Chapter 4
"Wani razannenan ihu ta saki ta yarda wayar a firgice ganin rahma tsaye tana kallonta,da sauri ta fara kici-kicin cire rigar jikinta gabanta na tsananin faduwa,wayarta ta ciro daga jaka ta fara kiran ammi,cikin shagwaba da tsiwa tace ammiiiiiii sannan ta fashe da kuka,cikin mintuna da basu wuce 5 ba ammi ta shigo dakin ta tarar da rahma da yasmeen tsaye kamar wasu zakaru,,,,gurin rahma ta nufa tace cherie what's wrong na ganku tsaye kamar wasu sa'anni.......ammi wlhy yau se wannan yan iskan mutanen sun bar gidan nan duba kiga yanzun nan na dawo na tarar da yasmeen da kayana wanda zansa gobe idan za muje dauko yaya farhan a airport,ammi kayanne jikin yasmeen tana tsaye a tsakiyar gadona tana selfie wato dakina shine ya zame mata background din hoto,a tsorace ammi ta mayar da kallonta kan yasmeen data sunkuyar da kanta kasa sedai hankalinta yana gurin hadadden heel shoe din data gani a kafar rahma ne tana tunanin ta wacce hanyar zata mallakeshi
"Sai da ammi ta sake magana a karo na 2 tukunna ta dago a razane ta zube kasa tana kuka,a fusace rahma ta janyo wayar socket ta fara zubawa yasmeen tana ihu,jiyo ihun yasmeen yasa anna tasowa a tsorace har tana cin tuntube ta karasa babban apartment din first lady ta zube gaban ammi tana rokonsu da suyi hakuri,a zafafe ammi ta kalli anna tace wlhy banda mutuncinki da darajarki da tuni mun koreku daga cikin gidannan,kaf cikin masu aikin gidan nan wannan shegiyar yarinyar tafi kowa rawar kai da rashin mutunci don haka daga yau bana bukatar sake ganin yasmeen ta gyarawa rahma daki da kanki zaki dinga gyara mata,,,,da sauri anna ta gyada kai tana godiya sannan taja hannun yasmin suka wuce bangarensu na masu aiki
"Sai da yasmeen tayiwa kanta ruwan zafi sau 2 tukunna ta samu saukin ciwon da jikinta yake yi mata,saboda takaici anna ko maganar bata sake yiwa yasmeen ba,wayarta ta janyo daga karkashin pillow ta bude gallery ta fara kallon pictures din da tayi murmushi tayi tace ashe nima dai slay queen ce kalli yanda nayi kyau fiye da ita yar shugaban kasar ma,kusa da anna taje ta tsaya tace anna kalli hotunan da nayi dazu don Allah ki duba yanda nai kyau cikin rigar nan ga wata powder dana shafa har wani haske ta karamin kinga don Allah banyi kyau akan gadon nan ba....rankwashinta tayi akai cikin takaici tace wai ke yasmeen mahaukaciyar inace?ko minti talatin bakiyi da sakamu cikin masifa ba amma har kin manta ba abinda ya dameki ko toh ki gaggauta goge hotunan nan kafin ranki ya baci
"Cikin kwana 2 soyayya me karfi tsakanin shahid da rahma ya kullu tamkar sunyi shekara 10 tare,wanda ya zama yau ne ranar da shahid da rahma zasu fara fita a matsayinsu na masoya,ta dade jikin mirror tana makeup din da yayi matukar kyau sannan ta dauko dubai abaya peach colour tasa,hill shoe ta saka peach colour sannan ta yafa siririn mayafin abayar da akayi mishi ado da black stones ta feshe jikinta da perfumes sannan ta fita parking space din gidan,sakin baki tayi tana kallon hadaddiyar lamborghini din datai parking tana jiranta,cikin mamaki ta shiga motar zuciyarta na tayata tunanin ashe dama shahid me kudine?sun dade suna zagaye daga nan suka tsaya Evo mall sosai shahid yayiwa rahma siyayya harda hadadden diamond ring na proposal sannan ya tabbatar mata zeyi tafiyane nan da kwana 2 ze dawo ayi maganar aure don ba wasa ya kawoshiba,hugging dinsa tai kamar zata mayar dashi cikinta tana maimaita i love you so much shahid,murmushi yayi lokaci daya kuma ya hade ransa a hankali yace i love you too
"Yana ajiye rahma a gida ya kira number mubarak,hey kawai ya fada a takaice.....a takaice ya bawa mubarak labarin duk yanda sukayi da rahma sannan yace nan da 3 hours a nemo mishi likes and dislikes din zahra,,,,bayan 3 hours armaan ya karasa gidansu mubarak,kwance ya tarar dashi yana playing game,pillow ya dauka ya cilla mishi yace wake up mallam hope ka samo min abinda nake sonji,jikinsa sanyaye ya ajiye remote din hannunsa yace na samo maka amma fa wannan karon zahra ba kamar rahma take ba saboda zahra babu abinda yake birgeta kamar ace you are a musician,da sauri armaan ya zaro ido yace singer?daga kai mubarak yayi yace of course,,,,,idan har zahra zata ga mawaki toh lallai babu abinda zai hana ta fada sonsa kaga kuwa no way kayi wasa da hankalin zahra,,,,murmushi armaan yayi yace i can do it,zaro ido mubarak yai yace how?armaan taya zaka zama singer?taya dad dinka ze bari ka zama singer?karka manta you are the billionaire son kuma kai kanka young billionaire ne taya zaka tsaya gaban duniya kana waqa?ajiyar zuciya armaan yayi yace of course maganar da ka fada gaskiyane sedai ya zama dole in zama mawaki ko da na 1 week ne kuma zancen duniya zata ganni ka dena wannan tunanin saboda zan zama secret superstar zanyi amfani da mask babu wanda ze san fuskata,,,,a tare suka kwashe da dariya
"Da gudu ta shiga bedroom din ammi har tana cin karo da gado,murmushi ammi tayi tace cherie karki fadi fa,cikin rawar jiki tace ammi don't worry baxan fadi ba kalli nan,,,zoben hannunta ta ciro ta mikawa ammi,baki bude ammi take kallon zoben cikin mamaki ta kalli rahma tace cherie waya baki wannan diamond ring din?kinsan tsadarshi kuwa?tsalle tai taci gaba da bawa ammi labarin shahid tare da yi mata albishir nan da 2 days ze dawo ayi maganar aure
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro