Biyar
_NAHAR_
_05_
Ringing din da wayar takeyi ne ya tada her excellency daga bacci,ta bude ido a hankali tana dauke gashinta da ya rufe mata ido."who is disturbing my peace for goodness sake" cewar Hajiya Hairah.tana duba wayar taga sunan His Excellency yana yawo Akan screen din ta,da sauri ta daga wayar tana cewa "Hello Your Excellency,fatan kana lafiya". Daga daya barin naji murya me cika da kwarjini ta amsa da cewa "nikan maana only da yaren yoruba,Ina kika shiga ne,na shigo Kuma Ban jiki ba,kinsan Bana cin abincin kowa maimakon kafin ki fita ki ajjemin",tuba nakeyi yallabai kayi hakuri ta fada cikin kasa da murya,"dariya yayi sanin halin hajiyar shi,karki yaudare nikam,yanzu Ina aka je Dan fadamin naji.Hajiya hairah tace "I have been wanting to tell you tsautsayi ya ritsa da Zunnurain a Kano,so Kuma kuna ta conference dinnan Ban samu na fada maka ba,tayi mishi bayani sosai cikin dabara".a daya bangaren Naga his Excellency yanada nodding kan shi alamun ya gamsu da bayanan da tayi mishi sannan yace "I trust your decisions nasan bakya wasa da siyata,kiyi abinda kike ganin ya dace if anything goes out of hand sai ki nemi ni".
"ok dear take care,har zata kashe bansan me ta tuna ba tace yallabai to yanzu me zaayi serving maka na kira Chef Shola ta miko maka".yar dariya yayi kadan sanin dalilin ta na fadin haka sai yace "bakomai nikan akwai abinda sukayi serving yanzu zan samu naci,sai mun yi magana",ok.
Hajiya Hairah na sauke wayar His Excellency sai ta kira driver tace mishi "ya shirya in the next 30minutes tana so ta shiga government house na Kano wurin matar gwamnan".
Achan asibitin Kuma Dr Othman ya saka an hada mishi komai he is set Bayan yayi shawara da Dr Ashir Akan gwara su tafi da yaran chan Portharcout Kamar yanda Mummy din tace saboda idan aka samu matsala ko kadan ne shi zatayi blaming,har wurin motar shi Dr Ashir ya rako shi da baby Haifah Akan kafadarshi tana bacci ita Kuma Nahar tana bin shi a baya kamar jela.
Dr Othman ya saka hannu ya karbi Haira,sannan ya mikawa Dr Ashir hannu suka yi shaking hand yana cewa "sai munyi magana,stay safe"."ok baban babies" Dr othman yace.
Titi ya hau,sannan ya kira mummy a waya ya tambayeta a inda zai sameta,tace mishi tana government house yaje chan ya sameta,tsoki naji yayi Bayan ya kashe wayar wanda ni kaina bansan dalilin shi ba,yana juya kan motar zuwa state road.
Hajiya Nafisa tace "Hajiya Hairah Dan nawa ne hala kuke magana",sai tace "eh shi ne Hajiya ta Wai yana tambayar inda zai sameni nace mishi Ina nan".suka cigaba da hirar su ta siyasa da Kuma hirar maxajen nasu.
************
Assalamu alaikum, Ismail kenan da yake ta sallama a Bayan ya hau sama wurin maman shi,Jin shiru ba amsa,sai ya daga wani labule ni kaina sai da nace wow! Wata sliding door ce fara Ana hango wajen space din daga parlorn maman a sama,swimming pool ne madaidaici gefe da wasu kujeru biyu da Kuma flowers masu kyaun gaske da suk zagaye wurin,shiga yayi ya kwanta Akan daya daga cikin kujerun,ya rufe idon shi.
Bayan mama ta idar da sallah a dakinta sai ta fito parlor dinta,saboda taji muryar Isma'il din lokacin da take sallah,ta duba kan kujerun ta baya nan,ta juya zata koma dakin sai taga kamar alamar an taba labulen da yake parlor din,sai ta nufi wurin tayi sliding kofar ta shiga wurin.
Ta dade a tsaye a kanshi tana nazarin shi,duk da idon shi a kulle yake hakan Bai hana ta gane ba bacci yakeyi ba,ta kira sunan shi a hankali Amma bai amsa ba,sai ta janyo kujerar da take gefen shi ta zauna,ta dan taba shi,firgigit ya bude idon nashi saboda Bai ji shigowar kowa ba sai taba shin da yaji anyi.
Yana bude idon yaga mama ce,sai ya tashi zaune a hankali yana mata murmushi yace "yaushe kika shigo mama" sai mama tace "Ban dade da shigowa ba babana" tana gyara zama.
Ya sake gaisheta sosai,bayan ta amsa ta tambaye shi ya Aisha take sai yace "dama mama maganar ta ce ta kawoni".to Ina jinka cewar maman......
#Rufaidayusuf
#Aeshakabir
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro