Biyu
*_NAHAR_*
_02_
By Rufaidah Yusuf and AeshaKabir.
*****
Bayan fiye da awa guda, Isma'il ya sake daukar waya ya kira ofishin yan sandan saboda zaman da yayi da matarsa a asibiti yana bata baki. Har yanzu basu sanar da yan uwa ba saboda kar su daga hankalin su. Musamman ma akan ita Aishan da hawan jinin ya dade a jikinta wanda da kyar aka samu ya lafa, yanzu kuma faruwar wannan abun ya tayar da shi. Da yaga bacci take sosai, sai ya fita ya kira yar uwarsa yace ta zauna da ita. Domin yana ganin kaman zuwa ofishin sai ya fi. Yana tafe yana kokarin kiran abokin sa da yake aiki a can.
Wayar bata jima da shiga ba, a ka dauka all thanks to the connections he has a wajen. A ka'idar aikin su, sai anyi awa ashirin da hudu ake tabbatarwa mutum bata yayi sannan a fara neman sa. Bai wani jima ba ya karasa aka hada shi da DPO.
"Yallab'ai yanzu ya ake ciki gameda binciken naku,banji kacemin akwai wani progress ba,kaganni daga asibiti nake Aisha tana kwance, Kuma gaskiya banason komawa ba tareda an fad'amin cigaban da aka samu." Ya fada, bayan ya ajiye robar ruwan da ya shigo dashi. Shima karfin hali yake amma ji yake gaba daya he is dehydrated ga jikin sa kamar zazzabi zai kama shi.
"Muna iyakar k'ok'arinmu Akan case d'innan naku Amma Naga Ku kamar gani kukeyi Bama komai akai".
"Haba D.P.O ace abu almost 24hours kun kasa gano inda yarinyar nan take?" Ya tambaya.
Juyawa D.P.O yayi ya bar shi a wurin,ya bude baki zaiyi magana sai Muhyiddeen ya ce mishi "Haba abokina yanzu da ka fusata officer dinnan su waye kake tunanin zasu cigaba da neman su Haifa,ka dinga bawa kanka hakuri mana,zo muje office din nashi."
Rufe idon shi yayi ya bude a hankali. "Kaima kasan hankali na a tashe yake abokina na rasa mafita yanzu damuwata idan na koma me zance wa Aisha."
Abokin nashu bai tanka ba, sai ya sake cewa. "Hakkin kula da lafiyar yaran nan akai na yake domin a karkashin kulawa ta suke. Ban san inda suke ba, ko a wane hali suke ba. Dole na damu."
*********
Bud'e k'ofar yayi a hankali gudun kar yayi wani motsin da zai tashe su,domin Daren jiya yasha wahala sosai saboda kukan yarinyar,gashi tak'i zuwa wurin kowa.
Ya zauna a kujerar da take gefen gadon,sannan ya saka hannu ya d'auki remote din AC ya rage gudunta saboda gudun kar sanyin ya cutar da babyn da ke kwance gefen yarinyar da a tunanin sa ba ma zata wuce shekara sha biyu ba. mamaki yana kara kama shi yadda ya ganta yar karama haka wai da yarinya a
tare da ita.
Bude kofar aka sake yi,Yana juyawa suka had'a ido da Dr Ashiru, "Dr shigo ka rufe kofar nan please Bana so ka tashi yarinyar nan if not wallahi Kaine zakayi rainon..." ya fada yana bata rai saboda shi kadai ya san wahalar da ya sha kafin tayi bacci kasancewar me renon nata
bata farka ba ita sam.
Dariya Dr Ashiru yayi yace "zan so ace her excellency tana wurin jiya da daddare."
"So what idan tana nan? Hnm ni fa kaga idan magana ka shigo ka sakani a d'akin nan to ka koma inda ka fito ko Kuma ni na tashi na fita." Ya maida kanshi Kan kujerar Yana rufe ido.
Dr Ashir kuwa sanin halin mutumin nashi yasan abu kad'an ke b'ata mishi rai kuma yasan yanada abinda yazo fada mishi ya sa bai biya shi ba yace mishi "Haba Dr Othman kasan dai tunda kaga na shigo wurin nan akwai abinda ya kawo ni ko,to her excellency tace ta kira wayarka bata samu idan ina kusa da kai na kawo maka".
Jin an kira mummy ya bude idon shi ya Mika mishi hannu,ganin haka sai ya Mika mishi wayar.
"Hello Mummy,"
"Yes Zunnurain Ina ka shiga Ina ta Kiran wayarka bata tafiya,"
Murmusawa yayi. "lafiya Lau mummy bansamu bacci bane shiyasa na kashe wayar na Dan huta,"
Yana ji tayi ajiyar zuciya. "to kaga ai sai ka saka nayi tunanin ko wani abu ne Kuma tunda ka tsautsayin da ya faru jiyan,anyway ya masu jikin Ina fatan dai sun farka,"
"Ayi hakuri and yes mummy ita babyn dai tun jiya ta farka saboda ita ce ma ta hanani bacci. Amma dayar yarinyar ce har yanzu dai bata farka ba,Amma muna saka ran kowanne lokaci daga yanzu insha Allah zata farka."
"To Allah yarda zunnurain Bari na tashi na shirya Nima Ina da meeting zuwa jimawa kadan,I will call you after naji yanda ake ciki idan jikin nasu yaki sai muga abinda zaayi ko..."
Cikin jindadin kulawarta yace, "ok mummy take care." Kashe wayar yayi ya mika ma abokin sa sannan yace masa zai shiga office ya huta kadan kafin lokacin round yayi, because da kyar yakw budw idon sa.
****
Fitowarsu daga office din DPO kenan cike da hope din za'a iya samun su Nahar da Haifah duk da kuwa binciken sunayen mutane da suka bar garin Kano a ranar ya nuna babu nata balle ta bar number wani da ta sani. Bayan a shigar da complete report ma sai yan sandan suke ganin kawai wani wajen tayi saboda tayi kankanta ace wai har tayi tunanin barin gida kamar yadda Isma'il din yake tunani.
Da yake sun fi shi sanin kan aikin, bai yi musu ba ya musu godiya ya tafi zuciyar sa tana ta harbawa cike da fargabar yadda zai je ya sami Aisha.
Tuki yake a hankali, wayarsatayi kara.
"Hamma, sis Aisha ta tashi kuma ta dame mu mu tafi gida. Mama had to send the driver. Yanzu muna gida."
Ba shiri ya juya kan motar ya nufa gidan sa. Cikin sa'a bai tarar da wani hold up ba ya karasa unguwar Lamido Crescent.
Yayi mamaki tarar da mahaifiyar Aishan da kuma kanwarta a gidan. Cikin ladabi ya gaishe su sannan ya kalli parlor yaga bahu alamarta.
"Tana daki." Kanwar Aishan ta fada masa. Toh kawai yace sannan ya nufi kofar dakin.
Tun a bakin kofa yaji alamar kuka takeyi kuma ta rufe dakin. Kirjin shi ya doka, wannan kukan yana taba masa zuciya.
"Aishaaa!" Ya kira sunan ta gami da rokon ta bude dakin. Bai yi zaton zata bude ba amma sai yaji alamar ta bude din.
Jajayen idanun ta da suka jike da hawaye ta zuba masa tana turo kofar dan kar su mamanta su jiyo su.
Ita dai ta sani, zuciyarta ta fada mata! Yana da saka hannu a batan yarinyar ta!!!.
********
Dr! Dr! Cewar daya daga cikin nurse din asibitin tana buga kofar office din Dr Ashir.
Juyi Dr Othman yayi yana yin tsoki,ya bude kofar zai fara mata fada ya kalli halin da take ciki,sai ya tambayeta menene ya ke faruwa tace "patients din da kuka kawo yarinyar ta farka amma she's in a critical condition".
Bai jira ta gama magana ba yabi bayanta,wanda yayi daidai da zuwan Dr Ashiru wurin.
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro