Daya
*NAHAR*
_01_
Bismillahir rahmanir rahim.
Da mamakin yadda har yanzu bata fara jiyo kukan babynta ba ta bude kofar, da saurinta ta karasa wajen cradle din baby Haifah. Mamaki bai kama cika ta ba sai da taga wayam, babu Haifah babu alamar ta. Tashin hankalinta ya karu, duk da babyn tata bata rarrafe balle tafiya sai ta samu kanta da duba karkashin gado. A kidime ta mike, tana bude drawers tare da fatan ganin babyn a ciki. Wayam! Gudun zuciyarta ya karu sosai. Duk da haka bata gaskata abunda idanun ta suke ganin mata ba, tayi waje. Dakin me aikin ta ta shiga. Tas yake kamar ko yaushe. Idanunta suka fara yawo daga kan gadon da drawers din har gaban mudubi. Komai yana cikin tsari.
Dankari! Hankalinta ya kara tashi. Da zafin zuciya ta shiga buga kofar bandakin da ke dakin amma shiru taji. Tana budewa taga babu kowa. Ba tare da ta san me take ba, ta juya ta bar dakin ta koma falonta ta zauna tana mayar da ajiyar zuciya.
Toh meye ma take wani tayar da hankalin ta bayan ga Zahiri? Tabbas Nahar ce ta dauki Haifah suka fita da safiyar nan. Duk da dai ta san bata aike su ba.
Ajiyar zuciya tayi sannan ta koma ta zauna. Mamakin sauri da tsaftar yarinyar na kara shigar ta. Domin kuwa har ta gyara gidan tsaf.
Tana zaune, jiran su dawo sai ga mijin ta nan ya fito sanye da kananan kaya da alama ba zai fita aiki ba. Yayi mata kyau sosai. Duban shi tayi tana mikewa.
"Yau ba fita aiki kenan." Ta fada, tana jan hannunsa har sai da suka samu wajen zama.
Murmushi yayi, irin wanda yake kara mata son sa kafin ya ja kumatun ta. "The day says Saturday. Daman ina zuwa aiki Saturday ne?"
Ita ma murmushin ta sakin masa, sai dai nata bai zurfafa saboda yadda ta tashi a rude yau. Daman tunda sukayi sallar asuba ya lura yau din gata nan gata nan ne. Kamar bata cikin nutsuwarta.
"My bad! Wallahi tunda na tashi yau a birkice nake ji na. Musamman ma da na tashi naga babu Haifah babu Nahar."
Kallonta yake sosai, daga yadda take maganar ma kasan hankalinta a tashe yake. Sai ya kama hannunta ya sumbata sannan ya dan matse a nasa hannun yana duban fuskarta da har yau take masa wani kyau kamar ranar farko da ya fara ganin ta. Ita ma kallon shi take yi tamkar yau ta fara ganinsa. Kowanne da abunda yake ayyanawa a ran shi. Bai ankara ba sai ji yayi ta fashe da kuka. Hankalinsa ya tashi sosai ya kamo fuskarta.
"Subhanallah Mene kuma darling?"
Cikin sheshshekar kukan ta fara magana. "Ni tun asuba nake ji gaba na yana faduwa. Gashi na tashi ban ga Haifah
ba... ina tsoran faruwar wani abu..."
Kallon yadda take kuka da gaske ya bashi mamaki. "Ya kamata ki rage tunani marasa amfani darling. Ba yau asabar ba? Kin manta kin fadawa Nahar duk weekends abincin gargajiya za'a yi? Ba jiyan nan naga kin diban mata waken da zata kai markade ba? And it's obvious markaden ta tafi kaiwa."
Kamar wadda allura ta cake ta, take ta fara girgiza kanta alamar ta yarda da maganar sa. Hannu yasa ya goge mata hawayen sannan ya jawo ta kirjin shi tana shafa gefen ta a sigar rarrashi.
"Ina son Haifah sosai shiyasa hankali na yake tashi sosai." Ta fadi. Shi dai bai ce mata komai ba. Shiru sukayi na tsawon lokaci kafin ta kalli lokaci sannan tace,
"Banda abun Nahar ma ai yayi safiya da yawa. Dole ta dade." Har yanzu bai tanka mata ba. Karar wayarta ne ya saka ta tashi ba shiri.
Ta dan yi mintuna tana wayar kafin ta dawo ta same shi still a wajen.
"Bari na kawo maka black tea kafin ta dawo.."
Daga gira yayi sannan yace, "no i can wait. Minti nawa ne?"
Murmushi tayi. "Bana son fita baka ci komai ba sweetheart. Yanzu client dina ta kira ni akan zancen decoration din gidan ta. I was so disheveled that i forgot ina da appointment da ita."
Tana gama fada, ya sauke ajiyar zuciya a boye. Ba shi da bakin mita tunda shi ya amince mata da wannan aikin. Sanda ba a gari yake aiki ba, bai damu ba. Amma yanzu sai yake ganin kamar tana shiga lokacinsa musamman weekends da babu inda zai je.
"I wish you can postpone it zuwa Monday. Yau i want a complete day in with my darling amma it's fine." Ya fadi yana jefan hannunsa gefe alamun ya rage nata ta yanke shawara.
