Bakwai
_NAHAR_
_07_
Warce wayar hannun Isma'il din Aisha tayi da taga fuskar shi ta chanza Bayan ya karanta message din,wani kallo ta watsa mishi tace "ni nasani ai,nasani ba sai wani ya fadamin ba wato kiyayyar taka da Haifah har takai ka saka a sacemin ita,to wallahi ka sani duk abinda zanyi sai nayi iyakar karfina akai".duk sanyin Isma'il ranshi ba karamin baci yayi ba Jin wannan shirmen da Aisha takeyi,har ya bude baki zaiyi magana ya tuna abinda Mama ta fada mishi dazu da yaje wurinta,sai kawai ya tashi daga parlorn ta ya nufi nashi.
Daga kofar parlorn ta ya fita kwata kwata,sai Naga ya nufi wani side din daban wanda irin wannan kofar ce dauke a jikin shi.
Ya bude kofar,cikin shi parlor ne da ya d'ara na Aisha dauke da saitin red and golden royal chairs,sai carpet Shima kalar red dinne ,curtains ma red and golden,sai tv stand black and gold da ke a tsakiyar parlor din.Tabbas wurin yayi matukar yin kyau.
Direct ya nufi kan kujerar ya zauna ya dauko wayar shi daga aljihu Naga ya saka glass din shi Yana kallon wayar yafi 30mins yana duba wayar daga bisani ya ajje ta,hasken wayar ne ya saka nagane Quran yake karantawa.Remote din TV Isma'il din ya dauka ya kunna ya na kallon wani movie dake jikin flash din shi na Chinese me suna Crush,murmushi yakeyi shi kadai.
Karan wayar shi ne ya katse shi,yana dauka a daya barin aka ce mishi "Hello man kana Ina ne,Ina kofar gate na tambayi gate man din yacemin he's not sure ko kana nan ko baka nan" Isma'il ya amsa mishi "Ina ciki,Amma ina part dina idan ka shigo". Muhyiddeen ya shigo ciki Bayan yayi parking ya fito part din Isma'il din yayi niyyar wucewa direct,sai yaji Aisha ta kira sunan shi tana cewa "Malam dama Ina so na fada maka ne ka Jawa abokin ka kunne,ya fitomin da yarinya tun kafin nayi abinda kowa bazaiji dadin shi ba a gidan nan",Hmm kawai yace Yana gyada kanshi yayi gaba,ita Kuma tana ta ihun Wai ya maida ita mahaukaciya ma kenan tunda tana magana ya gyada Kai ya wuce ta.
Yana shiga shiga ciki ya tarar har Isma'il din ya Mike Shima yana shirin fitowa,yace "Ina Kuma zakaje daga shigowa ta ko zama banyi ba",sai Isma'il din yace "so nakeyi muje ka rakani Orphanage din chan nayiwa wanda suka bani yarinyar chan bayani kamar yanda DPO din ya bamu shawara,a hanya ma akwai maganar da nakeso muyi sai muyi Akan hanya".
**************
Motoci nagani sun Kai guda ashirin a jere da yan sanda a gaba da baya sai jiniya ce take tashi,Mummy na mota daya,Othman yana mota daban sai su Nahar su ma a wata motar daban.a cikin motar da Zunnurain din yake Naga yana ta bata fuska,shi fa gaskiya baya son wannan jiniyar Sam wani abun ma sai mummy yake fada a ranshi,chan km sai su Nahar din suka Fado mishi a rai,escort din da yake gaban motar su Nahar din ya kira a waya yake fada mishi "idan an shiga government house karka budewa yaran nan kofa su fito ka wuce da motar part din Mummy sai ka ajje su achan" yes sir naji ya amsa mishi sannan ya kashe wayar.
Bisa ga Al'ada duk lokacin da her excellency tayi tafiya ta dawo in dai Daddy yana gida a bangaren shi ake fara tsayawa,haka ma a wannan karan anan suka sauka.
Wucewa direct Mummy tayi sama wurin daddy din Othman Kuma a parlor na uku ya Yada Zango saboda shi ne wanda daga shi zaa hau saman,da ya duba yaga lokacin sallah yayi sai ya shiga wata kofa dake a parlorn,wani parlor ne Shima guda daya Amma it's divided into two shi ma,kowanne zaman kanshi yakeyi sannan akwai kofa guda biyu daya Naga ya bude ya shiga wanda shi Kuma bed room ne,komai na kalar dakin nude ne ya cire suit din jikin shi ya sakale sannan ya bude kofar toilet ya shiga,wanka yayi tareda alwala ya fito yayi sallah a dakin.bayan ya idar ya tuna ya bar yaran nan a parlor chan na biyu da sauri ya fita ya shiga parlorn kenan yagansu a zaune sai dariya Nahar din takeyi ga Kuma wani saurayin me kama da othman din tare da su,karasowa yayi ya zauna a 1seater din da ke facing din su fuskar shi ba yabo ba fallasa,sai da ya zauna sannan suka lura da zuwan shi.
Sauke Haifah yayi Akan kujerar sannan yace "Akiyy ka dawo ashe shi ne da na kiraka dazu baka cemin zaku dawo ba" sai Othman din yace mishi "Amir ka cika rigima ne ni bazan Iya da ciwon kanka ba" dariya Amir din yayi yace "a ina ka samo wannan yaran masu kyau haka",sai Othman din yace mishi "Ka Bari idan Mummy ta sauko sai ka tambayeta".Bai sake magana ba sanin cewa ba fada mishi din zaiyi ba.
Baa yi minti goma ba sai wata matashiya da take late 20s nata ta shigo na apron a jikinta tace her excellency tace Ku zo abinci ya zama ready,ok suka amsa tare sannan Othman din ya kalleta yace mata "Chef Shola,ga yaran nan ki kaisu waccan room din da ka opposite da naki,ayi musu wanka da kaya a luggage nasu ki chanza musu,sai kiyi serving nasu a daki ita babyn cerelac Zaki bata please" ok sir ta amsa mishi tana daukar Haifah sannan ta ja hannun Nahar.sai da yaga sun shiga dakin sannan yabi Amir din a baya.. ....
#Rufaidayusuf
#Aeshakabir
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro