Chapter 2
Flash back
Zavo restaurant and lounge shine gurin da ya zamowa manyan yanmatan wanda ake kira da slay queens gurin cin abinci musamman pani puri daya zamewa su rahma abinda sukafiso a wannan guri,banda zavo restaurant babu inda su rahma ke zuwa cin abinci musamman rahma data kasance ana tsaronta sosai kasancewarta yar mr president.....
"Yau ma kamar kullum zaune take a bakin gadonta ranta a matukar bace,wai meyasa ammi da dad sukeyi mata hakane?ace kamar yanda take haka bata isa taje ko nan da can ba sai tare da manyan bodyguards wanda ko kallonsu sam batason ta dinga,ammi ce ta turo kofa ta shigo fuskarta cike da kulawa ta dafa kafadar rahma tace am so sorry cherie,na fuskanci kullum nice nake bata miki mood dinki a cikin gidannan amma nima bason raina bane kinsan halin mahaifinki idan har ba da bodyguards ba bazai taba samun nutsuwaba,kina kallon hatta yayyenki maza da bodyguards ya amince su dinga fita ba don komaiba sai don kare lafiyarku da inganta muku tsaro a rayuwarku.......turo baki rahma tai tace stop it ammi,i said stop it nina gaji da irin rayuwar takurar da nakeyi a cikin gidannan don kawai mahaifina yana shugaban kasa?don kawai na zama yar shugaban kasa shikenan bazanyi rayuwar jindadi kamar kowaba?makaranta bodyguards,asibiti bodyguards,super market bodyguards what the hell is this ammi bani da wani lokaci wanda zanyi spending time tare da friends dina kamar yanda suma sukeyi?hannu tasa ta goge hawayen dake fuskarta tace ammi kinfi kowa sanin suwaye zahra da fadila a gurina kullum suna hanyar zuwa gidan nan don kawai su ganni suga lafiyata amma yau rana daya zan fita cin abinci tare dasu har sai an hadani da bodyguards?karki manta iyayensu suma suna cikin top 10 billionaires din kasar nan amma meyasa su ba,a takura musu haka?
"Murmushi ammi tai alamar gamsuwa tace toh ya isa yanzu na amince kije ku fita dasu fadila din amma fa ki tabbatar kin dawo kafin mr president yasan cewar baki fita da guard ko guda dayaba,murmushi rahma tai tayi tace thank you ammi ta bata peck a cheek sannan ta fita cikin zumudi,a parking space ta tarar dasu fadila har sun gaji da jiranta,jikinta sanyaye ta karasa gurinsu tace i,m sorry guys nasan nayi lefi amma ayi hakuri,tsaki fadila tai tace hey monkey wai ke meyasa kullum idan zamu fita dake sai kin jawo mana delay ki duba fa tun 2pm muke jiranki anan amma sai yanzu 4 kike karasowa
"Ajiyar zuciya rahma tayi tace bazaku ganeba babes,being a billionaire daughter is really amazing and fun but being a president daughter is boring at all.....a tare suka kalleta cike da mamaki suka ce what are you saying?kina nufin bakya jin dadin kasancewarki yar president?murmushi zahra tayi tace you better wake up from that stupid dream wlhy kullum addua nake Allah yasa na zama yar gidan shugaban kasa kamar ke rahma,tsaki rahma tai tace bazaku ganeba yanzu kuda kuke ya'yan billionaires ai kuna kallon yanda kuke spending kudin iyayenku ba tare da kowa yayi caring ba amma ni duk motsin da zanyi za,ace ga yar gidan barawon shugaban kasa blah blah blah.....in short being a president daughter sucks alot ki duba duk motsin mu yana kan idon dad saboda yana tsoron kar abokan gabarsa na siyasa su cutar damu,,,,,sun dade suna hira kafin suyi parking a babban farfajiyar restaurant din wanda sai yaran masu kudi kawai zaka gani a gurin,,,cikin isa yammatan suka fito daga hadaddiyar ferrari 2019 model black colour wanda akayi rubutu da manyan suna jikin number motan an rubuta RAHAMA BAGADAZA,murmushi tai ta kallesu tace cmon monkeys......a tare suka shiga reception din suka tsaya a canter,babban chef din restaurant din tayiwa murmushi bayan sun gaisa tace tana bukatar pani puri kamar yanda tai order dazu online,murmushi yai inda ya tabbatar mata yau basuyi abinciba a restaurant din saboda armaan malik ya siye duk abincin gurin anyi sadaka dashi kasancewar yau ne mahaifiyarsa ta cika shekara 3 da rasuwa kuma duk shekara yana siye abincin gurin ne ayi sadaka kyauta,,,,,a matukar zafafe ta kalli john cikin tsananin bacin rai tace armaan malik?who's that stupid person da har zai siye abincin gurin nan don kawai yana son yayi sadaka mahaifiyarsa ta mutu,har shi din waye da zeyi tunanin yin gangancin nuna isa a gurin da be isa yin komaiba,ajiyar zuciya tai tace john idan armaan malik yazo ka sanar dashi cewa rahma bagadaza yar gidan shugaban kasa ina tabbatar masa da cewa idan ma yayi hakane domin ya bata min rai toh ka tabbatar masa inada ikon da zansa a rufe wannan tsinannen shagon saboda mutanen kasar da shagon duk karkashin mulkin mahaifina suke,sannan ka fada masa wannan ya zama shine na farko kuma na karshe karya sake gangancin siye abincin gurinnan wai don kawai mahaifiyarsa ta mutu yanayi mata sadaka......ita mahaifiyar tashi wacece ita?
"Da sauri ya ajiye milkshake din dake hannunsa zai karasa gurinsu rahma,rike hannunsa mubarak yayi yace haba armaan ina zakaje kuma?kallon mubarak yai cikin mamaki yace mubarak kana nufin bakajin abinda wayancan yaran suke fada akan mahaifiyata?ajiyar zuciya mubarak yai yace ina jinsu armaan amma menene amfanin zuwa wajen nasu........cire sunglass din dake idonsa yayi yace mubarak kafi kowa sanin yanda nake kaunar mahaifiyata kafi kowa sanin yanda nake respecting iyayen wasu don kawai nima a girmama nawa iyayen amma meyasa waccan yarinyar zata zagi mahaifiyata a gabana?hakuri mubarak yaci gaba da bawa armaan suka bar gurin bayan ya sanar dashi zai taimakeshi akan duk abinda ya umarceshi....tunda armaan ya koma mansion dinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye sosai zuciyarsa keyi masa ciwo idan ya tuno abinda su rahma sukayi a zavo restaurant,wayarsa ya dauka ya kira babbar freind dinsa basma,bayan sun gaisane armaan yake tambayar basma menene abinda za,ayiwa mace yayi mata ciwo wanda har ta mutu bazata taba mantawa dashi ba,,,,,murmushi basma tayi tace babu abinda yafi komai ciwo a rayuwar mace irin namiji ya yaudareta zai aureta sai ranar bikin yace ya fasa,,,,,murmushi yayi yace yessssss sannan ya kashe wayar
"Direct message ya turawa mubarak yana tambayarsa duk wani information akan rahma,anan ne yake fada masa gobe shine ranar da rahma take zuwa check up asibiti,dariya armaan yayi yacewa mubarak yanaso kafin safiya ya samo masa number daya daga cikin manyan likitocin asibitin domin a gobene zai fara playing role dinsa matsayinsa na shahid.
Thank you for reading my story!!!
Don't forget to vote,share and comment
Heroine
Bạn đang đọc truyện trên: Truyen247.Pro