Sai da ta dan yi jim kadan. Har ranta taji tana so ta zauna din amma sai ta hasko irin makuden kudaden da zata samu once ta gama interior decor din. Client din tata matar wani dan house of reps ce. Recently ya samu mukamin so zasu koma sabon gida wanda ita kuma Aisha take so a bata contract din.
"I will make it brief, please." Ta fadi tana kallon shi. Da gaske ba zata dade din ba.
Mikewa yayi ran shi yana baci. Dazu tace tana cikin damuwa saboda rashin yarinyarsu a kusa yanzu kuma tana nema fita neman kudi ba tare da ta saka babyn a idonta ba.
"Haifah kuma fa! In ni zan iya kula da kaina ita zata iya ne?"
Sai da jikinta ya danyi sanyi jin yadda yayi maganar amma sai ta basar.
"Idan tana tare da Nahar kamar ina tare da ita ne. Kasan yadda Nahar take kaunar ta ai tamkar yadda nake son ta ne. Wani lokacin har kishi nake irin yadda Haifah take makale mata. So ba abun damuwa bane."
Kallonta kawai yake cike da bacin rai da mamakin yadda batun kudi ya saka gaba daya ta jinginar da yarinyar.
"Shikenan ai. Amma ki dinga ragewa Nahar wannan hidimar. Ita ma yarinya ce." A karo na farko ya nuna damuwarsa game da yar aikin nata.
"Su yaran kauye ai sun saba dama, banda abun ka."
"Ba kya ganin yanayin jikin Nahar dinne?" Ba shiri gaban ta ya fadi. Yau Isma'il ne yake tanka halittar wata a gabanta? Hakan ya sanya ta danyi saroro tana kallon sa. Kar dai Nahar din ta fara shiga zuciyar mijinta kamar yadda ta shiga na yar ta!
Gaban ta taji ya fadi har ma kamar jiri zai debeta.
Kawai sai taji fitar ma ta fasa. Waje ta samu ta zauna sannan ta kalle shi. Bai ce mata komai ba ya dauki makulin motar sa ya fice.
Ta dade a zaune kafin ta dauki waya ta kira client din tata ta bata hakuri. Ta yarda ta rasa contract din akan ta rasa shi, Isma'il dinta.
Cike da zafin zuciya ta kira kawarta take fada mata. Hankalinta bai gama tashi ba sai da taji Hauwan tana cewa, "ai dama naga sakarcin ki! Kilan ma sun fara soyayya kina zaune! Ya zakiyi ki dinga fita kina barinsa da ita a gida tsawon awanni! Dama na gaya miki ai! Ba zuciyar yar ki ba, har ta mijinki sai ta sace!"
Bata san sanda wayar ta sulale a hannun ta ba. Ba shiri ta saka hijabi ta fita gidan markaden. Amma mai markaden ta shaida mata sam bata zo ba. Da ta tambayi me shagon kusa da gidan nasu sai yace tabbas yaga fitar Nahar din tare da Haifah da safe.
Cikin tashin hankalin da yafi wanda ta shiga dazun ta dawo gida. Tana shiga ta fara ihu. "Na rantse da Allah baki isa ba Nahar! Kiyi ki dawo wallahi yau zaki bar gidan nan!" Ta fada da karfi tana hucin kishi da bakin ciki.
Da kyar ta samu ta daidaita kanta sannan ta kira shi tana kara sanar dashi basu dawo ba.
"Da kin damu ne?" Abunda yace kawai sannan ya kashe wayar duk da shima hankalinsa ya tashi saboda an shafe awa biyu kenan basu dawo ba.
****
Kamar wasa har azahar shiru babu Nahar babu Haifah. Sannan Isma'il ya sauko daga fushinsa sun shiga cigiyar yarinyar su da yar aikin.
In banda kuka babu abunda Aishan take yi wanda ba kadan yake taba zuciyar sa ba. Shi kuwa har police station yaje sukace ba zasu fara bincike ba sai an tabbatar bayan awa ashirin da hudu...
Yinin ranar a kwance kuma cikin kuka tayi shi. Washe gari kuwa sai da aka kaita asibiti saboda jininta ya hau.
Abu kamar wasa, yan sanda suka fara binciken neman Nahar.
"Ku duba duk tashoshin motocin garin nan a duba list din wanda sukayi tafiya da safe..." shugaban yan sandan ya bayar da umarni.
******
Yaya zakiyi idan kika wayi gari kika tarar yar aikin ki ta gudu da yarinyar ki y'ar wata bakwai?
Yaya zakiyi idan aka shud'e tsawon lokaci basu dawo ba?
Yaya zakiyi idan kwatsam ta kawo kanta gidan ki da yarinyar a hannu da ikirarin cewar yar ta ce ba taki ba?
Ya zakiyi idan likitoci suka ce sakamako ya nuna tana dauke da wata cutar kwakwalwa saboda haka ki bar mata yarinyar har sai sanda ta warke sannan ki karbi yar ki? Ya zakiyi idan mijinki da kotu suka saka hannu akan wannan yarjejeniyar?
Shin sace su akayi ko kuma dai guduwar tayi da ita?
Tabbas a karon farko, da wahala ki samu amsar abunda zakiyi din. Ku biyo mu a labarin mu domin samun amsoshi! I
*#AeshaKabir*
*#Rufaidayusuf*
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro