata sada su da main dining hall na gidan wacce mummy ce takira shi Akan yaje chan daddy na son ganin shi achan.
Yana sallama yaga kowa na gidan a zaune na gidan,Daddy y gaisar sannan ya gaisheda mummy sai Kuma step mum din shi,dukka suka amsa kusan tare,sannan ya ja chair ya zauna sai Amir ya gaishe shi,ita kuwa gogar taka ko kallon shi batayi ba ita a dole fushi takeyi da shi Akan zancen su na jiya da dare,sau daya ya kalleta sannan ya cigaba da cin abincin shi.
Bayan sun gama ne Daddy yayi gyaran murya yace naji duk bayanin su wannan yaran da ka tsinta din Kuma kamar yanda Mummyn ku ta fada din haka zaayi insha, zaku barsu Akan Yan uwanku na waccan garin,sannan nikuma insha Allah zan saka a hankali a dinga bincika min bayanan su,sannan Kuma menene report din na ita babbar Akan memory loss din?
Sai Zunnurain yace mishi "Daddy babu wani actual time da zatayi gaining memory nata Amma ba permanent bane,and insha Allah I will be watching every move nata akan matter din".
"That's very good of you son,Allah ya taimaka" his Excellency ya fada.i will see you all later in the day.
Mummy ce da girki ranar sai ta tashi ta raka shi zuwa main entrance na parlor sannan ta juyo.
Shima mikewa yayi ya tafi aka bar Anty da Haifah a hannun ta shi Kuma Amir yana gefen ta,a hankali Antyn ta rada mishi "yau bakaga mutuniyar taka ko kulamu batayi ba?".nagani Bari naje naji menene.
Yana zuwa kusa da Nahar din ita Kuma zata tashi a wurin,sai ya riko hannunta yace mata "ta koma ta zauna".ta koma ta zauna Amma bakin nan a gaba ta hade rai,sai ya tambayeta "abincin ne bakyaso ko menene ?" Sai tace mishi "ba Yaya bane jiya da dare naje na same shi nace mishi ya sakani a makaranta Amma ya koroni",dariya Amir ya keson yi Amma sai ya daure yace "me kika ce mishi",tace "haka nace mishi Kai da Anty Shola kukace nazo na fada mishi ya Saku a makaranta,shi ne Wai meyasa ku Baku sakani a makarantar ba".........
*ayi hakuri da wannan,Ina cikin uzuri Amma insha Allah gobe zanyi da yawa*
#Rufaidayusuf
#Aeshakabir
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro